Showing 9001 words to 12000 words out of 27378 words
Chapter 4 - The Sexxy Boss Part 2 Complete Hausa Novel By Maman Teddy .txt
kuwa tunanin ki ba'a allura a nan ? Yayi maganan yana matsa Famin Virgina ɗin ta da yayi mata , saurin rintse ido tayi tana faɗin Ashhh". It's ohk ". Yayi maganan yana cire hannun sa daga wurin , kamin ya cigaba da cewa " Waya ce Maki baa Allura Anan wurin , ranan da kika haife mana baby to Ni da kaina zan ɗinka ki... wani irin fiddo da ido Umaima tayi na mamakin rainin wayon da yake mata , wato bazai barta ta koma gida ba sai ta haifa masa yaro . Amma yanxu magani zaki sha kinji Matana".
Ji yayi ta sakin masa wani irin kuka da bai san dalilin zuwan shi ba , Cikin kuka take faɗin " Don ALLAH ka maida Ni gidan mu , wallahi ni yarinya ce bazan iya haihuwa ba ,mutuwa zanyi kashe Ni xakayi . Amma kuma kike da Wanda zaki Aura? . Saurin kallon sa tayi kamin tayi magana ne yace " bafa wani ya faɗa mun ke da bakin ki kika faɗa . Ki cire wa kanki Son Auren kowa , Ni zaki aura ai mugun baki kika yi mun wanda babu wanda ya taɓa mun irin shi , don haka dake zan zauna har sai maganan taki ta tabbata shahararrar mara kunya . Yayi maganan yana ɗaga hannu kaman zai sauke yatsun sa a kuncin ta . Rintse ido tayi da ƙarfi don ta sadakar da marin ta zaiyi . Tashi muje ki gasa jikin ki , ki taho kici Abinci. A hankali ta fara ƙoƙarin miƙewa ,amma ta kasa ganin haka yasa shi ɗaukar ta cak yana nufar privacy da ita tare da cewa " Ki saki jikin ki daren yau ma irin haka zan ƙara Maki.
***
Ganin Hajiya Turai da wannan yammaci yasa Ammie Maryam cike da mamaki saurin muskutawa tana faɗin " Lale maraba Barka da saukar baƙin dare. Fareesa ce ke bin bayan Hajiya Turai yayin da Surayya dake tare da Ammie Maryam ta nufe Hajiya Turai da gudu tana hugging ɗin ta tare da faɗin " Oyoyo Mummy . Murmushi Hajiya Turai tayi tana shafa kan Surayya kamin tace " Ke wato kin guje ni ko? , A'a Mummy Dama ina shirya zuwa a satin nan . Hummmm to ai shikenan ina nan ina baza idanu . Dariya Surayya tayi tana komawa mazaunin ta kusa Da Ammie tana zama. Fareesa ita ma na nufo Ammie Tare da gaishe ta . Muryar Hajiya Turai ne ya katse su tana cewa " Eh Ammien Umair kin ganni da wannan daren, nima wani labari ne ya tadani zaune tsaye da ya riskoni ,sai ina ganin Abun kamar ƙarya ce da sharrin da Al'umma suka saba . Kamin Hajiya Turai ta numfasa ne Ammie tace " Akan Umair ko?. Ƙwarai kuwa. Ai na sani dama kullum a haka ake . Meke faruwa Hajiya?.
Nisawa Hajiya Turai tayi tana gyara zama tare da labarta nawa Ammie duk abun da taji daga Bakin Ru'aifa ƴar leƙar asirin ta . Sauke numfashi Ammie tayi kana tace " Ina tunanin wannan Shirmen mutane ne kawai , babu yanda za'a yi ɗana yayi Aure ba tare da sani na ba ,haka kema ba tare da sanin ki ba Hajiya , amma ina tunanin wani Abu dabam ,ina zuwa . Hannun ta Ammie takai tana ɗaukar wayar ta dake a gyefen ta . A hankali tafara latsawa tana karawa a kunnen ta . Kiran Umair tayi dai dai lokacin da yake bamawa Umaima Exercise tana hawa stairs ɗin falon da sauka ,don ya bata abinci tasha magani a yanxu so yake ƙafafuwan nata su saki . Ganin ta tsaya tana maida numfashi don ta kai ta kawo yafi sau goma , yanzu ita ba ƙafan bane ya ke a riƙe ,zafin hawa da saukar ya dameta . Tsayawa tayi tana matso ƙwallah a zuciyar ta tana furta mugu azzalumi . Gani yayi bakin ta na motsi wanda tabbas yasan ƙunƙuni take wannan yasa shi hayewa stairs na uku yana facing ɗin fuskar ta . Cikin sauri ta juya ƙasa zata cigaba ,jin hannun sa tayi ya riƙo nata hannun . Cak ta tsaya zuciyar ta na bugawa dam³ . Juyowan da yayi da ita ne taji jikin ta na gogar nashi tana fuskantar shi , ƙirjinta da nashi suna gab da shafan juna , saurin kallon dogon rigar ta na English wears tayi , kana tayi baya cikin sauri tana cewa " Cigaba fa zanyi. Hannun sa yakai yana rungumo ta jikin shi tare da shafa bayan ta , kawai jin kansa yayi da yi mata hakan ba tare da ya san dalilin sa ba. Umaima zaki Aure Ni??. Wani girrrr yaji , wannan yasa shi saurin raba jikin shi da nata jin Kirar da ya shigo masa . Ɗaukar phone ɗin nasa yayi ba tare da ya kara a kunnen sa ba ,don ya ɗauke da maɗaukar magana a kunnen sa . Ammie Barka da dare .
Yowa Umair ya kake ya ayyukan? Alhmdllh Ammie. Daddy ya dawo ne?. A'a kasan yana gidan Hajiya Turai . Ohk " . Yayi maganan tare da barin wancen . Umair wani labari naji , Wai ance kayi Aure har da mata bamu sani ba. Shiru yayi cike da miskilanci n sa , kun san dama wa'annan muskilallun idan kuka ga sunyi shiru ,to zurfin tunanin da suke yi fi na mai yawan zuba kaman jarida. Ammie me ya faru wa ya faɗa maki?. Kai tsaye Ammie ta faɗa masa Hajiya Turai ce... Wani Murmushi yayi yana tunanin wato Ru'aifa ta hannun Hajiya Turai ta tazo wurin sa . Ohk Ammie that's not real ,ba gaskiya bace , Amma soon zai zama gaskiya ,ina so zan Auri wannan yarinyar da kika kawo mun a matsayin cleaner . Ohk wannan shine gaskiyar al'amarin eh Ammie . Yayi maganan kan sa tsaye . Kana kusa Da Umaima n ka bata mu gaisa .
Wani irin bugawa ƙirjin Hajiya Turai yayi da take gyefe , wato da gaske ne kenan, abun da take fadi a zuciyar ta kenan. Kallon Umaima yayi da ta faɗa duniyar tunanin Umma da gida , ji tayi ya sunkuyo yana haɗa bakin ta da nashi tare da manna mata wani irin Kissing , cikin sauri ta ɗago tana kallon shi , ɗan haɗe gira yayi na Arrogant Yana ɗaure fuska kaman bashi yayi mata kiss ɗin. Ammie zata yi magana dake . Yayi maganan yana katsewa . Can kuma sai ya kara kirar Ammie tare da manna mata a kunnen ta . Riƙe ko Ni zan riƙe maki ,tun da ina Son kiyi magana da Ammie na".
*GM🕊️*
*G*
*Littafin THE SEXY BOSS na kuɗi ne ban yarda ki karanta mun ba tare da kin biyani haƙƙi na ba... Regular group ₦300...Vip group₦500... Special ₦1000 via 6037312299 Mohammed Aisha keystone bank ko kuma ki tura katin MTN ta wannan number 08081202932 Idan VTU transfer zakiyi ki tura kai tsaye ta wannan number 09061466409*
A Hankali tasa hannun ta tana kara wayar wanda kamin tayi magana ne taji Muryar Ammie na cewa " Umaima kina lafiya ko? Fatan dai kina jin daɗin zaman nan tare da yayan naki?. A hankali jiki a sanyaye tace " Lafiya kau ,kin koma lafiya ?. Alhmdllh Umaima badai wata matsala ko?. Gyaɗa kan ta Umaima tayi tamkar wacce akace Ammie na wurin , miƙa mawa Umair Wayar tayi yana amsa tare da raɓata yana ce mata ki cigaba saura ki tsaya . Kai me zata cigaba kuma? Kai wai kullum a haka kake ne? Komai kana rinƙa yin shi kai tsaye irin na sojoji ,haba Umair .! ALLAH yasa ba dole kake mawa yarinya ba , ka nace sai ta so ka ,To ka sani nidai bazan mawa Umaima dole ba ,gwara ka lallaɓata . Dariya yayi yana sauka daga can ƙasa kana yace " Ammie ita a wa tace bata So na.! Ai duk macen da ta sameni ta cika mai Sa'a . Hummmm sannu da wasa kai , to ka kula da ƴar mutane sosai kaji?. To Ammie in Sha ALLAH , amma itama ai sai ta kula miki dani sosai ko. Kaji mun shakiyi datse kirar ka bani wuri . Murmushi yayi yana aje wayar a saman table yana juyawa gani yayi tana ta hawa da saukar , sarai yasan mugun ta ne yasa shi yayi mata hakan ,don a yanxu barci yafi buƙata tayi . Ba wannan hawa da saukar ba.
Juyawa yayi tare da nufan inda take . Ke meye sunan ki ma?. Banza ta masa ,duk da tsoron shi da take ji ,amma Haushin sa yasa ta yin masa shiru kaman bata ji shi ba..Kee.! Ya daka mata tsawa da yasa ta yin firgigi , tana ɗago da idanun ta tana kallon fuskar sa da babu wasa . Tambayar nayi sunan ki kika mun shiru?. Ƙwallah ne ya ciko idanun ta , hannu tasa tana ɗauke hawayen kamin tace " Umaima". Wuce ciki ki ƙwanta.
Juyawa tayi cikin sauri tana hayewa sama...shi kuma sauka yayi tare da nufar farfajiyar gidan , wani dan saurayi naga ya nufa yana miƙa masa hannu tare da basa wayar Umaima . Ga wayar nan Sim din na Ciki , ina so kamin zuwa gobe kamun bicike akan mai wayar duka ,inda take zaune da komai ma nata ina buƙatar sani Zuwa gobe . Ohk Sir . Hannu suka hada suna misabiha kamin Umair ya juyo zuwa ciki shi kuma yana shiga moton shi tare da fichewa daga katafaren gidan.
Kai tsaye up stairs ya hayo tare da nufar Bedroom ɗin shi . A tsakiyar Gadon da ya sauya bedsheet ya hango ta ta rufa abun ta , alamu barci ma ya fara ɗaukar ta . Ke tashi ki bani wuri , Bed ya koma na tsarar wasan ki ne? Wurin barcin ki kenan tashi ki ƙwanta a sofa cushine . Saurin miƙewa tayi dama a ɗaɗare take , tana nufar kujerar tare da ƙwanciya ba ko abun rufa . A hankali yake bin ta da kallo , murmushi n mugun ta yayi ganin yanda duk ya sauya masu ƴar mutane ,tamkar ba ita ce tazo da shegen surutun nan ba ,da firi firi. Nufar fridge yayi yana ɗaukar ƙwalban barasar shi tare da cup yana isowa bakin gadon , Umaima na jin shi yana ta ƙwalɓewa a haka barci yayi awon gaba da ita .
***
Ashiru ne tsugune gaban su Baba Ibrahim da Baba Sule , Abunka ga dattawa su ne da ƴar ta ɓata ,amma sai suna bai mawa saurayin Umaima haƙuri ,ko nace mijin ta wanda suke mata fatan zama mata a gare shi . Don har iyaye sun shiga ciki ,dama a cewan su sun bari Umaima ne ta ƙara hankali sai a tsaida auren nasu . Don tun ranan da Ashiru yazo ya bayyana mata abun dake zuciyar shi ya zama mata abokin gaba . Kullum ko a hanya ta ganshi zata zage shi ta uwa ta uba. Aƙwai lokacin ma da ta sanya ƴan makarantan su yin dandazo tasa kowa ya dauki dutse , ashirin da abokin shi na zuwa wucewa dama hanyar makarantar hanyar bin sa ce sosai ,nan suka hau jifan su da wannan duwatsun , wani ƙaton dutse da ya sauka akan Ashiru ƙwal nan Umaima ta juya makaranta tana dariya har da hawaye . Abokin ne da bai san dawar garin ba yace shi sam bai yarda ba ,nan Ashiru yayi ta bashi haƙuri ,daƙyar dai ya haƙura suka tafi .
***
Wuraren ƙarfe biyu na dare ne Umaima taji an ɗaga ta cak , ana nufar saman bed da ita , cikin sauri idanun ta ya buɗe , kallon Umair take da har a lokacin Mayen bai gama sakin sa ba. Ƙwanta nan Ni Bara na ƙwanta a sofa , kin wani takure jikin ki , ba zaki iya cemun na baki abun rufa ba ?. Shiru tayi tana duƙar da kanta don jikin ta rawa yake yi. Ki saki jikin ki babu abun da zan maki Yanxu sai da safe Kamin na tafi asibiti , dole sai nayi ko kina so ka Bakya so.!
*H*
*Littafin THE SEXY BOSS na kuɗi ne ban yarda ki karanta mun ba tare da kin biyani haƙƙi na ba... Regular group ₦300...Vip group₦500... Special ₦1000 via 6037312299 Mohammed Aisha keystone bank ko kuma ki tura katin MTN ta wannan number 08081202932 Idan VTU transfer zakiyi ki tura kai tsaye ta wannan number 09061466409*
RAMCY HERBAL💃💃Tabbas da kaji wane ba Banza ba , wani kaya sai amali , rugun babban motsi , margamargan dutse kafi gaban Aljihu ,wannan nima kaina da baki na na faɗi haka yake🤞. Ina kuke ƴan Uwana manyan mata ,shin kuna ina?💃 Matso kusa ga babban dama ta samu daga hannun wannan shahararriyar ƴar mutan Sokoto RAMCY HERBAL ta shirya tsaf don kawo mana magunguna da dama meye matsalar ki Amaryar Oga??
Uwar gidan Alhaji kefa? Maza saurara kiji wannan magunguna daban ne da saura daga taskar ƴar mutan Sokoto .
-Maganin ƙanƙancewar gaban ɗa namiji
-Maganin sanyi na mata da na maza
-Gumbar riɗi , gumbar aya ,gumbar ƙwaƙwa , gumbar dabino.
-Zumar ni'ima
-Zumar ƙiba
-Zumar goran tula
-Dambun ni'ima
-Zumar ƙwakwa da ta dabino
-powder hip up Dana breast elargement .
-tsumin ƴar gata
-Tsumin tabaje
-Maganin ciwon sugar
-Maganin hawan jini
RAMCY HERBAL ba anan ta tsaya ba , ta kuma taho mana da kayan gyarar jikin mu...💃💃
-Dilka Soap
-Whitening Cleanser
-malato soap
-Half cast soap
-shu'umin Humra tare da turaruka masu ƙamshi ,da zai rikita Oga in a few sec.
Ga masu buƙatar ƙarin bayani maza hanzarta ku tuntuɓi wannan number 07032209881 / 08109511467 .
Address: Sabon titin sokoto rima , kafin wajen sha'aban mai kankana mun gode.!
"Shiru Umaima tayi masa tana kallon gyefen ta ,don zuciyar ta ɗar ɗar take dashi a wannan tsohon daren , tunanin ta da tsoron ta kar yazo a kuma abun da akayi . Oya sleep . Yanda taji yayi maganan cikin sanyin murya wanda bata saba jin irin ta daga bakin shi ba yasa ta saurin ɗago da idanun ta tana sauke su a saman nashi . Ganin yanda ya kafeta da tsayayyun lulun idanun sa yasata komawa a hankali tana ƙwantawa . Blanket ya rufa mata , kana yace " Good night . Ganin ya miƙe yana nufan sofa ɗin yana ƙwanciya yasa ta lumshe idanun ta , a zuciyar ta tana cewa " Wannan wani irin juyayyen mutum ne? . Addu'oi tayi sosai tare da neman hirji kar ya matsota da haka barci yayi awon gaba da ita .
Ɓangaren Umair kuwa dama yace zai ƙwana a sofa ne ,saboda yasan idan yace tare zasu ƙwana a gado ɗaya sam ba zatayi barcin ba ,kuma magungunan da ya bata aƙwai wanda take buƙatar barcin sosai ,wannan yasa shi yin hakan . Duk da shi ba ma'abocin barci da dare bane , kullum yana cikin bincike akan kasuwancin shi ,da kuma research , amma a yau jin sa yayi barci nannauya na kama shi . Wannnan yasa shi miƙewa tare da nufar bed ɗin yana ƙwanciya a gyefen ta. Jin saukar numfashin ta yasa shi furtawa a sarari" Ji yanda take munshari ,wannan nan gaba ƙiban ta ya zai zama kenan?. Hannun sa yasa yana ɗago hannun ta ,da suke cure gubur guɓurr . Murmushi yayi yana rungumo ta jikin shi a hankali yanda ba zata tashi ba , tare da mata pillow da faffaɗan ƙirjin shi . Hannun shi ya ɗaura yana shafa saman gashin kan ta , wanda a cewan shi , Abubuwa biyu ne take dasu masu ƙyau , Daga daɗin durin ta ,sai wannan gashin nata da suka sauka har gadon baya kaman baƙar balarabiya . Fuskar ta ya shafa yana faɗawa tunanin waya turo Umaima wurin sa? A sarari ne ya furta , bata da ilimin da za'a turo ta wurina don basajar naɗar sirrika na , indai ko wani ne ya turo ta wurina to ya cika shashaa marar hankali . Da wannan tunanukan iri iri ya barci yayi gaba dashi...
Ƙarfe Hudu na subahi ya tashi , Juyawa yayi yana kallon inda take ƙwance jikin sa ta ƙanƙame sa ƙam. Hannun sa yakai yana ƙara hasken Gloves ɗin , kana yayi ma fuskar ta ƙurrr yana nazarin ta yanda zai raba jikin shi da nata ba tare da ta tashi ba. Sauke ƙafarsa yayi yana raba ta da jikin shi cike da dabara . Jin maganan ta yayi cikin sambatu irin ta masu barci tana cewa " Umma kar ki tashi ,sanyi ,ki bari a shiga Masallaci. Murmushi yayi yana daɗa rufeta da bargo kamin ya miƙe yana nufar toilet. Kaman yanda ya saba nafila yake zaman yi tun daga wannan lokaci har zuwa kirar sallah ta biyu haka ma yau ta kasance . Bayan ya gama sallah subahi ne ya nufi Laptop din sa yana buɗewa yana fara aiki da ita . Sakon Bin ciken da yasa akayi ne akan Umaima Yaga har an turo masa . Saurin shiga yayi don ya ƙagu yasan waye ya turo ta. Amma sai dai kashh duk abun da yake tunani ba hakan ya gani ba. Har Son kuɗin Umaima a layin su da yanda aka ɗauke ta tafi kowa ilimi sai da Aka Turo masa a makaman labaran. Wato san kuɗi ne ya 'sata shigowa koma ta a ƙaikaice kenan.? Murmushi ya bige da yi don komai nata da ya gani abun dariya ne ma a gare shi . A hankali ya fara tuno the first time da suka fara haɗuwa , lokacin da take matsowa gare shi da kararrafin turancin ta , My names are...heeyy hee it's ok it's ok". Ya tuna Sanda ya katse ta .
Murmushi yayi tare da girgiza kai ,maida laptop ɗin yayi yana Rufewa tare da miƙewa yana takowa zuwa gaban bed din da har alokacin take sharar barcin ta . Laɓɓan ta ya kalla , wanda duk da kasancewar ta baƙa amma saman su pink ne ga bakin ta ɗan mitsulu , a zuciyar sa ne ya furta " Sai rashin kunya ta aje . Kin haɗu da