Showing 3001 words to 6000 words out of 25209 words
Chapter 2 - RAYUWAR MAKARANTA FREE BOOK BY ZAHRA ROYAL.txt
fa muka fara zamanta"
Atu zatai magana Hauwa ta d'aga mata hannu tana kallon yarinyar kamin ta ce
"Zaku tashi daga kujerar nan ko kuwa, yanzu jikin yarinya yayi tsami, na rantse yadda nake cike da yaushin nan k'ila akanku zan sauk'e shi wallahi"
Hauwa ta k'are maganar tana maka masu wata uwar harara, Dole tasa ba shiri suka kwashe jakukunan su suka k'ara gaba suna tafe suna k'unk'uni.
Zama Hauwa tayi tana cewa
"Kaga y'an banza naga alamar makarantar nan sai ka zama d'an iska marar kunya tukunna zaka zauna lafiya da kowanne shege".
Atu zatayi magana Malami ya shigo ajin, gaba d'aya suka mik'e suna gaisar dashi.
Bayan sun zauna ya fara gabatar masu da lasin English zai rink'a d'aukarsu had'e da gabatar masu da sunansa Mlm Buhari.
Ana cikin Lasin Hauwa ta d'an saki dariya k'asa-k'asa tana ma Atu rad'a a kunne tana cewa
"Atu dubi yadda yake koyawa yana wani mik'e hannu yana rangwada kamar wani d'an daudu wallahi, ga iyaye a turancin nasa sai kace Nasara a gari"
D'an matsawa kad'an Atu tayi tana magana a hankali tana cewa
"Kinga Hauwa babu ruwana karya jiki wallahi, ke naga alama har yanzu bulala bata koya miki hankali ba dan.......
"Heeyyy you"
Da mugun sauri Atu ta kai dubanta inda Malam Buhari yake tsaye a gaban allo yana kallonsu fuska a murtuke.
Wani miyau Atu ta had'e tana magana k'asa-k'asa yadda Hauwa kad'ai zata jita ta ce
"Shikenan mun shiga uku yau zamu lallasu wallahi, ko miye ke ke ja mana wallahi Hauwa, na kusa daina zama tare da ke"
Tsaki Hauwa taja tana d'an tab'a tana nuna mata inda Mlm Buhari ya nufa.
Sauk'e ajiyar zuciya Atu tayi tana kallonsa ashe D'aliban dake kujerar bayansu dasu yake.
Suna ji yake cewa
"Surutun uban miye kuke min a cikin aji, kuzo ku fice min daga class ba'a min surutu a cikin aji dan uban mutum"
Fara masa magiya sukai suna cewa
"Dan Allah Malam kayi hakuri wallahi ba surutu muke ba, tabbayata take kawai na bata amsa kayi hakuri dan Allah"
"Ku fice min daga class na ce ko?"
Sumi-sumi suka fice daga class d'in su uku.
Bin bayansu yayi yana cewa
"You a nan zaku tsaya ku duk'a k'asa"
Kamar zasu fashe masa da kuka suka duk'a suna sake basa hakuri amma ko kallonsu baiyi ba ya koma class d'in ya ci gaba da gabatar da lasin nashi.
Yana gaf gamawa lasin d'in Malam Add'au ya biyo ta wajan class d'in ganin Yara a d'uke a k'asa yasa shi biyowa ta wajan.
Kallonsu yayi fuska babu wasa ya ce
"Kai ubanmi kukayi da aka fito daku waje?"
Zasu bada amsa Malam Buhari ya fito yana cewa
"Wallahi Malam Add'au surutu suke min a cikin aji, gasu nanma ka d'an lallasa min su kamin na gama lasin d'in nan"
Yana fad'ar haka ya koma class d'in su Hauwa na kallon abunda ke faruwa a waje ta window d'in class d'in.
Suna ganin yadda Malam Add'au ya zage sai jifgar Yara yake sai da yayi masu bulala goma-goma tukunna yana gamawa ya ce
"Ku tashi kunga wannan filin tsakiyar ajin naku ku share min shi tass ya sharu idan baiyi ba kuma zaku k'ara jama kanku wani dukan".
Da sauri suka mik'e suna kuka d'aya ce kad'ai batai hawaye ba a cikin su sai idonta dake gaf cika da hawaye.
Da azama suka shiga ajin suka d'akko tsintsiyar shararsu suka fito suka fara shara baji ba gani.
Bayan Malam Buhari ya fita ajin ya kaure da surutu.
Hauwa ta ce "gaskiya wasu Malaman suma akwai mugunta, ki duba ki gani tun d'azo suke sharar wajan can fa da alama wallahi sun jigatu"
"Uhmmm ai daga yanzu idan Malam Buhari ya shigo kinga sai kowacce ta kama kanta tayi shuru, ta rufa ma kanta asiri ai, tunda yanzu ansan halinsa ya tsani yana aji kana ma y'ar uwarka magana, kana masa surutun banza"
Hauwa zatai magana kenan suka ji ajin yayi wani shuru kamar mutuwa ta gifta da wajan.
Da sauri Atu da Hauwa suka kai dubansu a gaban Allo.
Ganin y'an SS3 ne suka cika ajin sunkai su biyar Maza biyu mata biyu.
A hankali wata daga cikinsu ta ce
"Surutun uban mi kuke mana?, kun cika mana kunne da surutu"
Shuru akai bamai iya bata amsa.
D'ayar ta sake cewa
"Ina shugabar class d'in nan take"
D'aya daga cikin y'an ajin ta ce
"Babu ba'a nad'a ba"
Wani namiji daga cikinsu ya nuna wata Binta dake zaune a gaba ya ce
"Kee daga yau ke ce shugabar ajin nan, daga yau idan muka zo muka taradda ajin nan ana surutu tofa kin shiga uku domin ko wanne hukunci a kanki zamu d'auka, dan haka da mun fita ki rubuta mana duk wacce tayi surutu a takarda, kin gane?"
Binta jikinta na kyarma badan tana son wannan shugabancin da aka bata ba ta amsa da eh.
Suna ficewa daga class d'in Binta ta zauna tana fashewa da kuka.
K'awarta Fiddausi ta dafata ta ce
"Kiyi hakuri yanzu dai ki yago faida ki fara rubutu duk wadda yayi surutu karma ki jama kanki".
Hauwa zata mik'e domin zuwa inda su Binta suke Atu ta rik'e mata hannu tana cewa
"Kee Hauwa mi kuma zakiyo wajansu?"
"Kinga ki cika ni na je na amshi faifar ni na rubuta mata, tunda naga ita da alama bazata iya ba"
"A'a fa Hauwa irin haka fa ne yasa na ce mu dawo baya da zama, da yanzu muna gaban da k'ila ni ce ko ke ce za'a nuna a matsayin shugabar class d'in nan, haka kawaii a d'ora maka nauyin da bazaka iya dashi ba, duk irin haka nake gudu"
Badan Hauwa taso ba ta koma ta zauna, tana hararar Atu tana mitar tana shigar mata hanci a kudundine wallahi.
Atu ta ce "eh na dai ji komi zaki ce, ki ce dai saura kije kiyi abun ya k'are kanmu, dama sai tsaya iya ke kad'ai ne to"
Su Binta suna d'akko Faifa ta mik'e a tana cewa
"To wallahi yanzu zan fara rubuta masu surutu duk wadda ya bari sunansa ya shiga a nan cikin faifar babu ruwana nayi gargad'i karma ka ce na fara ban sanar ba"
Tana gama fad'ar haka ajin yayi shuru, sai marassa jin ajin wasu dake magana k'asa-k'asa suna rad'a duk tana kallon kowa tana halkance da kowa, duk wadda ta ci karo da bakinsa na motsi rubutasa take kawai........
*RAYUWAR MAKARANTA*
*©Zahra Royal Star*
Page 2
A hankali aka buga k'araurawar fita break, gaba d'aya ajin ne ya d'auki surutu kowa ya d'auki y'ar jakar sa had'e da kular abincin sa yayi waje.
Hauwa ta kalli y'an bayansu dana gabansu ta ce
"Sorry amma ya sunanku ne?"
Harara Atu ta makama Hauwa tana k'ok'arin janta su fice waje amma ta dake tana kallon wa'inda ta tabbaya.
Murmushi suka saki, d'aya daga cikinsu ta ce
"Ni sunana Hadiza, wannan kuma Ammama sai kuma Fatee"
"Masha Allah, ko zamu iya zama K'awaye"
"Eh man babu damuwa ai, kuzo mu fita waje, inda muke zama muci abinci, naga kamar yau kuka fara zuwa ku hakane?"
Murmushi Hauwa ta saki tana cewa
"Eh yau muka fara zuwa"
Ficewa sukai a tare suna raha kamar sun dad'e da sanin juna, ba abunda Atu keyi sai kunbure-kunbure danmi Hauwa zata jawo masu wasu a cikinsu.
Zama sukai akan wasu duwatsu su duka. Atu na kallon yanayin makarantar kota ina d'alibai ke wucewa wasu na tafiya gida break, suna bi ta cikin daji su wuce. School d'in akwai girma sosai ta yadda zaka iya fita ta bayanta ta cikin jeji, ka dawo kowa bai sani ba, shi yasa da Malamai suka gane har nan wajan ana zuwa taran makara, saboda wasu y'an iskan school d'in suna biyowa ta cikin daji da safe.
Maganar Hauwa ta katse d'an shurun daya gifta jin tana cewa
"Wow Hadiza kwad'on tuwo kikazo dashi?, kai wallahi ina son kwad'on daddawa kuwa"
Murmushi Hadiza tayi tana kallonta tana yayyaka tuwon data zo dashi tana niyar kwad'awa ta ce
"Eh da shi nake zuwa, ku ai naga y'an gayu ne ku, da indomi da kawai fa kuka zo dashi"
Hauwa ta tab'e baki cike da jin haushin abunda ya faru d'azo bayan fitar su aji, kamin su shigo class sun aje kayansu sadda zasu dawo an bud'e kular su an sace Kwan guda biyu ba'abar ko guda ba, anci rabin indomin anbar masu sauran.
Tab'a ta Fatee tayi tana cewa
"Hauwa ga kwad'on mai da yaji ni kuma na Yi, Bismillah. Tunanin mi kike naga kinyi shuru?"
Tsaki Hauwa tayi tana cewa
"Wallahi abinci muka bari a cikin aji d'azo da safe muka tafi house d'inmu domin yin aiki da shara, sadda za'a shigo aji an samu wani d'an iskan ya bud'a mana abinci ya cinye rabi"
Dariya Ammama ta saki tana cewa
"Kashh dan yau ne zuwanku na farko shi yasa, amma ai wake barin kayansa a cikin aji ya tafi yawo, ai in gaya maku ba'a yin haka nan, daga yanzu ko jakarku karku sake ku k'ara barinta a class idan zaku fita, ku rink'a sagala abunku ku fita da ita"
Atu data fara cin indominta ta kalli Ammama bakinta cike da abinci ta ce
"Tofa ashe class d'in namu akwai b'arayi tabd'i jam"
"Ai ko b'arayi ma idan kinji b'arayi, baka da damar aje abunka mai mahimmanci a class ka fita, baka dawo kaga anyi ciki dashi ba"
Cewar Hadiza ta idasa maganar tana kai kwad'on tuwo a bakinta bayan ta gama kwad'a shi.
Wani faranti ta d'akko ta zubama Hauwa ta mik'a mata.
Amsa tayi ta fara ci. Atu dake kusa ta ce
"Ni dai na k'oshi ga Indomi idan zaku ci, ke kuma Hauwa baki cin indomin ne?"
Hauwa ta cinye kwad'on data d'ebo zata kai bakinta bayan ta had'iye ta ce
"A'a ni bazanci ba gaskiya ki basu idan zasu ci to, amma ni abun ne ya fice min a rai tunda aka bud'a aka cinye rabi na ce dama wallahi bazanci ta ba"
Tab'e baki kawai Atu tayi tana juyowa gasu Ammama dake ta d'arkar abincinsu, zatai magana ta kalli Ammama, sake da baki ganin yadda ta wani cire hijab ta d'aureta a k'ugunta sai faman cin kwad'onta take babu abunda ya sha mata kai.
Atu ta kasa hakuri ta ce
"Ammama miye haka Kuma Fisbilillahi?"
Ammama bakinta cike da kwad'on tuwo bata had'esa ba ta ce
"Mi kuma nayi?"
Atu ta nuna ta da yatsa tana cewa
"Dube ki dan Allah kin wani yaye hijabinki kina cin abinci, kuma ga mutane Maza na wucewa ta wajan nan"
Dariya Ammama ta saki tana duban Atu ta ce
"Ke nifa haka nake cin abinci na, dan yau kuka fara zuwa shi yasa zaku yita ganin sabbin abubuwan da baku saba gani ba, ke dai ci abincinki kawai, ai wajan ba hayaniyar mutane ma, shi yasa muka zab'i zama bayan gidajan Malamai arna da ake kawowa daga wata uwa duniya"
Zaro ido Hauwa tayi tana amshe zancen da cewa
"Kee dan Allah wai a nan wajan wasu ke kwana Malamai?"
"Kware da gaske kin dai gani, a nan suke kwana"
Hadiza ta bata amsa
Hauwa ta gyara zamanta akan dutsin da take zaune ta d'an gaji da zama a samansa kad'an ta d'an yatsine baki tana cewa
"Tabd'i jam, basu gudun dare yayi, yanzu Fisbilillahi ai bazan iya zuwa koda hanyar school d'in nan ba ce cikin dare bare ace na shigo cikinta, duba ki gani miye zai hana Tanbotse a school d'in nan, kota ina daji ce fa, gabas Kudu yamma arewa ki duba fa"
Ta k'are maganar tana faman nuna yanayin school d'in da hannu.
Hadiza zatai magana aka buga k'araurawar komawa class.
Da mugun sauri Ammama ta fara had'a kayanta data babbaje a wajan.
Su duka tashi sukai suna saurin had'a kayansu.
Hauwa ta dube su da d'an mamaki tana cewa
"Kubi a hankali mana wannan sauri haka?"
Hadiza ta kalleta da mamaki, sai kuma tayi murmushi tana kauda mamakinta ta ce
"Har yanzu da sauranki Hauwa, yo ai nan idan ba saurin mukai ba aka rufe mintina ashirin ko goma yanzu nan zakiga y'an SS3 sun fara jifgar mutane, danmi baka koma class cikin lokaci ba, bugu suke nake gaya miki duk wadda aka gani a waje bare idan ba'a dad'e da komawa break ba, gara muje ajin mun idasa acan, bana son abunda zai tab'a lafiyar jikina"
Atu data yi gaba tunda taji abunda Hadiza ta ce domin tama fi Hadiza rashin son a tab'a lafiyar jikinta.
Da sauri suka take mata baya a haukace kamar sabbin mahaukata suka idasa class d'in, domin har sun fara bugun duk wa'inda sukai saura a waje, ko kuma asa mutum tsallan kwad'i har sai ya idasa class da tsallan kwad'in.
Suna shiga suka baje akan kujera da yake kujerarsu tana kusa da juna ce, a haka suka fara uban surutu suna yi suna idasa cinye abincin da yayi saura.
Suna cikin haka suka ji class ya d'au shuru, ba shiri har Ammama na niyar kifar da sauran kwad'onta dake akan cinyarta ta kusa cinyewa ta tashi tsaye.
Da sauri kuma ta koma ta zauna tana rufe kular da sauri ta sata a k'ark'ashin kujera.
Y'an SS3 ne wa'inda d'azo suka bada umarnin a rubuta masu, masu surutu.
Jikin kowa yayi sanyi sai binsu ake da kallo.
Wata daga cikinsu tana yatsine baki ta d'an dod'e hancinta tana cewa
"Ohhh My God, class sai warin daddawa yake, dubeku k'azamai da'aAllah"
Wata ta dafa mai maganar tana cewa itama
"Ke kam Salma ai dole suyi k'azanta baki ganin har yanzu yarintar primary bata idasa sakinsu bane, duk sun cikama mutane aji da warin daddawa"
Itama ta idasa fad'ar haka cike da isgilanci suna watsa masu wani mugun kallo.
Ba wadda ya isa yayi koda tari ne a cikin ajin suna dai kallonsu kawai.
D'aya daga cikin Mazan ne ya ce
"Ina shugabar class d'in take?"
Da sauri Binta ta mik'e tana cewa
"Gani nan"
"Yawwa ki fiddo da faifar da kika rubuta mana y'an surutu ki fito gaban allo ki kira sunan kowa, kowacce taji sunanta ta fito nan gaban allo"
Ya idasa maganar yana kallon y'an class, da yawansu tsoro ya cika masu zuciya kowa na addu'ar Allah yasa dai baiyi surutu ba, Allah yasa dai ba sunansa a ciki.
Wato sunan data fara kira ne ya ba y'an class mamaki ba kad'an ba, wato Hauwa Rabi'u.
Da mugun mamaki Hauwa ta mik'e tana kallon Binta kallo irin na zaki ci uwarki ne idan na kamaki wallahi.
Atu ma dai mamaki take, ta ina Hauwa tayi surutu?, domin ita ce ta hanata yinsa da ba abunda zai hanata tayi komai ta fanjama fanjam.
Da haka tayita kiran sunaye ta kira ya kai mutum goma Sha.
Ba tausayi ko tausayawa a tafin hannunka zata ware a nan suka rink'a bugun wa'inda sukai surutu, bulala goma-goma.
Tabbas bulalar ta shigi Hauwa ba kad'an ba, domin tafin hannunta sunyi jawur.
Bayan ta koma kujera tana ta kallon Binta tana ayyana miya kamata tayi ma yarinyar nan ne ma?.
Bayan sun fita harda bada umarnin a sake rubuta wasu y'an surutun.
Hauwa ta mik'e bata sauka a ko ina ba sai a gaban kujerar su Binta.
Gaban kujerar ta buga da hannunta tana kallonta ido cikin ido ta ce
"Keee dan Ubanki ubanmi nayi miki da har zaki saka sunana a cikin y'an surutu, al'halin kuma banyi surutun ba?"
Shuru Binta tayi tana faman murgud'a baki.
Hauwa ta ce "kan Ubancan"
Ta shak'o wuyan hijab d'in Binta, y'an class na kallo babu wadda yayi gigin shiga fad'an, kowa na kallo, wasu ma so suke suga anci uban Binta, bare wa'inda ta rubuta sunansu cikin y'an surutu.
Hauwa ta sake cewa
"Zaki gaya min uban mi na tsare miki, ko kuwa saina gurji bakin shegiya yanzun nan?"
Binta ganinfa idan ba dagewa tayi ba itama tofa zata bata kunya ne a gaban y'an class mutumcinta ya zube.
Itama taci kular hijab d'in Hauwa tana cewa
"Naje na saka kiyi duk abunda kika ga zaki iya, da bakiyi ba zan saki ne?"
"Kutumar uba kaii yau zanci uban wata a nan wajan wallahi, har yanzu ban nuna maku kala ta ba wallahi a cikin class d'in nan, dole na fito da kalata ko an zauna lafiya, domin naga idan ba haka nayi ba bazan zauna k'alau da kowa ba"
Hauwa na k'are maganar ta daddage iya k'arfin ta kaima Binta wani naushi a tsakiyar bakinta, ai ko nan take bakin ya fashe ya haye yayi suntum ba kyan gani.
Wata uwar kururuwa Binta ta saki tana kuka tana cewa
"Wayyo Allah na shiga uku na, ta fasa min baki, na rantse da Allah bazan yarda ba, idan na yarda Allah ya tsine min"
Hauwa data sake ta tana rik'e da k'ugunta tana wata girgiza ta tsallar neman fitina tana makama mata harara ta ce
"Ai ko yau sai dai Allah ya tsine miki yarinya, kuma wallahi na sake naji wata magana ta fito daga shegen bakin nan naki akaina saina miki abunda yafi wannan kin san hali na yanzu sarai ba sai na tsaya na sake miki wani dogon bayani ba, gobe ma dan Allah ki sake rubuta sunana a cikin y'an surutu kin ji?"
Kuka kawai Binta ke yi domin ta lura Hauwa idan ta biye mata tofa dukan banza zata ci, dan bata da k'arfin k'arawa da Hauwa. Dole tasa ta koma ta zauna y'an class sai faman mata dariya suke k'asa-k'asa wai danma suna tsoron kar su fito fili da dariyar taci uban shege wajan sa sunansa a cikin y'an surutun aji.
Ai ko kamar sun sani duk wadda taga bakinsa na murmushi ko alamar dariya sunansa kawai take dafkawa a cikin faifar dake gabanta.
Kuma sai akai sa'a babu malamin daya sake shigowa har Hauwa tayi ta'asarta ta koma ta zauna.
Ammama har saurin cewa take "kai amma wallahi kin birge ni, da kika yi ma shegiya haka, dama haushi take bani, sai wani iyayin tsiya cike da ciki, kinyi maganinta ai"
Atu ta harari Hauwa tana cewa itama
"Keee dai Hauwa kinji dad'i wallahi, ke dai idan baki nemi magana ba baki jin dad'i a rayuwarki"
Kallonta Hauwa tayi rai d'an b'ace ta ce
"Dakata Atu miye nayi na jan magana a nan wajan kuma?, ita duk abunda tayi min baki gani ba kenan?, sai ni kike ganin laifi na, saboda dama na saba haka ko?".
"Hmmm"
Kawai Atu ta ce tana gyara zamanta a cikin kujerar da suke tana fuskantar Hauwa kamin ta ce
"Ko kad'an ba haka bane, itama batai dai-dai ba, domin Allah d'azo banga ko naji kinyi surutu ba, amma ai bai kamata kiyi mata haka ba ko?"
D'aga mata hannu Hauwa tayi tana cewa.
"Kinga kefa na lura bak'i k'i na barta taci bulis ba, kuma kema kin san bazan tab'a bari