Showing 15001 words to 18000 words out of 25209 words
Chapter 6 - RAYUWAR MAKARANTA FREE BOOK BY ZAHRA ROYAL.txt
Abdallah a kanta, hatta Lubna itama iya tsawon shekaru bata san dashi ba, inda har yanzu Lubna tak'i ta bari su haihu, Abdallah kuma yana son Yara ba kad'an ba, amma ya fuskanci matsalar tana daga wajan Lubna, dan ita cewa tayi bazata haihu yanzu ba, haka kawai aja mata tsufa da wuri.......
*RAYUWAR MAKARANTA*
*©Zahra Royal Star*
Page 7
*No. 12, Kawo Bos Stop Kano Nigeria*
Kwance take akan gado tayi d'ai-d'ai sai sharar bacci take.
Tsaye yake akanta yana kallonta cike da mamakinta, a hankali yasa hannunsa ya d'an bubbuga k'afarta.
A d'an firgice ta tashi tana mistsitsike idonta, kallonsa take cike da magagin bacci ta turo baki gaba tana cewa.
"Fisbilillahi Honey miye haka?, zaka wani tayar dani ina baccina mai dad'i"
Tsaki yaja yana cewa.
"Kin duba k'arfe nawa kuwa?"
"To ina ruwa na da k'arfe nawa, yanzu miye zanyi maka kuma?"
Kallonta yake ransa ya soma b'ace ya ce.
"Kin san fa da tafiyar da zamuyi zuwa Rimaye, kuma harda ke na ce zanje, dan mi zaki nemi waje ki kwanta, kuma kin san da tafiyar, tunda tun jiya na gaya miki"
Tsaki taja ciki-ciki ta ce
"Nifa gaskiya baza ni ba, bazanje wannan K'auyen ba haka kawai, kaima dan ba yadda zanyi ne na hanaka zuwan"
"Mi kike nufi ne garin Iyayen nawa kike kira da K'auye?"
Tashi tayi ta sakko daga gadon tana nufar toilet tana sake cewa.
"Ni karka min wata fassara yawwa, amma gaskiya ni bazan biku ba, sai kun dawo gaskiya, domin yanzu idan ma na ce zan biku to tsayar daku zanyi kawai saika dawo"
Tana idasa fad'ar haka tayi shegewarta toilet ta barsa nan a tsaye.
Wayarsa sa ce ta d'auki k'ara, hakan yasa ya katse tunanin daya fad'a ya ciro wayar daga aljihon gaban rigarsa, yana d'aukar kiran, ganin Abba ne ke kira.
"Yeah Abba gani nan zuwa insha Allah"
Abinda ya ce kenan ya katse kiran.
A hankali yayi parking motarsa a parking lot na gidansu. Mai gadi ya k'araso wajan yana mik'a masa gaisuwa, gaisawa sukai a mutumci, kamin yayi cikin babban parlon gidan nasu.
Sallamarsa a parlon tayi dai-dai da sakkowar Nahna, daga kan bene. D'an kallonta yayi ganin yadda taci wani magani, kamar wacce take jira ace tak ta fashe da kuka.
Tsaki ya saki yana duban su Abba da Momy dake a shirye dama shi suke jira kawai, hakan yasa suka mik'e a tare.
Momy ta kalli Abdallah da d'an mamaki tana cewa.
"Ah ina ita Lubnar take?"
Sosa kansa Abdallah yayi yana d'an basarwa ya ce.
"Momy wai bata da lafiya ne shi yasa, bazata iya zuwa ba"
Kallon tuhuma take jefansa dashi kamin ta ce.
"Na rasa wacce irin mata ce Allah ya baka Abdallah, amma komai ya kusa zuwa k'arshe da izinin Ubangiji, domin bazan zuba ido mace d'aya ta lalata maka rayuwa haka ba, ace tsawon shekara sha biyar, ko wadda zai irink'a maku addu'a baku aje ba, ace kuma matsalar komai da kake ciki matarka ce sila dol..... Da sauri Abba ya d'aga mata hannu yana yin gaba yana cewa.
"Please Momyn Yara ki bar zancan nan muje kawai"
"Uhmm"
Kawai Momy ta amsa tana kallon Nahna dake turo baki gaba. Momy ta makama mata harara ta ce.
"Ke kuma idan baki daina mana wannan bak'in halin naki ba, na rashin son jama'a da mutumta danginki, sai naci Ubanki wallahi, dan ubani garin Mahaifin naku kike ikirarin kefa baki zuwa K'auye, saboda kin raina mutane, haka naga kina ma Hauwa wani jijji da kai, ki kiyaye Nahna wallahi"
K'ara zunburo baki tayi tana cewa.
"Kiyi hakuri Momy"
Ko kallonta Momy batai ba tayi gaba rik'e da jikarta a hannu, tana d'an latsa wayar dake hannunta.
Abdallah shima ya jefa mata wani kallo daya sa Nahna Shan jinin jikinta ya ce.
"Idan baki daina wannan halin naki na wulakanci ba, wallahi wata rana saina barki kwance, shashasha kawai"
Shima yana fad'ar haka ya fice daga parlon yana tsakin tsaki.
Da saurinta ta take masa baya, kamar tayi kuka haka take ji, dan Allah ya gani ta tsani zuwa K'auye a rayuwarta, duk sadda zasu je Rimaye kullum sai ranta ya b'aci.
*Government Secondary School Rimaye Katsina State Nigeria*
Ammama ta d'an kalli tsiraron mutanen da yau suka zo school d'in, sakamakon an gama exams ta first term, ana wasan sati d'aya kamin a bada hutu. Bobe zata kasance juma'a ne ranar da za'ayi hutu ce.
A hankali ta juyo inda su Hauwa suke ta ce.
"Please kuzo muje hanyar gidan mutum d'aya musha magarya mana, da zaman banzar da muke Yi"
Da sauri ko Hauwa ta mik'e tana cewa.
"Kuma wallahi kamar kin san zaman nan ya ishe ni haka, shi yasa jiya ban shigo school d'in nan ba, duk ga yarinyar data jamin zuwa nan yau"
Ta k'are maganar tana nuna Atu, data mik'e tana kallon su Ammama da sukai radin tafiya shan magarya.
Atu ta girgiza kai tana cewa.
"Kai Kai Kai shan magarya har kuma wajan gidan mutum d'aya, gaskiya bada ni ba Hauwa kema bazan bari kije ba"
Wata y'ar iskar harara ta jefama Atu tana yin gaba tana cewa.
"Su Hadiza dalla can ku rabu da ita ni kunga tafiya ta, kuzo muje, dama idan aka biye take ai babu abunda za'ayi, matsoraciya kawai"
Da d'an gudu Atu tabi bayansu tana cewa.
"Dan Allah karku sa dole sai munje wata shan magarya, ni gaskiya tsoro nake ji wallahi"
Hauwa ta d'an tsaya tana rik'e k'ugunta ta ce.
"Wai tsaya Atu wani ya ce ki biyo mu ne?, kiyi zaman ki mana, dole aka ce ki biyo mu shan magarya ne?"
Dafe kanta Atu tayi ta ce.
"A'a amma ai kin san bazan tab'a zama na barki ki tafi ke kad'ai ba ai ko?"
Ci gaba da tafiya Hauwa tayi su Fatee suna take mata baya, sai nausawa cikin daji suke, suka fito daga school d'in suka mik'e titi kamar zasu bar gari.
Ba dan Atu na so ba ta bi bayansu, sai dan bazata iya zama ita d'aya a cikin school d'in ba, saboda duk yawanci babu yawan D'alibai.
Sosai suke shiga cikin daji suna kutsawa duk inda suka ci karo da magarya sai sun tsaya sun tsiga son ransu, sai da suka cika leda ko wacce ta samu da yawa, Atu badan tana so ba ta d'an d'iba kad'an.
har yanzu zuciyar Atu cike take da tsoro kar ace suga wani wadda suka sani a cikin dajin nan, ko su had'u da y'an SS3.
Sun gaf isa gidan mutum d'aya, suka tsaya, sai da suka ci uban yawo kamin Atu ta bud'e baki ta ce.
"Dan Allah Hauwa mubar tafiyar nan kizo mu wuce gida haka nan"
Juyawa sukai su duka suka kama hanyar dawowa school suna tafe Hauwa na cewa.
"Ban tab'a ganin matsoraciya irinki ba, ba gashi yanzu har munje mun dawo ba, bamu had'u da kowa ba, da har kina cewa zamu had'u da y'an SS3, idan ma mun had'u dasu ai suma shan magaryar ne ya kawo su, miye zasuyi mana?"
Tana rufe baki Atu ta tab'a ta tana nuna mata hanyar dake gabansu idonta a zare.
Gaba d'aya suka ja suka tsaya suna duban Y'an SS3 dake a gabansu suna masu kallon yau zaku ci ubanku"
Wani miyau Atu ta had'e tana cewa.
"Ai dama sai da na gaya maku shikenan yau mun bani mun shiga uku, Allah kad'ai yasan matakin da zasu d'auka akanmu"
Tsaki Hauwa ta saki da ganin farko ta d'anji tsoro amma sai ta ce.
"Ke dallah can karki wani damu babu abunda zasu iya yi mana"
Ita dai Atu ba dan ta yarda ba suka k'arasa inda suke.
Nan take ko, suka sasu duk'awa k'asa kan gwaiwowinsu.
Su Hadiza ba abunda y'an cikinsu keyi sai kuka, cike da tsoro suka fara basu hakuri.
Sai cewa sukai.
"Kaii dan ubanku ubanmi kuke a cikin daji haka?, saura wani abun cutarwa ya sameku kuja ma makaranta b'acin suna ko?"
Had'e hannu Atu tayi alamar ban hakuri tana cewa.
"Dan girman Allah kuyi hakuri"
"Ai ko yau zaki gane shayi ruwa ne, domin wajan Malamai zamu kaiku, su ai kunga sai kuyi masu bayanin abunda kuka je yi a cikin daji"
Kuka Atu ta fashe dashi tana cewa.
"Dan girman Allah karku kaimu wajan Malamai, kuyi hakuri kuyi mana hukunci a nan, ba sai munje wajan Malamai ba"
Wani daga ciki y'an SS3 ya ce
"Ke rufe mana baki, fad'a min sunayenku d'aya bayan d'aya"
Ya idasa maganar yana sakko da jakarsa, ya yago faifa.
Hauwa ko a jikinta saima ta fara fad'in sunanta, harda su Hararar Atu domin ji take duk ta zubar masu da mutumci harda wani yi masu kuka.
Haka suka rubuta sunansu, suka tasa k'eyarsu a gaba zuwa cikin makarantar.
Suna tafe Atu na sharb'ar kuka, Hauwa sai harararta take, Atu ko ji take kamar ta shak'o Hauwa.
Suna gaf shiga makarantar Atu taga giftawar wata mota mai shegen kyau, dan kamar ta tab'a ganinta a wajan gidansu Hauwa da dad'ewa.
Atu duk da halin da take ciki hakan baisa ta kasa cewa.
"Lahhh Hauwa Kinga wata mota can ta wuce kamar nasan motar nan a gidanku, kamar y'an uwanku dake Kano ne suka zo Rimaye"
Da mugun sauri Hauwa ta waiga, sai dai motar har tayi nisa kad'an take hango ta.
Hauwa ta ce.
"Ehh k'ila sune, domin dama Inna ta ce min yau ne zasu zo, kuma kamar can zanyi hutuna ma. Amma ni wallahi banso zuwansu ba"
Ta k'are maganar had'e rai.
Atu ta ce
"Kamar ya baki son zuwa?, birnin ne baki son zuwa?"
"Ke miye a birni to wadda K'auye babu?, ni haka nan bana son zuwa, saboda kinga wannan Nahnar na tsane ta, kamar yadda take nuna min bata son y'an K'auye, duk sadda naje Kano fad'a kawai muke da ita, sai wannan matar Y Abdullahn Lubna, dan ita tsabar wulakanci ta ce ma Nahna ban waje, shi yasa y'an Birni basa birge ni, wulakanci ne dasu wallahi"
Atu ta sake rik'e baki ta ce.
"Tabd'i jam mu kinga bamu da y'an uwa a birni gaskiya, idan ko hakane to basu da kirki"
Hauwa zatai magana suka k'araso inda Malamai ke zama a bakin wata bishiya suna shan iska duk sun fito daga office nasu.
Atu sai y'an cikinta suka k'ara hautsinawa.
Ashe har Y'an SS3 sun rigasu isa sunyima Malaman bayanin komai.
Suna zuwa Mlm Add'au ya banka masu wata uwar tsawa ya ce.
"Wato ku y'an iska ne ko?, to maza ku nuna mana yadda ake hawan bishiya, tunda naga shan magarya kuka je maza ku nuna mana yadda ake shan magaryar"
Su Hadiza sai hakuri suke basu, suna duk'awa k'asa gaba d'ayansu.
Sauran Malaman suka sa Y'an SS3 d'in su d'ebo masu Daman bulali masu yawan gaske.
Ai ko Atu tunda tayi tozali da yawan bulalin da aka d'ebo ta fara kuka kamar k'aramar yarinya.
Ko wanne Malami sai da ya d'auki bulala biyu-biyu masu kauri da tsayi, Malaman dake wajan sun kai su biyar a zaune a jere.
A tafin hannu suka fara bugunsu, Hauwa ce ta farko, ko wanne Malami dake zaune a wajan, sai yayi masu bulala biyar-biyar, idan ka had'a kusan bulala arba'in da biyar kenan.
Iya buguwa sun bugu domin hannun Hauwa sunyi jawur jini har yana kwanciya, Atu da Ammama ne kawai kake jin kukansu a wajan, baya ma Atu tasha kuka kamar ba gobe, sai tsine ma Ammama Atu keyi, domin ita ce ta fara kawo maganar tafiya shan magarya.
Tafe suke bayan an gama masu hukunci Atu sai jan majina take a hanci tana cewa.
"Ai wallahi Ammama kin cuce ni bazan yafe ba"
Murtukewa Ammama tayi tana murza hannunta daya duka tana cewa.
"Haba Atu da wanne zanji ne?, kima kyale ni da dukan da mukasha"
Tsaki kawai Atu taja tana kallon Hauwa ta ce.
"Ke kuma gobe sai ki k'ara janmu muje shan magarya"
Shuru Hauwa tayi tana murgud'a baki.
Idasawa aji sukai suka d'au sauran kayan su, suka fito suka kama hanyar zuwa gida.
Shigar Hauwa gidansu yayi dai-dai da sawo kai da Abdallah yayi, sai Allah yasa sukai k'aro da juna.
A mugun zabure Hauwa tayi baya, amma duk da haka sai da Abdallah ya d'aga hannun ya sharara mata mari.
Da sauri ta rik'e kuncinta tana kallonsa da mamaki.
Dama ya saba mata haka, tasan da dad'ewa ba wani k'aunarta Y Abdullah yake ba.
Zata bud'e baki tayi magana, ya riga ta cewa.
"Ke wacce irin marar hankali ce?, shashasha kawai k'azama, dube ki da'aAllah, kina tafiya kamar ba mace ba, babu natsuwa ko kad'an a tare dake"
Wasu hawaye masu zafi ne suka soma gangaroma Hauwa, tana jin zuciyarta na k'ara tsanar Y Abdullah duk da wata zuciyar tata na bala'in sonsa da birgeta.
Ta sake jin saukar maganar sa yana cewa.
"B'ace min da gani a nan wajan"
Jiki a sanyaye ta rab'asa ta wuce tana goge hawayen dake mata zuba.
Tana shiga da gudu taje ta haye cinyar Momy dake mata dariya sai murnar ganin juna suke, harta manta da abunda Y Abdullah yayi mata ma.
Abba dake kallonsu ya a murmushi ya ce.
"Ah ah Hauwar Abbanta, baki ga Abban naki bane, Momynki kawai kika gani ko"
Da sauri Hauwa ta mik'e taje inda Abba yake ta rungumesa tana cewa.
"A'a Abba duk murnar ganinku ne yasa ai"
Wani tsaki Nahna dake gefe, ta saki k'asa-k'asa tana bin Hauwa da wani kallon banza.
Inna ma murmushi take tana kallonsu cike da sha'awar ahalin nata.
Tashi Hauwa tayi ta ce.
"Momyna bari naje na cire uniform nazo"
Zata wuce ta gefen da Nahna ke zaune ko ci kanki bata ce ba, kuma ta ganta itama, amma Hauwa ta k'ara kame kanta domin idan raini ne Hauwa ta tsane sa, shi yasa ko kallon inda take batayi ba, Momy na sane dasu zatai magana Inna ta rigata cewa.
"Wato har yanzu baku daina wannan gabar a tsakaninku ba ko?"
Momy ta amshe da cewa.
"Ai Inna ba mai matsalar nan sai Nahna ita ce mai wulakancin, kuma wallahi idan ta sake saina ci mata mutumci wallahi"
Inna ta ce
"Ai itama harda Hauwar, idan ita bata tanka mata ba, ita tayi mata mana, tunda dama ai ta girme ta, dan ni gaskiya bana son irin abunda ke faruwa a tsakaninsu, kuna jini d'aya amma bakwa jituwa da juna"
Abba yayi gyaran murna yana ma su Hauwa nasiha da akan su so jununsu, amma Nahna bana jin nasihar Abba tayi tasiri a tare da ita, domin Abba na fita waje Nahna ta ce.
"Momy amma please yau zamu koma gida ko?"
Dak'uwa Inna tayi ma Nahna tana cewa.
"Ungo nan kinji Nahna, ashe kece marar mutumcin dama?, to a nan zaku kwana, ko zaki koma ke kad'ai ne?, ai ga hanya nan bismillah............
*RAYUWAR MAKARANTA*
*©Zahra Royal Star*
Page 8
*Government Secondary School Rimaye Katsina State Nigeria*
A hankali Hauwa ta mik'a hannunta ta amshi Report d'inta. A hankali Malamin ya bita da murmushi yana kallon y'an class d'in ya ce
"A first term d'inmu ga wacce tazo ta d'aya a cikin ajin nan, dan haka ku tafa mana please"
Gaba d'aya ajin ne ya d'auki tafi, murmushi mai sanyi kawai Hauwa ta saki tana komawa ta zauna akan kujera.
Tofa tunda Mlm ya fad'i haka, wasu daga cikin y'an class d'in suka fara bin Hauwa da wani kallon uku saura wasu hassada ce cike da cikin nasu.
Duk K'awayen Hauwa sune suke bi mata a report d'in, Atu tayi na biyu, Hadiza na uku, sai Ammama na hud'u Fatee na biyar, sai ko su Asiya da Hafsat dake bin bayansu.
Abunda ya k'ara jan wasu y'an surutai a cikin ajin kenan, wasu ma cewa suke ai Malamin dake basu Report d'in saurayin Hauwa ne, sonka kawai aka nuna ba wai adalci akai ba.
Asiya dake tafiya da Hafsat bayan an sallami kowa an raba report anyi hutun sati uku, kowa na tafiya a k'asa d'alibai cike da farin cikin hutun da akai masu.
Asiya ta kalli Hafsat dake cika tana batsewa ta ce.
"Amma gaskiya an cuce mu wallahi, ace duk class d'inmu a rasa su waye za'a ba na d'aya dana biyu har zuwa na biyar, sai masu biye ma wancan yarinyar mai iskokai a saman ka?, wannan abun da kinji kin san wallahi son kai ne kawai aka nuna mana"
Tsaki Hafsat taja tana cewa.
"Ke nifa na tsane ta wallahi, ta fara tare mana wani abun da mu ya kamata mu fara samunsa ba wai ita ba, da sauran rukuninta, dole ne sai na ja mata kunne, dan naga sai wani shewa suke kamar da gayya ma"
Tana idasa fad'ar haka tayi gaba inda take hango su Hauwa suna tafiya ita dasu Ammama, Asiya na faman kiranta amma ina tayi gaba, idonta ya rufe da masifa.
Su Hauwa suna cikin tafiya kawai suka ga an Sha gabansu.
Da d'an mamaki Fatee ta kalli Hafsat, ta d'an harareta dan itama haushinta take ji ta ce.
"Ke kuma Malama miye haka?, muna tafiya zaki wani zo ki tare mana gaba, bama son k'auyenci fa"
Wani mugun kallo Hafsat ta jefama Fatee tana nunata da yatsa ta ce.
"Keee kinga rufe min bakinki a nan wajan, mai warin baki Kawai, ki daina ganin kunyo na farko a cikin class d'inmu, idan banda wannan shashashar dake d'oraku tana baku satar amsa, ku kun isa ku goga damu ne?"
Hafsat ta k'are maganar had'e da nuna Hauwa tana wani mata kallon banza
Hauwa ta rik'e k'ugunta tana k'arema Hafsat kallo a tsanake, Atu zatai magana Hauwa tayi saurin sa hannunta ta rufe bakin Atu
Tana d'an harararta ta ce.
"Karki sake ki ce komai, dan tsaf na sanki yanzu zaki b'ata mana lamarin"
Ta sake juyowa wajan Hafsat dake tsaye. Zuwa can saiga Asiya ta iso.
Hauwa ta d'an taka ta matsa kusa da Hafsat sosai kamin ta nunata da yatsa ta ce.
"Ya ma sunanki ne baiwar Allah?"
Wata uwar harara Hafsat ta dankara ma Hauwa ta na jan dogon tsaki ta ce.
"Ba'a sani ba, wata k'ila ko sunan Gyatuma ne dani ba..... Bata idasa maganar ba taji wani gigitaccan mari tasssss, wadda ya kusa sa jinta da ganinta daina aiki.
Da mugun sauri Asiya ta nuna Hauwa tana huce ta ce.
"Kutumar uban nan Kaii, shine zaki mare ta?, ke wace ce?"
"Ni uwar da ta haife ta ce, baki ji miye ta ce bane daga k'arshe?"
Hafsat dake rik'e da kuncinta cikin jin rad'ad'in marin da ta ji shi a bazata, take kallon Hauwa da d'unbin mamaki.
A zabure Hafsat ta kai hannunta domin rama marin da Hauwa tayi mata, kamar k'iftawar ido taji an rik'e tsintsiyar hannunta.
Ido cikin ido Hauwa take kallon Hafsat ta ce.
"Ai wallahi Uban kuturu yayi kad'an bare na makaho, ke kin isa na tsaya ki mare ni?"
"Ni kuma kika mare?, ai na rantse da sarkin mulkin Allah yau sai na rama mari na wallahi"
"Hhhh au haka dan Allah?, sai ki mare ni mu gani, ai mari na mare ki, kuma