Showing 24001 words to 25648 words out of 25648 words
Chapter 9 - JININ SARAUTA 2 Complete By Oum Afnan.txt
a cikin ,alabarshi ta zauna har sai cikin yayi qwari ta dawo,saboda yina jin kunyarta da irin wuyar da tasha ace zulaikha tazo ta bashi da safely.
Saida cikin diyanah ya shiga Wata na bakwai sannan suka dawo qasr da tsireren ciki,ba wanda yasan plan dinsu sai Sarah itama takanje time to time har suka dawo,wannan abu ya caki zuciyar zulaikha da kuka ta koma wajen boka ya shaida mata yarinyar itace magajiyar wannan masarautar bazaa iya zubarwa ba.
Dole ta chanja dubara,itace kawo mata jiko Wanda in tasha er zata iya mutuwa,amma tar diyanah ke kallonta,saidai ta kar6a tayi kamar xata sha taje tayi pushing dinsa a toilet.
Lokacin da cikinta ya shiga Wata Tara ,shine aka wuce kasar Egypt don ta haihu acan kuma a lokacin ne ,gimbiya zulaikha tayi nufin qaddamar da nufinta na kashe su'adah saidai zakaran da Allah ya nufa da cara dole yayi,daganan abubuwan da suka faru suka faru
°°°
CIGABAN LABARI
Oum Aphnan✍️
[7/27, 5:31 PM] Bamalli✌️: 81 - 85
*Jinin Sarauta*
Cikeda Murna gimbiya khalesat ta nufi sashenta ,barorinta suna rirriqe mata da rigarta dake sharan qasa,Dole tayi murnan tafiya don ita dama bamaison zaman waje d'aya bane,gwara ta bi baba saratu ,tasan zata hadu da er uwanta Zarah ,suyita flexing a can gidansu.
Suna shiga parlour nata ta umurci kuyanga zubaida mai kulada suturunta da ta harhada mata kaya a madaidaicin Akwatine kurum
Tana wucewa saudah ta taso daga kujeran da take tazo nata kujeran ,tawani dunkule hannu "Hutawarki lafiya,er sarki jikan sarki " buge bakinta tayi da hannu
"Kam kam kam wallahi saina rama "
Gwale tai mata ta dirko akan kujeran suka fara zagaye kujerun falon
"Wallahi zaki rame anmata", Aikuwa ta suri throw pillow tana Dad'a k'ara qaimi wajen gudunta....sunyi kewaye na uku ya shigo dakin da gudu taje ruqunqumesa
" wayyo yaya na ka 6oyeni "
Jawota yayi ya fiddota ta gabansa ,itama ya kamo hannun Saudah ,tsugunawa yayi daidai fuskarsu "Qawa da qawa mun gansu a Rana... Jiki kamar ba yanxun nan kika bada umurni aka kora mana muguwar mu ba,saigaki kina aikin En yara "
Fincike hannunta Gimbiya khalisah tayi ta rungume Saudah "Hhh to dai na wasa ne,En baqinciki saidai Ku mutu"
Suka ko kwashe da dariya suka tafa hannuwansu.
Janyo hannunsu yayi yina dariya ya shiga ya zauna a 3seater ya zauna da kowacce a 6ari 6arinsa.
"Princess ynx bin su mommah zakiyi kibar nanne da yayanki?"
"Iyyeh lallai ne,sosai ma gobe ishaallah mun bar garin nan,kamar yanda kaima zaku wuce kaida aminiyata kowa ya koma ya banni ina fama da kewa "
"In natafi zakiyi kewata khalisah? "
"Sosai ma,ko ynx innadade ban ganka ba ji na nake kamar zanyi kuka...ina sonka yayana"
Tafada tana Dora kanta a kan cinyarsa
Saka hannu yayi yina shafa sumarta A hankali ya furta "Nima ina tsananin son ki er qanwata"
°°°
Rayuwa mai juyi juyi ,yanzu duk hanyoyin da faridah ke samun kudi ya toshe dama alhj bilyane jigo kuma an tsiyace,ga her excellency ta kirata wai karta qara zuwa mata gida mijinta ya fara zargin halaqarsu,ga PA Sam ya ma sa masu gadi a daina Barinta ta shigo masa gida ,gidansu itama kanta bazata iya zuwaba,yanzu ta dogara ga Allah ne ta dogara da aikinta ,don hakanema ta nema gidan ma'aikata na cikin asibitin ta koma da zama
Sam yanxu iskanci da biye biyen mata da maza sun fice mata a rai,yanzu ita soyayyar su'adha ne ya dawo mata sabo fil, tun sanda aka tabbatar mata da mahaifarta ta lalace kuma bazata ta6a haihuwaba ,tayi la'asar ta zama na Allah ,kullum ka ganta da cazbi da hijabi ,sai ko ka ganta tana kuka ko addu'a Sam duniyar ta fice mata a rai ,kullum tana ganin kukan marasa iyaye da En uwa in sun mutu a asibiti , tambayar ta shine ita in ta mutu wa zai yi kukan mutuwarta ?
Kamar kullum yauma Asabar zaune take tun da tayi sallar subahi akan darduman sallanta,kiran wayarta ne ya katseta ,da kamar bazata daukaba ,ganin ba number qasar nan bane
Sai kuma Wata zuciyar tace dauka fareda kila PA ne ya yafe maki
"Assalamu alaikum" shiru akayi ba a tankaba
Kamar zata kashe sai taji ance "Hello faridat ce kuwa?"
"Eh nice dawa Nike magana ?"
Dariyar ashararanci ya saki"Hhhh mata kenan masu duniya ,wato baki dauki muryanba ko? Karki damu alhj bilya ne,naji abun Asshan da ya faru dake a bakin qawarki na tausaya maki,saidai na barkine ki horu ki gane sata bai da riba, amma yanzu tunda naji labarin kin nafa'a kin rabu da qananun En iskan nan ,to kizo ga ticket din jirginan ki biyo ni Algeria... "
Wasu siraran hawayene suka sirnano mata
"Alhj bilya Nagode da jajenka a gareni ,saidai ina maka kyakyawar albishir ,tun ranar da na Bar ka ban kuma aikata wani abu da addini da al'adata ya hanani ba,kuma ka sani ina farinciki da wannan sabuwar rayuwar da Nike ciki a yanzu ,ina fata Allah ya kar6i tubana ,sannan in riski Allah ina mai imani,so kaima ina gayyatarka da ka shigo motar nadamar da na shiga ko ka samu rabauta duniya da lahira ,don yanzu dai ka manyanta ya kamata ka fadaku kasan annabi ya faku"
Wani muguwar dariyar rainin hankali ya saki "Lallai igiyar talauci tagama nadeki tayi maki cik!
Ba laifinki bane ,rashi ya kawo hakan amma still zan Baki dama ,yau zan taso daga Korea zuwa Algeria ,so daga yau zuwa dare duk abunda kika yanke zaki iya sanar dani,sai ki iskeni a can Algeria din"
"Hmmm ai shi kyakyawar aiki shine Wanda aka dawwama anayi ba'a fasaba ,shikuwa kauda aikin sa6o shine kaucema aikatata ,alhj bilya Nagode inamaka fatan shiriya ,kuma tunda ka ta soni a gaba,to zan karya layin nan ynx ,yanda bazama ka sake samuna ba ,bare kasa tubana yayi girgid'i"
Kirit ta kashe wayar.
°°°
Bayan sati guda da faruwar Abun
Farida na zaune a falon ta bayan sallr magriba tana laziminta ,tana jiran sallar isha,TV dinta da ta kamo tashar Aljazeera ne ta sauya zuwa CNN sannan ta rage qarar, ta cigaba da Jan carbinta in a dimly light room, tun tana lazimin tana tuno rayuwarsu na baya da mijinta da su'adah har ta fara shesheqar kuka tana add'ar mafita,yau gata kowa ya gujeta ,saboda mugun halinta da sa6on Allahnta
Kuka sosai takeyi ,a daidainan taga an hasko qonannen jirgin da yayi hatsari a yammacin yau wanda da ya taso daga Algeria zuwa Nigeria ,kafin aka fara nuno Manyan mutanen da ke cikin jirgin da suka rigamu gidan gaskiya ciki kuwa harda Hoton alhaji bilya da shahida.
Kuka ta fashe da shi ,kafin ta wuce suuu ta tafi sujudah"Allah Nagode maka ,da ban bisuba ,da yanzu na sameka cikin hanyar sa6onka ,ko yanzu nagode😢"
°°°
Gimbiya zulaikha kuwa daga gidan basu ajeta ba sai a bayan gari ,sannan suka juyo, ana fitar da ita kuwa ,kuka ta fashe dashi ,tanata lisafe lissafen yanda zata samu kudin zuwa wajen bokanta,don tasan kota koma gidansu raina mata wayo zasuyi gwara taje aimata maganin kowa,taje ta zauna a gidansu kamar na sati 1 kafin a tunzuro mai martaba yazo ya maidata....to amma ina zata samu kudin ? Bayan ba'a Barta ta dauki ko tsinke
Zinaren jikinta tagani ,a take murmushi ya su6uce mata ,anan take ta zazzaresu duka ta Tara a qaramar jakan hannunta ,mai daukeda ATM da sauran tarkacenta dasu keys din sashenta,sai kudi bai wuce 10k ba,napep ta Tara ta shiga ,kasuwa zaka kaini"
Kallonta yayi ,kallon tsaf ,ya San hajiya ce "To hajiya drop ko?"
Jinjina masa kai tayi
Tunda suka fara tafiya take masa masifa ,musamman in akazo gargada
"Kai wallahi na gaji kar kaje ka gwara mun kai da wannan emerciated keken naka,ka watsar mun da haqora,waima kasan no wacece? Nifa Matar sarkin garin nan ne,yanzu haka a pos dinnan inada kudin da zan siye kekenka da kai kanka goma ,to karka wahalar dani"
Fakan idonta yayi ya kalla jakan hannunta mai daukan ido
"Wow ga dama tazo".... Jan Wata arnen burki yayi ya dawo baya ragwaf ,aiko ta bugu kum idonta wasu tartsatsin wuta sukayi mata flashing ,kafin ta dawo hayyacinta ya fito da gudu ya warce jakar da gudu ya cancani hanya
Ihu ta fasa ta daura hannu aka" Na shiga uku ya kwacemun jakata, Ku taimaka mun" ta bisa a guje ko ganin gabanta batayi ,jama'a ma suka Dane masa baya din a kamosa
Sambatu ta kamayi "Wannan jakar shine ya qunshi duk fatana in ba'a kamasa ba shikenan ,nida gidan sarauta har Abadan ,don banda kudin siyen baqaqen karnukan da zaa yankawa Aljannu susha jini suji dadin yin aiki da zafi zafi" ai kamar Wanda aka mintsina ta kara yankawa da gudu ,batai auneba saidai taji mota tayi sama da ita ,kafin ta yunkurawa ta mike,Qatuwar motar daf tazo ta murtsiketa akan kwantan.
Haka kanta ya dagargaje namanta ya manne akan kwalta jini na sharara
Shikenan Allah ya kar6i ransa
Gimbiya zulaikha ta rasu batareda ta cimma burinta na komawa fadanba bare ta cutar da khalisah kamar yanda ta ci buri
FOUR YEARS LATER
Abubuwa da yawa sun faru masu dadi da maras dadi ,ciki kuwa harda haihuwan En biyun gimbiya diyanah duk maza, Dr Khalid an masa auren gida da er uwansa dukda baiso yanzu haka yarinyarsu kwananta sittin, suna qasar Spain yaje karo wani course rabonsa da 9ja shekaru hudu kenan,sai a wannan karon yike fatan dawowa da matarsa Habiba da diyarsu little diyanah
PA ma ya dawo da Haj Farida ,bayan yaje har gidanta yaga irin rayuwar da takeyi, sannan yaji labaran kyawawan dabi'unta a bakin makwftan ta da abokan aikinta ,yanxu haka suna zaune lafiya ,Haihuwane dai babu
Saudah kam da Gimbiya khalisah an zama manyan babes ,tamkar En shekaru ashirin nonuwa ya cika kirji ,suna gwara kan manyan maza .
A kuma wannan karon ne ,PA Yusuf ya harraqo da kudurinsa na son Aurenta
Shima kuma yanzu haka VP ya kasa ya tsare kawai aurenta zaiyi ,dukda hidimar za6e yataso bays samun zama amma ya turawa khalisah text msg cewar yina cikin layin manema
_Mu Had'e a littafi Na uku don jin Rayuwar Khalisah bayan girmanta kuma Waye zata aura_
Taku har kullum Hassenart Bamalli
(Oum Aphnan)