Showing 24001 words to 25209 words out of 25209 words
Chapter 9 - RAYUWAR MAKARANTA FREE BOOK BY ZAHRA ROYAL.txt
harda su fitar da munshari.
Dai-dai inda Nahna zata taka idan ta tashi ta zuba man gyad'an, tana gama zubawa ta rufe robar ta maida kitchen. Koda ta dawo toilet ta shige kawai tayi wanka da sauransu. Bayan ta gama ta shirya ta d'an zauna tana jiran tashin Nahna da ta hakimce akan gado.
Can ko sai gata ta mik'e tana sakin hamma harda wata mik'a ta saki tana bin Hauwa da wani kallo na uku saura kwata.
Murmushi kawai Hauwa ta sakar mata, wadda yasa Nahna saurin tsarguwa. Anya ba wani abu Hauwa ta shirya mata kuwa?, take tabbayar kanta.
Girgiza kai tayi kawai ta mik'e domin nufar toilet, sai dai taku d'aya biyu tayi, tayi taga-taga zata fad'i ihu ta saki tana son kamu wani abu karta kai k'asa amma ina ji kike rigijahhh, ta fad'i wani marayan kuka Nahna ta saki da ihu tana saurin dafe k'ugunta daya bugu sosai harda k'afarta ta dama.
Mi Hauwa zatai idan ba dariya ba, sai da tayi son ranta kamin ta mik'e ta fice ko ci kanki bata ce ba bare ta ce mata sannu.
Tana fita Nahna ta kai dubanta a inda take zaune, hannunta ta d'ago jin wata lema-lema a inda ta fad'in. D'an murja hannunta tayi jin maik'o a hannun nata, ganin mai ne aka zubar a wajan, yasa Nahna sakin tsaki tana rik'e baki a fili ta ce.
"Wato dai Hauwa ta gane abunda na yi mata kenan jiya?, shine itama ta rama yanzu kenan?. Idan fa banyi da gaske ba wannan aljanar yarinyar sai ta kassara ni, gara na yarda muka man yak'i na, na rabu da ita harta koma inda ta fito shegiyar kamar aljana wallahi"
Ta k'are maganar tana dafa bango ta mik'e da kyar tana yatse ne baki wata y'ar k'ara ta saki, tana dafe k'ugunta had'e da runtse idonta, tana jin yadda k'ugun nata ke mata wani zafi.
K'afar tata ma da kyar take dangyasa ta, da kyar ta lallab'a ta shige toilet tayi wankata ta fito domin shiryawa.
Tana cikin shiryawa taji wayarta na k'ara alamar kira. D'an kallon wayar tayi, wayar da da kyar aka bar mata ita, k'arama ce, y'ar ta rik'ewa a hannu.
Ganin Aunty Lubna ce ke kiran yasa tayi saurin d'auka, domin suna shiri sosai da Lubnar.
"To Aunty insha Allah dana gama breakfast zan tahu gidan naki"
Abunda naji Nahna ta fad'a kenan ta sauk'e wayar.
A k'asa ko Hauwa na zaune su Abba da Momy suka fito.
Momy ta kalli gidan yadda yayi tsaf dashi sai tashin k'amshi yake ta ce
"Wow Mashaa Allah, hala D'iyata ke ce da wannan gyaran ko?, nasan dai wancar malalaciyar bazata iya wannan aikin ba"
Murmushi ta saki tana cewa
"Momy ina kwana fatan kun tashi lpy?, Abba ina kwana?"
Cike da kulawa Abba ya amsa.
Ta k'ara kallon Momy ta ce.
"Eh Momy amma harda itama mukayi ai, har breakfast ma mun gama tun d'azo"
Kan darning table d'in suka nufa Momy na cewa.
"Ke Hauwa ki fad'a min gaskiya?"
Murmushi kawai Hauwa tayi tana zuba masu abunda ta girka.
Itama ta zauna suka fara ci a tare.
Zuwa can sai ga Nahna ta sakko anyi wanka anci gayu.
Zama tayi akan Darning table d'in tana gaida su Abba da Momy.
Momy ta kalle ta tana cewa
"Ke kuma wannan gayun fa?"
Sosa kanta Nahna tayi tana cewa.
"Momy dama Aunty Lubna ce ta kira ni, wai tana so naje gidanta yau"
Tab'e baki Momy tayi tana cewa
"To zaki je, amma keda Hauwa zaku tafi"
Da sauri Nahna ta ce.
"Nida Hauwa kuma?"
"Eh ko baza'a je da ita d'in ba?"
"A'a Momy ni ban ce ba"
Nahna ta k'are maganar had'e da d'an sosa k'eya, ganin wata uwar harara da Momyn ta aika mata da ita.
Hauwa zatai magana Momy ta d'aga mata hannu ta ce.
"Ke ma kimin shuru, idan har ba so kike na soke mata tafiyar nan ba gaba d'aya, dan har in ba tare zaku je ba, to wallahi itama bazata je ba"
Abba dake zaune ya ce.
"Idan sun tashi tafiya Isa driver ya kai su mana shikenan"
"Eh dama shine zai kai su, ya dawo da su kuma"
Momy ta k'are maganar had'e da mik'ewa a tare ita da Abba, har waje ta rakasa domin zai wuce Company.
Tana dawowa zata haye sama ta ce.
"Idan kun gama ki kira Isa driver ya mik'a ku, saura kuma kije kisa ku kai dare kinji"
Nahna da ta ji haushin zuwa da Hauwa ta ce.
"A'a Momy baza mu kai daren da baki so ba insha Allah"
"Yayi kyau"
Kawai Momy ta ce ta haye sama.
Tana barin wajan Nahna ta watsama Hauwa wata uwar harara tana zuba abincin ta fara ci, tana sakin tsaki.
Dariya Hauwa ta saki tana mata haibaice tana cewa.
"Ohhhoo dai a haka za'a ganni a barni, zama dani dole, K'anwar nak'i, ko ank'i ko an so"
"Hmmm tsmwww"
Kawai Nahna ta saki, danta yima kanta al'k'awarin bata sake tankama Hauwa, karta sake mata wata muguntar ta nakasata a banza, yanzu ma da kyar ta lallab'a ta sakko karsu Momy su gane ta fad'i, da kyar ta d'aure har sai da ta gasa jikin nata bare k'ugunta inda ta bugu.
Hauwa ta fara tashi tana niyar barin wajan suka ji k'arar kiran waya, kallon wayar sukai a tare ganin wayar Momy ce ta bari akan Darning table d'in, ganin sunan Inna yasa da sauri Hauwa ta mik'a hannun ta d'auki wayar.
Kiran ta d'auka da zumud'i tana k'arawa a kunnanta.
Dai-dai lokacin Kuma Abdallah ya shigo parlon.
Abunda aka fad'a a cikin wayar ne yasa ma Hauwa sakin wani dogon salati, had'e da sakin wayar jikinta na d'aukar rawa, wasu hawaye suka fara mata zarya, jikinta ne ya k'ara d'aukar rawa, ta tafi luuuu zata fad'i, da mugun sauri Abdallah yayi tsalle ya tarbeta a jikinsa, nan take ta zube a jikinsa a sume.
Nahna ta mik'e tana zare ido hankalinta yayi mugun tashi, daga ita har Abdallahn.
Miye aka gaya ma Hauwa ne da ya sa ta shiga wannan hali?.
Jikin Nahna har yana rawa hannunta na kyarma ta mik'a hannunta domin d'aukar wayar da Hauwa ta saki a k'asa, Abdallah ya rigata kai hannusa ya d'auki wayar.
Har yanzu Hauwa na jikinsa a sume, hankalinsa a mugun tashe yake ya ma kasa kara wayar a kunnansa, sai magana ake daga cikin wayar ga dai sunan Inna sun gani, amma ga muryar namiji na fitowa daga cikin wayar.....
*To aka ce laifin dad'i k'arewa, a nan na kawo k'arshen Free pages, har yanzu masoya ba'a fara komai ba, a wannan book d'in, yanzu ne ma tafiyar ta soma akwai rikice a gaba. Shin miye ma aka gaya ma Hauwa ne daya sata suma haka?, wai tsayama mi zai faru idan aka sanar da Hauwa akwai auran Abdallah akanta ne?, wacce irin rigima za'ai idan Lubna tasan Abdallah nada mata a wani wajan, kuma y'ar uwarsa ta jini?, kaiii jama'a akwai fa kallo, akwai rigima akwai sark'ak'iya, akwai sauran kallo, akwai sauran rikici wadda zato bai zata ba a wanga book. Ku dai kawai masoya book d'in RAYUWAR MAKARANTA mu had'u a paid book insha Allahu*
Hi Masoya book d'in RAYUWAR MAKARANTA, karku shagala da yawa fa, domin book d'in RAYUWAR MAKARANTA yanzun ne tafiyar tashi ta soma, na kud'i ne akan raina d'ari hud'u ne kacal #400, zaka iya turo kud'in ka ta wannan account number d'in.
π
8130479973 Fatima Rabi'u Opay bank.
Sai ka turo shaidar biya ta wannan number d'inπ08130479973