Showing 18001 words to 21000 words out of 27378 words
Chapter 7 - The Sexxy Boss Part 2 Complete Hausa Novel By Maman Teddy .txt
saurin leƙawa ta window n na baya tana ƙwaɗa kirar sunan Fatima Tare da ɗaga mata hannu". Sakin manjan da Aka aiketa Fatima tayi tusss ledar ta fashe a ƙasa . Umaima..!! Ta faɗi maganan tana rugowa da gudu tare da biyo motar. Ambato sunan Umaima da fati tayi ne yasa Mazan layin yara da manya miƙewa suna biyo motar . Cikin sauri Umaima ke faɗin " tsaya anan na sauka ,daga nan mota bata shiga ko ina . Ja yayi ya tsaya a gyefe n kucalcalin layin . Kamin suyi magana Umaima tuni ta wangale ƙofar tana ficewa dai dai Fatima na ƙarosowa . Rungume juna suka yi Fatima na kuka tana faɗin " Umaima dama kina nan baki mutu ba. Juyawa tayi tana kallon motan da Umaima ta fito kana tace ' Alhmdllh Allah ya cika mana burin mu aƙwana biyu kacal ana uku . A hankali ta kai bakin ta kunnen UMAIMA tare da cewa " Kin samo kuɗin ne? Lallai Umaima ke mai Sa'a ce. Jimun banza wani mai Sa'a ? Marar Sa'a babu abun da na samo sai masifa. Umaima tayi maganan a zuciyar ta ,don bata da Amsan bai mawa Fatima ,ganin yanda jama'a suka zagaye ta . Hannun ta taji an kama cikin sauri ta ɗago tana kallon waya kama ta haka?. Magajiya ta gani da Uwale da sauran matan Auren layin da suka yi lulluɓi suka fito jin ance Umaima ta dawo. Muje daga cikin gida cewan Magajiya tana kallon Umaima dake ta kallon jama'ar layin , yara abokan gwabzawan ta kowa na kirar sunan Umaima Umaima. Baba Uwale ce tace mawa Ammie Hajiya ku taho mu shiga gida ko. murmushi Ammie tayi tana bin cewa " To badamuwa. Muryar Baba ne ya katse su dana Baba sule da yazo cikin sauri yana faɗin " Alhmdllh Umaima Allah ya dawo mana dake . Ai ga mutanen da suka taho da ita nan. Baba ne yayi saurin cewa " alhmdllh Hajiya mun gode Allah ya saka da Alheri kun taimaki rayuwar wannan yarinya. Murmushi Ammie keyi kana tace " Ba komai Malam ai yi wa kaine , Umaima tamkar ƴa tace. Juyawa yayi ga Umair dake can jikin moton shi bai ƙariso inda suke ba. Don tun da yake a rayuwar shi bai taba shigowa local unguwa geto irin wannan ba. Hayaniyar su har ƙwaƙwalwar sa ji yake kan sa nayi masa kaman ya rabe gida biyu.
Muryar Baba Sule yaji yana cewa" Sannu ɗan nan . Yowa Baba mun same ku lafiya?. Lafiyalau mu shigo daga ciki ko?. Yayi maganan yana kallon Umair , murmushi Umair yayi yana cewa " Ohk. A tare suka juya suna nufar zauren gidan su Umaima da tuni su Sun shige . Yaran layin kuwa bin Umair suke da kallo , a hankali suna faɗin " Laaa balarabe ne . Sai kika ga yara zuuuuuuuu sun biyo bayan sa .
A zaure ne Yaya Hannatu ta shimfiɗa nasu Baba da Umair tabarma , anan suka zauna tare da fara zantawa ,har akayi suka tsinci Umaima... Shiru Umair yayi don bai san me zaice masu ba. A hankali tafara tuno da maganan da Umaima ta faɗi mawa Ammie a moto. Murmushi yayi yana cewa " Ammie nace ta kawo ta gidana ,nan ya labarta masu yanda Ammie ta ganta tana rara gyefe a kofar gidan sa ,da ganin ta ta fahimci baƙuwa ce , wannan yasa ta riƙeta har na tsawon ƙwana biyu . Sauke ajiyar zuciya Baba yayi yana faɗin " Alhmdllh Allah mun gode maka daka sa wannan yarinya ta faɗa hannu na gari. Ba Sule ne ya bude baki zaiyi magana sai yaji Muryar su Baban gida matasan layin kusan su ashirin sun rufo zauren suna faɗin " Allah ya ƙara kiyaye ka Sir Umair Ahmad moddibo . Dama kowa yasan ka ta halin kyautatawa gashi kuwa mun gani yau da idanun mu . Allah yakaara maka ɗaukaka. Zauren ne ya amsa da Amin har da Umair da bai san sunan sa yazo har nan ba. Tuno da Umaima bincike tazo yi akan sa ya fahmta dalilin da yasa tazo har nan Lagos. Miƙewa Umair yayi yana nufar cikin wa'anan matasa tare da jan zugar su har suka isa bakin moton sa. Buɗe wa yayi yana fiddo da minti minti na kuɗi ƴan ₦500 yana damƙa mawa ɗaya daga cikin su tare da cewa " a ba ma kowa. Ihu suke yi suna godiya yayin da Baban gida ke faɗin Umaima ta kawo mana Arziki layin nan...Ai dama ita kullum a haka take ka manta wacece Umaima?. Cewan ɗaya daga cikin su... Shidai Umair bai tsaya sauraren su ba ya bar wurin tare da nufiway soron gidan su Umaima.
***
Ɓangaren Su Ammie kuwa Umma da Hajiya Balki da sauran matan gidan banda godiya babu abun da suke yi , Haka Baba ya shigo yayi nasa . Umma ta so ta ƙwana ganin yamma yayi amma Ammie tace a yau zasu koma. Sallama sukayi bayan sallar magriba Umma har zaure, su Baba Sule kuwa har bakin moto da su aka je. Umair ne ya jira fitowar Umaima don suyi sallama. Wannan yasa shi bai bi zugar Ammie ba. Ba don taso ba Umma tace tazo suyi sallama , saboda bata son Umma ta fahimci Wani Abun ne yasa ta fitowa kaman yanda tace . Koda ta iso zauren shiru tayi tana jirar jin mai kuma zaice. Kusan mintuna biyar sannan ya motsa bakin sa yana cewa " Ki sanar da Baba Nan da 2weeks Daddy zai zo maganan Auren mu , saboda a wannan satin za wuce Oustralia.
Kallon sa tayi kamin ta sa wani irin dariya na rainin Hankali. Amma lallai Umair ka iya rainin hankali, Waye za'a yi maganan Auren nasa Ni?? Allah yayi mun tsari na haɗa zuri'a da mazinaci.! Mugu.!! Mun rabu nida kai rabuwa ta har Abada. Baiyi mamakin furucin ta ba duk da bai taɓa tunanin zata ƙwantar masa da kai don tace masa a'a ba. Murmushi yayi yana dannewa wani ɗaɗɗatan abu da ya tokare masa a maƙoshi. A hankali ya tako kusa da ita.
Hannun sa yakai yana riƙo nata tare da yi kaman zai shige mata. Saurin ja baya tayi ganin yanda yake shirin mata iskancin da ya saba. Nan fa zauren gidan mu ne yanzu zanyi maka ihun ƙwarto .! Ƙara sakar mata murmushi yayi. Lallai wannan Ɗan duniya ne . Tayi maganan a zuciyarta . Tsinkayar Muryar sa taji yana cewa " Dama ai bance da Amincewar ki zan Aure ki ba ,amma ki sani sai na Aure ki ,ko kina So ko Bakya so.! Ina da wanda zan Aura , ba kai ba ,ka jira zaka ji labari Inshaallh. Baya yayi yana dariya kana yace " Ohk kina Son shi kenan wanda zaki Auran? Ohk a shawarce ki Aure Ni ,Don bazan bari kije mawa wani a matsayin ragowa ba. Wani irin ɓaci ranta yayi nan da nan kawai sai ga Hawaye shar shar . Sai na dawo.! Yayi maganan yana juyawa tare da barin ta nan tsaye.!
*MMN TEDDY*
*M*
*Littafin THE SEXY BOSS na kuɗi ne ban yarda ki karanta mun ba tare da kin biyani haƙƙi na ba... Regular group ₦300...Vip group₦500... Special ₦1000 via 6037312299 Mohammed Aisha keystone bank ko kuma ki tura katin MTN ta wannan number 08081202932 Idan VTU transfer zakiyi ki tura kai tsaye ta wannan number 09061466409*
RAMCY HERBAL💃💃Tabbas da kaji wane ba Banza ba , wani kaya sai amali , rugun babban motsi , margamargan dutse kafi gaban Aljihu ,wannan nima kaina da baki na na faɗi haka yake🤞. Ina kuke ƴan Uwana manyan mata ,shin kuna ina?💃 Matso kusa ga babban dama ta samu daga hannun wannan shahararriyar ƴar mutan Sokoto RAMCY HERBAL ta shirya tsaf don kawo mana magunguna da dama meye matsalar ki Amaryar Oga??
Uwar gidan Alhaji kefa? Maza saurara kiji wannan magunguna daban ne da saura daga taskar ƴar mutan Sokoto .
-Maganin ƙanƙancewar gaban ɗa namiji
-Maganin sanyi na mata da na maza
-Gumbar riɗi , gumbar aya ,gumbar ƙwaƙwa , gumbar dabino.
-Zumar ni'ima
-Zumar ƙiba
-Zumar goran tula
-Dambun ni'ima
-Zumar ƙwakwa da ta dabino
-powder hip up Dana breast elargement .
-tsumin ƴar gata
-Tsumin tabaje
-Maganin ciwon sugar
-Maganin hawan jini
RAMCY HERBAL ba anan ta tsaya ba , ta kuma taho mana da kayan gyarar jikin mu...💃💃
-Dilka Soap
-Whitening Cleanser
-malato soap
-Half cast soap
-shu'umin Humra tare da turaruka masu ƙamshi ,da zai rikita Oga in a few sec.
Ga masu buƙatar ƙarin bayani maza hanzarta ku tuntuɓi wannan number 07032209881 / 08109511467 .
Address: Sabon titin sokoto rima , kafin wajen sha'aban mai kankana mun gode.!
Tsayawa Umaima tayi nan Wurin motsi ta kasa sai aikin sharar ƙwallah tana tunanin Maganganun Da Umair ya gama watsa mata . Hango Baba Sule Tayi daga wajen soron yana takowa da'alama shigowa zauren gidan zaiyi ,nan ta yi saurin juyawa tana nufar cikin gidan. A tsakar gida ta tadda kaf matan gidan , da sauran mutane wanda su taho mawa Umma jejeto ,wuce su tayi ba tare da ta tanka kowa ba , Tayi cikin ɗakin Umma .
Tun daga Wannan rana Hajiya Balki ta yanke hukuncin kar a bar Umaima ta fita ko nan da can ,Bata ba fitar gida,kullum tana zaune gu ɗaya. Fatima ce da sauran ƙawayen ta ke shigowa suna tayata fira. Idan Umaima taji har hantsi yayi Fatima bata zo ba ,zata aika a kirata su zauna fira.
Zaune Umaima da Fatima suke , Suna cin Tuwon da Umma tayi shi yanzu da wannan yammacin . Umaima wai naji baki mun maganan Kuɗin bane ? Wannan matan data kawo ki itace ministan ko. Ke amma fatima baki da hankali wallahi , wannan mutfa fa da kika munzo tare dashi ai shine Umair ɗin ,ita kuma watan nan matan mahaifiyar sa ce. Nan Umaima ta cigaba da laburta mata abubuwan da suka faru , don har Lalatan da yayi da ita bata ɓoye mata ba . A ƙarshe ne ta faɗa mata maganganun da yaɓa mata a zuwan nan da sukayi tare . Tun da Umaima ta fara bata labarin Yanda suka yi da Umair Fatima ta fara zubda Hawaye . Kai Amma wannan Mutumin mugu ne Wallahi babu na biyun shi. Hala ma shiyasa kika amince da Ashiru don nayi mamaki da kika yarda ki Aure san. Eh fa ,don dana Aure Umair gwara na Auri Ashiru ko banza nasan shi ba mazinaci ba ne. Kuma ki sani wallahi ba sona tsakani da Allah Umair keyi ba ,kawai don nayi masa mugun baki ne .
***
Ɓangaren iyayen Ashiru kuwa ,tun da suka zo kaico kaico Suka yi magana da Su baba Sule akan tsaida Auren Umaima da Ashiru. Wanda hakan yasa su Amincewa tare da Hamdala . Sati uku aka sanya na Auren , don an fi tsawon shekara guda dama ana Son tsaida magana Umaima ke kauce kauce tayi ta masifa ita bazata Auri Ashiru ba ,sai ta gama sakandire. Sai a yau su Baba suka tsaida rana .
Kowa a dangi farin ciki yake yi da Wannan Aure , duk da Umma bata aje ba,ba kuma ta bai mawa wani Ajiya ba . Amma tace Allah shi ke rufa asiri .
Wasa wasa lokaci nata tafiya , yau gashi saura ƙwana shida bikin Umaima da Ashiru , a wa'ancen ranakun sam ko tuna Umair bata yi , amma sai a yanzu tayi ta tunanin sa , sosai take tambayar zuciyar ta mai yasa take hakan ,don so take ta manta shi a rayuwar ta , wanda a cikin zuciyar ta ta yi masa suna da "Mayaudari. Fatima ne da ƙawayen Umaima suka shigo gidan , a bakin Kitchen suka tadda Umaima tana rafka tagumi kaman yanda ta saba da kullum. Cikin sauri Fatima ta ƙarako inda Umaima take tana cewa ":Ga Ashiru can a waje yana jirar fitowar ki ,shida Abokin shi . Tashi muje nasan bai wuce hidimar bikin ne .
Nisawa Umaima tayi tare da ɗaga kanta sama , ganin hijabin ta a saman igiyar shanya yasata raruma tana sanyawa tare da cewa " Ku mu je ko.! Tun daga nesa Hango Umaima Ashiru ke washe baki , har suka iso . Gaishe su Tayi cikin mutuntawa , don Umaima ta sauya ƙwarai kaman ba ita ba . Kullum a cikin kasale da zazzaɓi take wanda har Muryar ta ya sauya , yawan hargogowan nan duk ta daina shi . Malama Umaima ya hidimomin? Da kuma shirye shiryen? Cewan Ashiru yana murmushi . A hankali Umaima tace " Lafiya lau ya naku shirye shiryen ?. Alhmdllh cewan Ashiru yana faɗaɗa murmushin sa . Yanzu da Aƙwai wani Abu da kuke buƙata ne?.
Juyawa Umaima tayi tana kallon Su Fatima da suka amshe ta suna cewa " Sai dai za'a bamu kuɗin walimar ƙawaye. Hummmm Ni Bara na shiga daga ciki idan kun kammala ku sameni a gida . Umaima tayi maganan tana masu Ashiru sallama tare da juyawa tana nufar cikin guda .
Can ƙuryar Ɗaki ta shige tana ƙwanciya a gadon Umma tare da rufe idanun ta kaman mai jin barci . Motsin Shigowa taji wannan yasata buɗe idanun ta tana kallon Umma dake shigowa. Miƙewa tayi zaune , Nan Umma ta zauna bakin gadon tana kallon Umaima kaman mai tsartan Wani Abu ,sai kuma tanisa tare da cewa " Umaima kina lafiya kuwa? Meke damunki kwana biyu ?. Nisawa Umaima tayi kana tace " lafiyana qlau Umma ,kwana biyu zazzaɓi ne kawai sai yawon kasala da nake ji. Bari Malam ya shigo sai a aika chemist a sayo maki maganin zazzaɓi . To Umaima tace tare da lumshe idanun ta. Miƙewa Umma tayi tana fichewa daga kuryar dakin , a zuciyar ta tana tunanin ƙila zullumin Aure ne ke saka Umaima hakan.
***
Ɓangaren Umair kuwa a sati biyu ne yaso ya dawo gida nageria , kullum tunanin sa yana kan Umaima , Aikin nasa ne yaga zai ɗauke sa fiye da sati uku ,wannan yasa shi a sati na Ukun ya kira yayan Mahaifin sa yana sanar masa da Batun Umaima tare da roƙon sa kan a je a nema masa Auren ta . Cike da jin daɗi Alh Iblo yake sa masa Albarka ,don dama burin su suga Auren Umair ɗin . Yana datse kirar Ya kira Alh. Ahmad moddibo yana sanar masa kan zai je nema mawa Umair Auren Umaima anan Garin su. Sam Daddy Bai jah ba ,hasali ma addu'a yayi na nasara.... Ana saura kwana uku bikin Umaima Alh Iblo ya taho nema masa Umair Auren Umaima . Wanda Anan ne yake jin an kusa bikin ta saura kwana uku ma yanzu haka . Shiru Alh Iblo yayi kamin yayi masu fatan Allah ya basu zama lafiya. Godiya Su Baba Sule Sukayi ta masu tare da masu haƙuri . A haka Alh Iblo ya tafi . Bayan tafiyar Alh Iblo ne Ya kira Umair a waya yana bada baki da basa haƙuri ,sannan ya sanar masa da Cewan An mawa Umaima baiko da wani ,yanzu haka ma saura kwana uku bikin . Ai bai bari ya ƙara ji daga bakin da ba , ya katse wayar yana sawa a yankan masa tikitin tafiya , don a cewan shi a washe gari zai dawo gida Nigeria , sam ba zai bari ayi wannan Auren ba .!
Kuyi manage wannan Pls ba yawa 🙏
*N*
*Littafin THE SEXY BOSS na kuɗi ne ban yarda ki karanta mun ba tare da kin biyani haƙƙi na ba... Regular group ₦300...Vip group₦500... Special ₦1000 via 6037312299 Mohammed Aisha keystone bank ko kuma ki tura katin MTN ta wannan number 08081202932 Idan VTU transfer zakiyi ki tura kai tsaye ta wannan number 09061466409*
*Night Update🥱*
Hankalin Umair sosai ya tashi da jin maganan Alh Iblo , wanda bai shawara da kowa ba ya yanke hukuncin dawowa Gida Nigeria . A kusa can Abuja Daddy ne ke sanar mawa Ammie abun da iyayen Umaima suka faɗa mawa Alh Iblo na An riga an mata miji sai dai Umair yayi haƙuri . Shiru Ammie tayi tana faɗawa Duniyar tunanin ya Umair zai amshi wannan zance? Anya zai iya haƙuri kuwa? Don a ƙwayar idon Umair take ganin mahaukacin Soyayyar Umaima , wannan yasa yana ɗaya daga dalilin da ta amince da maganan nasa bata ɗauke shi a shirme ba. Sauke Ajiyar zuciya Ammie tayi tana kallon Daddy kana tace " To Allah yayi mana zabi mafi alheri . Amin ya Allah Daddy yace , kana Ammie ta muskuta tana fitowa daga Part ɗin Daddy , Direct Bedroom ɗin ta ta nufa . Bedside Drower ta Kai hannun ta ,tare da ɗaukar Wayar ta ,don ta kira Umair ta rarrashe shi ,ta kuma basa haƙurin matar mutum bata taɓa Auren mijin da bana ta ba . Abu kaman Wasa ta kira layin sa yafi sau biyar amma switch up .wannan yakuma ɗaga Hankalin Ammie ƙwarai . A wannan ranan dai barcin ta rabi da rabi ne.
Ɓangaren Umair kuwa ƙwana yayi zaune yana jin wani irin zafi a zuciyar sa , a cewan sa shi sam bai taba niman abu ya rasa ba . Bai kuma taɓa ƙwalla fa rai a abu bai samu ba. A kan ta baza'a fara ba. Ƙwana yayi yana shan sigari baya duba koda lafiyar sa . Cikin matsanancin ɓacin Rai yake furta " duk wanda yayi kuskuren Auren matar shi sai yasa shi ya ƙare Rayuwar sa A gidan Kaso na har ƙarshen rayuwar sa. A washe gari ne Umair ya taso daga jirgin Oustralia zuwa gida Nigeria .
***
Wani irin dariya Hajiya Turai tasa kamin ta juya tana kallon Aminiyar tugun ta wato Hajiya mulaika . Masha'allah Allah mun gode maka , da wannan Aure ba'a bashi ba , don tamkar shigar sauri yayi mana ,ya kauce mawa tugun mu. Don haka yanzu wasan zai fara . Kyacewa da dariya Hajiya mulaika tayi tana miƙamawa Hajiya Turai hannu suka tafa . Ƙwarai Turai wannan gaskiya ne , kinga sai mu zabo masa ko wacece muce zamu yi masa Auren Huce takaici. Eh kuma da Hjy mulaika kin kawo mafita kwarai , to mai zai hana Musa Ru'aifa?.