Showing 66001 words to 69000 words out of 91990 words

Chapter 23 - NOOR ALBI (Hasken Rayuwata) Writing By Mamuhgee.txt

08 Jan 2025

4255

Gama Bata dakin Suka Bata lokaci Mai tsayi kafin suka bar dining room din zuwa bedroom dinta inda suka qarasa shiriricewa kafin yaje yayi wanka ya fice aiki guraren 1pm bayan A Abdoul tuni ya Isa office yafara ji da baqinsu na jiyan da Basu Gama dasuba.


Bayan fitarsa wanka tayi ta Sanya guntuwar doguwar Riga sofia tazo suka shiririce da fira wuni guda sai yamma sosai Suka fito ta sauya kayanta Dan Kai sofian gida da kanta.


Bayan fitarta yadawo Dan Haka shi kadai yaci abincin dare ya fito yakoma yayi wanka ya Sanya pyjamas black ya zauna Yana amsa wayoyi cikin nutsuwa da rashin hayaniya.


Sai karfe tara saura tadawo daukeda shopping bag sbd sun biya itada sofia sunyi shopping a _Lenox square_ turarukanta taqaro da undies da Bata gajiya da yawansu harma da singlets dinta da yawanci Abba ya tadasu aiki.


Direct dakinta ta wuce tafara aje kayan takira Cindy tace ta jera Mata su closet ta tube ta shige toilet.


Wanka tayo da brush ta fito har lokacin Cindy na aikin jera kayanta
Dan kayan Doguwar rigar bacci Mai tsantsi ta saka har qasa tareda daura qaramin silky scarf akanta ta dauki turaren _Nirvana Black_ ta fesa a jikinta ta kalli Cindy dake aiki tace"


Abinci Yana dining ko kitchen?


Yana kitchen sbd Sir AB na gamawa na tattara gurin amma siddika ta dafa Miki fish soup din dakikace Yana kitchen.


Nufar kofar fita tayi tana cewa"


Sai gobe zansha soup din yanzu zansha low fat yoghurt na kwanta ba Sosai nakejin yunwan ba.


Kai tsaye kitchen ta nufa ta bude fridge ta dauko qatuwar roban yoghurt din ta bude ta zuba a cup ta maida tareda juyowa zata dauka cup din ta fito taga mutum tsaye bayanta Yana kallonta hannuwansa nade a kirjinsa.


Ajiyan zuciya ta sauke sbd ta firgita bataji shigiwansa ba.


Kallon kitchen din yakeyi koina sbd baisan yaushe ranar daya taba shigowa kitchen din ba tsawon shekaru sai yau Dan Haka ya yabawa su Cindy da komai na kitchen din yake fes Kamar ba'a aikin komai cikinsa.


Cup din takai bakinta ta kurba yoghurt din tana cewa"


Kana buqatan wani Abu ne?


Matsota yayi sosai har Suka jingina da qaton table din Dake kitchen din Yana kallonta da rigar jikinta Mai santsi data Gama lafewa jikinta Kuma batada bra ya lashi yoghurt din bakinta da Bata qarasa hadewaba yace"


Meyasa Kika Dade a waje?


Kallonsa tayi tareda Dan maraice fuska zatai magana yace"


Daga yau Bayan school ko Ina karki sake zuwa bada izininaba,harda gidansu sofia.


Kallonsa tayi tareda gyada Kai tana kokarin aje cup din hannunta ya riqe hannun yakai cup din bakinta ya ringa Bata abakin harta shanye duka ya aje cup din tareda Kai fuskarsa wuyanta ya shaqi qamshin sabon turarenta Mai masifar qamshin dayayi Masa ya kalleta da murmushi gefen bakinsa yana qara zura kansa cikin wuyanta yace"


Hmmm I love it...


Hakan daya fada yasata sake tura kansa wuyanta ya shaqo qamshin da kyau ya lumshe fararen idanuwansa tareda Kama qaramin qugunta ya cira sama ya zaunar Kan table din Yana kallon rigar jikinta datasan tagama tashi aiki daga yanzu...
Aikuwa balle hannun rigar yayi ta zame ta sauka ta tsaya gurin cikinta..
Ta zura hannu ta zagayo bayansa take ya kwashe rigar tata fararen cinyoyinta suka bayyana suna cikin abinda yake qara rabasa da hakurinsa akanta ya zare scarf din data daure kanta ya saki qasa sukai baya Yana kissing bakinta dakeda sauran zaqi da sanyin yoghurt take cup din data gama Sha dashi ya Fado qasa ya fashe da qarfi..


Ms Na'ima da shigowar kenan babban palon daga dawowarta
Tayita Kiran A Abdoul Bata samuba hakama Turakin tayita Kira Baya dauka Dan Haka ta tawo taxi tadawo gida sbd tafiyar tata tayi dare sosai.


Qarar dataji ta fashewar Abu a kitchen ya sanyata daka tawa daga ita har Cindy data bude Bata kofa Suka waiwaya suka kalli hanyar kitchen din da mamaki Ms Na'ima ta kalli Cindy zatai magana suka Kuma Jin qarar faduwar wani abun da sauri Ms Na'ima ta nufa hanyar tana cewa"


Siddika ce a kitchen din take fasa Kaya sbd batasan zafin kudin siyansu ba ko? Banason asara kun sani dukkaninku Dan Haka bazan dauka ba.......
##MAMUH#


NOOR ALBI Na kudi ne pay at +234 903 234 5899
Or arewabooks for more pages.
*_Mamuhgee 38_*
Nufar kitchen din tayi ranta a bace Dan dama da takaicin A Abdoul da Turakin da basu daga wayartaba tadawo hakama Laylah tayita kiranta bata samu itama Dan Haka duk Rai bace tadawo gidan Dan Haka take neman saukewa zafafe Kan Siddika tunda ga Cindy agabanta tabbas siddika ce a kitchen din sbd su biyu ne kawai masu aikin gidan.


Kokarin Isa kofar take tana daf da shigewa siddika dake dakinsu gefen kitchen din ta fito tana kallom Ms Na'iman da batasan da itaba,
Ta juya tayiwa Cindy kallon mamakin yanda sukai cirko cirkon ganinta
Ta maida kallonta ga Ms Na'ima da dan farin cikinta na dawowarta ta karba handbag dinta tana cewa"


Sannu da dawowa Lady Na'ima (sunan dasuke kiranta dashi kenan duka masu aikin gidan harma da securities)......


Kalmar lady Na'ima da siddikar ta furta shine ya Shiga kunnen Laylah dake baje ajikinsa Kan table din rigarta a zame,
Ta janye bakinta daga cikin nasa da sauri tana Jan rigarta ta rufe kirjinta ta kallesa Yana Mata wani irin kallon karma tafara abinda take Shirin Yi din wato janyewa ta gudu.


Marairaice Masa fuska tayi cikin tsananin tsoro da shakka take kallonsa lokacinda tagama maida rigarta Allah yasota yau ba barka kayan yayiba hannun kawai ya fincike Dan Haka da hanzari tadaure rigar tareda saukowa Kan table din ta Kama hannunsa da sauri ta jasa bayan kofar kitchen din idonta na neman cikowa da hawaye tace"


Dan Allah Abba karka fito ka tsaya anan..


What??" Ya furta Yana kallonta da alamar she's not serious tace ya boye a bayan kofa acikin gidansa.


Kokarin fitowa yakeyi ta saki hawayenta Suka gangaro tace"


Abba idan kafito mum ta ganka ahaka zanyi dagawa Anne hankali ta maidani Nigeria.....


Kallonta yayi mamakinsa na qaruwa yace"


Like seriously¿


Gyada Kai tayi tana qarawa da cewa"


Yes.


Ms Na'ima kuwa da mamakinta a fili ta kalli siddika kafin ta kalli Cindy data Gama jiqewa da zufan tashin hankalin da firgici tace"


Idan siddika na Nan a tsaye waye a kitchen din da aketa barin Kaya suna fashewa?


Wani mugun yawu Cindy ta hadiye a sirrance tareda tattaro nutsuwa da fuskewa tace"


Ms Laylah ce a kitchen din tana dumama madaranta ne,
May b she drop something by mistake.


Qarasawa kitchen din Ms Na'ima tayi tana cewa"


Kaya har da yawa hakan
Kodai ba lafiyanta ba.


Tana saka Kai cikin kitchen din Laylah tayi saurin fitowa bayan kofar ta tareta bakin kofar tana kokarin boye firgicinta tace"


Laahh mum yaushe Kika dawo?
Sannu da zuwa....munyi kewanki sosai....


Kallon kitchen din mum tayi batareda ta qarasoba tana kallon kayan dake zube a qasa tace"


Lafiya dai ko?
Garin Yaya duka Haka barin Kaya?
Ki kula da zubarda Kaya Haka kada kwalba ya Miki rauni wata ran.


Jan hannun mum din tayi Suka fito kitchen din tana cewa"


Zan kula Inshallah,
Yanzu dinma shagala nayi ban ankaraba.


Dakin mum din Suka dunguma su dukan suna gaf da shigewa yafito kitchen din kansa tsaye fuska a kame
Itace tafara ganinsa Dan Haka da hanzari cikin salo ta qarasa Jan mum din daki tana cewa"


You must be very tired mum,kifara wanka da sallah Bari na hado Miki tea Mai zafi Kisha ki kwanta ki huta.


Juyawa tayi Cindy tabiyo bayanta suka baro siddika na kokarin gyara dakin kafin mum din ta fito wanka duk da fes yake sbd tsarin gyaran da ake Masa kullum Koda batanan.


Kitchen ta nufa ta hadawa mum din tea Mai zafi da kauri tareda bread da butter takaiwa mum din dakin wadda harta fito wanka ta saka Kaya tana kokarin kwantawa batareda tayi sallarba.


Karban tea din tayi ta shanye tareda hayewa gado cikin wata masifaffiyar gajiya da ciwon jiki.


Daukan kayan Laylah tayi ta fice tareda kashe Mata wuta bayan Tai Mata Saida safe.


Siddika tabawa kayan da tea din tace ta maida kitchen ita Kuma ta nufi dakinta tana sake gyara zaman rigarta da taketa riqewa Kar mum din tagane a balle take.


Tana shiga ta rufe kofa tareda sai alokacin ta sauke ajiyar zuciya Mai qarfi tana dawowa hayyacinta Dan kuwa tashiga firgici da tashin hankali har sai tajima Kamar mararta ta qulle takai hannu akan mararta datai tauri tareda lumshe ido tanajin tsananin kaunar cikinta da ba lallai yakai labariba idan mum tasan dashi Dan kuwa dukan mutuwar da zatai Mata kadai zai iya hallakata da cikin...


Ba tsammani taji hannunsa Kan nata hannun Yana zagaya hannunsa qugunta ya rungumeta gabaki daya hakan.


Wata Ajiyar zuciyan takuma saukewa tareda sake lumshe ido tana kwantar da kanta jikinsa ta bude Baki tace"


Thank you Abba.


Ajiyan zuciya ya sauke ahankali shima tareda bude Baki qasa qasa yace"


This should be the last dazaki sake threatening Dina akan Zaki tafi kisani tsayawa irinsu bayan kofa...


Murmushi Mai sauti ta sake tareda zamewa daga jikinsa ta kallesa tana cewa"


Yaushe kashigo Nan Wai?


Bakin gadonta ya Isa ya zauna tareda janyota ta zauna Kan cinyarsa Yana kallon idonta yace"


Lokacinda kikaje Kai mum dinki daki.


Dogon hancinsa ta taba tareda Dan shafawa tace"


Ta kwanta zaka iya tafiya yanzu ai.


Dauketa yayi daga jikinsa tareda kwantar da ita gefensa ya kwanta shima ajikinta tareda lumshe idanuwa Yana cewa"


Kiyi bacci kema.


Daga kwancen suke abubuwansu har bacci ya dauketa ajikinsa hannuwanta na cikin rigarsa shikuma nasa na cikin gashinta dayake yamutsawa baccin ya daukesa shima.


Asubar fari suna Gama sallah ta takura Masa da marairaicewa da komai har sai data hada da hawayen qarya data lura bayaso ko kadan kafin ya fice daga dakin yakoma samansa ya kwanta baccin safe yayi gaba dashi.


Tana sane taqi fitowa breakfast Dan Haka daga mum sai shi sukai breakfast din cikin sabuwar soyayyar da mum din ta qaro Masa.


Qarfe goma ya fice aiki Dan Haka bata fitoba sai after 10 din sosai sanyeda Riga da jeans da hular sanyi ta nufi kitchen acan gurinsu Cindy tayi breakfast dinta suna Mata fira musamman Cindy dakeson tambayarta harda yanzu da mum Na'ima tadawo za'a cigaba da dafawa Sir Turakin Green tea dinda ake dafa masan gurin cin meal na safe da dare Amma ganin siddika agun yasa take shakkar tambayar.


Bata saka musu hannu a aikintaba saidai anan ta tsaya suna aiki tana zaune Kan kitchen island tana fira dasu tana latsa wayarta.


Karfe biyar na yamma mum ta jata suka fita zuwa gurin gyaran Kai dasu qafa spa dai sukaje sbd wuni baccin hutawa mum din tayi shiyasa Suka fita da yamman zuwa gyare gyare yau gurin mijinta zata kwana Dan hakane Suka fiton da yamman.


Akaro na farko Laylan taji fitarta batai Mata Dadi ba sbd Yafada Mata karta Kuma fita idan ba school ba batareda ta sanar Masa gashi ba Daman fadawa mum hakama ba Daman qin zuwan shiyasa Bata ce komaiba Suka fiton.


Harda ita akai gyaran shine qarin dadewarsu Basu dawo gidanba sai after 8,
Lokacin Bayan bacci sosai tanajin Yar gajiya
Yunwace dai bata wani hi sbd fruits dinda taci sosai acan.


Zaune yake a palon qasan sanyeda jallabiya milk color,
qafarsa daya na Kan daya shiyasa kake iya ganin coffee brown slippers na Ferregamo Dake qafarsa,
Hannunsa riqeda iPad Yana dubawa Yana sauraron A Abdoul Dake zaune Kan 1 seater Yana Masa bayani a natse.


Shigowa sukai palon tana Jin qamshinsa tasan Yana palon dan Haka ta Dan rage tafiyarta ta dawo bayan mum Dan da itace a gaban.


Suna shigowa Ms Na'ima tayi Masa wani kallo tana neman kashe Masa ido daya Amma kallo daya yayi musu ya dauke Kai tareda cigaba da abinda yake har Saida suka kusa shigewa.


_Zainab_""


yakira sunanta cikin sauti Mara alamar Wasa ko kadan acikinsa.


Dakatawa tayi daga inda taye ta tsaya cak zuciyarta ta Dan harba sbd idan bashine yakira sunanta ba har mantawa takeyi da sunanta na asalin kuma sunan mahaifiyarta.


Ahankali ta juyo jikinta amace ta tako tadawo inda suke ta kalli fuskarsa taga ko dagowa baiyiba ya kalleta
Duk sai taji jikinta ya qara mutuwa,


Mum ma dataji yanda ya Kira sunan Laylan dakatawa tayi daga shigewa ta waiwayo tana kallonsa.


Sai daya aje tab din hannunsa gefe ya dago ya zubawa laylan su a fuska ganin lipstick dinta data shafa Yana Nan daram a bakinta har lokacin kamar ma lokacin ta shafa,
Ya gangaro da idanuwansa Kan suturar jikinta,


Skinny jeans ne ajikinta da doguwar pencil gown Wanda take tsage gefe gefe daga qasa har zuwa gurin qugunta sai Ana ganin jeans din ta inda yake yanken...


Siraran cinyoyinta lafe jeans din yake jikinsu sai silky scarf datai rolling dashi akanta ko wuyanta ba Sosai ya sauka ba.....ya dauke idanuwansa dasuka sauya take da wani bacin ran fitarta daga kanta...


Gabanta ya sake mummunan faduwa tana cigaba da shiga sanyin jikin ganin yanayinsa.


Kai tsaye batareda yakuma kallon gefentaba yace"


Meye time yanzu?
Bana fada karki Kuma fita idan ba school ba?
Akwai school ne yau?


Girgiza Kai tayi tana sauke kanta qasa jikinta na mutuwa da ganin bacin ransa.


And menene wanann a jikinki da Kika saka Kika fita dashi?
Wannan kayane?


Hawayen idonta dasuka taru ne Suka gangaro ta bude Baki ahankali tace"


I'm sorry Abba,
Zan kiyaye Inshallah bazan karaba.


Miqewa yayi yabar gurin batareda ya tanka hakurinta ba ya wuce sama.


Da mamakin Mai girman gaske Ms Na'ima tabi bayansa da kallo har yashige kafin ta maido kallonta Kan Laylah Dake tsiyayan hawaye sosai tadawo gabanta tace"


Baby kinwa Abbanki laifine da bana Nan harya hanaki fita anyhow yanzu?


Laifin me kikai?


Kinje yawone kinyi dare sosai ba?


Girgiza Kai tayi Ahankali hawayenta na sake gudu tace"


Siyayya naje tareda Sofia mukai dare shine yace karna Kuma zuwa koina sai school.


Da mamaki Ms Na'ima tace"


To ai wannan baya cikin dalilin hanaki fita gskia,
Ina nakejin Hana fita a turai saikace Muna Nigeria,
Lallai wannan saidai ke Amma Kam Ni ba magana irin wannan a tarihina....wuce kije daki Zan magana dashi anjima idan mun kwanta Zaki cigaba da fitarki koina kikeso,
Zan lallasar Miki shi anjima idan naje......


Maganar mum din ta qarasa dama lissafinta taji nauyin zuciyarta na tsananta yanda mum din keta nanata idan taje sun kwanta..


Dan Haka juyawa tayi tabar gurin ta nufi dakinta tashige tareda rufo kofar sai lokacin taji kuka na son zuwar Mata Amma ta danne ta qarasa tsakiyar dakin ta aje handbag dinta tareda cire kayan jikinta suka tayi wurgi dasu ta shige toilet.


Wanka tayo tana fitowa sallah kawai tayi ta Haye gado ta kwanta tareda dunqulewa ta rufe ido saidai zuciyarta Dake cikin Hali na qunci Babu yanda zata iya bacci musamman da kunnuwanta Suka jiyo Mata karar rufe kofar bedroom din mum data San sama zata gurin Abban koba komai tafiya tayi ta dawo yau Kam Dole gurinsa zata kwana ga gyara anyo masa.....


Wasu hawaye ne Suka gangaro gefen idonta ta rufe idon tana sake duqunqunewa cikin bargo zuciyarta na Mata nauyi.
##MAMUH#


NOOR ALBI Na kudi ne pay at +234 903 234 5899
*_Mamuhgee 39_*
Daqyar taga asuba tayi ta tashi tayo alwala tazo tayi sallah tana idarwa ta danyi karatun Qur'an tasamu nauyin zuciyarta ya sauka kafin ta miqe takoma gadonta ta Haye Tareda komawa cikin bargo sai alokacin bacci ya iya daukanta mai nauyi.


Bata fito breakfast ba sbd baccin datakeyi sai 12 ta farka tayi wanka ta fito taje ta gaida mum tadawo dakinta tayi zamanta anan tasa Cindy ta kawo Mata abincin taci tana gamawa takira Anty Sa'adah suna fira sama sama dan tasamu tasake sakewa.


Anyi Sa'adah data fahimci tana cikin yanayi Mara Dadi ta saki Ajiyar zuciya tareda Kiran sunanta tace"


Laylah kinsa yanayinki dai yanzu ba'a son damuwa ko?
Karki saka damuwar komai a ranki sbd lafiyanki Dana cikinki Dan kuwa qaramin ciki bayason saka damuwa arai zai iya fita,


Kinsamu Allah yasa daga haduwar qaddara so daya da Turaki yayi dake kin samu cikin gwara ki lallaba abinku ki haife kinsamu naki jinin,
Hakama su Anne da Turakin kin saka musu da dukkanin alkhairansu akanmu....


Nidai banason wani Abu ya samu cikin Nan Laylah sbd bakisan yaushe Allah zai Kuma kawo wannan rabonba na yaqara zuwa ya nemeki harki samu wani rabon Dan Haka gwara ki lallaba wannan din tunda kince so dayane Kuma bada saniba.


Kunyar qaryar dataiwa anty Sa'adah tun farko datake maimaita Mata yanzu da damuwar Jin cikinta zai iya zubewa sanadin damuwa yasa taqarajin duk batajin dadin komai.
Haka suka Gama wayar ba wani walwala ta miqe tayo alwala tayi asr prayer ta koma ta miqe a kujera tana chatting da Sofia itama taji ko zata sake.


Wuni tayi a daki Bata fito ko kofar palon ba hakama washe gari wuni tayi a daki taqi fitowa komai a daki Cindy ke kawo Mata.


Kwananta biyar Bata zuwa cin abinci dasu wasan boyo ma takeyi dasu gabaki dayansu sbd ko mum din datake zuwa gaidawa zuciyarta Shiga wani Hali takeyi sbd yanda mum din koyaushe take nuni da wani alamun mijinta Yana Mata yanda takeso,
a tafin hannunta yake,
Kullum biya Mata buqatanta yake, dadai sauran makamantansu duk da ba ita take fadawaba Amma koyaushe alamominta da wayarta da Haj Zinat na nuni da hakan Dan Haka sai kawai ta taqaita zuwa dakin mum din
Qarshema Bayan kwana biyu cewa tayi batada lafiya Dan Haka saita daina fitowama kwata kwata Dan wani radadi takeji cikin zuciyarta bakuma dama ko halin nunawa.


Shi kansa Abban ko txt dinsa dayake Mata ada kullum ya daina Yi itama batai Masa ba saidai kullum dare saitayi kukan data tabbatarda na mugun kishine Dake cinta Amma ba dalilinta na yin hakan shiyasa abun yake cin ranta.


Daqyar taga anyi sati biyu ta koma cigaba da zuwa makaranta sai tazama Bata wani zama gidan dama mum ko anan Atlanta ba wani zama gida takeba kullum tana gurin yawo.


Tunda Suka koma school sofia datasan da sabon cikin data samu koyaushe itace ke kokarin cheering dinta kayan ciye ciye harma da maganinda Aunt siya ta rubuto Mata na masu cikin kullum sofia ke Kai Mata school acan take Sha itakuma ta koma da sauran gidansu Dan bazasu Bari Laylan taje gida da maganinba a samu matsala.


Yau da wuri tadawo daga makarantar sbd gajiya da bacci ma kawai ita takeji Dan Haka ko data shigo harabar gidan tayi parking motarta ta fito rataye da qaramar Gucci quilted shoulder bag dinta ta,
Jikinta Kuma Diva abaya ce ajikinta maroon sai gyalen abayan data daura akanta yayi gefe daya.


Palon tashigo kai tsaye batasan dasuba a palon saidata shigo tayi Ido biyu dashi daidai shigowarta daidai dagowarsa ya kalli kofar sbd qamshinta dayaji hancinsa ya shaqo.


Cikin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login