Showing 9001 words to 12000 words out of 25209 words

Chapter 4 - RAYUWAR MAKARANTA FREE BOOK BY ZAHRA ROYAL.txt

nawa kike, kike ikirarin Y Abdullah ya so......



"Ke Kinga dakata kinji na ce ina sonshi ne uwar shirri?"


Hauwar ta katse Atu da sauri.


"A'ato alamu nake gani mana, ke idan banda abunki ina zaki kai wannan uwar gidan tasa uwar bak'in kishin tsiya?, Ina gani fa idan aka zo da ita garin nan yadda take miki wani kallon banza, ke koda mace ta gani tana kallon mata miji ranar saita gane bata wayo, ke kam mi zaki dashi ma?"


Wani abu Hauwa taji ya tsaya mata a zuci ita fa sai yanzu ne ma ta tuno cewa fa ashe Y Abdullah yana da mata.


"Mtswww aikin banza kawai nina manta da shegiyar matar nan tasa Lubna wallahi, y'ar banza kawai"




"Hhhhhh yo yada haka da zagi kuma Hauwa"


Atu ta k'are maganar had'e da dariya. Wani bugu Hauwa ta kawo ma Atu, ai ko da sauri ta goce tana k'ara sakin dariya son ranta, Hauwa ko ta cika tayi fam, da haushin Atu.


Da haka dai suna gaf k'arasawa school d'in suka hango y'an SS3 na gaf k'arasowa wajan taran makara, da gudu suka idasa shiga school d'in, shima sai da Atu taja hannun Hauwa sukai saurin shiga, domin suna k'arasowa suke rufe bakin shigowa school zasu fara tarban makara.




"Waii waii Allah ya taimake mu, yau dai ba'a tare mu ba, yau bamu da rabon shan wahala"


Harara Hauwa tayima Atu tana cewa.


"Nifa da kin barni bafa zanyi gudun nan ba, haka kawai na tabbata ko kwas d'in bata idasa ba wallahi tsabar mugunta ce cike da cikin wa'incan bayin Allahn"


Hauwa ta k'are maganar tana banka masu harara.


Jawota Atu tayi suka nufi cikin school d'in suna k'arya wata kwana domin zuwa house d'insu, da yake house d'insu d'aya da Atun.


Suna idasawa kota ina shara ake Yara da manta y'an SS1-SS2.


Fatee ce ta k'araso wajan tana cewa.


"Hauwa kuyi sauri ku d'akko tsintsiyarku, ku fara shara, domin idan suka ga mutum a tsaye bugunsa suke wallahi, koda irin mik'ewar nan yayi danya d'an huta, wallahi babu ruwansu sai dai kawai gaji bulala a gadon bayanka"


Atu ba shiri ta aje jakarta tana d'aukar tsintsiya tabi ayarin masu shara.


Hauwa ma tana turo baki tabi bayansu. Ba k'aramar shara sukai ma filin house d'in ba, da yake yau A'lhamis ana duban tsafta house to house.


Bayan an shirya house d'in an jera D'alibai akan layi, Malamai nabi house to house suna duban tsaftar house da ta D'alibai.


Fatee dake kusa da Hauwa ta kai dubanta a y'an yatsun Hauwa ta d'an rik'e baki da mamaki ta ce.


"Kaii kaii kaii Hauwa yau zaki ci duka, mi yasa baki yanke farcenki ba?, kin san yau A'lhamis ana duban tsafta?"


Zaro ido Hauwa tayi tana kallon y'an yatsun hannunta dake cike da farce zak'o-zak'o.


Ta ce "d'an girman Allah baki da Reza na yanke kamin su k'araso inda muke?"


"Wallahi tana can nesa damu cikin Jakar school d'ina"


Fatee na rufe baki kawai Malamai da y'an SS3 suka shigo house d'insu Hauwa, suka fara duba yanayin tsaftarsa, had'e da duba tsaftar D'alibai. D'aya bayan d'aya ake bi ana duba jikinka da hannuka idan ka yanke farcenka.


Duk wadda bai yanke ba k'asa ake duk'ar dashi.


Tofa kusan Hauwa kad'ai ce aka sa duk'ar k'asa.


Bayan Mahukunta sun wuce sunsa making d'in da house d'in yaci, kawai Hauwa bata san hawa ba, ba taba san sauka ba, ta fara jin bulala kota ina a jikinta.


Ta rud'e ta rasa inda zata sa kanta, domin kota ina jin bulala take a jikinta. Sai can taji saukar muryar wacce har abada bazata mance da ita ba wacce ta fara bugunta, a wajan taran makara Lamratu ashe ita keda house d'in da suke.


Lamratu na jifgar Hauwa tana cewa.


"Kaga y'ar iska k'azama dake, a kanki ke d'aya kinja mana rage maki a house d'ina, ai ko yau ba abunda zai hana banji uwarki ba wallahi"


Kallonta Hauwa kawai take tana kawo mata bugu tana tarewa da hannunta. Miye zatai ma wannan matar ne domin ta kiyayeta?.


Lamratu a zuciye ta ce


"Kee wai bake bace na ce karki sake wani abu ya k'ara had'a ki dani bane?, ai ko yarinya kin bani kin shiga uku tunda Allah ya kawo ki house d'ina, idan bazaki daina jakkanci ba ni kuma bazan daina kilarki ba son raina"


Ta idasa maganar tana d'aga bulalar dake hannunta tana kai mata wata shaud'a a gadon bayanta.


Wata irin gantsarewa Hauwa tayi kawai ta zube a k'asa ta fara wani juyi, tana yi tana wani irin gurnani kamar zakanya.


A mugun tsara ce wasu suka fara ja baya.


Lamratu kuwa murmushi ta saki tana cewa.


"Ai wallahi ba aljanu ba ko kukar bulishiya ce a kanki yau saina sauk'e miki ita a kanki"


Tana k'are fad'ar haka ta k'ara k'aimin kaima mata jifga baji ba gani.


Wata shegin juyi da Hauwa tayi sai gata ta kamo k'afar Lamratu ta fyad'a da k'asa sai gata rashe-rashe a k'asa a zube.


Mi d'alibai zasuyi idan ba dariya ba.


Wani mugun haushi da tsananin kunya ne ya rufe Lamratu.


Hauwa kuwa ta haye ruwan cikinta ta fara kai mata naushi ta hanci ta baki baji ba gani tana wasu surutai tana cewa.




"Keee dan uban da ya haifeki kin isa ki tab'a mana godiyarmu ki zauna lafiya, daga yau idan kika sake sai mun zubar miki da hak'ora, mun tsiyayar miki da idonki ko mu maida ke kurma"


Kuka Lamratu ta saki tana cewa


"Dan Allah ba wadda zai kwace ni ne daga hannun wannan mahaukaciyar, wayyo Allah na zata kashe ni"




Fatee dake gefe tsaye ta saki wata dariyar mugunta tana cewa k'asa-k'asa


"Wahoho dole K'anwar nak'i, ai na d'auka girman kai bazai bari ki nemi taimako ba, ai wallahi masu aljanun nan sune dai-dai daku"


Atu ko tana daga gefe ta rik'e baki tana kallon Hauwa dake jikin Lamratu tana gurzarta kamar wacce ta samu kayan wanki.


Da gudu wasu Malamai suka k'araso wajan da kyar da sub'in goshi aka b'anb'are Hauwa a jikin Lamratu tana yi tana wata jijjiga tana ihu tana cewa.


"Ku cika mu muka ce, ku barmu da ita yau sai mun sumar da ita tunda ta tab'a mana godiyarmu mu, ku gaya mata ba'a tab'a mana godiyarmu a zauna lafiya"


Addu'a Mlm Bahari dake kusa da Mlm Shamsu, dama Mlm Shamsu Malamin Arabic ne, nan take ya fara tofa mata wasu addu'o'i.


Wata irin y'ar iskar mik'a Hauwa tayi tana sakin wata uwar atishawa mai k'arfi, kai ka ce aljanun gaske ne suka fice daga jikinta.


Har wani baccin munafurci ya d'auketa, Mlm Bahari ya bada umarnin a kaita zuwa class a kwantar da ita kamin ta farka.


Bayan an wace da Hauwa Mlm ya kalli Lamratu yana cewa.


"Ya kamata ku daina irin wannan hukuncin da bugun Yara a tsakar rana ko sanyin safiya irin haka, komai na iya faruwa dama, dan Allah a kiyaye gaba please"




Wata muguwar harara Lamratu ta raka Mlmn da yayi maganar da ita.


Uwar kunya duk ta isheta tana tashi ta fara zagin sauran y'an house d'in nata, tana hucewa a kansu.......


*RAYUWAR MAKARANTA*






*Zahra Royal Star*






Page 5




*No. 12, Kawo Bos Stop, Kano Nigeria*




Kirrr kirrr kirrr


Ringing d'in wayarsa ta karad'e gaba d'aya parlon.


Lubna dake zaune akan kujera ta d'ora k'afa d'aya kan d'aya, ta d'ago tana jefa masa wani kallo irin na zargi.


Ko kallonta baiyi ba ya tashi domin d'aukar wayar.
Da wani mugun sauri ta sha gabansa tana rik'e k'ugunta tana masa kallon tuhuma.


Da kyar Abdullah ya iya bud'e baki domin ransa ya fara b'aci ya fara gajiya da halin Lubna ya ce.


"Miye haka Lubna?, kinzo kin shiga gabana ki bani waja na wuce na ce"




Wani kallon uku saura ta jefama Abdullah, duk cewar tana mugu-mugun shakkarsa ba kad'an ba, to amma indai akan kishinsa ne hankalinta ma barin gangar jikinta yake bata wani shakkar masa tujara akan hakan.




Ta ce "dole na tare gabanka mana, miye dan an kira ka, zaka wani tashi kaje d'aki ka d'auki waya?, mi yasa baza'ayi wayar a gabana ba, idan ba wani abun kake kullawa ba, wallahi Honey ka sani bazan tab'a iya had'a kowacce mace da kai ba"


Hannunsa na dama yasa a fuskarsa ya d'an kama kansa da ke neman fara masa ciwo, saboda hayaniyar da Lubna ke masa.


Idonsa masu kamar mai jin bacci had'e da muryar nan tasa mai cike da isa da izza ya ce.


"Lubna karki sake na d'au mataki a kanki, wadda zakiyi nadama a nan gaba, dole ne aka ce miki sai nayi waya a gabanki, ko kuwa ke kullum d'an k'aramin tunaninki bai da aiki sai kitsa miki cewa ai da mace nake waya?"


"Ai dole ka ce haka mana, ya za'ai hankali na ya kwanta, kana koyarwa a wannan shegiyar school d'in taku kaine fa shugaba a cikinta, gaka da kyau da izza, da komai ka had'a na rayuwa ya za'ai y'an matan makarantar nan bazasu haukace akan ba, gasu dama ance sai shegen rawar kan tsiya ne dasu, ga son Mazan mutane, ni kuma wallahi naga y'ar iskar data isa da shigo min cikin gida, bance ub.......


D'aga mata hannu Abdallah yayi yana cewa.


"Stop kinga, I'm tired of hearing your words, kullum sai kin mai-maita min su, kuma kin san baki isa kin hanani hud'd'a da D'alibai na ba, so give me a place to pass"


Yana idasa fad'ar haka wayar dake hannunsa ta sake d'aukar k'ara.


Kallon wayar yayi yana rab'awa ta gefanta ya wuce.


Da d'aki zai nufa taga kawai ya fice waje yana gaf fita parlon ya d'auki kiran da aketa masa a wayar.




Bayan ya fito ya can cikin wayar aka ce


"Abdallah wai sai yaushe ne zaka samu time zamu je rimaye ne?, ina buk'atar ganin uwata fa kai idan baka buk'atar ganin Kakar taka"


Murmushi ya saki yana cewa.


"Abba barka da dare"


"Barka kad'ai, ko gaisawa ban bari munyi ba, kai d'in ne hidimar ka tayi maka yawa, idan bazaka samu zuwa ba gara ka bari kawai ni naje naga uwata"


Murmushi Abdallah ya sake saki, wadda yasa kyakykyawar fuskarsa mai cike da kwarjini da haiba ta k'ara kyau da cikar zatii, murmushin da Abban ne kad'ai ke ganinsa, dan ko Lubna a yanzu bata cika ganin murmushinsa ba, saboda yanzu kullum cikin b'ata masa rai take, akan bak'in kishinta, ba damar taji yana waya sai ta ce ai da mace yake waya, ba damar mace D'alibarsa ta kirashi ko akan matsalar karatunta ne, yanzu sai ta fara nuna masa halin k'auyancin nata, a wacewarshi, abunda take yi da haukan da takeyi akansa haukane da k'auyanci da gidadanci.


Sauk'e lumfashi yayi yana cewa.


"No Abba insha Allah zamu je very soon, kawai so nake na samu time na tafiyarmu da wuri"


Daga cikin wayar Abba ya ce.


"Ya kamata dai, dan so nake naje naga Y'ata Hauwa nasan yanzu ta sake k'ara girma"


Wata irin halbawa zuciyar Abdallah tayi, jin sunan da aka kira Hauwa, shifa har mantawa yake da wannan yarinyar marar hankali mahaukaciya, wani abu ya tuno kuma yasa shi lumshe ido yana hango irin rigimar da za'a sha a lokacin da abun ya fito fili.




Sunyi magana sosai inda daga k'arshe yake cewa


"Karka damu Abba itama tsohowa mai ran k'arfe saita gaji da ganinmu ne insha Allah"


"Haka dai kake fad'a k'ila sai lokacin da muka d'ibar maka na tarewar Hau.....


Da sauri Abdallah ya ce


"Abba sai munyi magana"


Ya datse kiran, yana kallon Lubna da fitowarta kenan ta rik'e k'ugunta.


Sauk'e ajiyar zuciya yayi yana hamdala bata ji mi Abba yake cewa daga k'arshe domin wayar zaka iya jiyo mai magana, danshi akwaisa akwai iya k'ure k'ara yadda zaiji mutum sosai a cikin waya.


Baiyi aune ba Lubna ta matsa kusa dashi ta warce wayar dake hannunsa tana jujjaya ta tana cewa.


"Wato saboda baka da gaskiya shine dan kaga na fito zaka kashe wayar, idan ba wayar munafurci kake ba mi yasa ka katse ta, ka ci gaba da wayar mana idan kana da gaskiya"


Abdallah harya d'aga hannunsa zai kai mata mari, sai kuma ya dunkulesa waje d'aya.


Kallonsa take da mamaki ta saki wata shewa tana cewa


"Ahayeee aren't you just slapping me?, kuma kaji in gaya maka wallahi daga yau bazaka sake waya da wata y'a mace a wayar nan ba"


Tana idasa maganar ta buga wayar da k'asa nan take ta tarwatse.


Zaro ido waje Abdallah yayi yana bin Lubna da kallo, ganin yadda ta fasa masa waya kuma ta shigewarta parlo ta barsa cike da baki.




Tana cin galaba akansa ne dan taga bai da hayaniya, baya son yawan magana a rayuwarsa, shi yasa take anfani da wannan damar domin takurama rayuwarsa, akan bak'in kishinta da mugun zarginta akansa.


D'aukar wayarsa yayi yana shafa sumar kansa wacce a kullum take a gyare, ya bud'e k'ofar parlon ya shiga ciki.






*Government Secondary School Rimaye Katsina State Nigeria*




Zama Atu tayi akan kujerarsu ta class, tana duban Hauwa data ware tana ta hidimarta bayan dawowarsu cikin class, yadda kasan ba ita ce ta gama bori d'azo a house ba.


Atu ta ce "tabbas Hauwa kin shallake tunani na da hankali na, kin cika Hauwa hatsabibiya wallahi, ina dai raba ki Hauwa da yin k'aryar aljanun..... Da mugun sauri Hauwa ta toshe ma Atu baki da tafin hannunta tana zaro ido waje, tana wurga idonta tana bin y'an class d'in da kallo, ganin hankali y'an class ba kansu yake ba kowa ma harkar gabansa yake yasa Hauwa sakar mata baki tana cewa.


"Gaskiya Atu bana son irin abunda kike min wallahi, haba dan Allah, yanzu da wani yaji ki fa? Shikenan kin tona min asiri kennan?, idan bazaki iya ganin yadda nake ba kiyi shuru da bakinki, domin wallahi ko ba k'aryar aljanu duk wadda ya tab'a ni nima sai na tab'a sa, kin sani kuma ai"




Girgiza kai Atu tayi tana cewa.


"Ni dai gaskiya nake fad'a miki"


"Rik'e gaskiyar tak'i wata rana k'ila tayi anfani"




"Au yanzu bata da anfani fad'ar ta kenan?"


Gyara zamanta Hauwa tayi tana hararar Atu ta ce.


"Da alamar haka gaskiya, nifa bana son shiga sharra ba shanu"


"Au haka kike ce?, tom shikenan na daina shigar miki sharra ba shanu, idan hanyar da kika d'auka mai b'illewa ce ki ci gaba kinji Hauwa?"




Turo baki tayi tana sa hannunta ta dafa kafad'ar Hauwa ta ce.


"Nifa ba haka nake nufi ba, ba dai fushi kikai dani ba dai ko?"


Wani murmushin gefen baki Atu tayi tana kallon Hauwa cike da sonta duk rashin mutumcin Hauwa ita kam bata mata shi, duk muguntar Hauwa bata ma Atu, bata ma son abunda zai b'ata ranta, daga Inna sai Atu sai Abba sune mutanan da Hauwa ke bala'in so a rayuwarta, sune kad'ai wani lokacin idan suka fad'a mata magana d'aya take daina shi.




Atu ta ce "ni ko kad'an ba fushi nayi ba, ai kin sani fushi ba d'abi'ata ba ce"


"Hakane kam na sanki ai ke y'ar Aljanna ce, ban tab'a gani ko tab'a jin labarin kina fushi ba"


Atu zatai magana tana murmushi su Ammama suka shigo class d'in, domin duk yanzu ake dawowa ajin.


Zama sukai Hadiza ta aje kular abincinta da jakarta, tana juyawa ta fuskanci Hauwa da Atu tana cewa.


"Wai wani labari naji a cikin makaranta, na ce amma idan haka ne Ubangiji ya saka miki da alkhairi Hauwa"


Zatai magana Atu ta wurga mata wani kallo shuru tayi tana turo baki gaba, Fatee ce ta amshe zancen da cewa.




"Ai ko abinda kika ji dai shine gaskiya, domin ko yau Lamratu ta ci Jakin duka nake gaya miki harda su neman taimako"


"Duk girman kan nan tana?, amma wallahi naji dad'i, inama house d'inmu d'aya da yau naci dariya, dan ba abunda zai hana banyi ta ba, sai dai ta kashe ni"


Cewar Hadiza ta idasa maganar suna sakin shewa had'e da tafa hannu da Ammama.


Shuru sukai jin Binta na cewa.


"To y'an class d'in nan Malam Bahari ya ce a gaya maku gobe zaiyi texs had'e da amsar book d'in ko wannan mu domin zai duba note d'in mutum gaba d'aya, idan ma mutum yasan baya yi to yayi k'ok'ari yayi shi kamin zuwa gobe"


Tana idasa fad'ar haka taje ta zauna a kujerarsu.


Wani tsaki Hauwa tayi tana bin Binta da harara, Binta ko yanzu ko kallon saitin kujerar da su Hauwa take bata ma yi bare abunda zai had'ata da Hauwa.


Atu ta kalli Fatee tana cewa.


"Please Fatee kina rubutun Mlm Bahari duka ne?, ki bamu nida Hauwa muyi"


Hauwa ta amshe da cewa


"Ke ni fa bazan yi ba, text d'insa kawai zanyi, ni bazan iya rubutun nan ba, ya cika rubutu da yawa idan ya shigo wallahi"


"Kar Allah yasa kiyi d'in, ke ce zaki ci jifgar banza ai ba ni ba ko?"


Fad'ar Atu tana amsar book d'in da Fatee ta mik'o mata, fateen na cewa.


"Kinga Hauwa ki rufa ma kanki asiri ki amsa kiyi rubutun nan, Mlm Bahari fa ba bugu yake ba, mugun Jakin aiki ne yake saka mutum, wadda sai ka gwammace dama bugun naka akayi wallahi ina gaya miki, shi zaki ga duk rashin jinmu muna kiyaye note d'inshi, idan ya shigo shida Mlm Add'au".


Tsaki Hauwa taja tana tab'e baki ta ce


"Nifa badan ina tsoronsa zanyi ba yawwa a'ato"


Dariya kawai Atu tayi tana yin rubutun ta ce.


"Da kar kiyi mana y'ar neman rigima"


Bugun wasa Hauwa ta kai mata tana cewa.


"Atu bana son abunda kike min fa"


Hadiza ta kalli Atu ta ce.


"Yawwa please idan kin gama ki d'an bani zanyi na shekaran jiya, da yayi ban idasa note d'in ba, wani waje ya goge, dad'i dashi idan baka da saurin rubutu bakwa idasa rubutu a tare dashi, dole ne sai ya wuce ka"




Da to Atu ta amsa tana rubutunta.


Hauwa ta ce.


"Kinga Fatee zaki ara min book d'in idan naje gida zanyi ni, dan banzan iya yanzu ba gaskiya"


To kawai Fatee ta amsa suna mik'ewa a tare jin an kad'a k'araurawar fita break, yau tunda suka shigo class ba Malamin daya shigo har aka kad'a k'araurawar...........




*RAYUWAR MAKARANTA*








*©Zahra Royal Star*






Page 6




*Government Secondary School Rimaye Katsina State Nigeria*






Class d'in yayi shuru sai muryar Mlm Bahari dake tashi yana kiran sunayen y'an class d'in, sai kuma magana k'asa-k'asa dake tashi ta y'an class d'in.


Mlm Bahari dake tsaye rik'e da takardun text d'in da yayi masu jiya bayan ya amshe book d'in kowa, littatafan na aje gefansa, sai ya gama raba masu text d'in kamin yazo ga book d'in.




A hankali yake kiran sunayen mutane duk wadda yayi abun kirki sai ya tsayar dashi an tab'a masa.


Masu k'ok'arin ajin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login