Showing 21001 words to 24000 words out of 25209 words

Chapter 8 - RAYUWAR MAKARANTA FREE BOOK BY ZAHRA ROYAL.txt

ba, harda kwanciya domin ganin yadda Nahna ke kiran ta bani ta sha uku, yadda take wage baki tana ihun azo a taimake ta.




"Wayyo wayyo wayyo Momy kina ina ne?, dan Allah kizo ki sosa min, wayyo k'aik'ayi ko ta ina jikina, ji nake kamar zan mutu, na shiga uku wayyo wayyo All......
Ta kasa k'arasa maganar jin wani mugun k'aik'ayi ata bayanta, da sauri cikin fitar hayyaci tasa hannun nata a baya zata sosa wajan, can taji wuyanta ya d'auka jikinta ya k'ara d'aukar wani mahaukacin k'aik'ayi wadda yafi dana da, da take ji, ihu ta k'ara saki don k'arfinta.


A rud'e kamar da gaske Hauwa ta sauka k'asa bayan ta gama tikar dariyar tata, Nahna na ganin yadda take mata dariya da yadda ta kasa bata taimako tasan ba wadda yayi mata wannan shegiyar muguntar sai Hauwa.


"Momy!! Momy!! Momy!!"




A rud'e Momy ta sakko tana cewa.


"Innallihi Hauwa miye na wannan kiran har kinsa gaba na ya fad'i Fisbilillahi?"


"Momy Ina Abba?"


"Abbanku ya fita Masallaci"


Zata sake magana Momy taji yadda Nahna ke ihun neman taimako.


Da sauri Momy ta zaro ido waje tana dafe k'irjinta ta ce.


"Subhanallahi mi ya faru Hauwa mi ya faru da Nahna?"




Gaba Momy tayi a mugun rud'e domin ihun da Nahna keyi na fitar hankali ne hakan ya k'ara rud'a Momy sosai, dan har tana tun tube wajan shiga d'akin.


Hauwa da ta rufa mata baya, suna shiga d'akin Momy tayi saurin runtse idonta tana cewa.




"Subhanallahi ke Nahna miye haka?, babu fa sutura a jikinki, miya shiga kanki haka ne?"


"Wayyo wayyo Momy ki taimka min ki sosa min, ko ina na jikina k'aik'ayi yake min".


Da sauri Momy ta matsa kusa da ita tana tallafo ta a jikinta ta fara sosa mata ko ina na jikin nata da har yayi jawur tsabar kartarsa da Nahnar keyi.




Momy a rud'e ta ce.


"Wai mi kika shafa ma jikin naki ne?".




"Wallahi Momy ban sani ba, daga watsa ruwa a toilet"




"Innallihi wa'inna alaihir. Hauwa d'akko min wayata na kira doctor yazo"


Da mugun sauri Hauwa ta k'ara sauka k'asa ta d'akko wayar, ko kad'an bata ji wani tausayin Nahna ba, gobe ma ta sake gaya mata maganar banza.


Tana kowawa Momy har hannunta na kyarma wajan danna number doctor.


Ba'a b'ata lokaci ba Doctor ya iso shima hankali a tashe, domin tunda ya taho Momy ke k'ara faman kiransa kamar zata tada gari, sai uban kira take masa.




Da kyar tasa ma Nahna wata riga marar nauyi har yanzu soshe-soshe kawai take harda su kuka yanzu domin yanzu da ta sosa zafi ma take ji, domin duk ta karce jikin nata.




A tare Abba da doctor suka shigo gidan, inda Abba yayi mamakin ganinsa, ya tabbayeshi ko lafiya?, wani ne ya kirasa a gidan, bai da labari.


A tak'aice Doctor yayi masa bayanin da Momy tayi masa shima.


Ai ko hankali a tashe shima Abba ya haura sama wajan d'akin su Nahnar.


Abba na shigowa ya matsa kusa dasu yana cewa.




"Wai mi ya kawo mata wannan susar jikin haka?"


"Abban Yara nima ban sani ba wallahi, haka na zo na tadda ta, nima Hauwa ta kira ni fa na zo na ganta a haka"


Juyawa yayi inda Hauwa take tsaye harda su kukan munafurci take yi da hawaye kamar gaske ya ce.


"Hauwa mi ya sami y'ar uwarki?"


"Abba nima ban sani ba wallahi, kawai ni dai ta zo ta shiga toilet har tana gaya min cewa y'an K'auye k'azamai ne basa wanka, dan taga banyi wanka ba sai ita, shine fa ta shiga da wata bak'ar leda wai ko k'awarta ta bata ko sabolo ne zatai wanka dashi, k'ila shine yasa ta jin k'aik'ayin"




Duk irin halin azabar da Nahna ke ciki hakan baisa ta kasa gane mi ye Hauwa ke shirin k'ulla mata ba, nan ta k'ara tabbatarwa kanta cewa tabbas Hauwa ce silar sata a wannan halin da take ciki, tabbas ta rantse da tsarkin mulkin Allah sai ta rama bazata tab'a barin Hauwa ta ci bulis ba.


Nahna tana kuka tana susar jikinta ta ce.


"Wallahi Abba ba abunda nasa nayi wanka dashi, kawai watsa ruwa nayi, amma ban san miya kawo min k'aik'ayin ba nima".


Ta wutsiyar ido take ma Hauwa kallon zamu had'u ne, itama Hauwar kallon ina jinranki ta aika mata dashi.




Da kyar dai aka samu Doctor yayi mata wata allura tasa ta bacci had'e da kashe k'aik'ayin.


Inda doctor ya k'ara masu jawabin cewa, akwai abunda ya sa mata k'aik'ayin nan, ba wai haka nan kawai ya same ta ba, akwai abunda ta shifa ma jikin nata..........




*Hi Masoya book d'in RAYUWAR MAKARANTA, karku shagala da yawa fa, domin book d'in RAYUWAR MAKARANTA yanzun ne tafiyar tashi ta soma, na kud'i ne akan raina d'ari hud'u ne kacal #400, zaka iya turo kud'in ka ta wannan account number d'in*.
👇
8130479973 Fatima Rabi'u Opay bank.


Sai ka turo shaidar biya ta wannan number d'in👉08130479973


*RAYUWAR MAKARANTA*








*©Zahra Royal Star*








Page 10 *list free pages*








*No. 12, Kawo Bos Stop Kano Nigeria*








A gajiye ya shigo gidan, yana d'an sauk'e lumfashi kad'an. Turus yaja ya tsaya yana bin parlon da kallon cike da tsananin mamakin Lubna. Miye take har yanzu da ba'a fito an gyara parlon ba?, ko ina kaca-kace yake.


A hankali ya taka ya nufi darning table shima dai a hargitse yake, baya jin ma tayi wani abinci. D'an dafe cikinsa yayi yana jin yadda y'an hanjin cikinsa ke masa k'ugin yinwa.


Ransa idan yayi dubu ya fara b'aci, ransa na soya ya nufi sama, inda yake jiyo tashin kid'a kad'an kad'an yana fitowa. K'aramin parlonta ya nufa yana tura k'ofar ya ci k'aro da ita zaune tana danna waya tana cin biskit daga ita sai wata y'ar riga iya gwaiwa, ko d'ankwali babu akanta, tana zaune ta d'ora k'afa d'aya kan d'aya, tana cin biskit da su samosa, hankalinta kwance parlon ma yayi kaca-kaca.


Motsin da taji ne yasa da sauri ta mik'e tana kallonsa, d'an sauk'e lumfashi tayi tana dafe k'irjinta ta ce.




"Ohhhh wayyo ashe Kaine ka dawo?, harka bani tsoro fa"


Wani kallo da ta ga ya jefa mata yasa ta d'ansa hannunta tana sosa keyarta, takowa yayi har inda take yana binta da kallo, tabbas ita gata tsaf k'amshi ne kawai ke tashi a jikinta, jikinta gyare yake, tana da tsaftar jikinta amma bata da tsaftar mahalinta.


Da kyar ya iya bud'e baki tsabar b'acin rai ya ce.




"Yanzu Fisbilillahi Lubna kin duba gidan nan kinga yadda ya koma?, ko ina kaca-kaca, sai ka ce ba mace a gidan"


Turo baki tayi gaba ta ce.


"Dama fa na mance na fad'a maka mai aikin tawa ce aka ce wai aure za'a mata a can K'auyensu, shine yau da safe ta tafi na sallameta, zuwa gobe ko jibi za'a kawo min wata daga gidanmu"


Wani kalar abu yaji ya tokare masa mak'oshi. Wato dai gidansu ake d'aure mata gindin komiye ma take masa a cikin gida.


"Ke yanzu bazaki iya tashi ki gyara gidan ba, har sai an kawo wata y'ar aikin?, ke kina ganin rayuwa zata tafi a haka ne?, komai ace sai anzo anyi miki, to gaskiya na fara gajiya da abunda ke faruwa a gida na, idan Zaki canza ki canza tun kamin ranar nadama ta riske ki, tun Kuma kamin na d'au mataki akan ki"


D'agowa tayi ido cikin ido ta ce.


"Ban gane miye kake k'ok'arin cewa ba honey?, kamar ya ranar nadama ta zo min?, abunda nake har wani abu ne marar kyau?, nifa na ce maka ko a gidanmu komai yi min ake, to dan haka bazai yuwu ace nazo gidan aure na ba, ace bazan huta ba a'ato, mai aikin nanma fa ba kaine ke biyanta, to miye na abun fad'a? Dan yau kawai kazo kaga gida a haka"




"Haka zaki ce ma ko?"


Ganin tayi shuru tana kallon k'asa tana wata jijjiga yasa shi d'an shafa sumar kansa ransa ya gama b'aci sosai. Tafiya ya somayi tana nufar k'ofa domin fice mata daga parlon, idan ya ce zai ci gaba da yin magana komai yana iya faruwa, zai iya mata abunda zatai dana sani har k'arshen rayuwarta, shi yasa kawai yayi saurin ficewa daga parlon, dan idonsa sunyi jawur jijiyoyin kansa sun tashi sunyi rud'u-rud'u, to komai na iya faruwa idan bai bata waje ba.


Shiga yayi d'akinsa shima dai kamar yadda ya barsa a haka yazo ya iske sa, hatta gadon daya barta kwance akansa, ba'a gyarasa ba yadda ya barsa a haka ya zo ya same sa.


Ransa ya k'ara b'aci sosai amma a haka ya haÉ—iye b'acin ransa, ya fara rage kayan jikinsa, da kansa ya fara gyara gadon, domin bazai iya kwanciya d'akin a haka ba, da kansa ya d'an gyara d'akin, gyaran da yayi ba wani yi masa yayi ba, ya shiga wanka, shima toilet d'in sai ya wanke sa sosai har sau biyu, yana tausayin kansa ace yana da mata amma yake duk wannan aikin, amma yasan abunda zai mata dole ne ma Hauwa tayi saurin tarewa a gidansa, koda su Abba basu amince ba, idan ba haka ba kuma zai je ya k'ara wani auren ne, domin ba zai zauna mace d'aya ta rink'a sa masa ciwon kai ba.


Fitowa yayi daga toilet d'in bayan ya gama wanka, ya shirya tsaf yana d'an tunanin ina zaije ya sami abinci?. Idan ya ce zai tafi GRA, unguwarsu dare ya d'an fara, da sauri ya d'akko wayarsa ganin k'arfe takwas da y'an minutes yasa shi d'aukar key d'in motarsa ya yanke hukuncin can zai tafi, ya ci abinci a wajan Momy kawai, duk da yasan tabbas sai ta tabbaye shi dalilin zuwan nasa.


Da d'an sauri ya sakko k'asa ganin Lubna a parlon k'asan yasa shi k'ara shan mur ko kallon inda take baiyi ba ya nufi k'ofar waje.


"Honey ina zaka je kuma cikin daren nan?"


Lubna ta k'are maganar da d'an k'arfe ganin ya fice ko waigowa baiyi ba, bare tasa ran zai bata amsa. Zama tayi kan kujerar parlon tana tab'e baki.




*No. 14 Audu Bako Way, Nassarawa GRA Kano Nigeria*




A hankali Momy ta kalli Hauwa dake tsaye wajan Darning table suna zaune har Nahna da ta d'an samu sauk'i, sun fito cin abincin dare. Nahna sai cika take tana batsewa so kawai take ta samu ratar da zata rama abunda Hauwa tayi mata, tama rasa miye zatayi mata domin rama abunda tayi mata.


Maganar Momy ta katse mata tunanin data lula inda taji tana cewa.


"Hauwa ki zauna mana, ko abincin da akayi baiyi miki ba, ki shiga kitchen ki dafa wani abu"


Da saurinta kuwa ta ce.


"Eh gaskiya Momy bazan iya cin wannan abun ba"




Abba daya kai lumar abinci a bakinsa ya had'e abincin dake bakinsa ya ce.


"Y'ata Sakwara ce fa, da Miyar agusi"


"Eh Abba ni ban cika cinta ba gaskiya"


Kallon Abincin Hauwa tayi gashi dai yaji naman kaza harda ma ganda zak'o-zak'o a cikin Miyar, amma ita dama can Sakwara bata wani dameta ba, bata cikin jerin abincin da ta take so.




A hankali Momy ta dafa ta ta ce.




"Yawwa tunda hakane kije kitchen ki dafa ko indomi ce, tunda kinga dare ya riga da yayi"


"To Momy tama ishe ni Indomin"


"Yawwa to je ki dafa"


Nufar kitchen d'in tayi tana murnar cin Indomi domin Allah ya sani tana son Indomi, bare idan tayi mata dahuwa ta gani ta fad'a.




Nahna dake zaune ta saki wani murmushin mugunta tana hango ta inda ya dace ta rama abunda Hauwa tayi mata, murmushi take tana girgiza kai domin ta hango muguntar da zatai mata.




Suna zaune suka ji sallamar Abdallah. Da d'an mamaki Momy take kallonsa ganin yadda ya zo ya zauna akan Darning table d'in, ya kalli Nahna yana cewa.


"Ke zuba min abincin nan yinwa nake ji dama"


Abba daya gama yanzu yana niyar mik'ewa ya ce.


"Ahh ahh Abdallah miye kazo yi a gida irin wannan lokacin?"


"Wallahi Abba naje gida ne sai na iske har yanzu jikin Lubna ba lafiya, bata ko iya dafa abinci ba yau, shine yasa na zo nan na ci, domin kasan bana son cin abincin saidawa"


Amsawa da kai kawai Abba yayi ya fice daga wajan Darning table d'in ya haye sama abunsa.




Momy ta d'an hararesa tana cewa




"Nifa wallahi Abdallah ban wani yarda da kai ba, indai akan matar nan taka ce, komi sai ka rink'a wani k'areta"




Abincin da Nahna ta zuba masa ya jawo ya d'an soma ci, sai kuma ya ce .


"Momy da gaske fa nake"


"Hmmm Abdallah kenan, ai shikenan a juri zuwa rafi dai, wata rana tulu zai fashe ai"


Tana k'are maganar ta tashi itama, tabi bayan Abba sama.




Suna zaune su biyu sai ga Hauwa ta fito daga kitchen d'in, bata gama dafa Indomi d'in ba, jin muryarsa yasa ta fitowa, amma ko kallonsa batayi ba ta haye sama dan wani fisari da ta ke ji ya rik'e mata mara.




Yana kallonta ta wutsiyar ido harta haye sama, babu hijab a jikinta, daga ita sai wata dogowar rigar bacci har k'asa, amma duk da haka yana iya hango albarkatun jikinta wadda Allah ya zuba mata, yadda kasan ba Hauwa y'ar shekara sha hud'u ba, kamar wata babbar mace haka ta koma masa a idonsa, yadda take hawa benen jikinta na girgiza taku d'aya biyu sai jikinta ya motsa, yadda take hawa benen da d'an sauri abun kallo ne, shi sai yanzu nema yake k'are mata kallo, Hauwa na da wani irin jiki na ban mamaki, wadda duk k'aryar namiji da jin kansa sai ya kalleta ya sake kallo. Motsin Nahna ne ya katse masa hanzari da tunanin daya afka, Wani tsaki ya saki jin motsin Nahna da ta tashi ta nufi kitchen da saurinta.


Wani haushin kansa ya fara ji, duka nawa Hauwar take da har zuciyarsa ta fara kwad'er ta masa ita?, ba komai yaja masa hakan ba sai Lubna duka laifin ya d'orasa akan Lubna, idan badan ita mi zai sa ya kalli wancan yarinyar.




A wajan Nahna tana shiga kitchen d'in tayi saurin bud'e tukunyar da Hauwa ke dafa Indomi da ita, ruwan Indomin har ya fara tafasa, tasa magi da komai sai kwai da ta aje daga gefe da alamar soya Kwan zatai, ba wai dafawa ba.


Da sauri ta jawo Gashiri dake cikin leda, ta bud'e. Sai da ta cika hannu dashi ta zuba a cikin ruwan Indomin dake tafasa, tana zubawa tayi saurin rufewa ta maida gishirin inda yake, da saurinta ta fice ta k'ofar baya dake kitchen d'in ta nufi lanbo dake bayan kitchen d'in, idan ta tashi shigowa ta shigo da k'ofar gaba, dan karma ayi zargin ita ce tayi aika-aikar.


Abdallah yana tashi baima kowa sallama ba yana gama cin abincin nasa ya fice daga gidan gaba d'aya.


Hauwa da ta sakko k'asa tana satar kallonsa a lokacin da ya tashi yana nufar k'ofa.


Sai da ta bari ya fice kamin ta idasa sakkowa ta nufi kitchen da sauri, domin tasan yanzu ruwan Indomin ta ya tafasa.


Tana zuwa ko ya tafasa kamar ance tasa chokali ta d'an d'ebo ruman Indomin ta d'akko magi ko idan magin Indomin bai ji ba ta k'ara ta d'an d'ebo ruman ta kai bakinta, da wani irin sauri ta furzar dashi, tana tab'e bakinta girgiza kai ta farayi ita dai iya saninta ai bata sa gishiri ba, to waye yayi mata hakan?, bata yarda ba ta k'ara d'ebo ruman ta kai baki, nanma jau taci uban gishiri yayi yawa. D'an tsayawa tayi tana kallon ruwan dake tafasa har yanzu tama kasa magana, sai can ta saki wani shegen murmushi, girgiza kai ta farayi tana sauk'e ruwan Indomin ta zubar dashi ta wanke tukunyar ta sake maida wani ruwan tasa farin magi da wani magin Indomin, yana sake tafasa ta d'akko karas da girinbis da ta yanka ta dafasu daban tun d'azo tasa su, tasa Indomin minti kad'an ta sauk'e, tana a tsaye bata k'ara barin kitchen d'in ba, tana gama dafuwar Indomin, ta sauk'e ta juye ta a filet ta soya kwai daya ji al'basa da d'an jajjage kad'an da ta sa masa, tana idasa soyasa ta juye sa a saman Indomin.




Fitowa tayi ta nufi sama, bata buk'atar zama akan Darning table ta ci abincin yanzu, so take ta tabbatar shin Nahnar ce tayi mata wannan abun ko kuwa?.




Tana shiga d'akin taga babu Nahna zama kawai tayi dan tasan duk inda taje tana nan shigowa d'akin.
Tana gama tunanin zucinta kuwa sai ga Nahna ta shigo d'akin tana dariyar mugunta. Da sauri ta tsayar da dariyar tata tana kallon Hauwa dake cin Indominta hankali a kwance, sai saka luma take yi.


K'ara ware idonta tayi wai ko dai bata gani ne sosai ba, again dai gani tayi Hauwa sai cin indominta take har wani lumshe idonta take. Hauwa na kallon yanayinta ta wutsiyar ido, kuma tuni ta harbo jirginta tuni tasan ita ce kennan tayi mata hakan?.


"Hmmm"


Kawai Hauwa ta saki tana girgiza k'afar tana yi tana cin Indominta.


Ganin fa kamar zata gane akwai abunda ta shirya mata, yasa Nahna kame kanta tana wani basarwa taja tsaki ta zauna akan gadonta tana latsa wayarta.


Ta wani maze yadda kasan bata aikata komai ba.


Washe gari da safe, kamin kowa ya tashi, Hauwa ce ta fara tashi, ta gyara ko ina na gidan, domin basu da wata y'ar aiki, duk aikin gidan Nahna ce keyi idan babu school, idan akwai kuwa zata tashi tunda safiya ita da Momy suyi aikin su, kamin gari ya gama wayewa sun gama har abincin safe, haka suke yi, shi yasa ma Hauwa ta saba da aikin irin na gidan, domin duk hutu a nan take yinsa, ko can Rimaye ma wajan Inna tare suke aikinsu suma, Inna b'ata tab'a barin Hauwa a sangarce ba, shi yasa komai ta iyasa bata jin wahalarsa, haka ma Nahnar itama Momy ta hureta da ayyukan gidan.


Hatta abincin safe Hauwa tayi sa a safiyar. Nahna na sane tak'i tashi, domin tasan yau Momy baza ta fito da wuri ba, tasan suna nan sune zasuyi aikin, shi yasa tabar Hauwa ita d'aya tsabar mugunta da son kai. Hauwa ko tana sane da abunda ta shirya mata yau da safen shi yasa bata tayar da ita ba, da ba komai itama tasan bata aikin nan ita d'aya, amma Nahna harta manta da ta ma Hauwa wani abu.


Hauwa bayan ta gama ta shigo d'aki, hannunta rik'e da wata y'ar roba dake cike da man gyad'a, murmushi ta saki ganin yadda Nahna ke sharar baccinta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login