Showing 6001 words to 9000 words out of 25209 words

Chapter 3 - RAYUWAR MAKARANTA FREE BOOK BY ZAHRA ROYAL.txt

ba, idan ba'a tab'a ni ba ai bazan tanka ba, dan haka ki kama bakin ki kiyi shuru kawai yafi miki"


"Ai shikenan ina gudar miki ranar da zaki tab'o wacce tafi ki iya rigima ranar ta gurji baki babu abunda zanyi kuma ba"




Hauwa zatai magana kenan Malam ya shigo class d'in, dole tasa tayi shuru suna mik'ewa gaba d'aya suna gaisar dashi.




Har ya fara goge allo da kansa sai kuma ya juyo inda su Binta suke yana cewa


"Ina shugabar class d'in nan ta zo ta goge min allon nan?"


Nuna masa Binta akai dake rik'e da bakinta har yanzu yana mata wani zugi, daurewa kawai take.


Kallonta yayi sosai yana cewa


"Ke mike faruwa ne da bakin naki?"


Da kyar ta bud'e bakin maganar ma da kyar take yinta ta ce.


"Malam bigewa nayi da bango ban lura ba, shine yasa ya kunbura haka"


Daga can baya Hauwa ta saki wani murmushin gefen baki, tana duban Atu data saki baki tana maganar zuci. Wato kenan dai Hauwa taci bulis, yarinyar nan ta fara tsoronta.


"Allah ya shirya ki Hauwa"


Atu ta fad'a a hankali yadda ita kad'ai zata ji ta.


Murmushi ta saki itama tana ce mata.


"Amin idan da gaske kike"


Hararar wasa Atu ta maka mata kawai tana girgiza kanta, suka maida hankalinsu ga Malamin da yake ba Binta amsar cewa.




"Ayyah sannu fa, sai a rink'a kula daga yanzu, kije wajan y'an SS3 ki tabbaya ina Health take za'a nuna miki ita ki ce ta baki magani, zata baki"




Girgiza kai tayi da sauri domin bata son abunda zai had'a ta da y'an SS3 ita a yanzu ta ce


"A'a Malam idan naje gida zansha kawai"


D'aga k'afad'arsa yayi yana d'an tab'e baki ya juya ya ci gaba da lasin nashi.............


*RAYUWAR MAKARANTA*







*©Zahra Royal Star*






Page 3




"Dan Allah ki tak'o k'afa mu wace dajin nan, kinsa an tashi school mun biyo ta cikin daji haba dan Allah, kuma kin k'i kiyo sauri"


Cewar Atu dake tafiya da sauri, domin dajin tsoro ma yake bata.


Hauwa dake kallon wasu dondozen y'an mata su uku dake biye da su suna tafiya suna nuna su kamar masu neman rigima dasu yasa Hauwa d'an tsayawa tana cewa


"Kee tsaya dan Allah kamar fa Binta nake gani tare da wasu, miye take nufi ne, badai jawo wasu tayi ba domin su rama mata abunda nayi mata ba?"


Da sauri Atu ta waiga tana d'ora hannunta a saman kanta ido a waje take cewa.


"Shikenan mun shiga uku, yanzu miye kika ja mana ne haka?, da munbi su Hadiza da duk haka bata faruwa ba, da yanzu na sani mun shiga cikin gari ma"


Tsaki Hauwa tayi tana rik'e k'ugunta tana sake kallon y'an matan da suka k'araso kusa dasu yanzu.




Binta dake kallon Hauwa ta makama mata harara tana nunata da yatsa ta ce


"Yawwa anti Amina ita ce ta bige min baki a cikin aji babu uwar dana yi mata Kuma"


Wani kukan kura Amina tayi sai gata a gaban Hauwa tana k'ok'arin shak'o wuyan hijab d'inta tana cewa




"Kutumar uban miye tayi miki da har zaki fasa mata baki?"


Da sauri Hauwa ta matsa gefe hakan yasa hannun Amina bai kai jikinta ba, ta dubeta a wulakanci babu tsoro akan fuskarta ta ce




"Kinga Malama karki sake k'azamin hannunki yayi gigin tab'a min jiki wallahi, kuma na fasa mata bakin ko akwai abunda zaki yi ne a akai?"


"Jar ubancan kayyasa, ke Amina kika tsaya wannan k'aramar al'hakin take gaya miki magana son ranta baki ci uwar shegiya ba"


Cewar wata dage gefe mai d'an jiki domin da kyar take tafiya ma tsabar y'ar kibar da taima jikin nata yawa.


Atu dake gefe ta matso cike da tsoro ta ce


"Kuyiwa girman Allah kuyi hakuri, bazata sake ba nan gaba in..... Da mugun sauri Hauwa ta katse Atu da cewa.


"Kaiii amma dai Allah ya isa tsakanina dake wallahi, miye ruwanki a cikin fad'an nan, wa'innan zan ba hakuri? Ubangiji ya kiyaye ni, dan haka kiyi min shuru da bakin nan naki"


Hauwa na rufe bakinta Amina ta ribaceta ta duk'a ta kamo k'afarta kawai sai dai Hauwa taji anyi zama da ita an fyad'a da k'asa.


Ihu Hauwa ta saki tana sakin wata uwar kururuwa mai k'arar gaske, juye-juye ta farayi tana birgima a k'asa kamar macijiya, tana yi tana wasu surutai kamar wacce aljanu suka shafa.




Zaro ido su Amina sukai suna duban Binta cike da tsoro Amina ta koma gefe tana cewa.


"Mun shiga uku ke Binta ba dai mai aljanu kika kwaso mana ba, kinfa san ina tsoron mai aljanu?"


Binta da y'an cikinta ke kuka itama ta ce.


"Wallahi ban sani ba, yaufa suka fara zuwa makarantar"




"Shegiya amma shine kika bari muka haye masu da rigima haka kawai, baki gama fahimtar wace ita ba, ki ja mana masifa"


Cewar mai k'ibar cikinsu sai zufa take sharcewa ganin yadda Hauwa ke wata irin lankwasa kamar macijiyar gaske.




Atu dake gefe itama bala'in tsoro ne ya rufe ta duk d'aukarta ko aljanun gaske ne suka shigi Hauwar a yanzu.


Basuyi aune ba Hauwa ta mik'e ta rarumo Amina ta kad'a da k'asa ta haye ruwan cikinta ta fara kai mata yakushi a fuskarta kota ina.


Ihu Amina take tana k'arawa tana cewa.


"Wayyo Allah na shiga uku nah dan girman Allah kuyi hakuri na rantse banzan sake shiga harkar god'iyarku ba, ku yafe min dan Allah"


"Wuuyihohooo sai ni d'an gidan sarkin aljanu, ubanwa yasa ku tab'a min masoyiya Abar k'auna ta, yau sai kun gano duniyar aljanu yau sai kun d'and'a kud'arku wallahi"


Cewar Hauwa tana yi tana ihu had'e da lauyar da harshe kamar mai aljanun gaske, idan kaga yadda take baka tab'a cewa ba aljanun gasken bane.


Mai k'ibar nan ce ta daddage iya k'arfin ta banga je Binta dake nanik'e da ita ta zura da uban gudu ko waige bata yi, tana cikin gudu wani dutse ya tab'e ta, ta zube a k'asa rikijahh, ihu ta saki tana tashi da kyar duk ta ji ciwo a hannunta da gwaiwarta amma tsabar tsoro haka ta mik'e ta ci gaba da tik'a gudu kamar wacce mutuwa ta biyo.


Duk da irin halin tsoron da Atu take ciki hakan baisa ta kasa dariya ba, tana kallonta yadda take gudu da kyar.


Sai da Hauwa ta tabbatar Amina ta bugu iya buguwa sai kawai ta sauka kanta tana faman sakin tashiwa. Haba kamar jira take tana ganin ta sauka akanta, Amina ta mik'e duk da irin dukan data sha, ta fanska da gudu itama, ganin haka Binta ta take masu baya.




Hauwa na ganin sunbar wajan ta mik'e tana kakkab'e jikinta tana sakin wata uwar dariya har tana d'aukewa k'asa harda su kwanciya tsabar dariyar mugunta.


Kallonta Atu take cike da mamaki tana cewa.


"Wai tsaya ba dai aljanun k'arya kikai masu ba?"




"Ke duk zama da nake tare da ke na tab'a tayar da aljanu ne?, ai kema kin san banda wasu aljanu"




"To amma ke dai kam baki da mutumci wallahi, kinga Hauwa ki kiyaye kanki da k'arya irin wannan, sai na gasken sun shiga jikinki haka kawaii su shiga jikinki a banza, sufa ba'a masu haka wallahi in fad'a miki"




Da sauri Hauwa ta mik'e ta fara tafiya Atu ta take mata baya tana cewa.




"Kefa matsalata dake yima mutum mugun fata wallahi, yanzu miye nayi wadda ba dai-dai ba iyee?, baki ga mutanan data d'ebo min bane, idan na ce zan tsaya tofa jifgata zasuyi la'ada waje wallahi ai sarkin tawa yafi sarkin k'arfi, yanzu wannan rusheshiyar dana gani tare dasu idan ta haye ruwan cikina ai na shiga uku na, amma yanzu dana yi masu haka baki ga yadda suke gudu ba kamar wa'inda mutuwa tayi ma sallama"




Atu ta sauk'e ajiyar zuciya tana cewa.


"Tsakani da Allah Hauwa kinfi k'arfin kaina, kowaye ya shigo komarki ya bani ya shiga uku wallahi"




"Yo a'ato kinga laifi na ne?, idan ba haka kayi ba naga alamar bazaka zauna da kowa lafiya ba, yanzu da irin hakurin da kike badawa nayi masu ai da yanzu wata maganar ake ba wannan ba yarinya, gobe ma su sake shiga harkata, ke basu bama wallahi hatta y'an SS3 ko Malamai suka ce zasu k'ara min muguntar da bata gimshe ni ba mataki kawai zan d'auka da bazai masu dad'i ba".




Atu da d'an daka ta da tafiya tana cewa.


"Kinga Hauwa ina jiye miki ranar nadama, kinga ki rufa ma kanki asiri abun naki ya tsaya iya d'alibai kad'ai banda Malamai, D'aliban ma banda y'an SS3"


Wani uban tsaki Hauwa ta saki tana hararar Atu ta ce.




"Kefa baki da wayo wani lokacin, babu abunda zan fasa wallahi, su y'an SS3 uban waye su da baza masu hakan ba, mi yasa suke jifgar yaran mutane, so kawai nake su k'ara shiga gonata wallahi".


Har suka isa inda zasu rabu ko wacce ta wuce gidansu Atu bata k'ara magana ba, sai da Hauwa zata wuce ta santar gidansu taji Atu na cewa.


"Dan Allah gobe ki fito da wuri, dan wallahi bazan sake bari na makara ba, kisa nayi tsallan kwad'i ko wankin toilet, kin san dai bazan bari a dake ni ba, ki rufan asiri ki fito da wuri"


Da to kawai Hauwa ta amsa tayi gaba abunta.




Tana gaf shiga gidansu taji wani yaro ya kwashe da dariya yana kallonta.


Da mugun sauri ta kai dubanta gare sa a d'an mamakance take dubansa tana nuna kanta ta ce.


"Kai da ubanwa kike?"




Dariya yaron yayi yana nunata yana cewa.


"Wai kin ganki kuwa kamar wacce tayi birkid'a cikin k'asa wahoho ku dubeta kamar wata biranya"


Yara suka taro a wajan suna mata dariya.


Cije baki tayi tana ware k'afa tabi yaran da gudu tayi sa'ar cafko wadda ya fara janta fad'an.


Kwalar rigar yaron taci tana cewa.


"Yau ba abunda zai hana banci ubanka ba wallahi, kaga d'an iskan yaro, ni sa'arka ce iyee?".




"Ni ki cika ni na ce dan..... Wani uban bugu ta kai ma bakinsa wadda yasa shi ba shiri had'e maganar da yayi niyar k'arasawa.


Ta k'ara kai masa wani mari a fuska tana cewa.


"Naga ubanda ya tsaya maka a garin nan, daga yau idan ka ganni ka jani fad'a"




Kuka yaron yake sosai ta sake shi zata juya ta tafi taji muryarsa ya baza da gudu yana cewa.




"Kuma wallahi Allah saina gaya ma Umma ta, kuma Allah ya isa ban yafe ba"




"Ba uwarka zaka fad'amawa ba ko ubanka ne ina jiranku"


Ta idasa maganar tana idasa shigewa gidan nasu.


Inna dake d'uke tana wanke shinkafa ta kalleta rai a d'an b'ace ta ce.




"Da waye kuma kuke fad'a a waje?, wai ke dai kullum baki girma sai na jikin ki Fisbilillahi Hauwa?"


Zunburo baki Hauwa tayi tana zama akan wani banci tana kallon Inna ta ce.


"Inna kinfa san bana fad'a sai idan an tab'a ni ko?"


"Ke dan Allah ni rufe min baki, zaki tashi ki cire kayan makarantar nan kizo ki wanke so ko kuwa sai kin gama sani maganar da kika saba?"




Inna na rufe baki aka kwad'a sallama a k'ofar gidan, Inna na niyar amsa sallamar kawai taga mata rik'e da yaro a hannunta.


Inna ta dubi Matar jin tana cewa.


"Ina matsiyaciyar jikar taki mai jawo miki magana?, wannan y'ar iskar yarinyar ita ce zata zama ajalinki k'ila, tsabar masifar ta, Kuma wallahi sai an biyani kud'in maganin da zan je Kyamis na saima D'ana magani, kuma kiyi mata gargad'i karta sake tab'a min yaro wallahi, dubi kiga yadda ta fasa masa baki ya haye yayi suntum"




Tashi tsaye Hauwa tayi tana cewa.


"Kinga baiwar Allah shi yaron naki bai sanar dake irin abunda yayi min bane, ko kuwa kema irin iyayen nanne wa'inda basa ba Yaransu tarbiyya, daga gani Allah ba'a basu tarbiyya daga house ba"




Inna ta matso kusa da Hauwa bata ankara ba Inna ta gwafje mata baki tana cewa.


"Baiwar Allah dan Allah kayi hakuri hakan bazata sake faruwa ba, kuma kud'in magani ga naira d'ari biyar nan, ki sai masa maganin, amma shima yaron naki ki rink'a masa fad'a, bai kamata yana jan manya wa'inda suka girmesa ba"




Matar tana hararar Inna ta ce




"Kinga baiwar Allah bani kud'i kawai na wuce dan naga alamar baki son laifin jikar ki"


Inna ta k'ank'ance Ido na matsifa domin matar ta fara bata haushi yanzu ta ce.


"Bari na fito miki a mutum baiwar Allah idan baki ma D'anki Jan kunne ya daina shiga harkar Hauwa ba, to kuwa wallahi babu abunda zance mata, zan bari ta ci ubansa ta saita masa tarbiyya, tunda ke naga alamar baki tashi bashi ita ba"




"Au hakama zaki ce?"


"Haka na ce ko akwai magana ne?, bar min cikin gida, ko yanzu nasa Hauwar tayi min maganinku ku duka daga ke har yaron naki marar kunya"


Inna ta k'are maganar had'e da wurga mata d'ari biyar d'in. Ta duk'a k'asa ba kunya ta d'auke kud'in tayi waje tana mitar dama Inna ita ke d'aure ma Hauwa gindi take duk abunda take so a cikin garin nan.




Matar na fita Inna ta dawo da dubanta inda Hauwa take sai faman kunbura baki take.


Inna ta ce "wato Hauwa baza ki daina d'aukar min magana ba ko?, hala yauma a makarantar kin jawo min abun magana ko?".


"Nifa Inna babu maganar dana jawo miki a makaranta"




"Yi min shuru na ce, ai nasan halinki kad'an daga aikin ki, yanzu idan ba jan maganar ba, miye na daga dawowarki ki kama yaro ki mammake Fisbilillahi?, so kike ayita zagin iyayenki suna kwance a kabari basu ji ba basu gani ba haba Hauwa"


Turo k'aramin bakinta ta d'anyi tana bubbuga k'afa cike da shagwab'ar da Innar kawai take ma ita ta ce.


"Inna fa kin san bana jan fad'a haka nan kawai saifa anja ni"




"Ke dallah tafi can, to idan anja kin mi yasa bazaki iya hakuri bane?, ke bazaki iya hakurin zama da mutane ba dai ko?"


Inna ta sake cewa.


"Ai bari dai K'anin Ubanki ya dawo na gaya masa yayi min maganinki wallahi"




Da sauri Hauwa ta ce "dan Allah Inna kayi hakuri, karki sanar da Abba, kina ji shine ya hana a kaini makarantar kwana da yanzu na tafi ba mai k'ara kawo miki k'arata ma bare ace nayi wani abu"


"A haka kina uban rashin ji zai d'auke ki ya kaiki Makarantar kwana?, zab'ar baki da tunani ko, ai yayi min dai-dai abar min ke a nan yafi min kwanciyar hankali kina nan d'in ma walaAllah cika bare an kaiki Makarantar kwana, ai abun naki k'aruwa zaiyi, da ma dai kamar da makarantar kwanar take da sai na bari a kaiki, amma yanzu itama ta lalace kwata-kwata ba abunda ake a cikinta sai shashanci"............


*RAYUWAR MAKARANTA*








*©Zahra Royal Star*








Page 4






"Dan Allah kayi sauri Kinga k'arfe bakwai ta kusa haba Hauwa dan Allah"




Cewar Atu dake tsaye a k'ofar d'akin Inna tana jiran Hauwa dake shafa mai kamar wacce bata son tashi.


Inna dake jin radio ta aje radion dake hannunta ta kai ma Hauwa dak'uwa da hannu tana cewa.




"Zaki mai da hankali kiyi abunda ke gabanki ko kuwa?, Atun tayi tafiyarta ta barki. Shashashar yarinya kawai. Ke Atu da zaki biye ta tawa da kinyi tafiyarki kin rabu da wannan sharmammar wallahi, idan dan ita ne bata k'i kullum taja maku bugun makara ba".




Turo baki Hauwa tayi dai-dai ta idasa shafa man ta jawo Koko da k'osanta ta zata fara ci kenan, Inna ta warce farantin da aka zuba k'osan, tana cewa.


"Zaki tashi ki fara saka kayan makarantar ne ko so kike yanzu jikinki yayi tsami?"


Bubbuga k'afa Hauwa ta fara yi, ta mik'e tsaye tana d'an hararar Atu dake mata dariya k'asa-k'asa.


Inna ta kalli Atu tana cewa.


"Yawwa jikata, zauna ke ki fara cin k'osan kamin ta gama sa kayan"


Zama Atu tayi ta fara shan kokon, ba'a d'au lokaci ba Hauwa ta fito da jakar school d'inta had'e da Hijab d'inta a hannunta ta zauna kusa da Atu suna cin abincin a tare.


Hauwa ta d'akko k'osai zata sa a bakinta sai ta d'an dakata ta ce.


"Inna please ba dai Dankalin Hausa kika soya min ba dai ko?, kin san baci nake ba, ni ina wadda Abban Kano ya kawo min na turawan nan shine nake so"


Ta idasa maganar tana turo baki had'e da tusa k'osai a bakinta ta taune.


Inna ta d'an harareta ta ce.


"Ke ni ki mai da hankali ki ci abinci ko kun tafi, ga kular abincin can idan kinje makarantar kin gani"


"To Inna yaushe Abban Kano zai zo ne garin nan?"


"Son ganinsa kike ne?, ke da shekaran jiya ya kira ya ce a baki waya kika ce ke baza ki amsa ba, saboda bai kaiki Makarantar kwana ba"




Hauwa ta mik'e tana zare hannunta daga cin abincin da take tana cewa.


"A'a Inna nifa ina son ganin Abba, kawai na tsani zuwansa da Y Abdullah, dole ace idan zaizo garin sai dashi yake zuwa ni kuma na tsani wannan Y Abdullahn mugu ne fa"


Harara Inna ta makama mata tana tab'e baki ta ce.


"Kanki ake ji dai, da da kike cewa shine za'a aura miki fa"


"Subhanallahi Inna, haba Inna Fisbilillahi wane irin fatane wannan kike min?, Ina zan kai irin izzar Y Abdullah da jin kai irin nashi, kofa kallon arzik'i bai maka bare naje na aure shi, yo duka nawa nake ma ina zan kai Y Abdullah tab yanka ni zaiyi ya cinye nama na d'anye Dan.......




Inna ta katse ta ta ce "keee ni da'aAllah kimin shuru, kin cika zuba da yawa yarinya sai ka ce mai suna zubaida haba dan Allah, a haka Y Abdullahn zai soki kina surutun banza da wofi fad'i ba'a tabbaye ki ba?"


K'ara zunburo baki tayi gaba tana sa Hijabinta ta ce.


"Kefa Inna yarfa mutane gare ki Allah"


Ta k'ara kai dubanta inda Atu take tana tusa k'osai bakinta har yanzu bata idasa ba ta ce


"Ke kuma sai kiyi sauri kizo mu tafi mayyar k'osai kawai, yanzu duk zancan da nake yi hala ke kunnanki baiji bane hala?"


"Mi kike cewa?"


Atu ta fad'a tana mik'ewa bakinta cike da k'osai, sai da ta cinye sa tas, domin Allah ya sani tana bala'in son k'osai ba d'an kad'an ba.


Tsaki Hauwa tayi tana k'ara mata kallon banza ta ce


"Ba'a sani ba kinji?"




Murmushi Inna ta saki tana kallon Atu ta ce


"Rabu da mutuniyar taki, kuje Allah ya tsare hanya"


Da amin suka amsa suka fice bayan Hauwa ta d'auki kular abincinta a kitchen d'in Inna.


Suna hanyar school Hauwa tana ma Atu mitar Y Abdullah da irin girman kansa.


Atu ta d'an juya idonta tana rik'e baki had'e d'an mamakin Hauwa ta ce


"Wai tsaya ma Hauwa duka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login