Showing 33001 words to 36000 words out of 91990 words

Chapter 12 - NOOR ALBI (Hasken Rayuwata) Writing By Mamuhgee.txt

08 Jan 2025

4237

kafin suka aje wayar tanajin nutsuwa da kwanciyar hankali akan maganar datai da Annen Dan kuwa magana da Anne na Bata nutsuwa shine abinda tasabu dashi a zamansu.


Wanka tayi kafin ta fito komai na dakinta da siyayyar da akayo Mata angama tsarasu ako Ina take dakin yazama na cikakkiyar budurwa
Tana fitowa Cindy data Gama aikin tana ficewa tabar siddika datake qarasa kunna Mata humidifier itama tana gamawa ta fice.


Zama tayi gaban mirror tana kallon fuskarta akaro na farko data zauna tana qurewa kanta kallo tareda Shiga tunanin wannan wace irin rayuwace tasamu kanta aciki kuma wadda take ga Kamar Jin dadin yayiwa marainiyar kamarta yawa.


Mai tashafa da body mist ta miqe ta duba closet dinta da aka gama gyarawa shaqe da Kaya saidai abin sanyin jikin shine yawanci ba kayan mutunci bane Dan mafi yawansu wanduna ne da skirt na Yan gayu da batasan yazatai sabo da sakawa
Dogayen rigunan ciki qalilan ne Suma duk ba masu mayafai bane saidai idan ka saka ka daura qaramin scarf akai.


Batada zabi Bayan saka wando da Riga Takoma bakin gado ta zauna tana daukar sabuwar wayarta da har cikin ranta tayi farin cikin samun wayar sbd waya dasu anty Sa'adah duk da tanajin tanason kira taji abbanta Amma tasan Momy bazata taba iya magana da itaba Dan Haka ta hakura da hakan tunda anty Sa'adah na waya da ita tanajin komai tana fada Mata hakanma yayi zataci gaba da Masa addua ta jira hukuncin ubangiji akan ranar haduwarta da Mahaifinta.


Da daddare ba dalilin rashin fitowarta cin abinci Dan Haka Dole ta fito sanye cikin Riga da wando masu Fadi kalar Ash kanta daure cikin qaramin scarf saidai gashinta ya fito kadan
Tana shigowa dining room din taga ba kowa aciki tasaki boyayyar Ajiyar zuciya tana Shirin juyawa saiga Turakin ya doso dining room din sanye cikin Ash Armani's da slippers baqaqe da Suka bayyanarda Hasken qafafuwansa
Kyakkyawar fuskarsa a sake saidai bakuma Wai Yana murmushi bane ko dariya
Tana ganin hakan ta dawo tana matsawa daga hanya Yana kawowa ya dago fararen idanuwansa yayi Mata kallo daya ya dauke Yana amsa siririyar gaisuwarta datai Masa itama bayan ta sauke idanuwanta daga kallonsa.


Ms Na'ima Dake gefensa ta miqa Mata hannu ta Kama suka qarasa dining din tana cewa"


You look fresh my girl.


Sunkuyar da Kai kawai Laylan tayi suna zaunawa.


Bayan sun Gama cin abincin Kai tsaye kallon Laylah yayi bayan ya miqe yace ta samesa Palo idan tagama.


Kasa hadiye ruwan dake bakinta Tai sbd wata irin fargaba data sameta ta dago ahankali ta kalli Ms Na'ima Dake Mata murmushi tace"


Take it easy Girl ba komai bane zaiji abubuwan dakike buqata ne da Kuma raayinki Akan abinda kikeson karanta.


Kallon Ms Na'ima din tayi tareda bude Baki cikin sanyi da nutsuwa tace"


Me zance?


Wata dariyar Jin Dadi Ms Na'ima tayi ta Jin dadin Laylah tafara zama tafin hannunta akan sai abinda tace.


Ta Kama hannunta suka miqe zuwa gurin Turakin tana cewa"


Daddynki ne kibar Masa zabi da kansa ya zaba miki kawai dai ki dage kiyi karatu sbd akwai yiyuwar rayuwa Mai kyau agaba idan kikai karatu zamuji Dadi Sosai agaba.


Gyada Kai kawai tayi batareda tana fahimtar komai da Ms Na'ima din ke fada ba Dan duk Bata nutsuwarta.




Zaune yake gabaki daya yagama sauya iskar palon da qamshin jikinsa Wanda Babu Wanda zaiyi haduwa biyu zuwa uku dashi batareda ya Gama sanin wannan qamshin nasane na musamman.


Saida suka kawo tsakiyar palon kafin ya dago daga wayar daya keyi ya zuba musu idanuwansa take Laylah ta Dan rage takunta ta danyi bayan Ms Na'ima itama kanta Ms Na'ima din idanuwan Turaki kasheta sukeyi Dan Haka ita qafafuwanta sauri suka qara Kamar ansaka musu batir ta qaraso gefensa ta zauna tanajin a duniya batajin akwai ranar dazata iya barin Turakin ya iya kallon wata macen da sunan so ko makamancin hakanba Dan kila Aron hauka zatai ta halaka koma wace da danginta gabaki daya.


Dauke kallonsa yayi daga kan Laylan wadda duk tabi ta rikice Tama Rasa gurin zama saitayo gurin Ms Na'ima din tana kokarin zama a qasa.


Muryarsa dake sake rudar da ita sbd kamewa da Rabin Wasa ko kadan acikinta ya furta"


Gobe za'a fara fita Dake zuwa harkar makaranta Dan Haka ki ringa kula Nan ba Nigeria bane karkiyi qawayen banza ok??


Bata Gama gane meyace ba kawai dai ta gyada kanta cikin biyayya tareda furta "nagoge" ahankali.


Daga Haka Ms Na'ima ce ta ringa tsarowa Laylan zance da nasiha akan ta dage tayi karatu.
Ita dai Kai kawai take gyadawa Bata iya bude Baki.


Sai kusan goman dare tadawo bedroom dinta ta sauke numfashi tareda Ajiyar zuciya tana zare kayan jikinta ta nufi toilet tayo alwala ta fito ta Sanya kayan bacci Kamar yanda Ms Na'ima ta Gama Bata tsari da yanda zata ringa gudanar da komai.


Face cleanser ta Gama goge fuskarta kafin ta kwanta Wanda shikuma a spa din dasukaje aka karbo Mata shi akace ta ringa shafawa kullum kafin kwanciya shima duk aikin Ms Na'ima ne.


Washe gari qarfe goma A Abdoul yazo ya dauketa a motar Turakin yakaita Emory inda dama tun zuwanta washe gari aka fara process na shigar da ita Dan Haka Koda A Abdoul yakaita har process da payment nata na extra classes anyi komai tareda da daukar Mata wata Sofia Yar asalin nijar da zata ringa koyar da ita wasu abubuwan da Hausa kafin tagama iya turancin da wasu abubuwan.


Dan Haka washe gari tun safe tafara zuwa makaranta
Da farko hankalinta ya tashi sbd kasa Shiga cikin mutane tayi Saida Sofia ta ringa Bata qwarin gwiwa tana nuna Mata zata iya kafin ta Dan daure ta iya Shiga mutane Amma Kam Koda suka tashi akazo daukarta tagama ficewa hayyacinta sbd rashin sabo.


Ko data jera kwanaki tana zuwa makarantar Saida Dole Anne ta hadata da Dr Meenah suka koma communicating ta waya sbd ta ringa magana da Laylan Kota fara sakewa cikin sauran dalibai.


Ahankali ahankali tafara sakewa da makarantar sbd Sofia Dake tayata komai tun daga kan muamala da mutane har karatun da magana da kalolin abincinsu da yanayin muamalantar komai.


Taci wuya matuqa kafin tasake ta Saba da komai shikam karatu duk da tsakanin dagewar datakeyi da maida hankali sbd kullum shine burin Anty Sa'adah dinta akan ta maida hankali hakama Anne Da uwa uba Ms Na'ima da itama take sake cusa Mata cewan Turaki nason tayo kokari ta samu ilimi sosai sai hakan ya shigeta take maida himma duk da sai ahankali da bazai yiyu ace tasamu budewar Kai lokaci daya ba saidai ba laifi turancinta na samun cigaba sosai tunda Babu inda a qasar zakai rayuwa bada yaren turancin ba shiyasa shikam tuni ya Dan fara shigarta sama sama Dan ko Sofia Bata cika Mata Hausa ba da turancin take Mata magana hakama a gida datai Sabo da Cindy Sosai Dole Haka suke turancin Dan Haka kawai tafi Jin nutsuwa da Cindy akan siddika duk da siddikar ma tana jinta ba laifi sbd da ita kawai take zaunawa tayi hausarta yanda tasaba sai kuwa idan tana waya dasu Anne Dan anty Sa'adah ma ba laifi yanzu tuzama Yar gayun Abuja maganarta daya biyu turancine na ukun.


Sun samu hutun farko results dinta ba laifi tunda dai Bata Fadi duka ba Dan Haka a Dan hutun saita dage itada Sofia suna Dan tanason tayi karatun yanzu da gaske.
Ta bangaren zamanta da Ms Na'ima wadda da qarfi da yaji Ms Na'ima tasata tazama 'yarta Dan Haka Dole mum Na'ima take kiranta Kamar yanda Ms Na'ima din tace ta ringa kiranta,
Batada matsalar komai a gidan saima gata datake samu sosai Dan kuwa kudi sosai mum Na'ima din ke karba hannun Turaki na kullum qaryar siyayyar Laylan na kayan shafa ko kwalliyar kokuma shoes da handbags Dan Haka ba laifi duk ta karba takan yiwa Laylahn siyayya acikin kudin ta riqe sauran.
Sofia ma tanajin dadin qawancen da Laylah sbd sosai take samun designers Kaya a hannun Laylah Dan Laylahn nada kyauta tunda yanzu Allah yakawo sauyi rayuwarta.


Ta bangaren Turakin ne iyakacinta dashi dining room idan za'a ci abinci sai Kuma a kaidarsa duk bayan kwana biyu yakan zauna cikinsu Bayan cin abinci yayi fira da Ms Na'ima Wanda itadai daga yagama tambayarta karatu take sulalewa tabarsu Dan ba laifi ta rage tsoronsa da fargabar haduwa dashi Dan yanzu tagama daukarsa matsayi daya da abbanta tunda Anne tayi Mata bayanin irin kusanci da qaunar Dake tsakaninsu tareda kusancinsa da mahaifiyarta sai wani irin girmansa qaunasa irin ta shiqiqinka Mai girma tashigeta tana Masa kallon uba,Mariqi Kuma mijin yayarta 'yar uwarta datakewa kallon uwa ta wani bangaren.
*_Bismillahi fa yanzu zamu Shiga labarin._*
##MAMUH#




Follow me at Arewabook @mamuhgee Dan samun complete books Dina dama sauran pages na Noor Albi Dake fara sauka acan.


👇👇
Eznah
Tarayya
Deen Marshal
Ubayd maleek
Min qalb
Buri daya
Kaunarmu
Noor Albi
Dacewa
Dawood
Zucuyarmu daya
Auren raba gardama
Taurus biyu
*_Mamuhgee 20_*




Sungama session dan haka hutun dasukai Mai Dan kwanaki ne taso zuwa Nigeria Amma Mss Na'imah tace sai Ankara Gama wani session dinn
Anne ma ce Mata tayi ta zauna har gaban Dan Haka Dole ta hakura Amma taso tsananin ganin Anty Sa'adah wadda yanzu iyakacinsu vidcall Wanda kusan kullum awuni sai sunyisa yafi so biyu sbd yanzu Kam saidai raunin wani ilimin Kuma Amma wayewa da zama babbar yarinya Laylah tajima dakaiwa saidai nutsuwarta da sanyinta na Nan sai suka qarawa yanayin nata burgewa sbd sai yanayi kamar ajine da yayi Mata yawa,
Ta bangaren addini ma na laifi suna attending Islamic class a wata private school duk weekends itada Sofia Wanda ma sai daga baya da kansu suka gano gurin taiwa mum Na'ima mgnar aka sanyasu suka fara zuwa dakansu Dan ba laifi yanzu tana Jan mota sosai Dan musamman Turaki ya siya Mata motarta fara Sol kirar infinity QX50 wadda taqarasa sauya rayuwarta gabaki daya
Ga qananun kayan tuni tayi sabo da sanyasu tunda babu wasu kayan idan basuba,
Hakama ta bangaren 'yan matanci Sofia ta Bata sosai dason kwalliya saidai dayake Bata Saba ba sai son jambaki kawai yashigeta Dan Haka duk wasu kamfanin lipsticks masu tsada ba kalar da batada Dan koyaushe kwalliyarta Bata wuce lipstick da mascara sai eyeliner duk da Bata cika sanyataba Dan idanuwanta sunfi Mata kyau ahakan gashi tayi haske sosai idan ta Sanya liner cikin idon sai tayi Kamar zata gurin wata biki ko taro shiyasa Bata cika sakawarba saidai lipstick da idan ya zauna bakinta yake qara Mata kyau da burgewa sosai.


Daga dakinta ta fito tana waya da Anne dake sanar da ita zuwansu Inshallah itada Sa'adah idan Sa'adah tasamu Gama exams din datake
Cikin tsananin farin ciki take tana cewa zata bisu idan sunzo tayi hutu itama,
ta nufi kicin tana cigaba da wayar tana Shiga Cindy dake hadawa Turaki black ginger tea ta dago ta kalla Laylan tana Mata nuni data jira tagama saisu hadawa mum dinta abinda tace Dan tafiya zatai.


Jin mum Na'ima tafiya zatai yasata kallon Cindy bayan tagama wayar tace"


Yaushe mum din zatai tafiya?
Banji tafada ba.


Siddika ce data Gama wanke qaton kifin dazasu gasa ta kalli Laylah tana cewa"


Yau zatai tafiyan Amma kaman kwana biyu ne zatai
Kuma nasan zata sanar Miki.


Gyada Kai Tai tana cewa"


Ok bani snacks dina Bari idan sunyi ku kashemun Zan wuce Sofia na jirana karatu zamu wuni Yi yau a gidansu.


Siddika hannuwanta ta kalla tace"


Hannuwana da kifi Zan Bata muku idan na taba.


Cindy ma Dake juye tea din data Gama dafawa cikin kulawa tace"


Tea din sir AB ne bari nakai Masa Yana jira saina dawo na hada Miki.


Kallon farin gold tray din dak hannun Cindyn tayi tareda miqa dogayen hannayenta da agogon Emporio Armani glitz ke daure akai ta karba tana cewa"


Kawo nakai saiki hada abubuwan.


Karba tayi ta juya ta fice daga kicin din Kai tsaye ta nufi hanyar palonsa na qasa dayake zama da baqi wani lokacin.
Tana Isa Tai knocking ahankali tareda tura kofar tashigo Jin A Abdul yace tashigo Dan yasan Cindy ce dayace ta kawowa Turakin tea.


Qamshin turarenta na splendid wood(Yves saint Laurent) yafara shiga hancinsa yaci gaba da abinda yakeyi batareda ya dago yaduba Wanda ya shigo din ban Dan yasan itace tunda yasan qamshin turaren Na'ima ba wannan bane hakama qamshin bana Cindy bane datake maid.


A Abdoul ya dago yana ganinta kallo daya yayi Mata ya dauke kansa daga kallonta Yana maida kallonsa kan Turaki Dake duba iPad sbd Ganin kayan Dake jikinta.


Qarasowa tayi ahankali ta gaidasa tareda gaida A Abdul din shima tana kokarin ajiye tray din Turaki ya dago idanuwansa suka sauka Kan dogon pencil jeans din Dake jikinta Wanda ya fitarda tsayi iya kaurin cinyoyinta harma da fadin hips dinta Dan rigar jikinta _Satin wrapped blouse_ ce batada wani tsayi kanta daure da scarf fari Hasken fuskarta dake glowing yafara maida kallonsa akai kafin ya maida idanuwansa Kan siraran cinyoyinta yanason mamakin fitar tata ahaka Amma dai baice komaiba ya amsa gaisuwarta tareda maida kallonsa kan A Abdul daya dauke Kai yaqi waiwayowa Yana duba wayarsa.


Juyawa Tai ta fice
Yakuma Dan dagowa ya kalla kofar data fita kafin ya dawo da kallonsa kan abinda yake Yana daukan tea din yafara Sha suka cigaba da abinda sukeyi.


Tana fitowa Kai tsaye dakinta taje ta dauko handbag dinta da keys na motarta ta fito ta nufi tana kokarin Sanya half-zip jacket akan kayanta ta nufi dakin mum Na'ima
Anan take sanar da ita tafiyar gaggawace ta kamata zuwa Athens kwana biyu zatai tadawo.


Daka tawa da fitarta tayi Saida mum din tagama suka fito tare Dan takaita airport,
Koda suka fito itace agaba saddika na bayanta da luggage din mum Na'ima sai Cindy dake gefenta dauke da nata snacks din suka saka a mota suka juya ciki daidai fitowar Turaki Wanda ke gaba Ms Na'ima na gefensa idanuwansa suka sauka akanta lokacinda take tsaye jikin motar hankalinta nakan wayar Dake hannunta..
Lipstick dinta daya zauna dakyau akan lips dinta ya kalla kafin ya dauke Kai Yana sake kallon shigar tata
Ya wuce ya shige motarsa da A Abdul ke jiransa suka fice daga harabar gidan.
Suna fita Suma su Laylah suka fice ta biya ta dauka Sofia suka kaita airport sbd hanyar airport din Bata Gama ganewa dukda Google map take amfani da dama zuwa gurare.


Bayan tafiyar mum Na'ima duk sai taji kadaici ya kamata Dan Haka sai kusan yamma tadawo gida daga gidansu Sofia
Tana dawowa wankan kawai tayi bayan tayi sallah ta saka doguwar free chiffon shift gown tasaka tareda hula ta fito tana qamshin mist na Creed ta nufi palo ya zauna tana Yan latse latsen wayarta har lokacin sallah yayi Takoma daki tayi sallah
Lokacin cin abincin dare nayi tafito Kai tsaye ta nufa dining room bakowa Dan dama tunda sukazo qasar masu aiki suka daina shigowa dining room lokacin cin abincinsu
Ms Na'ima ce ke serving dinsa.


Zama take kokarin Yi saiga isowar qamshin _bois elite_ Dan Haka tasan shine zai shigo saita fasa zama ta dakata tareda waiwayowa kadan Jin shiru
Tana kalla kofar Yana sanyo Kai sanye cikin Armani's da slippers gashin fuskarsa akwance sosai farar fuskarsa sai cika ido takeyi
Bata ankaraba sai Jin idanuwansa tayi cikin nata ya dago ya zuba Mata nasa dasuka shanye nata girma da haske,
Faduwa gabanta yayi da sauri ta sauke Kai tana cewa"


Barka da saukowa Abbah.


Amsa Mata tayi Yana qarasawa gurin zamansa ya zauna.
Juyowa tayi ta nufosa zuciyarta na bugawa da idanuwansa dasuka shiga nata saitakejin kamarma tsoro ya kamata da rudu Dan Haka jiki amace ta qaraso batareda takuma dagowa ta kallesa ba Dan yaune Karo na farko da idanuwanta suka taba shiga Suka hadu da wani
Duk da tamkar uba yake gareta Kuma mijin Yar uwarta saitaji fargaban hakan yashigeta.


Gasashen kifine akai da akai garnishing dinsa dasu lemon
Sai fruits da farar pasta.


Matsowa Tai tazo gefensa ta tsaya ahankali,


Qamshintane ne yayi wa hancinsa shigar qarfi daidai lokacinda ta tsaya gefensa zuba Masa Masa abincin.


Agogon diamond Rolex Dake hannunsa ya kalla Yana dan maida bayansa jikin kujerar dining din ya jingina sbd dauke hancinsa daga gurin Dan akaron farko da yaji qamshin mace ya damesa ga lokacin Shan maganinsa ya kusa sbd maganin dayakesha yanzu yafara basa reaction shiyasa ya rage tafiye tafiyensa ayanzu Yana buqatan tsayawa kusada gida.


Pasta din tazuba Masa tareda kifin a gefe da boiled cabbage da aka dafa da kishiri kawai.


Komawa tayi ta zauna a darare bayan ta zuba kifin kawai kadan a plate tana zaunawa tafaraci Dan tayi tagama tabar gurin.


A natse yake cin abincinsa babu Mai magana acikinsu sai ita Dake Dan sauri tayi tabar gurin Dan atakure take yau gashi ba mum Na'ima agurin.


Ba zato sbd hankalinta da baya a natse taji qatuwar qayar kifi a maqoshinta da sauri ta aje fork din hannunta tana daukan ruwa da sauri Tasha Amma takasa hadiyewa sbd azaba da girman qayar..


Tari ta fara ba shiri tana riqe maqoshinta cikin tashin hankali da firgicewa
Dago fararen idanuwansa yayi ya kalleta saiyaga yanda idanuwanta sukai ja take tana riqe maqoshinta cikin tsananin firgici da azaba tana neman miqewa a rude.


Aje spoon dinsa yayi Yana kallonta da dukkanin hankalinsa yace"


Is everything ok with you??


Kasa magana Tai tuni idanuwanta suka fara gangaro hawaye cikin azaba da tsoro tace"


Wuyana,
Qaya..


Ganin yanda take sake rikicewa jikinta na rawa yasashi miqewa Yana nufota da cup din ruwa a hannunsa ya miqa Mata Yana cewa"


Karba Kisha..


A rude ta karba cup din Tasha ruwan Amma tana hadiyewa tarin azaba yabiyo baya take tafara fita hayyacinta Dan kuwa cikin tarin jini taga Yana Dan biyowa wasu irin hawayen firgicine suka balle Mata tahau rawar jiki tana kuka...


Ganin hakan sai hankalinsa shima ya Dan tashi ba zato Kai tsaye ya Kama hannunta yajata zuwa hanyar bedroom dinta Kai tsaye zuwa lokacin tafara kuka sosai Mara sauti jikinta Babu inda baya rawa har tsakiyar kanta takejin zabazar Dan Haka batareda ta saniba ta sake qanqame hannunsa Dake riqe da nata,


Toilet dinta Kai tsaye ya nufa da ita ya duqar da ita gaban wash basin Yana buga bayanta ahankali yace tayi kokari tayi amai.


Kasawa Tai duk yanda taso yin Aman saima sake tokale maqoshinta da qayar keyi jini nasake Dan digowa dan Haka saita qarasa rikicewa gabaki daya.


Ganin hakan saiya Kuma janyo hannunta ya nufi cikin jacuzzi da ita ya sakar Mata shower akanta
Take tasake rikicewa Dan bata wanka a qarqashin shower a tub take wanka sbd tanada tsoron ruwa,,,, qanqame hannunsa Dake riqe da nata Tai tana fizgar Numfashi da qarfi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login