Showing 21001 words to 24000 words out of 27378 words

Chapter 8 - The Sexxy Boss Part 2 Complete Hausa Novel By Maman Teddy .txt

01 Jan 2025

3406

Wani irin Kallon Hajiya mulaika take mawa Hajiya Turai kana tace " A'a wanda zaki saka ,sai kin tabbatar jikin ki ne , saboda kin san fa komai ba don Allah zamuyi shi ba. Na farko asirin sa zamu tona a duniya ,ko ta hanyar sharri ne ,dole gwamnati ta ɗauki mataki . Daganan ne zamu fara cin dukiyar sa ,muyi facaka da ita . Shiru Hajiya Turai tayi sai kuma tace " To yanzu wazan hada shi da ita ta kuma iya mun wannan Aiki ,cikin sirri?. Gyara zama Hjy mulaika tayi kana tace " Baga ƴata Nusaiba ba.! Sauke numfashi Turai tayi cike da farin ciki tace " Ƙwarai kuwa ,yanzu idan kin koma sai ki mata bayani , Ni kuma zan samu mahaifin sa da maganan ,nasan dole zasu amince ,tun da babu wata mafita bayan hakan.!




****
A hankali suke tafiya kusan su Biyar hannun su duka kowa yasha lallin fulawa mai ƙyau ciki harda Amarya Umaima , wanda a yau biki saura Ƙwana biyu. Yaran layin kunsan Amarya da farin jini haka kowa kebin ta irrrrrr.




A zaure ne sudai su Fatima sun ga Umaima ta saki wayar hannun ta yayi ƙasa tana furta ' Innalilahi wa'inna ilaihir rajiun . Kallon kallo suka tsaya suna yi ita da Umair .wanda ganin ta yasa duk wannan raɗadin da yake ji ya ƙwaranye. Umaima Yaudara ta zakiyi? Wani zaki Aura bani ba? Anya kina Son shi kuwa? Hummmm Bakya son Umaima da kina Son shi ba zaki taɓa fitar dashi a matsayin mata miji ba ,bayan kin san nine Mijin ki.! Zaki jefa rayuwar sa cikin haɗari maslaha ɗaya ki hakura da wannan Auren idan ba haka ba ,kin fi kowa sanin ko Ni waye .! Na baki Daga yau zuwa gobe Duk shawarar da kika yanke , ga card ɗina ki Kirani. Ya ƙare magana yana wurga mata card tare da ficewa . Nisawa Ummalo tayi ƙawar Umaima kana tace " Wannan me baƙar tabarau ɗin Waye kuma ? Umaima kin san shi ne.??. Shiru UMAIMA tayi tabbas maganan Umair ya firgita ta ƙwarai . Duƙawa tayi a hankali tana share hawayen fuskar ta ,tare da sa hannun ta tana ɗaukar katin....!








*MMN TEDDY*
*O*




*Littafin THE SEXY BOSS na kuɗi ne ban yarda ki karanta mun ba tare da kin biyani haƙƙi na ba... Regular group ₦300...Vip group₦500... Special ₦1000 via 6037312299 Mohammed Aisha keystone bank ko kuma ki tura katin MTN ta wannan number 08081202932 Idan VTU transfer zakiyi ki tura kai tsaye ta wannan number 09061466409*


*Morning update🥳*


Miƙewa Umaima tayi jiki a sanyaye tana kallon Su Ummalo da Fatima , kana tace "kumu tafi !. Bin bayan ta suka yi yayin da Fatima ke faɗin mun shiga uku.!! Ɗakin Hajiya Balki suka shiga don tun da bikin ya ƙara so kusa ta tattaro ta dawo gidan da zama ,a cewan ta ba zata koma ba sai anyi biki an watse . Tun da suka shiga ɗakin Ƙawaye da Son jin gulma sukayi ta baza idanu wai ko zasuji Umaima tayi magana Umair , amma kuma shiru , a haka da ɗaya da biyu kowa ya watse ,don Umaima katin Hajiya ta ɗare tana juya masu baya kamar mai barci ,amma nan kuwa sam ba haka bane , damuwa ne ya taru ya lulluɓeta . Rintse ido tayi tana saurun buɗe su ,hango fuskar Umair tayi tana sakar mata wannan murmushin nasa , hushiryar sa da ya raba tsakanin fararen haƙoran sa na bayyana. Ɗan tsaki ta jah kana ta furta mugu kawai . Jin wannan magana nata yasa Fatima da ita kaɗai tayi saura cewa " Umaima wai ya ake ciki ne? . Juyowa Umaima tayi tana muskutowa daga ƙwance bata tare da ta miƙe ba tace " Kaman ya kenan Fati.." hummmm sauke numfashi Fatima tayi kana tace" Umair ,Ni anawa ganin mai zai hana ki Auri Umair kaman zai fi mana , kiyi duba fa , da gaske yake a yanzu . Wani irin murmushi Umaima ta saki ,kana tace " Baki san waye shi bane,Amma ina da yaƙinin Umair ya Aure Ni to ba zaman daɗi zamuyi ba ,mugu ne macijin sari ka noƙe ,azabtar dani kawai zaiyi ,don duk izayar nN da yayi mun bai ishesa bane shiyasa yake son Aure na ta rabani da duk wani farin ciki na. Kar fa ki manta da baki nayi masa kan Allah yasa ayi mawa ya'yan sa haka shine yace " Zai Aure Ni don dole.




Shiru Fatima tayi kamin kaman wanda aka tsikara tace " Amma dai kin san kunfi dacewa dashi ba Ashiru ba. Dacewa.? Umaima ta maimaita maganan kamin ta taɓa baki tana faɗin , idan na Aure sa da wannan ƙanƙantan shekarun nawa ,kashe mun Rayuwa zaiyi ,matar shi kan ta abun ki tausaya mata ne ,mugu kawai ". Umaima tayi maganan tana tuno da maganan sa da yake cewa " Ni bana barci da kaya , haka kuma nake son Matar da zan Aura ta kasance. Hummmm to ai shikenan Umaima kin fini sanin waye shi ,tun da ke kika zauna dashi . Cewan Fatima tana murmushi .


***


Bayan Umair ya fita ne yana shirin fita layin ya haɗu da Baba Sule , Wanda kallo ɗaya yayi mawa Umair ya gane sa . Cikin matsanancin Fara'a ya kalli Umair da shima shi yake kallo " Cikin mutuntawa Umair ya gaishe da Baba Sule ,kana Baba Sule ya amsa yana faɗin Saukar yaushe ? Ko kun zo ɗaurin Auren ne?. Wani irin bugawa ƙirjin Umair yayi sai ya ɗan yi murmushin yaƙe yana cewa " Ina Baba.? Au Baku haɗu ba kenan da Malam Ibrahim ?. Eh Bamu haɗu ba. To muje Na kaika shagon shi. Shiru Umair yayi yana bin bayan Baba Sule , a zuciyar shi yana cewa " Dama Baba Kasuwanci yake yi?. Gani yayi sun fito bakin hanya Baba Sule na shirin tare Abun hawa .! Cikin sauri Umair ya ce dashi" Ah Baba baga mota na can mun barota ta a layi, mai zai hana muje mu shiga sai muje Ai ban kawo shagon da nisa ba. Murmushn su ta manya Baba Sule Tayi kana yace " Ai shagon a kasuwa take . Juyawa sukayi tare da nufar Moton da Umair yazo da shi kirar wane yaro . Suna shiga Umair ya fara driving basu ɗau mintuna goma ba suka isa kasuwa . Bin shagon Umair yayi da kallo ,shago ne ɗan madaidaici , ga yaran shagon suna ta sallamar customers . Ɗaga kansa sama Umair yayi yana duban Shagon ,anan ya fahimta shagon siminti ake sayarwa . Ba Bismillah Umairu shigo daga ciki ,cewan Baba Sule yana shiga Umair ya biyo bayan sa. Masu saye da sayarwa wurin duk idanun su ya dawo kan Umair , kowa na tunanin ne ya kawo wannan matashin attajirin nan cikin kwacalcalin Kasuwar ? Wai kuma ya rasa inda zai zo sai shagon sayar da siminti .




Zaune Baba yake akan Sallaya yana zikiri don rana yana gab da faɗuwa. Shafa addu'a yayi yana kallon Baba Sule da Umair da suka zauna a gyefe suna jirar kammalawan sa .aaa Umairu kune da yammaci?. Murmushi Umair yayi yana sunkuyawa cike da ladabi yana gaida Baba ,kana ya baba ya amsa yana tambayar sa kowa da kowa. Ba tare da Umair ya basa Amsa bane ya kalli Baba Sule kana ya juya yana kallon Baba tare da cewa " Baba Wai Shin gaskiya ne an mawa Umaima miji bani ba?. Kallon sa Baba Yayi kana yayi shiru sai kuma ya ɗago a yana girgiza kai tare da cewa "Ƙwarai Umairu , yau saura kwana biyu kenan. Sai daga baya Aka zo da maganan ka , haƙuri xakayi Allah ya baka wata wacce tafi Umaima.




Ina Baba bazan samu ba. Yayi maganan idon sa na kaɗawa daga fari zuwa ja. Umaima ba matar kowa bace ,matata ce.! Baba don Allah ku warware wannan Sa ranan A maida akaina. A jibin a bani ita . Ƙara ware ido Baba yayi cike da mmki , kamin yayi magana Baba Sule yafara ba Umair haƙuri ,tare da masa bayanin idan suka raba wannan Aure sunyi ƙaranta ,kuma sannan Mutan unguwa zasu ce sunyi Auren kudi ne , kuma kar ka manta Umaima ba tsarar Auren ka bace ,ka fita komai . Cewan Baba yana kallon Umair wanda jijiyoyi n jikin sa sun tashi , gargasar hannayen sa sun mimmiƙe . A hankali ya furta " Shikenan Baba Allah ya basu zama lafiya." Amin su Baba suka amsa .


***


Tun daga wannan Rana Umair barci ya gagare idon sa. Yayin da zuciyar sa ke saƙa masa abubuwa da yawa da zaiyi akan Umaima ,don har tunanin yasa a sato Masa ita sai da yayi , ya kulleta a tare dashi suyi rayuwa har mutuwa . Amma tuno da karamcin wannan gida yasa shi fasa yin hakan . Kullum a tunani yake a kuma shan barasa . Zaune yake shida Julayb ,Julayb ne ya aje karan sigarin kana yace "Wai Umair kana da hankali kuwa? Akan mace kake kokarin kashe kan ka ?. Jubi fa kwalebe nawa ka shanye na barasa baka tunanin lafiyar ka?. Banza Umair yayi masa kana cikin Muryar maye yace " Kaje Garin su Umaima yau ka gani an ɗaura mata Auren?. Kallon sa Julyab yayi kana yace " Idan an ɗaura to me xakayi? . Cireta a rayuwa ta zanyi. Murmushi Julayb yayi ba tare da ya bari Umair ya fahimta ba yace " To yau zan tafi ,tun da kasan yau ne ɗaurin Auren ..


***


A yau asabar ƙarfe biyu aka ɗaura Auren Umaima da Angon ta Ashiru . Wanda tun da Aka ɗaura Auren nan Ashiru fara'a bakin sa yaƙi rufuwa ,haka mutane da dama sun halarta wannan daurin Aure ,don Baba aƙwai shi da mutane kwarai.




Tun da aka ce an ɗaura Auren , Umaima hankalin ta ya fara tashi , babu tunanin wanda take yi sai maganan Umair.! Yaudara ta zakiyi???. Wani irin bugawa ƙirjin ta yayi tuno da wannan maganan tasa . A haka ta wuni babu walwala . Wanda da misalin yammaci aka kawo mota aka ɗauki amarya zuwa gidan mijin ta wato Ashiru . Don basu da nisa daga layin su Umaima sai inda aka kaita . Gidan yawa ne don a cikin gidan aka yi mata ɗan Platt Mai ƙyau. Mata ne kusan bakwai a gidan kowa da mijin ta da yayan ta . Kuma duka yayyun Ashiru ne .




Su Fati kuwa sai fara'a ake ,ana ta shiga da fita , wanda wuraren ƙarfe takwas kowa ya watse . Abun da Umaima bata taɓa gani ba shi ta gani. Bayan Mutane sun watse ne , Ashiru ya shigo da yayyun sa mata don shine karamin su , acewan su sun rako Auta ɗaki. Wani sarawa kan Umaima yayi cikin ta na murdawa sakamakon jin ƙamshin turaren Angon nata , wannan yasa ta saurin miƙewa tana sauke mayafin da aka rufa mata . Muryar babban yayan su taji tana cewa " Alhmdllh Mun kawo Angio....kamin ta rufe baki ne Umaima ta fara amai , kaman zata fidda hanjin cikin ta ...!
*P*




*Littafin THE SEXY BOSS na kuɗi ne ban yarda ki karanta mun ba tare da kin biyani haƙƙi na ba... Regular group ₦300...Vip group₦500... Special ₦1000 via 6037312299 Mohammed Aisha keystone bank ko kuma ki tura katin MTN ta wannan number 08081202932 Idan VTU transfer zakiyi ki tura kai tsaye ta wannan number 09061466409*


*NIGHT UPDATE🥱*




Tsayawa Duka dangin Ango Ashiru sukayi kana Yaya Hadiza tayi saurin nufo Inda Umaima ke tsugune tana sheƙa amai kaman zata fidda ƴan hanjin ta . Tallabota Yaya Hadiza tayi kana tace " Umaima lafiya dai ko. Babbar yayan su Ashiru ne cike da masifa ta kalle Umaima tana cewa" Wani lafiya ,ai dagani kun san babu lafiya wannan. Sam Ashiru ba zai ƙwana a ɗakin nan ba , sai an tabbatar Wannan yarinyar ba ragowa bace. Subhanallah Yaya Uwauwa wannan maganan bai dace ta fito daga bakin ki ba ,da girman ki fa?. Cewan Ashiru cike da damuwa . Kai da Allah wuce ka rufe mun baki , Kai yaro ne , Kalli fuskar ta , kasan a haife na haifi Umaima don na kusa jika da ita . Ba yau nafara ganin mace watsatstsiya ba. Don haka A kiramun Safara'u maƙociyar mu yanzu ,tazo tayi gwajin fitsarin Ta ,ko anan zamu fahimta gaskiyar Al'amarin. Juyawa Umaima tayi tare da durƙushewa anan wurin. Tana sakin wani marayan Kuka kana ta fara cewa " Umair ka cuceni ,ka cuta Rayuwa , Bazan yafe maka ba ,wayyo Ni ,wayyo Rayuwa.! Juyawa Yaya Uwauwa tayi tana kallon Yaya Hadiza kana tace " Kunji magana ta yafito ko?. Hummmm a jura zuwa rafi dai . Shiru Falon yayi kowa da abun da yake saƙawa a zuciyar sa na tsawon minti ɗaya . Kana Yaya Hadiza ta cika hannun Umaima tare da jan wani dogon tsaki . Ai dama wannan shaka shaka na wannan yarinyar Ni tuni ina zargin ta . Allah shi kyauta kai ka nace gashi nan ta jawo mana Abun magana a maƙota da dangi ,a koma ana cewa ka Auri karuwa.! Yaya Hadiza ke maganan cikin matsanancin fushi tanayi tana kallon Ashiru da ya sauke hular shi yana firfita don wani irin gumi ke karyo masa .




Yaya Uwauwa ce ta amshe Hadiza da cewa " Ai wannan tafi ragowa karuwa dai ,gatanan ƴar malam taƙi halin malam ,waye bai san mahaifin ta ba , shi fa yake kirar sallahn masallacin layin nan , wallahi kin fita Zakka a cikin yan uwan ki da gidan ku baki ɗaya . Kin kuma jawo mana Abun kunya a idon duniya . Tana gama faɗin haka ta juya fuuuuu. Yaya Hadiza ce ta kalli Ashiru dake tsiyayar da ƙwallah . Umaima.! Ya kira sunan Umaima da a yanzu kukan ya gagara mata sai sauke ajiyar zuciya ,tana cura ji take kaman ta haɗiye ranta ta mutu ta huta. Tana nan zaune ne taji y Kira sunan ta , wanda sam ta kasa Amsa shi ,sai numfarfashi da take yi ,ji take ƙirjin ta na mata zafi kaman zai ɓalle wani ya fito mata ta huta . Umaima me yasa kika yi mun haka?. Ba laifi na bane , Shi ne ya mun haka?. Auwalu??? Ashiru yayi maganan cike da fusata ,don shi har a yanzu bai ɗigon raguwar soyayyar Umaima a zuciyar sa ba ,sai ma wani wutar soyayyar da yake ƙara mamaye zuciyar sa. Kaman ba zata basa amsa ba , sai kuma tace " Sir Umair Ahmad moddibo.! Wani irin bugawa zuciyar Ashiru yayi ,don tabbas yasan Umair ba ƙaramin mutum bane a Nigeria baki ɗaya ,ba state ko ina na Nigeria ambaton sunan matashin ake yi. Cikin gwasalawa da wawantar wa Yaya Hadiza tace " Au iskancin naki har ya kai ga Nan? Kin san waye Sir Umair kuwa da har zaki masa wannan sharrin , don an kawo ki gidan mijin ki a ragowar ƙattai . Kinje wani ƙato ya gama buga maki iska sai Kizo mawa ƙaninmu a matsayin ragowa . To hattara kar ki ƙara faɗin munin abu akan Sir Umair , don kaf dangin ku zai ƙarar Bakya kaɗai ba ,mubafaka muguwa kinci mana mutunci tsakanin mu dake ALLAH ya isa.!




Wani irin fashewa da kuka Umaima tayi tana ɗaura hannun ta aka ,sam ta rasa me ma zata ce fadi take wayyo Ni Umaima ,Ni naja wa kaina ..! Kai Da ALLAH sake ta yanzu ka fito ,iyayen ta da suka kawo mana Ragowa gindu a fafake su taho su dauke ta ,don har da ajiyar ƙwarto.' girgiza kai Ashiru yayi kana yace " Ina son ta a haka , ku barta zan Zauna da Umaima , har ta haifi ɗan ta ko ƴar ta zan riƙe su mu cigaba da zama har Abada...sakarcin banza ,au Dama Kai shashasha ne nasani . Idan soyayya ya rufe maka ido ,mu namu idon a bude yake ,yanzu wannan shedaniyar a yau sai ta bar gidan nan.!


***


Umair lafiya me yake damunka haka?. Ammie ke Tambayar sa cike da mamaki ,Daddy ne yake furta Umair kana lafiya kuwa? Kasan me kake sha a tsakiyar falo? A gaban ma'aikata ,idan baka ji kunyar mu ba ,ai kaji tsoron Abun da mutum zai je ya faɗa. Wannan fa giya ce.! Cewan Daddy Yana pointing ɗin Ƙwalbar barasan da hannun sa . Meye Daddy ,Ammie wannan ce kaɗai zai ɗabemin kewar rashin ta kusa dani. Ina Son Umaima ,Ina son ta , but she Go and live me aside. Why she do that to me???. Daddy Bana da kyau ne ,ko kuwa bana da matsayin da wata ɗiya kaman Umaima zata soni ne??. Dad you now what??? Yayi maganan cike da murya ta maye ,kana yace akan ta na fara jin daɗin Sex ,I need her." Kamin ya rufe baki ne yaji mari tassssss". Cikin wani irin huci Daddy Ke kallon Umair kamin yace" Tashi ka fucemun daga falo mara kunyan wofi . Umair kai naka giyar kudin da ƙuruciyar da haka yazo maka?. Miƙewa yayi ya na tangadi. Nigeria is urs'. Bana wa bane ba, since before now na tsani Nigeria , a yau zan ɗauki visa na zan koma ƙasar Momy na nayi rayuwa ta . Yana gama faɗin haka ya juya yana tangadi ya nufi hanyar fita daga falon. Umair .!! Ammie ta ƙwada kirar sa idon ta na zubda Hawaye . Bai bi takan ta ba ya sa kai yana ficewa daga falon. Cikin sauri Ammie ta juya tana bin bayan sa tare da kirar sa.




Kar ki taka ko nan da can.! Taji Muryar Daddy Yayi maganan a fusace . Cak taja ta tsaya tana kallon sa hawaye na bin kumcinta . Daddy ya Zamu yi mu sa Umair farin ciki. Ammie magana kika tsaya yi , Ya Umair fa ya fita ,kuma ba a hayyacin sa ba , nasan ma da kansa zaice zaiyi driving lemme go and escort him . Cewan Surayya da duk abun da ya faru

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login