Showing 18001 words to 21000 words out of 25648 words
Chapter 7 - JININ SARAUTA 2 Complete By Oum Afnan.txt
ladabin dalibin /daliban ga malaman su kai harma da dalibai En uwansu.
Jagorancin sharan masallaci fisabillillah
A wannan matsayin ta rubuta baitin yabo ga sayyadina rasulullahi cikin harshen larabci ,baiti mai tsayin shafi goma.
Ta fito gasan musabuqu na kasa da kasa sau biyu tana kar6owa makaranta ,kambin na biyu da na d'aya ....Lallai dole makaranta tai kewa gamida kishin rabuwa da wannan dalibi/daliba...kamar koda yaushe ba kowa bace face DIYANATU ADAM..Attakabir
Wani ihu akayi ,ana sowa shafa kawarta da hafsat suka rakota kar6an kyaututtuka ,kanta a sunkuye tana hawayen da bata San ko na menene ba.
Zuwa tayi ta tsaya a gabansa ,ga jerin tulin littafai a gefensa ,na sahihul Bukhari da sahih Muslim ga qur'anai masu fassara,sai wani qaton kwali an rufesa cikin Leda da rangadeden sunanta da larabci.
A inda yike tsaye,wani bafadensa ke miko masa shikuma ya bata,a sanyaye take dukawa ta kar6a,kanta a k'asa, har yanzu bai tantace idonta ba ma,itakuma inta kar6a ta bawa su shafa su rik'e,har aka kawo kan wannan kwalin ,qyam ya tsaya yina kallon sunan,a hankali bakinsa ya furta "DIYANAH"
Gigif ta dago idonsu ya sarqe da na juna,dan murmushi yayi don ya gane tayi mamakin sane
Bakinsa ya motsa a hankula "BARAKALLAH"
Hawaye ta sharce da hannunta a maimakon ta bashi amsa,sai kurum ta kama zata kar6a,rikewa yayi saida mai cameran ya daukesu tar,sannan ya sakar mata ta wuce, ba kamar sauran ba da ko kallo basu ishe shiba.
Taro sai son barka,bayan an gama da d'alibai ,sai kuma manyan baki,da iyayen yara suka soma kar6an sifikan suna tofah Albarkacin bakinsu,tareda bawa makaranta gudunmawar da suka buqata.
Shikam yarima komawa yayi ya zauna tareda dan kwanta wa akan bayansa,sosai tsayuwar da yayi ta gajiyar dashi.
Anzoda sifika yafi sau nawa baice komai ba,sai a qarshe ,ya mik'e ya kar6a sifikan
"Diyanatu Adam".
Ras gabanta ya fad'i ta fara waige waige,to me yasa yike kiran sunana?
" ke diyah ,ki fita dayallah ki fita" cewan dalibai En uwanta
Mikewa tayi ta soma ratsowa cikin filin.
Harta qaraso gabansa ,kar6an wasu mukullaye guda biyu yayi a hannun bafadensa ya riqe sannan ya soma magana a taushin gaske tamkar ance yayi dole.
Jinjina ya fara da yiwa makarantan ,sannan ya d'aura da "A maimakon fadan mai martaba, fada ta baiwa wannan makaranta kyautan filin tsohon stadium na garin nan ,don yin makaranta mai yalwa fisabillillah,kuma ni yarima mu'iz na d'auki nauyin ginin ,za'a fara daga ranar jumu'a inshaallah.... Wani kabbara aka dauka amma kasa shiru ya cigaba,saida aka fara duka kafin aka natsu.
"... Bayan hakan still dai,na baiwa daukacin yaranda aka yiwa yaye kyautan dubu Goma goma da turamen atamfa da shadda,in mun tashi yanzu za'a shigo dashi kafin taro ya watse.
Sai kuma a qarshe a karan kaina na yiwa Diyanah Adam, kyautan makullayen nan guda biyu,d'aya gidane kyauta ma iyayenta,na godiya ga barinta karatu da suka yi .
D'aya na motar da nazo a cikine ,kyauta ma yarinya ,kasancewar ta gwarzuwan shekara da kuma kujerun umrah guda uku"
Hayaniya na bar muku my fans,koni na gigice musamman kyautar motarsa da ya bata,saboda motar motace mai numfashi yau d'innan ya fara hawanta ,fakafakan mai kudi bai isa ya iya hawanta ba.
Sunkuyar da kai baba mai hura tayi cikin tafukan hannunta ta fashe da kuka
"Ooh haihuwa mai rana,yau mun bar gidan gado zamu zauna gidan kanmu, yarinyar da tafita cikin damuwar rashin anko,zata dawo da kyautar mota ,gida da kujerun Makkah?
Kasa godiya tayi saidai tayi shiru tana kallon makullan cikin tafukan hannunsa ,mika mata yayi.
A hankali muryarta na rawa " Nagode ranka shi Dade ,babanah yahanani kar6an duk wani kyauta da aka bani don karatuna,in na kar6a zaneni zeyi"
Tana kaiwa nan ta ruga da gudu cikin dalibai
Murmushi yayi,yarinyar ta burgesa,tarbiyyan ta ya qayatar da shi,dama bata cancanci kar6an wannan kyautan a hannunta ba.
Don haka aka kira babanta ,da kyar ya fito yina sumbatu,don yina cikin matsin talauci amma akwai qana'a wa ubangiji
Shima saida aka matsa masa ya kar6a tareda jero godiya,kamar zai ari baki
Haka dai taro ya watse,kowa ka gani suna cikin farinciki
Hotuna kuwa har Wanda basu magana da Diyanah yau sunzo daukan photo da ita,baiwa kenan daga Allah
**
Yarima d'aya daga cikin motocin En rakiyansa ya shiga ta kaishi gida.
Suna shigowa harabar gidan Gimbiya zulaikha ,na zaune can ta qarshen gidan ,karkashin wani rumfa mai kamada bukkah ,an kawata cikin rumfar da carpet da tim tim na Alfarma,a kishingide take kuyangi na marmatsa mata yatsun kafa ,wasu na mata firfita da hira,wanda rabi duk hiran cikin gidan ne,suke kawo mata tsaigumi
Da Sauri ta miqe,suka saita mata takalminta tabi bayansa da Sauri, su kuma ta wuce suna zind'enta
Dasauri ta saita kafadarta da nasa ,which a duniya yinason a girma masa.
Itakuma daukan sa take a banza tunda ta auresa
"Barka da dawowar shalelen yarima na"
Murmushi yayi mata na saman le6e ba tareda ya ce mata komai ba
Harara ta aika masa da saqonsa,inda sabo ta saba da mummunan miskilancinsa da har ita matarsa yike gwada mata.
"Ga dukkan alamu cikin duhu akwai magana...Na kasa tantance hakan,wai shin mai ya haddasawa mijina farincikine har ya shamakantar da idonsa wajen ganin Adon tauraruwar ziciyarsa bare ya yaba?"
Ta watsa masa tambayar daidai sunkai gaban varendar part dinsa,da ya tsaru tamkar ginin bankin zamani.
Juye mata daqwadaqwan idanuwansa na gado yayi akanta ,ya qare mata kallon sama da qasa sannan ya shige qasaitaccen falon ,ba tareda ya tankata ba,ya nemi wajen zaman sa na dindindin ya zauna ,yina furzar da numfashin huce gajiya.
Itakuma da Sauri tazo tana kwance masa nad'in kansa
"Cikakkiyar matan aure,takan sadaukar da komai nata don farin cikin mijinta,ko kanaso kace min na rasa wannan daman matsayin ne a zuciyarka yarima na?"
Qasaitaccen murmushi ya jefeta dashi ,mai halshen damo,hakan ko a take yasa gabanta fad'uwa
"Kyakyawar rayuwa daga yau ake mata tanaji, kuma cikakken uba shi yike Samar wa ,zuriyarsa uwa ta gari Wanda zasuyi Alfahari da ita tun anan gidan duniya har zuwa qiyamah,tafe Nike da wannan ma'anin a koda yaushe"
Murtuke fuska tayi tana hararan iska
Sannan ta fara magana cikin inda inda
"ban ..ban fahimcekaba Prince, kardai kace min ka sake d'ebo kiya da karashin da kasa ba rakatowane,masu son 6ata maka suna da sarautanku"
Fuskarsa ba yabo ba fallasa
"A'ahfa zulaikha kiyiwa bakinki linzami ,nadade INA umurtanki da Wannan ,kuma shi sha'anin Aure hada shi
Ake tundaga sama"
Had'iye wani malolon takaici tayi da qyar.
"Me kake nufi? So kake kace min auren yaran mutane zaka sake yi, kwana kad'an su Mace?"
"Lokaci shi zai gwada mana hakan zulaikha"
Eaidu kum Kareem💕
[7/27, 5:31 PM] Bamalli✌️: *Jinin Sarauta*
61 - 65
_Don Allah kuyi haqury banson karya Alqawari ,kunsan hidimar sallah mutane ,basu bani damaba,lokacin da zan maku kuma darene ,ba chaji dan Wanda na samu dashi nayi maku typing..._
"Amma yarima..." Dakatar da ita yayi da hannunsa
"Ammmm inason in huta" sosai ranta ya 6aci tayi masa qur da ido
Ganin hakan yasa ya had'e hannunsa guri guda don yayi mata fifitan maganan da ya sossoka mata "Don Allah dai👏"
Murmushin yaqe tayi ta tashi ta fita
**
Shiru yayi cikin tashin hankali bayan farka wa da yayi daga wannan mummunan mafarkin.
Itadin dai ya hango cikin wani irin surquqin baqin daji ,ga wata yarinya can da bazata wuce shekaru ukuba,tana miko mata hannu tana kuka .
Itakuma ta kasa qarasawa gareta ,saboda baqin Aljanin da ya kamata yina ciccijeta.
Da qarfi take qwalla kiran sunansa "yarima...yarima Mu'iz ka ceci jinin ka!"
Rashin makama yayi,gadai ita a hannun Aljani yina cizonta,ga kuma yarinya a can nesa bakowa tare da ita tana kuka,to wa zai kama?
Kurum sai ya tsinci kansa da afkawa aljanin da duka,waigowa yayi a zafafe kamar zai mazgesa,saidai yina dumfarosa sai wani tartsatsin wuta ya ringa fitowa a ranqwalelen zoben Azurfansa yina nufar jikin Aljanin ,wannan shi zaisa ya kauce a kansa ya qara shaqo ta,ita din dai.
Kuka still takeyi tana nuna masa yarinyar ,kamar an kimsa masa a baki yaji ya fara jero Ayatul kursiy,in yakai ya dawo ,kafin ya kai qarshen na biyun ,saiga Aljanin ya falla da gudu.
Itakuma yarinyar sai gata ta tako zuwa inda suke duka,a take ya rungumesu cikin farinciki
"Iyalina ,kune Alfahari na"
Daganan ne gigif ya farka,zufa na tsatsafo masa,dukda sanyin AC dake huda d'akin
A hankali ya shafi zoben hannunsa "Royal ring" ya fad'a a hankali,kawai sai ya miqe,daga cikin blanket d'in ya qara jibgawa zulaikha dake gefensa,sannan ya fad'a toilet don d'auro Alwala ,saida ya fito ya shimfida sujudah kafin,ya waiga ya kalleta ,ta dad'a qudundunewa a ciki da alamu sanyin dakin ya soma yi mata yawa.
A hankali ya taka ya rage acn sannan ya tada sallah Nafila,cikin sujudansa yina roqon masu,haihuwa shi da zulaikha, a gefe guda yina rokon Allah ya bayyana masa hasken da ke cikin lamarin watannan yarinyar har aka kira sallan subahi
Sai sannan ya tashi bayan yaji qarfi a ransa,ya je yayo wanka ya wuce masallaci ,bayan ya tada ita ta hanyar zungurin qafarta da hular hannunsa
Tsaki taja ta juya ta d'ayan 6arin ,ranta na suya ,ta tsani wannan d'abi'ar wai don yayi alwala shikenan bazai ta6eta ba? Humm!
"Ki tashi lokacin sallah yayi,nasan kina jina" ya fad'a cikeda gadara,kafin ya juya ya barta cikin 6acin rai
**
Bayan kwana uku En murna sun gama zuwa yiwa su Diyanah da iyayenta murna,sai kuma batun komawa sabon gida ya taso,da fari fir baban yace bayi komawa wai shi talakane,in ya koma wannan gidan 6arayi suka biyo sa me zai basu?....Saida En uwa suka tarun masa kafin ya yarda ya koma ,mota kuwa ,ya barta a cikin makarantan su Diyanah har wannan lokacin ba aje an d'akko sa ba.
Sun tare lafiya ,Diyanah ta cigaba da zuwa makarantan bokonta ,Agefe guda kuma tana qoqarin shiga Assanawiyyah(Islamic secondary).
Katsaham saiga malaminsu har gida wai In ba damuwa ,Diyanah zatabi d'alibai aje fada ayi godiya .
Mutseke ido baban yayi yina tsiya "Haba kar amaida mun yarinya kamar Amalanke mana...su sauran d'aliban En uwanta ba mutane baneba? Suje su kad'ai ko dai saida ita saboda ga fatararru an bamu kyautan gida?"
Haquri sukayi ta basa suka juya suka tafi,a gida haka yayi ta fad'a kamar zai ari baki ,kowa tayi shiru suka zabga tagumi suna saurarensa ,saida ya idar din kansa kafin Diyanah tace
"Toh Abbah kayi hakuri, nima ko sunzo ra'ayinmu dayane ,bazani ba"
"Yawwa er Albarka jeki d'ebomin ruwa a buta inyi Alwala" take anan fuskarsa ya washe ya fara fara'a kamar ba shiba
Saida ummanta ,baba mai hura taga wucewarta kafin tace "Malam ,kar mu zama butultattu mana! ,aidai ko,munci arziki tunda gamu cikin wannan tamfatsetsen gida Albarkacin tabarraki,sai don Ance aje godiya ne zakace sunyi ma ba daidaiba,? Bayan mune nan yafi cancanta da muje d'in ?..."
"A'ahahh kinga dakata! Dakata! Kinaso yarinyar ki taita yawo bad'ad'a kenan gidan sarakuna,ke bakisan illan hakan ba ko? To diyanah ba maroqiya bace da zasu fake da 'ya'yanmu suna zuwa maulah"
"Ya ilahiy🤦♀️Malam maulah kuma? To shikenan Allah shi gyara"
Da Sauri yace "amin" kafin ya qwalla ma diyanah kira "Wai ruwan yaqi d'ebuwane?"
Da gudu ta taho da butan a hannu.
Abban diyanah kenan shidai ba dai sababiba,ammafa in akan gaskiyarsa ne.
**
Sai bayan da ya komo daga masallaci ne ya na shigowa tundaga bakin get yike qwalla mata kira
"Er albarka maza shirya ki tafi,yanzu shugaban makarantan yake fahimtar dani a masallaci alfanun zuwan naki,gashi yace En uwan nakima sun wuce...ki Sauri ,gidan shi d'an sarkin ne dai nikeji"
Kwa6a kwa6a tayi kamar zatayi kuka "baba wallahi bansan zuwa irin wannan wajen....kuma ma ni bansan gidansa ba"
Raunana murya yayi "I hakuri kinji..shirya ki hau Babur dina in kaiki ,ai mu mazane mun sani"
**
A bakin get din gidan ya ajeta saida yaga shigarta sannan ya juya ,sanye take cikin doguwar rigar Atamfa ,na ankon saukansu da sai daga baya aka kawo mata da farin hijabi,sabo"
Da sallama ta shiga gidan ,tana tafiya sand'a sand'a,ko ina shiru kamar ba mutane ,mamakine ya kamata,to ina d'aliban koda yike ai ba hayaniya zasuyi ba suma.
Wani gaban varendar ta 6ullo ,Mai tsananin kyau anan taja tunga ta tsaya tana tunanin komawa
Gimbiya zulaikha tun shigowar ta take kallonta ta kitchen, ganin tana waige waige ,sannan ta fara sand'a yasa tayi saurin kiran "ke ! Zonan" ta fad'a tana kware glass din windown.
Dam ,gabanta ya fad'i ,ta tsaya cak tana muzurai ta kasa motsawa .
Ran zulaikha ne ya 6aci a hasale ta zagayo da Sauri ta fito haraban,tana zuwa gabanta batayi wata wataba ,ta sharareta da mari
"Ke 6arauniya ce?"
A take ta tsaya cak dafe da kunci tana kallonta,a take idonta ya qeqaeshe ta nemi d'igon hawaye ta rasa, sai zogi da idon ke mata kamar wacce aka watsa mata borkono.
"Ke kuchaka ,ba dake Nike magana ba? Waye ke? Er gidan uban waye ke,da zaki shugomun gida kimun sata!"
A sanyaye tace "Me na Satan maki"
"Ubanki kika Satan min,kawai bansankiba zaki shigomun gidane,inba sata kika zo yiba,to wajen wa kika zo,nine dai kad'ai matar yarima to wajen wa zakizo"
"Wajen me gidan naki Nazo hajiya"
Salati ta rafka tana tafa hannu "Nashiga aljannah ni zulaikha....qarshe duniya En mata sun fara biyo maza har gida...sa gwuiwarki a qasa ,zube daon ubanki,yau saina koya maki darasi zakisan baa tunkarar mijina a kwana lpy"
..
Ta soma gargagi tana kwalla ma balki kira,wai a kulle mata get,takira mata mai gadi.
Gofana tayi akan gwuiwoyinta tana sauraran ikon Allah
Hayaniyarta ne ya ishesa cikin izzah da fusjar da ke nuna kinfa dameni da hayaniya ya tunkarosu,shi Sam vaima lura da diyanah ba
"Zulaikha me kika sha yau?..duk kin hana mutane barci?"
Nuno masa diyanah dake kan gwuiwoyinta tayi
"Yarima dole a takawa mai gadi birki ko a kaisa garden ya koma kulada furanni tunda qofa ya gagaresa ,taya zai ringa barin wainnan ,nasty in responsible nonnative individual din suna shigo mana gida,to da tayi mana sata bacin na kamata
Da Sauri ya waigo ya kalli Diyanah, yina yamutsa gira kamar ya ta6a ganin fuskar
" ke lafiya, garin yaya hakan ta faru?"
Sai a sannan ta samu hawaye suka soma gangara mata a fuska
Cikin shesheka ta soma magana amma kuka yaci qarfin ta ta kasa
"Wal..wallahi niba 6arauniya ba..ba..bace, daga islamiyya aka turomu wajenka...shine fa.." Hawaye ne suka cigaba da ambaliya,amma ta kasa cigaba da maganar.
Jinjina kai yayi ,tabbas sai yanzu ya wayeta,watannan hafizar?
"Ya Isah...Tashi ki biyoni!"
*Posting sai Asabar inshaallah*
[7/27, 5:31 PM] Bamalli✌️: *Jinin sarauta*
66 - 70
"Yarimana ,kasantane? Waye ita? Bai kamata kana yayo kowasu tarkace kana kaisu parlourn ka ba ,that is your privacy, so plz saurareta nasan taimakone ,basu suje ,Allah shi kyauta..."
Wani mugun kallo ya jefeta dashi masu ma'anoni kala kala
Murya can kasan maqoshi "I need a sakina ,so plzz...kawai sai ya taune sauran maganarsa ya wuce hanyar part dinsa
Cikeda ixzah yike mulmula jiki tamkar mai jin nauyin jikinsa, naman wuya ya wani sama waje kaman toron sa.
Itadai diyanah binsa tayi da ido ta kasa motsi.
Itakuwa gimbiya zulaikha wani mugun kallo ta watsa mata,kafin taja arnen tsaki ta wuce tana qwafa,hakan ya sashi waigowa still tana duqe kamar miskiniya
Juyo da jikinsa yayi gaba daya, ya saki timbinsa tareda daura hannuwansa a qugu ,yina kallonta.
" uhum" ya fada yina dage mata gira,sum sum ta mike tabi bayansa.
°°°
Wani kasaitaccen falo suka shiga, duk dakiyar diyanah saida ta Nuna qauyencinta a sarari, ta kasa zama a kujera saidai ta xauna a qasan shifid'ed'en darduma kirar Saudi mai taushi gaske kamar katifa,sannan ta sunkuyar dakai tana gaishesa tareda gabatar masa da ko ita wacece,dakuma dalilin zuwanta
Zama yayi mai kama da kwantawa ,a jikin wani qasaitaccen royal kushin,yina sauraronta ta gefen kunnensa amma idon sa na kan screen din wayarsa,ya hade cunkusashen gashin giransa tamkar baya appreciating maganarta
Amma a badini yaba komai nata yike,ladabinta da komanta,yes yasan zulaikha tafita kyau kamar sama da qasa,amma kuma tanada sassanyan kyau kuma akwaita da kyawun hali, ai wannan shine abunda ake nema wajen mace ta gari ba fitsara da budewan idoba...sannan kuma abinda yafi so awajen mutane a girmamasa ,itakuma ba girmaba har muryarta kyarma yikeyi saboda kwarjininsa a idonta.
Tunda tagama wassafa masa dalilin zuwanta ta duqar dakai ,shiru taji yayi magana amma shiru,a hankali ta dago idonsu ya sarqe da na juna
Da sauri ta sauke kanta qasa "amm,ehh toh,wai na ce ina ne En uwan nawa suke, sai in je wajansu?"
Dariya ta basa, yadan murmusa kadan
"A cikin list din ajendar na nayau,ba list din kar6an makarantanku,so mun tura wani ya wakilcemu ,suna can fada"
Yina ta wani sa harafin jam'i tamkar ba shine shi ,shi d'aya ba.
Yunkurawa tayi a hankali tamike tsaye "tom shikenan Nagode ,bara inje" ta fada tana soma tafiya.
Shiru yayi bai tamkataba yina shafa qasumba,"wow yariyar nan akwai kayafa,koda tana cikin hijabi" bai auneba ya ga takai Kofa,gyaran murya yayi
"Amm na ce ba?"
Dakatawa tayi ta waigo tana kallonsa
"Inkinje gida kineman mu izini wajen baba"
Qwalalo ido tayi waje.
"Ban...fahimce kaba yalla6ai"
"Eh ko wani ya rigani ne?"
"Mene ranka ya Dade?"
"Diyanah ni ba yaro bane,banso in shiga sahun manema,while akwai me nema,so kicema babanki inason zuwa in gansa da kaina"
Kantane ya dauki nauyi gingiringim ,Sam ta kasa gane manufarsa ,amma kurum saita jinjina kai.
Kije compound ,zan waya, zaa maidake gida,kuma daga yau na haramta maki fita, ke daya zan turo maki da driver"
"Ranka shi Dade...nifa er ba kowa bane"
"Bani magana biyu,kuma ki sani daga ynx duk motsinki yina cikin kulawata,so a kiyaye"
Bata kuma magana ba ,ta fita da sauri.
Jinjina kai zulaikha tayi bayan ta gama la6e tana jinsu
Da sauri ta koma dakinta ,ta kame Baki saboda wani kuka mai sauti da ya zo mata
Tana zuwa ta tsallake En aikinta ta wuce bedroom, ta saki wani marayan kuka.
Ni kam me zanyiwa yarimane yayi tasiri akansa?
Duk izzar yarima shine zai qarewa watannan yarinyar er talakwa ,mummuna?
Duk dagawarsa ,ban ta6a jin yayiwa mace kalma ya wuce biyuba ,har su gama zance,yau shine yace zaibi baban yarinya gidansu don Neman aure, a maimakon saidai yasa a kirasa ,kuma ya ringa turawa ana dakko yarinyar zance parlournsa?
Wannan yarinyar ba hakanan ta shigo ba,akwai sa'an da ta kar6a,ji fa zamana dashi kusan shekaru bakwai zan iya cewa sau uku ya ta6a takowa dakina saidai ni in bishi ,amma ya hakan ,cikin qanqanin lokaci ya nuna zalamarsa gamida kishinsa akan watanan mummunan halittar?
Telephone din dakinta ne ya dauki ruri,ranta a 6ace taje ta d'aga
"Hello...AF salamu Alaikum" tai maza ta sauya furucin hello dinta don tasan bayason ta ce masa hello
"Uwargidata ,kina ina kika bar mijinki cikin kewa bayan kinsan na tashi" ya fad'a cikin nishadi
Jan hanci tayi ,saboda toshewa da yayi sakamakon kukan da tayi.
Kaji makiri,wai kewata ?