Showing 12001 words to 15000 words out of 25209 words

Chapter 5 - RAYUWAR MAKARANTA FREE BOOK BY ZAHRA ROYAL.txt

sai wani kankanba suke suna wani shan k'amshi.


Ciki harda wata Hafsat da Asiya.


Atu ta kalle su tana tab'e baki, dan Allah ya sani Atu ta tsani mutum mai nuna girman kai da son asanin shi wani ne, su kuma ta lura haka suke nuna isa da wata yangar banza a cikin makarantar. Tab'o Hauwa dake hidimarta tayi, ita ko a jikinta ma.


"Wai ke tunda muka fara school d'in nan, baki lura da wa'incan su Hafsat d'in ba, sai jin kai da d'aukar kansu su wasu ne, baki lura bane?, dan naga basa ma shiga harkar y'an class d'in nan, sai mutum ya kai suke masa magana"


Tsaki Hauwa taja tana shirin magana Mlm Bahari ya kira sunanta.


A hankali ta mik'e ta fice gaban allon, y'an class d'in sai binta suke da kallo ganin yadda Mlm Bahari ke jifanta da murmushi.


Tana k'arasowa ya mik'a mata takardar yana cewa.


"Wow gaskiya kinyi k'ok'ari Masha Allah, da haka kike maida hankali a class ai da ba haka ba, kinyi k'ok'ari sosai, y'an class a tafa mata dan Allah"


Sosai aka d'au tafi, ita kam Hauwa d'an k'aramin murmushi ta saki ta amsa ta koma ta zauna.


Tana kallon su Asiya ta wutsiyar ido yadda suka bin ta da harara k'asa-k'asa.


Zama tayi tana cewa.


"Idan banda abunki Atu, ai basu tab'a shigowa gona ta bane shine yasa, ina nan ina jiran ranar da zasu tab'o ni zan nuna masu ko wacece ni"




Ammama data amshe takardar Hauwa tana murmushi ta ce


"Kaii ashe zamu ci wannan text d'in, duba ki gani duk abunda kika fad'a mana shine muka rubuta, kuma kinga kin cinye goma bisa goma fa Wow, ashe Hauwar tamu ba banza ba, kan nata yana ja"




Dariya Hauwa kawai tayi. Tabbas akwaita da wasa da jan fad'a, amma ta b'angaran karatu, baka tab'a cewa tama iya wani abu, sai anzo fagen exam's ko wani abu, nan ne zaka ga takardunta sunyi kyau sosai, dan ko a class bata cika idan Malamai sunyi tabbaya ta tashi ta bada amsa ba, a'a a wajan exam's ko text ne kake gane Hauwa tana da shegen k'ok'ari"




Atu ko murmushi itama tayi domin ita tasan Hauwar akwai kaii kawai dai bata nunawa saita kama ne.


*Asalinsu Hauwa*




Asalinsu Hauwa, iyayenta y'an katsina ne, Fulani ne gaba da baya. Inna su biyu ne ta haifa Rabi'u sai Nura Abba kenan, Mahaifin Hauwa wadda suke kira da Abbi. Abbinta mai kud'in gaske ne, sai Mahaifiyarta Hauwa'u, mace mai kirkin gaske, tunda ta auri Rabi'u basu tab'a samun haihuwa ba, har tsawon shekaru masu dama, har tsofa ya fara tasar masu, Mahaifiyar Rabi'u wato Inna, bata wani matsanta masa cewa ya k'ara aure ba, Abba ko shi ya riga Abbi aure shi yasa ya rigasa samun y'ay'a duk da haihuwar ta Allah ce, har D'an Abba yayi wayo wato Abdallah, Shuru kake ji, har Matar Abba Haj Nuriyya ta sake samun ciki, amma ta b'angaran su Abbi shuru, sosai Hauwa'u ta sake tada hankalinta, Abbi ne ke k'ara kwantar mata da hankali harda ma Inna, tunda Hauwa'u take bata tab'a ganin suruka mai kirkin Inna ba, da sanin ya kamata, domin harda ita ake sa baki domin tausarta da kwantar mata da hankali.


Lokacin da cikin Nuriyya ya shiga wata Tara, dai-dai lokacin ne kuma Allah ya d'orawa Hauwa'u wani ciwo, kullum da zazzab'i take kwana, tak'i kuma aje asibiti da ita, Inna ce tayi mata jan ido harda Innar aka tasa ta a gaba suka je asibiti, an mata gwajeje, sakamako na fitowa doctor yayi masu kyakykyawan albishir d'in cewa Hauwa'u nada shigar ciki na tsawon wata uku.


Wai wai wai karko so ganin irin tsananin murna da farin ciki da wa'innan ahali suka shiga, dan Abba da kansa yazo katsina aka had'a wata y'ar lifaya akaci aka sha.


Inna a ranar ta ce a bata Hauwa'u ta tafi da ita Rimaye, Mahaifar su Abba, ta tayata rainon cikinta.


Ba yadda Abbi ya iya shima ya tattara kayansa suka koma Rimaye kusa da Inna.


Kota ina Hauwa'u gata take gani kulawa ta musamman Inna ke bata, sai abunda take so take ci, da ta motsa kad'an Inna zata fara tabbayar Ina ne ke miki ciwo?, shi kansa Abba daga can Kano kullum cikin aike yake masu na kayan dad'i, duk da babu abunda suka nema suka rasa. Cikin Abba da Abbi baka tab'a gane wanene yama fi wani Dukiya, idan kaga gidan da suka gina ma Inna a Rimaye zakai mamaki, babu alatun duniyar da ba'asa mata ba, shi yasa koda Hauwa'u ta dawo garin da zama bata ji komai ba, saboda babu ce kawai babu a gidan Inna.


Bayan wasu kwanaki Nurriya ta haihu, Y'a mace, murna sunyi sosai inda Abdallah ne cikin Family yanzu dan har ya fara d'aukar wasu nauyi na Familyn nasa. Ranar suna akasa ma yarinyar sunan Inna wato Nana Khadija, suna kiranta da (NahNah).
Duk da lokacin Hauwa'u tana laulayi hakan bai hanata zuwa sunan Nahna ba, har kwana biyu sukai a Kano ita da Inna, suka dawo.


Cikin Hauwa'u na wahalar da ita sosai, wadda har Inna abun ya fara bata tsoro, domin idan suna zaune da Hauwa'u ta kama cewa


"Inna anya wannan cikin bana tafiya bane kuwa?, ki duba kiga kullum cikin ciwo nake, yau lafiya gobe babu"


Murmushin k'arfin hali kawai Inna tayi tana cewa.


"Kufa yaran zamanin nan, kun cika raki da yawa, mu zamaninmu duk ba haka mukai renon cikin ba, kema dan haka lafiya lau zaki sauka, baga y'ar uwarki nan ba Nurriya ta haihu k'alau"


Murmushin itama Hauwa'u tayi tana d'an gyara zamanta akan kujerar tsakar gidan da suka fito suna shan iskar hantsi, cikin nata yayi girma sosai haihuwa yau ko gobe, ta ce.


"Hakane Inna, amma kin san ko wacce haihuwa da kalar nata salon"


Ware y'an yatsunta Inna tayi tana kai ma Hauwa'u Dak'owa tana cewa.


"Ungo nan Hauwa'u, ke kin tab'a haihuwar ne?, ba sai yanzu ba, baki san ya take ba, dan haka kisa ma ranki salama insha Allahu lafiya sumul zaki sauka"


Inna ta k'are maganar cikin zolaya.


Dariya Hauwa'u tayi tana sa tafin hannunta ta rufe fuskarta, domin idan irin wannan wasan ne ta saba da Inna, idan ka gansu ka rantse da Allah ba suruka bace, kai ka ce uwa da Y'a ne.


Abdallah ya fara aikinsa ya zama cikakken mutum yanda yake koyar a wata makaranta mai suna School Of Hygiene dake cikin garin Kano, an basa babban matsayi, Abba ba dan yaso aikin ba, sai dan Abdallah ne ke so, Abba yaso yayi aiki a companynsa, amma ganin kota ina babu abunda Abdallah bayayi hatta aikin Companyn yana zuwa, kawai ya raba aikin biyu ne. A wata rana yaje shopping suka had'u da Lubna, D'iyar wani hamshakin mai kud'i ce itama, tunda ta d'ora idonta akan Abdallah Allah ya d'ora mata bala'in sonsa da k'aunarsa. Ta addabama rayuwarsa, har sai da ya amince da ita, aka kai maganar wajan manya, ba'a wani dad'e ba su Abbi sukai jagoranci aka d'aure auran, ba'a wani ja lokaci ba. Inda haka nan akai bikin Hauwa'u na gaf Hauwa'u haka ta d'aure aka gama hidimar biki, dan Allah kad'ai yasan abunda take ji, d'auriya kawai take. Anyi biki da kwanaki, halin Lubna wadda Abdallah bai san dashi ba ya fara fitowa fili, domin k'azama ce da ta sosai ta saba komai a gida yi mata ake, hatta gyaran gado bata iya ba, shi kuma Abdallah yafi so komai nasa ace matarsa ce ke masa shi, ba wai y'ar aiki ba, idan yayi mata k'orafi sai ta rink'a ce masa "yafa tuna ba y'ar Malam Shehu ya aura ba, da zata je tana masa bauta kamar wata jaka, to ita bafa mai aiki ya auro ba. Danma tana mugun shakkarsa domin ko a school d'insa baya d'aukar raini kowa ma ya sani, duk Malaman makarantar ana masu shaidar bin mata da son y'an matan tsiya amma banda Mlm Abdallah ya kame kansa, k'aryar yarinya ta ce ya tab'a mata wata maganar banza, babu fuskar ma yarinya da zata kawo masa raini, amma sai cikin gidansa, kodan taga gadon baccinsa ne, kuma bai d'auki y'ar aikin ba, sai dai ita Lubnar tasa aka samo mata daga gidansu, da kanta take biyanta duk wata, to amma wani lokacin y'ar aikin ba zuwa take ba, saboda itama akwai hidimomin Yara dake kanta, ta sake y'ar aiki yafi sai biyar duk batai dacen su ba, a haka dai da kyar ta sami wata y'ar yarinya, tun wata rana da ta kama yarinyar wai tana kallon mata Miji tana jifansa da murmushi, wai harda cewa tana kashe masa ido, shi a lokacin ma Abdallah dariya abun ya basa, ko wacce y'ar aikin da zata samo tsabar zargi da rashin yarda suke rabuwa da y'an aiki da yawansu, kwata-kwata bata son wata Y'a mace ta rab'i mijin nata ko misik'ala zarratin.






Ranar wata Litinan, Hauwa'u ta tashi da nak'uda, ranar su Inna sunga tashin hankali, wadda basu tab'a gani ba, domin suma Hauwa'u ta rink'a yi tana rik'e da cikin nata, ba abunda take sai Addu'a a bakinta, domin Inna tana ganin yadda cikin Hauwa'un ke juyawa kamar D'an dake cikin nata zai fasa cikin ya fito duniya, tsabar yadda fatar saman cikin ke juyawa.


Hankali a tashe Abbi ya d'auke su sai Katsina suka nufi asibiti, kamin su isa Inna ta d'auki waya ta kira Abba dake Kano shima hankali a tashe a ranar, duk da Yamma tayi, haka ya tasa Abdallah gaba da Haj Nuriyya suka taho Katsina, da Abdallah ya gaya ma Lubna sai cewa tayi Allah ya tsare ita fa ba zata wata katsina ba, yaji mugun haushin abunda ta ce, dan kawai suna sauri ne, hankalinsa kuma baya gareta yau da ya bata mamaki wallahi.




Sadda su Abba zasu iso Hauwa'u ta wahala iya wahala, dan har Abbi yasa hannu za'a shiga da ita tiyata, a ciro abunda ke cikin nata, Inna ba abunda take sai kuka, zuwan su Abdallah nema yasa Abdallahn rarrashin Inna, yana kwantar mata da hankali, Inna ta lura da babu Lubna a tafiyar, taso ta ce wani abu, to amma ganin hankalinsu ba'a kwance yake ba yasa kawai ta shanye maganar. Shi ko Abba wajan Abbi ya nufa shima yana basa baki, Momy (Haj Nuriyya) itama ta kasa zama sai zarya take, ga Nahna dake hannunta yarinyar sai wani irin kuka take kamar wacce ake zarema rai, ta rasa inda zata sa kanta, kukan yarinyar duk shi ya k'ara rud'a masu tunani, domin har Inna sai da ta amshe ta amma yarinyar nan tak'i shuru kamar wacce ake mintsini.




Ana gaf shiga tiyatar Hauwa'u da aka turo akan gadon asibiti ta ce ma doctors su d'an dakata.




Kamo hannun Nurriya Hauwa'u tayi tana kallon Abba da Abbi tana cewa.


"Ba lallai idan an shiga dani tiyar nan ba na fito da rai na, ina rok'on wata alfarma a wajanku?"


Da sauri Inna ta k'ara rik'e hannun tana cewa.


"Haba Hauwa'u ki fad'i komiye a wannan duniya kike so ayi miki kamar anyi an gama insha Allahu"


Murmushi mai ciwo Hauwa'u ta saki, tana k'ara jan lumfashi, da take fitarwa da kyar, ga wata irin zufa da takeyi cikin k'arfin hali ta ce.


"Ina so idan mace na haifa, dan Allah Abba da Abbi ku aura ma Abdallah ita"


Ta waiga inda Abdallah yake zaune kansa a k'asa idonsa sun kad'a sunyi jawur, saboda yana bala'in son Hauwa'u, domin sun shak'u kamar ita ce ma ta yaye shi tun yana yaro yake zuwa katsina ya dad'e a wajanta.


Ta mik'a masa hannunta ya taho a hankali ya rik'e hannun nata, da ta cire sa daga hannun Nurriya ta rik'e na Abdallahn.


Ta ce
"D'ana nasan zaki rik'e duk yarinyar dana haifa da daraja, dan Allah karka bari tayi kukan maraice, koda ace namiji na haifa karka bari yayi kukan rashin uwa kaji D'ana"


Wasu hawaye ne suka soma gangaroma Abdallah, dole tasa doctors tura gadon da take da sauri aka shiga d'akin tiyatar da ita, saboda ganin yadda jikinta ya d'auki wata irin jijjiga.


Inna zubewa tayi a wajan tana kuka marar sauti, Momy ma idonta sunyi jawur ga Nahna dake kuka kamar wacce aka gaya ma miye zai faru.


Bayan tsawon awa biyu doctors suka fito suna share zufa, hannun wata Doctor rik'e da jinjiri a hannunta wadda aka nad'e da farin tawul.




Da mugun sauri su duka har suna rige-rigen tabbayar Ina Hauwa'u take, ko wanne tabbayarsa ita ce ina Hauwa'u take, basu damu ma da abunda aka samu ba.


Doctor cike da tausayin wa'innan ahali da kyar ta iya bud'e baki ta ce.


"Sai hakuri, dama tun kamin ma mu shiga tiyatar da ita Allah ya amshi abunsa, tiyatar ma babu ranta mukayi mata, domin munga abunda ke cikin nata har lokacin yana motsi, shine yasa kawai muka ceto abunda ke cikin nata. Gata nan Y'a mace ce aka samu"




Doctor na rufe baki Inna ta zube a sume, wani irin salati suka saka a tare, da gudu wani Doctor ya matso da gado aka sa Inna aka yi d'aki da ita. Ya tsaya yana ma Doctor d'in data gaya masu mutuwar fad'a yana cewa.




"Danmi zata tsaya haka ta gaya masu mutuwa haka, ai ba'a sanar da mutuwa a tsaye haka, bare da irin su Inna a wajan", hakuri ta rink'a basu tana mik'a masu d'iyar.


Abba ne ya amshi yarinyar, Abbi ko duk ya zama kamar zararre yana tsaye ne kawai hawaye masu d'umi keta masa zarya akan fuskarsa.


Haka wa'innan ahali suka kasance a wannan rana cike da tashin hankali, da kyar Inna ta farka, domin sadda zata dawo hankalinta har ankai Hauwa'u gidanta na gaskiya, domin Abbi ne ya bada Umarnin haka, domin sunga alamar idan Inna ta tashi taga gawar Hauwa'u, ba k'aramin tashin hankali zata k'ara shiga ba.


Inna tayi kuka sosai, aka bata yarinyar data haifa ta rik'e yarinyar sosai tana kuka tana kallon fuskar yarinyar, kamar su d'aya da Hauwa'u, a hankali Inna ke sauk'e ajiyar zuciya tana rungume da yarinyar.


Kwanan Inna biyu aka sallamota daga asibitin suka taho Rimaye, a nan akai addu'ar uku. Madara aka fara ba yarinyar, kawai domin babu wacce zata shayar da ita.


Tunda akai mutuwar Abbi bai sake lafiya ba, kullum cikin ciwo yake, sai ya rink'a wani tari wadda tun yana b'oye ma Inna harta fahimta, domin idan yana tarin har shid'ewa yake, jini na masa zuba ta baki ta hanci. A ranar da Inna ta ga wannan abu idan ranta yayi dubu Toya tashi, a ranar bata bari ba sai da ta kira Abba take sanar dashi, shima kansa Abba hankalin yayi mugu mugun tashi ba d'an kad'an ba.


Da kyar suka lallab'a Abbi aka tafi dashi k'asar India, domin duba lafiyarsa, daga Abba sai Abdallah suka tafi aka bar Inna da Momy a gida Nigeria. Ba irin surutun da Inna batai ma Lubna, domin taga yarinyar bata da tarbiyya ko kad'an, ai ko Inna ta d'au alwashin su Abba na dawowa daga India zata sa a d'aura auran Abdallah da Yarinyar da Hauwa'u ta bari, gara ayi tun tana da rai, gara ayi auran ko hankalinta ya kwanta, domin taga matar Abdallah kanta rawa yake akan mijinta.




Dawowar da Abbi baiba kenan da ransa a k'asar Nigeria, domin a can tun kamin su isa India Allah ya amshi abunsa.


Abba yayi kuka, yayi kuka, kamar ransa zai fita shima, ji yayi kamar zai zare tsabar tashin hankali, Abdallah ne mai k'arfin halin kiran Momy ya fara sanar da ita yana kuka, inda suka yanke kar a sanar da Inna har sai an dawo da gawarsa.




Kusan satin su biyu suna ciku-cikun yadda za'a dawo da gawar gida Nigeria, saboda sai da suka isa k'asar Indiar suka fahimci Abbi rai yayi halinsa tun a cikin jirgi.


Idan Inna ta kira waya a Bata shi sai dai ayi mata wata k'aryar ko bacci yake ko wani abu. Tun Inna na yarda har jikinta ya fara bata ba lafiya ba.


A ranar da zasu dawo haka Nahna ta rink'a wannan kukan kamar irin wadda tayi a sadda Hauwa'u zata rasu.


Lokacin da aka shigo da gawar Abbi a cikin gidan Inna, lokacin da Inna tayi tozali da Gawar tasa, sai Allah yasa mata wata irin dangana da juriya, amma kam taci kuka kamar mi, a ranar ta k'ara rik'e Yarinyar da Hauwa'u ta haifa, tana kuka cike da tsananin tausayin yarinyar da zata taso babu uwa babu uba.


Bayan anyi arba'in, Abba yaso amshe yarinyar wacce taci sunan Mahaifiyarta Hauwa, ya rik'eta a gidansa Kano, inda Inna ta murje ido ta nuna baza tab'a basa Hauwa'u ba, ita kad'ai take gani taji dad'i. Ba yadda Abba ya iya haka ya bar mata Hauwa, amma fa komai na rayuwa Abba bai bari yarinyar tayi kuka dashi ba, hatta dukiyar da Abbinta ya bari, shine yake juya mata ita, kuma bai bar garin ba sai da aka d'aura auran Abdallah da Hauwa, tun tana jaririyarta. Sosai yarinyar tunda ta fara tasawa bata jin magana kwata-kwata, ga jan fad'an tsiya, amma akwaita da shegen k'ok'ari kamar mi a makarantar Boko da islamiya, saboda tun tana y'ar shekara biyar ta sauk'e al'qur'ani mai girma.


A sadda zata gama primary taso akaita boding school Inna ta hana, saboda bata son abunda zai raba ta da Hauwa. Hauwa ko tasha kuka tana shagwab'ar Inna da Abba sun hana a kaita boding school, shine da Abba ya kira yana rarrashinta tak'i amsar wayar, tana turo baki, inda Abba yayi mata al'k'awarin sai siya mata Keke ko mota a rink'a kaita school d'in saboda yaga akwai nisa sosai makarantar daga cikin gari.




Ai ko Hauwa nan take ta ce ita fa bata son komai a barta ta tafi da k'afarta, bata son asai mata komai, ba yadda Abba ya iya ya hakura da sai matan, ba dan yaso ba, sai dan farin cikin Hauwar, domin duk abunda take so shine yake mata.


Tun kamin ta kai haka suka had'u da Atu, a makarantar Islamiya tare suke zuwa, da yake unguwa d'aya suke, layin gidansu ne kawai ba d'aya ba, sunyi mugun sabo da Atu wadda har idan Atu ta nuna b'acin rai ga wani abunda Hauwar keyi, take daina sa ba gardama, daga Atu sai Abba sai Inna kawai suke iya tankwasa Hauwa wani lokacin.


Kuma har yanzu Hauwa bata san da auran

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login