Showing 21001 words to 24000 words out of 25648 words
Chapter 8 - JININ SARAUTA 2 Complete By Oum Afnan.txt
Kewar waccn baqar dagan dai
"Ayyah na bari Ku gama zancen ne,ko har amaryar tawa ta tafine"
Dariya ya saki da qarfi har yina doka qafa,shikansa ya rasa me yasashi nishadi ,saidai ya alaqantashi da haduwa da muminan mace mai tsananin son addini
"Ya akayi kika gane amaryankine zulaikha? Toh bamu tabbatar ba ,adai samu cikin addu'a Allah yasa baba ya amince"
Siririn tsaki taja a hankali
"Hmm yarima kenan,ai labarin zuciya a tambaya fuska,kuma ita yarinyar bata shaida maka ko tanada manemiba? Kufa sarakunan musuluncine masu kamanta adalci,kar a tauyesu"
"Madalla ga samun mace mai hikima da hangen nesa, tunanin hakan da nayi shi yasa na nemi ganin babanta ,don na lura wannan amaryar taki mai kunyace,anyama zata iya kula da miji? Inajin dai sai kina daurata a hanya"
Mere Baki tayi ta cire kan telephone din a kunneta ,ta babballara ma abun harara
"Hmmm Allah yasa abokiyar zamace"
Kawai ta kife kan ta kurma ihu,tareda fincike dankwali kamar zararriya
"Allah ya hadani da namiji mai Zara da son aure aure...wai baba ,baban budurwansa ma tun yanzu yina kiransa da baba ,nikuwa saidai yace babanki...
_Mun dawo ba sa'a,ba banda chaji ,kuma anmun wiping komai na wayata,plz manage_
[7/27, 5:31 PM] Bamalli✌️: 71- 75
*Jinin sarauta*
Yarima kamar yanda ya fad'a kuwa yaje ya samu baban diyanah ,da tambayar izinin aure.
Da fari baban fir ya nuna qin yardarsa dukda dai babu wani tsayayye dake zuwa,saidai gudun wulakanci inasu ina dan sarki? Saidai nacin yarima ,don yarima suittt ya sauke girman kannan ,kullum yina jelen zuwa bada haquri tamkar Wanda matarsa tayi yaji ,saida ya shawo kan baba adamu da qyar ta hanyar bin manyan unguwa da En uwansa maza .
Shikam baba yasan yinayi don fir,diyanah ta nuna batason auren yarima,a cewarta matarsa zata iya kassarata,amma da lallashi da ban baki aka shawo kan ta.
Viki kam sati biyu jal aka saka,da iyayen diyanah Suka nuna basu da qarfi yace shi diyanah yikeso ba kayan dakiba,so yayi alkawarin zubawa diyanah komai,amma bai hanasuba in zasu qara mata da wasu abun.
Shikuma yaje ya gyara part din zulaikha ya maidata sama da yafi yawan dakuna ,itakuma part din zulaikhan ya gyarawa amarya diyanah
Biki na matsowa yayinda duk istikharan da yarima zaiyi akan diyanah yake tabbatar masa ,gareta akwai wani haske amma an kasa gane ko menene.
A gefe guda kuma zulaikha ta lashi takobin bata barin diyanah ta shigo mata gida don babanta ya shaida mata tanada qwari ,asiri kafin ya cita da wiya ,hakan yasa ta fitini babanta itafa lallai saiya yi asirinda zai raba diyanah da yarima,ga biki nata matsowa ,ganin abun baban kamar yayi sanyi kurum shine ta roki jakadiyarta da taimata hanyar malamai
Amma saita kwantar dakai
"Lantana bawan Allah Nike nema Wanda xai duba mun yiwuwar xaman lfiya da yalwar arziki da watannan yarinyar ,in babu a farraqasu "
"Aah uwar dakina wallahi irin wainnan yaran da naga makircinta ya firgitaki,yafi sauki kije wajen rikakken kahurin boka,kinga ni nasan wani boka ana ce masa hatsabibi ,aikinsa kamar yankan wuqane amma fa akwai kauce hanya,amma gimbiya wajen biyan bukatarka sai ka hada da En duba, an tayaka da du'ai ,alabarshi in bukata ya biya ayi istingifari"
Murmushin kissa tayi
"Hmmm lantana ina tsoron zuwa wajen mutanen nan marasa imani,du kwaso qarya su Fada maka,a ringa hadamu Fada da abokiyar xamata da mijina"
"Karki damu na yi dayane" haka suka shirya suka wuce wajen boka ta labarta masa komai dangane da aurensa harda rashin shiga dakinta da bayayi
Anan ya tabbatar mata dole aurensu diyanah saidai ko ayi masu firaqu gamida shashatau yanda kwata kwata zuciyarsa zai kauce a kan ta
Godiya tai masa suka juyo gida.
Aikuwa suna shigowa zamanta ba dadewa saigashi kamar an bugosa
Jakadiyarta na kasanta tana marmatsa mata qafa
Da sauri ta mike "Yarimana Kaine a dakina?...wow dole in hada party na murna ,yau watarana"
"Ina kikaje Nazo nemanki bakya nan" kame kame ta fara
"Ya isah zanje sallah ynx ,innadawo ki sameni a daki, inaso ki shiryamun list din kayan lefe naki da na amarya"
"Angama yarimana"
Yina fita ta daka tsalle ta rungume jakadiya kawai saita fashe da kuka
"Jakadiya Nagode,wai yau ni yarima ya shiga dakina? Har yike tambaya ta shawaran lefe،ke nicema zanyi list?...gaskiya in komai ya tabbata kyautarki na musammanne lantana"
°°°
Ta 6angaren diyanah kuwa tundaga ranar yarima bai qara kiranta a wayaba,bare yazo gida,kuma kota kira bayi dagawa ,tun abun bayi damunta harya dameta har gobe biki bako lefe ,gida ya cika da jama'a En tsegumi na zundenta banda masu taranta sunayi.
Wata abokiyar wasanta ne ta ga giftawar diyanah zataje yin alwala a bakin tank
"Oh oh su diyah anfa tara kayan ruwa ,hajiya diyanah ...oh princess diyanah Matar yarima ,yarinya anyi manyan duwawuka ga kayan ruwa sun cicciko qirji"
Hawaye ne suka surnano mata a ido kurum saita cigaba da alwala .
Wato kallon er iska sukemun ,yarima ya yaudareni ya kwashi gara ya ware,to Allah ka zama gatana
Da sauri ta wuce daki ta shimfuda darduma ta fara wadha tana jero addu'oi a sujjuda
°°°
Ranar daurin aure karfe shadaya zaa daura ,amma yarima sai yayi kwanciyarsa a daki wai bashida lafiya aje akar6i auren ,sannan ya dauko akwatunan da gimbiya zulaikha ta hada set biyu duk tarkace kuma ko cika basuyi ba ,yace akai da 200k wai tayi hidima.
Haka En daurin aure sukaje mata da maza ,maza a waje mata suka kai akwatu da kudin biko
Baba saratu ,ta ja diyanah gefe ,ta bata wani magani "ki karanta fatiha qafa arbain da daya,kina tofawa akan garin nan ,sunanshi sassaqen gamji,sai ki sha da nono a cikin motar da zaa kawoki kinji ,da niyyar zaman lpy da mijinki da er uwanki ,ki riqe addu'a shine makaminki ,karki yarda da kowa sai ranki a cikin gidan nan ,ni sunana Sarah qanwar me gidanki ,naji sonki qwarai araina in mun hadu zamu tattauna "
Godiya tayi mata ta kr6a ,aiko tunda ta shiga daki batafitoba saida ta gama, na fatihan haka ta kasance sukuku har lokacin tafiya da ita,tayi kuka sosai shikenan zaa kaita gidan maqiyinta tana sane.
Bayan isha'i saida ta gabatar da sallah raka'a biyu kowanne da fatiha da qulhuwallahu ,tana idarwa ta maida goshinta a qasa ta jero _Lailaha illah anta subhanaka inniy kuntu minazzalimin_ 41 ,sannan ta jero addu'oin saa a gidan aurenta tana kuka ,hr saida akazo tafiya da ita sannan ta dago daga sujudan ta daga hannu tayi addu'ointa ta shafa ...suka wuce gidan ta.
°°°
Tunda aka kaita yina tsaye a gaban window yina kallonsu har suka gama shigowa ,amma baisa ya ji son ya ganta a ransa ba ,don yanzuma baqin auren yike gani.
Washegari gidan ya watse ,aka barta ita daya har bayan magriba.
Anan gimbiya Sarah ta shigo ,da wake danya kusan tiya duk an zaneshi da sunan Allahu...
"Tashi ki dafa da kanki da jar kanwa ,gashi ki farfesunshi ,kici iya cinki yanzu sauran kibani inje ayi maki sadaka"
Hakan kuwa akayi,saida ta tabbatar ta ci komai sannan ta kar6i ragowar ,tasata ta sake wanka ta bata kalan kayansu na sarauta daganan ta kira wayarsa
Kamar bazai daukaba ,sai kuma ya dauka "to yaya gani a dakin amaryanka ,kodai in tafine bazaka samu ganina ba nima,zalunci dai ba kyau kuma in ka yi wa 'yar wasu gani er uwanku nima a Wata masarautan Nike za ayi mun,sannan ai ba auren Cushe bane kai ka ganta kai raayi "
Shiru tayi tana sauraransa
"Oho dai in bazaka shigo ba sai inje in shaidawa mai martaba yazo a maida yarinya gidansu tun da girma da arziki ,kafin ka saketa daga baya ,ka 6ata mata suna ana mata kallon qaramar bazawara"
Kashe wayar tayi ta amsa da "toh"
A jaka ta dauko turare mai kamshi a dan kwalba da 'ya'yan idon zakara ,ki shafe a fuskarki in na fita kafin Ku hadu da yayan ,ni gobe zan wuce ga numberta ,ma ringa waya"
Godiya tayi mata sosai wannan shi ake kira haduwar jini
Oum Aphnan✍️
[7/27, 5:31 PM] Bamalli✌️: 76 - 80
*Jinin Sarauta*
To ba laipi a dai ranar anyi Abubuwa,daganan bai kuma bita dakinba,in zaifita saidai yabi ta kofan baya, in kuwa ya zama dole sai ta dakinta zaibi ,to bawai itaba dakinma bayison had'a ido dashi haka zai d'auke kai ya karkatar ta wani gefe,har ya wuce,in saqone saidai yaba gimbiya zulaikha ita zata aika mata ,gadara nau'i nau'i ,kwanan ta duk ta handame kullum ita keda miji,amma dukda hakan wata zubin in ya zauna sai ya ringa jin kamar rayuwarsa incomplete,wannan yasashi d'araran kansa,kullum inya ke6e saidai ya rafka tagumi ,bai san tunanin me zeyiba,gabadaya ya susuce.
A 6angaren diyah kuwa tun ranar farkon da akayi komai ,ya zura kwallo a raga ,ita koda taga bata period duk tunaninta dai matsalane da sauyin wajen zama ,zai kuma gyaru musammam da bata ciwo ta d'ashe ta kode ,yanzu cikinta yana Neman Wata biyar, ita kadai take rayuwarta har barorin gidan sun juya mata baya,ba mai gegen dakinta ,komai ita takewa kanta tundaga tsaftar muhalli har komai dasu girki.
A Wata ranar larabane gimbiya Sarah tazo k'asan da yarorinta Zarah da Doctor (sunan da ake kiran Dr Khalid tun yina qarami)
Tunda ta sauka ta ke wurga idanu ko taga zuwan diyanah, har dai ta qare ta tambaya mamansu
Shiru tayi don harga Allah takan manta da watannan halittar
"Sarah waike meye hadinki da yarinyar nan ? Sam kurace batason jama'a ni har mantawa nikeyi da tsiruwanta"
"Haba dai,anya mama ,er mutane an Barta a sashensu ,tareda watannan makiran"
"Ke saratu banson hadin fituna ,karkizo ki nemi raba masa kan mata kawai kawai,tace maki suna cutar da ita ne?"
"A'ah shikenan ,bara in kirata"
"Hello Anty"
"Diyanah kina lpy"
"Lpy Nike Anty ina yara "
"Gamu munxo ko kizo kiyi mana oyoyo,barorinki basu Fada maki bane"
Shiru tayi ,ni ina wani naga barori ai duk suna dakin isashiya me cikakken iko
"Kinyi shiru amaryanmu,da Matsala ne?"
"Laa ina tunanine,yanda duk suka watse suka barni ina barci ,Ashe sunzo gurinkune ganinan qarasowa cikin gidan"
°°°
Tafkeken mayafi ta saka aka Riga da zani na atamfa mai ratsin ja ,super dinkin yayi fitting dinta hakan ya fiddo matashin cikita na kusan Wata biyar.
Haka ta kullo dakinta ta ringa takawa a hankali tana tafe mayafin na Jan kasa tsabagen girma,irin na qosassun hajiyoyin nan.
Da sallamarta ta shiga duk suna zaune suna cin abinci a tafkeken darduman tsakar makeken falon
Aikuwa dagudu Khalid ya taso ya rungumeta "oyoyo antyna ,nayi kewarki"
Ya matso mararta...yamutsa fuska nayi saboda murdan da cikina yayi saboda azaba.
"Washhh" Ta Fada tana cije le6en qasa
Da sauri ta taso "yaya dai amaryanmu?"
Murmishi ta danyi me kamada na yaqe "bakomai" a hankali ta dogare hannunta a qasa kafin takai kasan ta zauna a hankali ,irin dai zaman masu ciki
Tunda tako zauna maman take kallonta,dagowar da zatayi suka hade ido taga yanda take mata kallon tausayawa ,tabbas tana kyautata hasashenta akan Diyanah
"Barka da rana hajiya"
"Sannu 'yannan ,meke damunkine Nene?"
"Laa bakomai wallh"
"Hajiya kin rigani maganane,ta dashe da yawa amma tayi fari kamar me shigar ciki,amma yaya ya sani?"
"Anti bafani da komai"
Saidai bata rufe bakiba taji bul wani abu ya gilma mata a ciki, ranar farko da dan cikinta ya fara motsi, dafe kwankwasonta ta baya tayi ,tareda rumtse ido da cewa " wash " ta wani yi zillo.
Dariya Sarah ta saki "hajiya mashallh da ya nuna kansa a dangi,lallai diya zurfin cikinki yayi ,hajiya wallahi motsi cikin yayi"
Gaddama ta kafe masu dashi batada komai, aiko Sarah ta tasheta suka tafi asibiti,ai ba'a kaiga test ba likitan ya kwantar da ita saiga da a daidai wajen cibiyarta .kenan watan ciki hudu da rabi,s take ya yi scan hakan ne dai ,ga yaro nan yina motsi,lafiyayye dashi...aikuwa tuni labari ya watsu a dangi diyanah Nada ciki,a gididdiga ranar shigar Ango daki kwanakin ciki.
Murna kam kowa keyi,saidai yarima ko a jikinsa bai damuba,itakuwa zulaikha kamar ta mutu don baqin ciki yanda taga kowa ya koma da diyanah saidai gogan ko a jikinsa tamkar ba shine mai Neman haihuwarba ruwa a jallo ba
Diyanah a maimakon ta samu farinciki sai qarin zullumi da damuwa ,kuka sin zamar mata jiki kullum tana cikin yinsa,tayi nadamar wannan qaddararren auren ,tayaya zata kawo yaro gidan da ubansa bai damu da uwarsa ba bareshi?
Sarah kam da ta fahimci tana cikin damuwa ne ta sameta ta titsiyeta saita Fada mata damuwarta
Nan ta zayyane mata komai, wato rabonda tasa mijinta a ido tun ranar da ta bar garin bayan biki
Tsoro abun ya bata "karki cemun bayan first night Baki qara saka yaya a ido ba" jinjina mata kai tayi fuskarta da da murmushi
"Aiko da damuwa wannan aikin watancan baqar daganne ,kuma ni nan na isheta" ta fice a dakin tana korafi,batareda tabi takan ,diyanah ba.
Sai kuma can ta dawo mata da turaren bintu Sudan ,madaran tace ta yi maza tai wanka ta shafa ta samesu a Fadan cikin gida ,kuma in tazo ta tunkari inda yariman yike zaune ta zauna,sauran bayanin saisun hadu
Kar6a tayi ,sannan tayi abunda tace,daganan ta nufi fadan saiga shegun barorinta na Binta ,a yau ,bata kulasuba suka rankaya har can
Tana ratsowa ya wani kafeta da ido ,qamshinta tunda ya dokesa yaji Wata muguwar shaawarta ya bijiro masa ,a take jikinsa ya kama rawa,shi tunani ma yike yaushe ne diyanah tazo gidan?
Sarah lanqwashe kai tayi ta labartawa sarki duk abunda yake faruwa da duk jama'ar gidan, itakam zulaikha idonta na kan yarima tana lura da halin da ya shiga, don haka ko jin zanturtukan Sarah batayiba ,saidai tsinkayen salatin mai martaba tayi
"Allahu Akbar,ka bata ajiyar qwanka amma kake cuzguna mata da cikinka,to yau ba sai gobeba ina umurtanka da ka aikomun da takardan ta ,ni yarinyatace ina kishin inga an wulaqantamun surukai"
Bakinsa rawa ya fara yi "Ciki fa kace baba? Wai diyanan ne keda ciki?"
Duk maganan da akeyi sarki bai daure raiba sai da yaji tambayarsa ,a take ransa yayi mugun 6aci "kar ka maidamu qananun mutane anan kaji...ciki rashin ciki inajiran takardan sakinta kafin dare
Kuka ya fashe dashi ya gofana gwuiwiyinsa a qasa.
" ka gafarceni nabi Allah nabika baba ,wallahi ni ban ta6a ganin diyanah a gidan nan ba sai yau,duk yanda akayi makaru akai mana don a rabamu amma ni inason matata...bazan iya rabuwa da itaba" kawai saiya tsinke da kuka
Mamaki ya ishi kowa lallai akwai lauje cikin nadi ,hakury aka shiga ba sarki daqyar ya haqura da sharadin in ya sake zslutar diyanah bai yafeba
Murna kamar mene a wajensa,haka suka rankayo zuwa gidan su ,kobi takan zulaikha baiyiba
Wannan abu ya soketa,don haka tana shiga ta dokawa boka kira,ta labarta masa komai
"Kyalesu yanzunnan zan tura masu d'an babule mai aman wuta" godiya tayi masa ta kashe wayar.
Cikin farinciki ya tallafota har dakinsa ,komai a sauya ba kamar sanda ta shigo ba kafin biki ya qara kyau da tsaruwa ,a kan kujera ya ajeta ya zauna yina kallonta duk ta qudindune a mayafi
"Me zan Baki tukwuicin shirin bani qaruwa da zakiyi?".
Murmushi tayi " komai ka bani ina maraba dashi".
"Na Baki soyayya ta"." Ngd ranka ya dade".
Hannunta ya kamo ya manna mata sumba a bayan hannu
Dasakin sumban da murdewan ciikinta da sauri ta duke ta kwalla qara ,bulllll jini ya kece ta qasanta harda guda guda.
Rud'ewa yayi iya rudewa ,he can't control himself ya kasa aiwatar da komai,sai sakin Baki yayi yina "aa'aah aaa'aah diyanah karkiyi mun haka plz" bai aune ba saidai ya ganta tana shivering.... Qwalla qara yayi ya sunkuceta,ya fito harabar gidan da gudu yina ihun kiran mutane, ga jini na binsu kamar an yanka dan akuya,da kan sa ya sata a back seat driver ya fita gidan, kwarar idonta ya tale qasan yaga yayi fari ,kawai sai ya hau ihun driver
"Titin bayan babanka ne da kake shafashi a hankali? Wlh in matana ta mutu saina kasheka kaima" haka yayi ta sumbatu da suke out of mind.
Suna shiga asibitin nurses suka kar6eta da sauri zuwa A&E
Daidai suma su Sarah suma suka qaraso ,fitowa yayi zai bisu da gudu Gaban rigarsa jam6ar da jini ,da sauri Sarah ta qanqamesa ,ta janyesa
"No yaya ,ba girmanka bane roaming within,with dix nasty looking cloth"
"Oh Ashe?
Saboda bake bace zakiyi loosing mata da hoped baby ba ko?"
A cikin A&E anyi nasaran fitarda retain product din,don suna shiga yaron na fad'owa ,haka akayi mata wankin ciki suka Samata drip a hannu daya dayan hannun jini.
°°°
Wannan shine ya cigaba da kasancewa da rayuwar diyah a cikin gidan, ta samu lafiya itada miji Wata sa'in,Wata sa'in kuma kashi ya fita muqami,ta samu ciki amma bai Wata biyu ya 6are,Sarah duk wasu sirrin kundin gidan sarautan da ta sandasu na tsari da dafa'i bankawa diyanah takeyi ,wannan shi yike sama take samun sassauci da tuni kila ta Dade bata gidan.
A lokacin da tayi 6ari na bakwai yina zubewane ,likitoci sukayi ittifaqin mahaifarta ta samu matsala da qyar zata iya samun ciki by her capacitation ,kota samu a lokacin cleavage zai zube kafi n ya shiga mahaifa, saidai ko a hada kwayoyin halittar su a saka mata a mahaifan ta cigaba da rainonsa shima in aka yi missing chance sau biyu toh bazata ta6a haihuwaba
Hankalin yarima ya tashi, ya kasa fadawa kowa damuwarsa sai Sarah,itakuwa tana tashi taje har dakin zulaikha ta yi mata kuturun wulakanci ,ta shaida mata haqanta ya cimma ruwa diyanah bazata iya kar6an cikiba,ita mai duwawun haihuwa saita haifawa yarima,su yanzu ta lafiyarta sukeji a samu ta rayu.
Bayan ta warkene ,Khalid ya tubure a gidan zai zauna wannan shine karo na biyu a wancan karon ya zauna hannun zulaikha ta azabtar dashi shine uwarsa ta gaji da kawaici ta d'auke danta, a wannan karon sai ya sauka a wajen nanne dinsa (tun yina yaro bai iya cewa Anty,sai nanne) ...Khalid xamansa wajen diyanah ya rage mata radadin kadaici,ta samu saukin damuwa ta riqesa tamkar danta .
Kwatsam saiga zulaikha da ciki kidifi🤔A wannan karon ansan gidan anyi ciki,haka taringa shaqan nauyayan kudade da sunan siyayya,ammafa suna account ko tuntun hulan baby bata siyaba,ciki na girma lalata na qaruwa
Saida ciki yakai Wata shidda kowa ya gama saka rai ta sa jakadiyarta ta nemo mata jinin masu haihuwa a asibiti ta shashafa wai cikin ya 6are,Ashe karyan ciki tayi don hankulan mutanen gidan su dawo kanta su so ta ,amma kwarya take sakawa.
A lokacin da zatayi 6arin saida ta tabbatar yarima sun tafi India duba lafiyar diyanah,shine tayi amfani da damar cewa ciki ya 6are
Shikuwa ta 6angren yarima ya yanke shawaran kai diyanah ne ai mata dashen dan