Showing 18001 words to 21000 words out of 25209 words

Chapter 7 - RAYUWAR MAKARANTA FREE BOOK BY ZAHRA ROYAL.txt

na mari banza, domin da baki tab'a min uwa ba, da bazan mare ki ba, ki sani iyaye ba abin wasa bane, daga yau ki sake tab'a iyayen wasu, wata k'ila ni na miki da sauk'i, akan abunda zaki tarba a gaba, idan kika tab'a Iyayen wasu, ki iya bakin ki Malama, kije gida a koya miki tarbayar iya magana, da alama har yanzu akwai rashin tarbiyya a tare da ke, akwai kuma ciwon hassada dake d'awainiya dake, to shi dai ciwon hassada cinye aiki yake dan haka Malama Hafsa kike ko wacece ma dai sai a taka a sannu"


Tana gama fad'ar haka ta rab'a ta gefanta ta wuce tana ce ma su Atu


"Kai please ku taho mu je, domin kun san ana Jira na a gida yau zamu wuce Kano, ni kad'ai suke jira, karma wannan mugun ya gaji da Jira na naje yayi min wata muguntar tashi"


Bin bayanta sukai suna mamakin Hauwa a yau, domin sun san da y'an jan fad'ar na kai da yau Hafsat ta ci ubanta har da Uwar.


Asiya cike da takaici ta dubi Hafsat dake had'iyar zuciya kamar zata mutu haka take ji tsabar haushin kanta da take ji, da tsanar yarinyar can Hauwa.


"Sai da na ce miki kwata-kwata bai kamata ki tare ta a nan ki ce zaki ci mutumcin ta ba, da kin bini a sannu zan gano mana hanyar da zamuyi maganinta, amma gashi ta baki kunya a gaban jama'ar makarantar nan, kin b'ata abun wallahi".


Kuka kawai Hafsat ta saki tana cewa.


"Ai wallahi bata ci banza ba, na rantse da Allah banzan yarda ba, saina rama wallahi. Amma yanzu mi kike tunanin zamuyi mata ne?"




"Karki damu, daina kukanki kawai ni nasan matakin da zamu d'auka, kawai ki bari a dawo hutu"


"Shikenan Allah ya kaimu a dawon"




Da haka suka ci gaba da tafiya
Suma.


Atu da Ammama ne har suna had'e baki wajan cewa.


"Amma gaskiya yau ba k'aramin birgeni kikai ba Hauwa"


Kallonsu ta d'anyi da mamaki kamin ta ce.


"Tofa yau kuma, to akan mi?"


Atu ce ta amshe da cewa.


"Kawai yau d'in ne kinyi aiki da hankali, bakiyi fad'an naki kamar yadda kika saba ba"


Dariya Hauwa tayi tana cewa


"Ai ko idan haka ne, karma kuyi saurin yanke hukunci, domin ba hankali nayi ba, idan ma shine kuke tunanin nayi, domin wallahi sa'arta d'aya su Momy na Jira na, zamu tafi Kano, amma da babu mai jira na a gida wallahi saina tsaya munci uban juna ni da ita, sai na nuna mata ruwa bafa sa'an gwando bane, har yanzu ina a matsayin Hauwar da kuka sani a'ato ba canzawa nayi ba"


Wani tsaki Atu taja tana tab'e baki ta ce.


"Ai dama ni na sani, ai barin hali sai mutuwa, Allah dai ya shirye ki"


Ammama ta amshe da cewa


"Ke ni fa ta wani b'angaran bana ganin laifin Hauwa, saboda mutane idan kana barinsu suna maka duk abunda suka ga dama, tofa ka bani ka shiga uku, amma idan kaja masu birki dole su ja su tsaya"


Da irin wannan firar suka rabu da juna kowacce tayi hanyar gidansu, suna cewa zasuyi miss d'in juna saboda hutun da akai, da hakan suka rabu.


Atu ce k'arshe zata bi layin gidansu ta d'an tsaya tana ce ma Hauwa.


"Y'an birnin Kano, a dai mana tsaraba please, kar a sake a dawo mana hannu rabbana a'ato"


D'an bugu ta kai mata a hannu tana cewa.


"Ke dai kika sani, tsaraba kuma banyowa"


"Karda Allah yasa kiyo jarababba kawai"


Dariya suka saki a tare cike da kewar juna suka rabu.


Hauwa na sayo kai d'akin Inna taji Y Abdullah na jan wani tsaki yana ce ma Inna.


"Wai Inna wannan yarinyar taki har yanzu bata dawo bane?, anya kwakwalwar yarinyar can ba tab'in hankali kuwa, kwata-kwata bata da natsuwa fa"


Wani kallo Inna take ma Abdallah, hannunta ta ware tana cewa.


"Abdallah Ungo nan, Jikar tawa ce mai tab'in hankali?, ka kiyaye ni Abdallah wallahi, kaga wancan wadda ya fita shin.....


Da sauri Abdallah ya tashi yana matsawa inda Inna take yasa tafin hannunsa yana zaro ido waje ya ce.


"Haba Inna, ya da haka Kuma, yi hakuri ba sai kin idasa ba, haba mai ran k'arfe"


Y'ar dariya ta saki tana harararsa ta ce.


"Ke ni sakar min baki ja'irin yaro kawai, yarinyar da Mat.....


Tashi yayi da sauri ba shiri yana toshe bakinsa yana cewa.


"Ni dai Inna sai had'uwa ta gaba gaskiya, na fita zuwa mota ina waje ina jiransu, idan sun shirya ta dawo, wannan magana da kike ta zarowa Inna, sauran wa'incan Yaran suji, suma raina ni"


Ya k'are maganar had'e da ficewa daga d'akin da sauri.


Inna ta d'aga murna yadda zaiji ta ce


"Da ka tsaya mana d'an rainin wayo"


Yana fitowa ya ci karo da Hauwa da ta gama jin duk abunda suke cewa, taso ace taji abunda Inna zata fad'a daga k'arshe, ta kasa gane ina maganar ta dosa, duk inda ta d'ora ta sai taga batai ba.


Allah ya so wannan karon basu yi k'aro ba, dan basa waje tayi ya wuce yana jefa mata wani kallo, ita dai tunda ta gaida sa bata k'ara gigin masa magana ba.


Nahna ta fito daga uwar d'akin Inna, tana wani lumshe idonta had'e da wani yatsine fuska ta kalli Inna dake dubanta ta ce


"Wai Inna ita wannan yarinyar bata dawowa ne haka, dole ma sai mun tafi da ita ne, a barta inda tafi wayo mana"


"Ke kinci ubanki yanzu nan wallahi, kaga ja'iran Yara, kowa ya taso Hauwa dai Hauwa dai, haba dan Allah ku barta ta huta mana ta shak'ata"


Zata k'ara magana Hauwa ta shigo ko kallon inda Nahna take Hauwa batai ba, sai ma wani siririn tsaki da Hauwar taja mata.


"Yawwa ga y'ar albarkar nan ma ta zo"


Momy da ta idasa sallar k'arfe d'aya saboda da tafiyar da zasuyi tayi sallarta, danta ga har sha biyu da rabi tayi, shi yasa kawai tayi sallar, dan sallar zata iya riskarsu kan hanya ne.


Ta fito daga d'akin tana cewa.


"Kinga NahNah zan sab'a miki, dallah tashi kije kiyi sallah kizo ki shirya muyita tafiya. Y'ata Hauwa kema tashi ki Shirya ko mun d'auki hanya, kar dare yayi mana akan hanya"


Da to Hauwa ta amsa ta tashi, ta shige, uwar d'aki, tana cire kayanta ta shiga toilet na cikin d'akin tayi wanka, tana fitowa ta shirya a gurguje tayi sallah, ta gama dama akwatinta har an kai sa mota. Itama kwata-kwata bata son tafiya tabar Innarta shi yasa yau d'in kwata-kwata bata wani jin dad'in yanayin.


Tana Jin sadda Nahna ta shigo tayi sallar itama, koda ta idar tana d'akin, nan ma ba wata magana sukai ba, ta rasa mi yasa basa jituwa da juna.


Komi Hauwa ta tuna jin muryar Abba ta fito da sauri tana cewa.


"Yawwa Abba, kasan na nawa nayo a school?"


"A'a d'iyata, yanzu nake cewa kina ina ne, dama abunda nake so na tabbaye ki kenan dama. Matso na gani Y'ar tawa na nawa Tayo"


Da saurinta Hauwa ta matsa da zumud'i tana damk'ama Abba report d'in nata.


Nahna da ta fito yanzu ta tsaki wani tsaki can ciki yadda ba wadda yaji ta tana maganar zuci.


"Yo na nawa zatai fa?, idan banda na k'arshen class, karatun k'auye har wani karatu ne"


Kamar Hauwa tasan miye Nahna ke kitsawa ranta. Ta d'an matso saitin da take tana kallon yanayin fuskarta yadda take wani tab'e baki tana b'ata fuska.


Tana jin lokacin da Abba ke cewa.


"Wow wow My daughter, gaskiya dole na baki kyauta domin kinyi k'ok'ari sosai ki ce first class fa mashaa Allah"


Abba ya idasa fad'ar haka cike da tsananin murmushi akan fuskarsa da murna, Momy ma amsa tayi tana yabawa sosai.


Hauwa dake tsaye kusa da Nahna a hankali ta d'an duk'a dai-dai tsawon Nahnar domin Hauwa ta fita tsawon k'afa ta ce


"Ohhh sai gashi kuma nayo abun kirkin da baki so ji ba, karfa kiyi tunanin makarantun k'auye abun banza ne, no ba'a nan take ba Aunty Nahna, idan mutum Allah ne ya basa kwakwalwa, to a ko ina yayi karatu bazai tab'a dakushewa ba, wannan daga Allah"


Da wani mugun sauri NahNah ta waigo tana kallon Hauwa da mugun mamaki. Ubanwa ya gaya mata zancan zucin da take yi ne, ko dai aljanu ne da ita?.


Hijab har k'asa Hauwa tasa tayi mata kyau sosai tasa ruwan k'asa.


Nahna zatai magana taga su Abba sun mik'e sunama Inna sallama gaba d'aya suka fita har Innar domin masu rakiya, har ita Hauwa sai ta take masu baya, dole tasa Nahna yin shuru ba dan ta so ba, itama ta bi bayansu.




Kamar yadda suka zo a mota d'aya haka Abba ya shiga gaba Abdallah na driving, sai Momy a baya da Hauwa da Nahna. Hauwa kamar tayi kukan rabuwa da Inna, amma ta d'an matse hawaye a b'oye ta shige mota, Inna sai tsiya take mata, wai dama so take ta tafi ta barta ne.............


*RAYUWAR MAKARANTA*






*©Zahra Royal Star*








Page 9






*No. 14 Audu Bako Way, Nassarawa GRA, Kano Nigeria*






A gajiye suka shigo gidan, dan haka suna shiga Parlon gidan, Nahna tayi saurin haurawa sama dan ko kallon inda Hauwa take batai ba.


Momy ta kalli Hauwa ta ce.


"Hauwa ki haura sama kema ki d'an watsa ruwa, kamin a fito cin abincin dare"


D'an yamutse fuska Hauwa tayi tana cewa.


"Nifa Momy dama Abba baiyi mana d'aki d'aya da Nahna ba wallahi, bana son abunda zai b'ata min rai"




D'an murmushi ta saki tana matsuwa kusa da Hauwa ta d'an dafa kafad'ar ta ta ce.




"Abunda yasa Abbanku ya had'a maku d'aki d'aya shine, tun kuna Yara dama ra'ayinku ba d'aya bane, Nahna ta cika rawar kai da yawa, ke kuwa kin cika rashin ji, halinku kwata-kwata bai zo d'aya ba, bama ku zama waje d'aya bakuyi fad'a ba, shine mu kuma nida Abbanku muka yanke hukuncin a had'a maku d'aki d'aya kowacce da gadonta, ko mun samu ku d'an had'a kanku, amma duk laifin na wajan Nahna, idan bata daina halin nan nata ba wallahi zan d'au mummunan mataki ne a kanta"




Da sauri Hauwa ta girgiza kai ta ce.




"Ko kad'an Momy karma kiyi mata komai, wata rana k'ila ta gane abunda take ba dai-dai bane, zan zauna a d'akin namu, amma....
Sai kuma tayi shuru.


D'an k'aramin murmushi Momy ta saki, tana cewa.


"Amma idan tayi miki ki rama, karma kiji kunyarta, ni na saki tunda ta riga ta zubar da girmanta, amma Hauwa kuyi k'ok'ari ku so junanku ke kuma idan tayi miki wani abun ki rink'a hakuri da ita kinji D'iyar albarka?"


Murmushi Hauwa ta saki itama ta haura saman tana d'aga kanta alamar taji kawai.




Momy ta bita da kallon tausayi, ita yarinyar tausayi ma take bata.


Abba daya dad'e a tsaye daga sama, ya sakko ta b'an garansu ya ce.


"Momyn Yara ko dai zan sa a raba masu d'aki ne?"


"No Karka raba masu please, nafi so su fahimci juna, su so junansu, bana jin dad'in rashin jituwarsu fa sosai"


Momy ta k'are maganar fuskarta ba walwala ko kad'an.




D'an murmushi ya saki yana kallonta ya ce.


"Ki daina damuwa kinji, ai Yara ne har yanzu, duka suka wuce shekara goma Sha hud'u, to nan gaba zasu daina ne insha Allahu"




D'an murmushin itama ta sakar masa ta ce.


"Hmm Yara fa ka ce?, shekara sha hud'u sune Yaran?, dama dai y'an shekara goma ne, sai na ce masu yarinta ke damunsu, idan basuyi hankali a yanzu ba sai yaushe?"




"Momyn Yara kenan, wallahi har yanzu Yara ne, yanzu fa suke shirin shiga JS3 fa karatun naso da saura ma, kofa secondry yanzu suka soma ta, ki bari kiga sadda Hauwa zata tare a gidan D'anki lokacin Zaki gane sun girma amma ba yanzu ba"




Da sauri Momy ta rok'o hannun Abba taja shi suka zauna akan kujerar parlo. D'an murza hannunsa tayi cikin hannunta tana kallonsa, kamin tayi magana ya rigata cewa.




"Ya dai Matar Abba?"


Ya fad'a da murmushi kwance akan fuskarsa, domin yasan abunda zata ce masa.


D'an turo baki tayi domin ita Momy indai a gaban Abba ne ji take kamar Yara suke har yanzun.


Murmushi ya k'ara fad'ad'a akan fuskar Abba yasa hannunsa ya d'an ja mata hanci yana cewa.


"Ke matar nan baki tsufa ne wai?, mi ya faru? fad'a min ina jinki"



"Kasan abunda nake so na fad'a ai"


"Noo fad'a min da bakin ki"


Sauk'e ajiyar zuciya tayi kamin ta d'anyi k'asa da muryarta tana cewa.




"Abbansu Hauwa, abunda nake so na ce shine, mi yasa Hauwa idan ta gama secondary bazata tare a gidan mijinta Abdallah ba?, idan yaso a gidan nasa sai tayi karatun na gaba please Abban Yara karka ce a'a"


Ta k'are maganar had'e da d'an k'ara murja y'an yatsun hannunsa dake cikin nata.


D'an sauk'e lumfashi kad'an yayi kamin shima ya ce.




"Ba wai nak'i bane, amma nafi so yarinyata tayi karatu sosai, bana so aje akaita matarsa ta nemi mai da ita shashasha, amma ya kike gani"


D'an murmushi ta sakar masa ta ce.


"Ko kad'an Lubna bata isa mai da Hauwa shashasha ba, shi yasa ma hankali yake kwance domin nasan halin yarinyata, bata barin ta kwana, bana shakkar zamanta tare da Lubna Abban Yara"


"Uhmmm"


Kawai Abba ya ce yana d'an zare hannunsa dake cikin na Momy ya d'an mik'e yana kallon saman silin d'in parlon, kamin ya ce.




"Abunda nake hangowa daban da naki, amma shikenan nima bana jinta, amma fa dole Y'ata ta fara karatu kamin ta tare a gidansa, bana so abunda zai kawo mata cikas akan karatunta. Sai nake ganin kamar karatun zai bata wahala a gidansa, kamar fad'an auran Abdallah a kanta zai iya kawo mata matsala a cikin rayu....


Da sauri Momy ta mik'e had'e da katse sa wajan cewa.


"A'a karka fad'i haka Abban Yara, kayi masu fatan alkhairi kawai Abban Yara, domin ni harga Allah na gaji da jiran gawar shano a wajan Lubna, domin wannan matar bata tsoron Allah, bana jin dan yanzu zata bari ta haihu, idan ka lura so take ma ta fara juya min Yaro, ni kuma wallahi bazan zuba ido na gani na kyale ba, dole ne na nemar masa mafita, hatta Yarinyata Hauwa bazan barta a haka ta shiga gidan Abdallah ba kariyar Allah a jikinta, dole ne nasa a rink'a sadaka a Masallaci ana sauk'e al'qur'ani mai girma, saboda mata na sanmu da zafin kishi, babu abunda wasu daga cikinmu bazasu iya yi ba, saboda kishi. Da zarar an sanar da ita babu haukan da baza tai ba"




Abba ya murmusa, ya fara hawa sama yana cewa.


"Hakane Momyn Yara, ki hawo sama ki d'an watsa ruwa akwai gajiya"


Bin bayansa tayi kamar yadda ya ce.




A b'angaran su Hauwa ko, tana shiga ta iske Nahna na shirya kayanta a cikin waduruf tana yi tana jin wak'a. Ganin ta shigo yasa Nahna tab'e baki tana binta da wani kallo.




Ko inda take Hauwa bata kalla ba bare tasan ma miye take.


A hankali ta matsa inda tata waduruf d'in take, had'e da gadonta dake gefen damarta, zama tayi kansa, kamin ta d'an mik'e da yake tana da kaya a gidan, sai kawai tasa akwatinta a cikin waduruf d'in bata wani fiddo kayan dake ciki ba, sai wadda ya zama dole zatai anfani dashi a yanzun.


Cire hijab d'inta tayi tana niyar tashi ta nufi toilet d'in d'akin nasu, kawai taji an jawota ta baya.


Da sauri take duban Nahna da tai mata aika-aikar.


"Ke kuma lafiya dallah can?"


Cewar Nahna.


Wani kallon uku saura kwata, Hauwa ta jefama Nahna kamin ta ce.




"Ban gane ba Malama, ina ruwanki dani Kuma?, wani abun nayi miki ne?, zaki wani zo da kwasassun k'afafunki ki wani jawo ni"


Wata uwar harara Nahna tayi ma Hauwa tana cewa.


"Gani nayi daga shigowarki, kin wani d'ibi hanyar toilet, kuma na tara ruwan zafi na, zanyi wanka, fatan dai ba Kashi za'a mana a toilet d'in ba ko?, domin dai nasan y'an K'auye ba abunda suka iya sai Kashi da cin tsiyar masifa"




"Hmmm"


Wani murmushin mugunta Hauwa ta saki, shi yasa a shirye tazo dai-dai take da Nahna wannan zuwan wallahi.


D'agowa tayi ta kalleta sama da k'asa tana nunata da yatsa ta ce.


"Au haka?, au ashe fa ku y'an gayu ne bakwa Kashi da fisari da tusa ko?, saboda kune shafaffu da Mai ko?, ki matsa ki ban waje na wuce Nahna"


Rik'e baki Nahna tayi tana cewa




"Keee ni kike kira da sunana gatsal haka kawai?"


"Au so kike na ce Aunty Nahna ko?, to kija girmanki tukunna sai ki dawo na ce miki auntyn, domin yanzu girma ya riga da ya fad'i, shi dama mutumci Madara ne idan ya zube baya kwasuwa"


Zata sake wata maganar Hauwa ta fisge hanunta ta shige toilet d'in, ta kuma rufe k'ofar toilet d'in da k'arfi.


Da sauri Nahna ta matsa bakin k'ofar toilet d'in tana cewa.


"Na rantse da Allah ki fito, karki tab'a min ruwan wanka na Hauwa, zanyi rashin mutumci wallahi"


Ko tak Hauwa bata sake ce mata ba.


Hakan ya k'ara hassala Nahna, sai b'ab'atu take a k'ofar toilet




Sai da Hauwa ta d'au lokaci sosai kamin ta bud'e k'ofar toilet d'in ta fito.


Lokacin da zata fito ran Nahna idan yayi dubu ya gama b'aci.


Bin ta tayi da kallon na tsananin mamaki, tashi tayi tsaye tana nunata da yatsa ta ce.


"Kan Uban nan kayyasa, au wankan kika yi da ruwan zafin da na tara?, ai ko baki isa ba wallahi"


Nan d'in ma ko inda take bata kalla.


Nahna toilet d'in ta shiga, can sai gata ta fito tana sakin tsaki tana cewa.


"Ai na d'auka wankan kike baki taran wani ruwan ba, da na rantse yau sai kin gane shayi ma ruwa ne"


Ta idasa maganar tana shegewa toilet d'in.




Murmushin mugunta Hauwa tayi tana d'an d'aure wani abu a leda tana yi tana cewa.


"Zaki ci ubanki ne yau wallahi, ke ce zaki gane shayin ma ruwa ne yau"


Zama tayi ta shirya a tsana ke ta shafa mai tasa kayan bacci, domin har bakwai na dare tayi da y'an minti na, shinfid'a abun sallah tayi ta gabatar da sallar da ake binta.


Tana sallame sallar taji ihun Nahna daga cikin toilet da sauri ta mik'e ba shiri sai kuma ta tuntsire da dariya tana tafa hannayenta tana cewa.




"Yanzun za'a fara wasan, ai dani kike zancan, duk wadda ya ci tuwo dani to miya yasha"




Tana rufe bakinta taga Nahna ta fito daga toilet da gudu sai soshe-soshe take tana buri a k'asa sai kiran "wayyo Allah na shiga uku na, k'aik'ayi ko ina na jikina, dan Allah ki taimaka ki sosa min wayyo na bani na shiga uku"




Mi Hauwa zatai idan ba dariya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login