Showing 9001 words to 12000 words out of 25648 words
Chapter 4 - JININ SARAUTA 2 Complete By Oum Afnan.txt
Kinsan kukan mahaifiya kuwa akan 6atacciyar 'yanta,?"
Sai a wannan karon mai martaba ya samu zarafin magana cikin sassanyar murya cikin dusashiyar muryarsa na girma da madarar izzah "Ya Isah haka ,Diyanah mike ni zan mata bayani" mikewa tayi ta koma mazauninta ,a take kowa ya nutsu har shi PA din duk suka zazzauna kamar dalibai a gaban malaminsu.
"Wannan itace mahaifiyar ki ,bisa bincike da hujjoji ,amma tabbatuwar nine mahaifinki ,wannan ni sai anyi DNA test saboda nima ji nake ke din ba d'iyata bace ba,don nafison diyanah fiyeda duk wata 'ya da zata kawo mun matsayin d'iya ,matsawar watannan zata zama silar shigarta damuwa,kinsan wuyar da ta shiga sanadiyyar ki? Ta rayu cikin ciwo da hauka duk saboda ke! Tsawon shekaru goma bata da sukunin ruhi a yayin da ke kike rayuwa cikin farinciki ,wannan ba gata bane ba Allah yayi maki? Kinsan halin mutu kwakai ko rai kwakwai din da zaki shiga da ace kina tare da ita? To ki sani ni na barwa su PA da VP din ke ,in wuya ta isheki da kanki zaki nemi masarautar Azajadar don nan ne rufin Asirinki,mu kuwa munada Wanda zai maye mana gurbinki,kingan sa d'an Albarka" ya qaresa kausasan maganganunsa yina nuni izuwa ga Dr Khalid, bai tsaya sanyaba ya umurci Dr Khalid da Gimbiya diyanah da su fito su tafi ransa a mugun 6ace .
Kuka Gimbiya diyanah ta fashe dashi suka soma firfita har akaxo kanta itace ta qarshe ta waigo ta kalleta "Princess khalisat, Sarki jabbar ,fushinsa dawamammiya ne,gabansa tabbataciya ne,ina umurtanki daki gaggawar Neman yafiya da afuwarsa ,kuma ki kawo kanki fadar Azdajar a nan kusa" tana kaiwa nan ta kulle kofa ta fita tana hawaye .
Kuka ne mai gunji ta fashe dashi ,ta fara qoqarin cire hannunta daga jikin qarfen "Wayyo Allah dady ,Abbah na ,kukaini wajen mahaifiyata da yayanah wallahi,had'iyan zuciya zanyi in mutu idan sukace sun juyamun baya ,inason mahaifiyata da yayahnah me sona"
Sai a wannan karan ummah ta soma magana cikin ranta tanajin zafi za'a d'auke mata su'adah ba tareda burinta ya cika a kanta ba "kiyi shiru su'adah ki bari ki warke ,ni da kai na, nayi Alkawarin kaiki har gaban mai martaba ki roki yafiyarsa muma bamusan ke 'yarsa bace ba ,sai a 'yan awannin nan ,amma dole zamu maidake don mai martaba uban kowane a wajen nan,koda ke ba 'yarsa bace,bamuda hurumin ya roki mubasa 'ya mu hanasa bare ke da hujjoji sun tabbatar da hakan "
"To nidai naji kawai Ku kwance ni in bisu" hawayene ya cigaba da gangara a idon PA ,shikenan yasan ya rasa daughter dinsa,rasawa na har Abadan ,kuka mai gunji ya kamayi yaje ya kwance hannunta daga jikin qarfen tako fita da gudu tana qwalla kiran "Nannah ,yayahnah!"
Tuni PA ya shiga buga goshinsa a jikin garu yina ihu tareda fadin "Why ? Fareeda why?,kin rabani da daughter da,kin tafi yawan dandin ki...Allah ya sakamun da duk namijin da matarsa ke zambatarsa a bayan idonsa,irina . Allah ya tona asirinsu,harsai duniya tayi tirrrrr dasu" gaban ummah ne ya ringa fad'i dam dam! ,kardai yusuf ya gane abunda mukeyi da fareeda ne?
**
Fushi sosai mai martaba yikeyi ,sai dakyar Dr Khalid ya shawo kansa amma dukda hakan saida yasa aka bada jininsa Dana Su'adah akayi DNA test aka tabbatar da shidin ne mahaifinta kafin ya sakar mata murmushi, ya bude hannu ,da gudu su'adah ta kwace hannunta a hannun Gimbiya diyanah taje ta fad'a jikin mai martaba "Barka da zuwa d'iyar albarka cikinmu fatan tsawon rai da lafiya hadida ilimi mai amfani Allah ya haskaka rayuwar ki ,ya dausashe qudurin maqiyanki akan ki, yau zamu wuce fada kuma za mu warware labarin komai gaban Wanda suka aikata"
Murmushi tayi "nagode babana" suma duk godiya sukayi har yusuf da goshin sa yayi sintsir an nade da bandeji
**
Qarfe takwas na dare,helicopter dinsu su'adah mai martaba ,saudah da gimbiya diyanah ,ta tsaya a qatuwar filin bayan cikin gidan sarautar mai kamada lambu ko gidan gona mai daukeda dogayen bishiyoyi da ruwaye kala kala da qoramu ga shanaye daga can gefe cikin wajen su ,filin wajen zaka rantse a wata kwarya kwaryan jajin turawa kake mai kamada na gona,ba a gidan sarautaba. Jirgin su bai gama daidaituwa ba ,saiga na PA ,VP da ummah da Dr Khalid ,daganan suka dunguma hanyar da zai sadaka zuwa cikin gidan tsundum ,Wanda yike da tazara mai nisa a tsakani.
[7/27, 5:30 PM] Bamalli✌️: *JNS 2*
31-35
Masauki mai kyau aka sauke dukkan su,shikuma Dr Khalid ya hau mota ya wuce gidan sa ,dukda tafiya ne Mara tsayi sosai,don a cikin fadan yike amma can ta qarshen katangar,amma Sam baya iya zuwa da qafa ,yinada bayi da barori masu kula dashi ,Abu dayane yayi masa cikas shine rashin macen aure da wasu damuwoyin cikin gidan yasa Sam baya sha'awar aure,don shekaru biyu da suka wuce anso a had'a sa aure da qanwar Gimbiya zulaikha, saidai ana kwanaki ya gudu ,baa sake jin duriyarsa ba saida aka shaida masa an aurar da ita.
Washegari fada ta dinke da Al'umman annabi kowa kagani yazo taya murna ana son ganin princess wasu kuma suce Gimbiya khalisat, Ita kam ado akayi mata na usulin gidan sarauta,tana fitowa manyan baqi da malamai da suke zuwa ganin ta suna mata Addu'oi da kyaututuka , tana zama wata kuyanga datafi manne mata zatazo tace anzo Neman ta,kai saida ta gaji don kanta ta wulle ta tafi sashen Dr Khalid, itada Saudah ,anan suka bararraje wani bawa ya zauna ya lanqwashe kafa yina koro mata matsayin ta a wannan masarautar tun ranar da dan saqo ya aiko da sallahun haihuwarta ,yina shaida mata yanda ake mulki ,ba dariya ba barkwanci.sudai in yayi yayi sai su had'e hannunta da bai karyeba Dana Saudah su kashe kamar shashashu.
Shikam Dr Khalid tunda yazo baiyi dariya ba ,ba wannan wasan da yikeyi dasu ta rasa dalilin sauyawarsa,amma ta zuba ido tana ganin gudun ruwan sa.
Qarfe hudu na la'asar dangi na kusa da na nesa suka had'u a wani mashahurin fili gab da gidan Dr Khalid, duk a cikin fadan bayan anyi decorating wajen an kafa tantuna,sosai kuyangu suka cika gaban kowa da drinks da samosa da spring rolls sai ruwa da Rabin kaza, su su'adah ma mamaki suka kamayi sanda akaxo canja masu shiga cikin wani shigar alkyabba tasha ado cikin shadda maroon Riga da wando yasha aiki harta qafafun wandon,gaba d'aya ta sauya kamar namiji ,banbancinta da namiji kwalliyar fuskarta da adon gwalagwalai.
Wata baba saratu da kanta ta shigo mata jijji6e6iya ana zuwa bayanta barorine cikin uniform mata,
Daidai su'adah zaa fito da ita suna gyara mata zaman Alkyabban itakuma ta shigo "Ina d'iyar d'an uwan nawa? Dama da rabon zan ga jinina?" Kurum saita fashe da kuka ta rungumeni tamkar ba wannan isashiyar matan ba...kam ta rikoni cikin jikinta muka shigo wajen taron,Anan ne gasskata sarauta gaskiya ne,yanda duk inda muka saka qafa manyan mutane maza da mata masu kudin gaske ke gaishemu,bayi na zubewa cikin sallamawa, take su'adah taji wani abu na tsirgar mata ,Izzah na hawanta kanta yina girma ,Ana gaisheta tana lumshe ido maimakon ta amsa ,har saida ta ajeta a wani madaidaicin kujeran royal mai adon blue da gowldin ko ina ya dauki haske masu chanja kaloli, da adon furanni.
Maimakine ya kamata to yaushe ne akayi duk wainnan abubuwan cikin gajeran lokaci? Gaskiya wainnan snacks da kajin saidai in ordernsu akayi ba a cikin gidan akayi ba, Ashe basu saniba ,mai Dubai hotel ne ya dauki nauyin duk wani cima da za'a ci na iyayen gidan sa ,kowafa ya hallara zallah dangi d'aya kowa ka gani da kwaya kwayan zanen mallanci bibbiyu a gefen kuncinsu....familyn ,kyawawane amma sun rabu kala biyu,da masu dogayen hanci masu matsaikaitan ido farare tar ,da masu matsakaicin hanci da qwala qwalan ido,don haka dukkansu irinsu gudane ,dole dan dangin na shigowa akwai kalar Wanda yike kama dasu .Quri quri ,Saudah tayi da ido tana kallon masu kama da bestyn ta,ada tana jin ita watace yanzu kuwa da taga yanda sarauta yike ,saita gane cewa mulki ba komai bane. Saida aka bud'e taro da addu'a kafin sarki ya fara da godiya wa daukacin dangi na kusa da na nesa da suka sama halartan taron gaggawan da aka kira ,saboda VP da iyalansa da komin dare zasu juya Abj yau .
"Alhmdllh waqa a bakin mai ita yafi dad'i, zamu so jin yanda, Al'amuran ta kasance a bakin Gimbiya diyanah Tindaga haihuwar magajiya (Su'adah) har zuwa salwantarta,sannan da yanda ta bayyana ,harma shigowar su VP cikin al'amarin,A taqaice dai zamuso jin labarin wannan masarautar"
Da addu'a Gimbiya diyanah tafara da bude taron da addu'a kafin ta d'aura
*Egypt 1999*
Ina farfad'owa daga barcina bayan an fito dani daga aiki an fuddamun Khalesat a cikina ,Nurse na kamo hannunta na fara da tambayar ta abunda na Haifa , Murmushi tayi ta shaida mun macece amma tana dakin Hutu.A take naji zuciyata bai baniba bansan sanda na shiga roqonta don Allah ta kaini inga d'iyata ba.
Muna shirin shiga dakin naji Gimbiya zulaikha, gatanan da ranta tanajina ,tana umurtan jakadiyarta da sukazo tare da ta bankawa dakin wuta duk jariran su qone ,sai ace akasine gobara ya tashi,amsawa tayi da to uwar dakina saidai zanje innemo fetur ke kuma kibar wajen nan kar zargi ya shigo, had'a ido mukayi da nurse d'in, kafin inyi wani magana nurse din ta janye ni da Sauri muka 6uya ,muna kaucewa na fashe mata da kuka ,nurse ki taimakeni ,don Allah likita yace wannan itace kad'ai qwan mijina a duniya da zai iya qyanqyashewa ,itama din dashenta akai mun dukkanmu rauni garemu ,karki bari mu rasata don Allah ,mijina dan sarkine ,yina azaban son haihuwa don Allah " rarrashina ta hauyi "karki damu er uwa yanzunnan zan miko maki erki kuma dama su ukune a ciki zan sa ma'aikatan a kaisu BCG sauran na cikin kinga in wutan ta tashi yaran mutane sun tsira "
Godiya na dinga mata ina rizgar kuka ,harta kawo mun babynah ,atake na koma daki da abata saidai muna shiga naji ban natsu ba nasan tabbas ana farautan ranta kuma komun koma gida Nigeria saita aiwatar da nifinta akanta ,nan ne ma take da daman,a take wani bahagon tunani ya fad'o mun nikuma ba tareda na aunaba ,na miqe naje na d'auko akwatin kayan haihuwa ta na zazzage ,na debo duk gwalagwalan da nazo dashi na watsa ,na dakko open check nayi rubutun zunzurutan kud'i ,sannan na dauki Biro mai gold ink nayi rubutu na kalmasa na saka cikin farin envelope ,shima bayi rubutu a saman ,na kira nurse din ta taimaka mun muka dauki akwatin da basket din ,na roketa ta taimakamun in cika qudurina ,ita ta taimakamun muka fita ta qofan baya,tafiya kadan muka riski wani waje ,anguwane mai dogayen gine gine da manyan bishiyoyi da dan shiru anguwan ,alamar dai unguwar nasu natsuwa ne.
Dan lungu na samu na aje kwandom. Babyn da feeding Bottle daukeda madarar yara a gefe ,nasata tayi mun gadi,itadai nurse da ido take bina.
Sai bayan nayi hakan na dauki wannan akwatu naje gefen hanya na aje ,sannan na daura envelope d'innan na danne da dutse .da Sauri na dawo nacewa nurse din duk mu tashi a wajen mu 6uya ,nikuma saman bishiya na hau.
Saida na kwashe kusan Rabin awa kafin wasu En matan larabawa sukazo wucewa ,har sun gifta sai qaramar ta soma mata magana da larabci "ukhty kinga wani akwatin qarfe me ruwan gwal ,kai gaskiya ya bani sha'awa ban ta6a ganiba sai a TV in muna kallon film din masarautun India, zo muje mu gani" bige hannunta tayi "Ke bazaki sauyaba ko? Kinfa San layin nan sunyi qaurin suna akwai Satan mutane,kije ki ta6a kya 6ace dama gashi magriba ta kusa" haka suka wuce ba tareda sun dauka ba.wannan magana tayi mugun tsoratar dani ,a take na yanke shawarin inje in dauki d'iyata ,amma kafin nan na hango wani matashi tafe yina amsa wayar hannu irin Samsung d'innan Nada kalar ja, ga dukkan Alamu Sauri yikeyi,cikin rashin kula yayi tuntu6e da akwatin ,dutsen da na danne envelope din ya fad'i masa a qafa ,envelope din yayi gefe,saurin riqe kafarsa yayi ya zauna gefe yina kashe wayar ,saman fatar qafarsa ta zabtaro,yina cikin jin zogin ya hangi akwatin ,kallon akwatin naga yayi na En daqiqu kafin ya Kali envelope din , dukda gari ya fara duhu ban iya kallan fuskarsa ,amma naga hakan.da Sauri ya daga bangon envelope din ya karanta ,kafin ya farke ya karanta ,shiru yayi dafe da kai,ni kuwa qirjina sai bugu takeyi ina duk addu'a da yazo kaina ,can naga ya mike ya dauki akwatin ya jefa takardan a aljihu,sannan ya biyo inda na aje khalisata ya dauketa a kwando ya tafi,ina ganin ya wuce na durko don inga sabon uban da Allah ya za6awa d'iyata ,saidai INA! Ashe gaggawa yike ya shiga motarsa ,ina zuwa saidai naga hayakin motarsa ya bar wajen ,a take anan na duqe na ringa rizgar kuka ,da shesheqa nadama ta bijiromin na sallama d'iyata a hannun Wanda ban sanshiba ,danasani ta kamani yanda ko hoto ban mataba da watarana nace na haifi yarinya nima ,ana haka Wannan nurse din tazo ta dagani muka wuto hanya tana rarrashina ,anan Nike shaida mata damuwata rashin sanin makoman yarinyata,kuma banda ko hotonta "karki damu munyi mata photo muje zan baki copy" kunji yanda mukayi da wannan nurse din ,aikuwa muna shiga naga dakin yara ana kakabi ya kama da wuta da jaririya guda d'aya, kuka na fashe dashi na gurfana gwuiwoyina a qasa "khalisat na rabaki da wannan wutan ,saidai bansan hannunda na jefakiba qilama yafi wannan wutan zafi a gareki,kilanma yanzu kema an kashe ki,Allah ne masani" abunda nayi ta sambatu akai kenan ,ina cikin wannan halin kurum sai ga zulaikha da jakadiyarta fuskarsu fal annuri suna ganina suka kya6e fuska irin na tausayawa ,zulaikha ta rungumeni tana hawaye "kiyi hakury diyah ,nafiki jin radadin rashin khalisat NASA rai da yarinyar nan,tunanin muma gidanmu zai armashi samun kukan jaririya a jikinsa Amma mai Afkuwa ! Ta afku sai hakuri" Jinjina mata kai kurum nayi na wuce dakinna fara had'a kaya na,don kuma bansan amfanin zamata a qasar ba,ni kad'ai na dawo nabar masu zaman kar6an jaririya da taryata a can,yarima kuwa yina Asibitin baisan inda kansa yikeba.
Sai bayan kwana biyu suka dawo ,lokacin damuwa ta ,ta ragu ba fawwala ma Allah saidai in natuna bazamu sake haihuwa ba musamman yarima sai in dauki hoton khalisat in ta kalla ina kuka, Daganan bala'u irida kala dukaita samuna ,wannan ace mayuine suka kamani ,wasu suce asiri wasu ace wankan jegone bansamu da kyauba,jinya safai safai yaqi jin magani ,har saida na koma gida jinya ,shine silar kar6an khalid a hannuna,aka ba zulaikha ,saida na kwashe shekaru takwas a haka ,amma dukda hakan yarima na qulafucina ,ana wannan sarki mahaifin mijina ya rasu gashi mijina bayida kwanciyar hankali yamace baison sarautan aba qanin babanshi ,shi bai cancanci sarautan ba tunda baida magajiya ,shinefa aka Nada baba Abubakar ,shima shekara d'aya bayan nan aka farka aka wayi gari ya mutu kuma a ranar nikuma na haukace,a take aka yimun sharrin ni na kasheshi saboda baqin cikin ba mijina ya hau gadon sarautan ba,shiyasa hakkin jinin sarkin yasa na haukace,En uwansu suka yimun caa ,ga haka tu6uran a lokacin sukace lallai sarki ya sake ni in bar masu gida annoba amma sarki ya qiya,yace in kuma har aka matsa saina bar gidan to shima zai gudu yabar masu sarautansu ,hakan nan aka kyaleni saidai an canjamun daki can karshen gida,wai bazasu zauna da mahaukaciyaba ,amma a hakan sarki dani muke mu'amalar aure kuma bani mishi haukan,koda akagane sarki na kwanciya dani ta hanyar sokanan haukan da zan ta zubawa ,sai aka shamakantar da ganina ,sannan haukan ya dada ta azzara sai an daddaureni ,wannan lallurar shine ya cigaba da bibiyata har wainnan kwanakin da nayi arba da hoton da na Adana Ina kallonta don debe kewa, ana cigiyarta matsayin 6atacciya ,ganin hotonta shi ya dawo mun da ganina kuma haukanma ya gudu ,kunji taqaitaccen Abunda ya faru....tsit wajen yayi masu kuka nayi ,lallai hakki bala'i ne,mun zargi baiwar Allah cewan baba saratu ,to Zulaikha saidai kika ga diyanah tayi lafiya kuma Allah ya dawo da magajiya cikinmu cikin aminci ,wayasanima ke kika kashe mun dan uwana sarki Abubakar? To tabbas Inda yaje kema saikinje" mikewa zulaikha tayi ta rik'e kugu "hmm na yadda da makircin dangin miji yanzu saratu har kin manta rikon danki da nayi tsakanin da Allah har naso bashi qanwata yaki? Yanzu sunje sun roro tsintacciya sunce ersu zasu qaga mun sharri,to gaskiya a binciki kwalwarta kila bata warkebane,amma lallai lallai wannan yarinyar ba jinin masarautar nan bane ba... " gyaran murya VP yayi kafin ya miqe tsaye "Aah fa Ku dakata ni zanyi magana ai nasan komai...... " zaro ido akayi idan kowa ya dawo kansa ,Yayinda Su'adah da Khalid ke kuka kamar ransu zai fita na tausayin tarikhin Nannah ,itama Saudah na tayata
Itakuma umman Saudah mikewa wajen taron tayi ta koma can gefe don ta amsa kiran Haj farida da ta gani aka screen din ta ,tana ta jero mata missed call tana tsoron dauka saboda VP ,shine tana ganin ya mike zaiyi magana tabar wajen da Sauri...✍️
```Kardai Ku sha'afa 🤩 Wannan littafin Zazzafa ne daga cikin gwarazan zafafan Alheri writers....Wanda suka had'a da:```
_*K'WARYAR SAMA🙄* zazzafa daga Alk'alamin *Maman teddy🧸*_
_*JININ SARAUTA(the gorgeous royal blood)* zazzafa daga Alkalamar *Hassenart Bamalli(oum Aphnan)*_
_Idan kinason biyan *NORMAL PAYMENT* ne ,to kowanne littafi d'aya *#100* ne duka biyun ne *#300*_
_Idan kuma *VIP* ne kikeson biya toh,kowanne daya *#200* ne ,in kuma duka biyunne *#500*_
_Idan kuma *SPC* ne kikeso toh kowanne d'aya *#300* duka biyun kuma *#700*_
_Zaki iya biyan kudinki ta daya daga cikin wannan hanyoyin biyan:_
_*BANK PAYMENT*_
7782217014
Mohammed Hassana
Fcmb
_*VTU TRANSFER*_
09065990265
_*MTN CARD PAYMENT*_
09065990265
_*SAI KI TURA SHAIDAR BIYANKI TA HANYAR SCREEN SHOTTING EVIDENCE DINKI TANAN👇:*_
08081202932
_SAI MUN JIKU MASOYAN AMANA,KUYI ZUWA DAYA KU KAFCI RABONKU CIKIN SASSAUK'AR FARASHIN GASKE🤌_
_Maman teddy🧸_
_Oum Aphnan takuce_
[7/27, 5:30 PM] Bamalli✌️: *Jinin sarauta 2🕊️*
36-40
Fareeda ina kika shige kwana biyu shiru kinji yanda case din erki ke watangariri damu?"
Tsaki taja "Excellency ni yike watangariri dani,tunda