Showing 6001 words to 9000 words out of 25648 words
Chapter 3 - JININ SARAUTA 2 Complete By Oum Afnan.txt
gatsali da rashin kunya "To kaima kuma me kakeso?" Dariya yayi ya Sosa keya ,kice ba nine zakin farko da kikayi arbah ba,karki damu kyakyawa,kinsan dolene ayiwa giwa hargowa don namanta ya isu,Kawai ki bada kai mu hau bori" tsaki taja cikeda 6acin rai. "Don zaku sakeni saika laleni? To wajen ma a kumbure take,sai a shafa mun sauqi na baya sun rigaka" "ohooo haka kikace?" Murguda masa baki tayi,ehd'in haka nace" mikewa yayi ya kakka6e hannunsa "to ki saurari shigowar yarana"
Yina fita ya turosu ,bayan ya gargad'esu da su jibgeta ba mercy ko tausayi, suka ko ringa kir6anta in ta sume ta farfad'o ,har wajen shabiyun rana ,saida Alhj bilya ya mulu sannan yazo polis station d'in, saidai Mae xe faru? Suna shiga suka ganta kwance warwam cikin jini .
[7/27, 5:28 PM] Bamalli✌️: 21- 25
Gabansa ne ya fad'i ras ,jikinshi ya fara rawa ,ya fara saurin baki "Ku me kukayimata ,Baku ganin yanda take zubar da jinine? To wallahi kusan yanda zakuyi da ita idan ta mutu wallahi a wuyarku bansan ta ba,Ku bani arzikina" haka ya juyar da idonsa ya ringa masu jaraba da kumfar baki,ya samu ya kar6e kud'insa shi kuma ya basu kasonsu .
D'aukarsa sukayi suka kaita babbar asibitin garin suka cike form din da sunan sun tsinceta ne,ba'a san en uwanta ba. saida ta kwana ta wuni kafin ta farfad'o,a lokacin anyi nasaran kwashe raguwar tsokar yaron cikin da ya zube,sukai mata wankin ciki. Tayi kukan takaici,bataga satan kudi bataga yaron cikinta da taita qulafuci ga shan duka da qwaqular gardi data sha a office,hakan yasa gabad'aya qasan ya fice mata a rai , bata warkeba a ranar ta tattara ta gudu.
**
Sauqi kam sosai ya samu a wajen Gimbiya diyanah ,yau kwananta uku da dawowa daga Asibiti,kuma a yaune take shirin kar6an girki a daga hannun Gimbiya Zulaikha,Rawar qafa kuwa da kiraye kiraye a waya daga wajen mai martaba har saida ta daina d'aukan wayan don kunyan Barorinta dake kaiwa da dawowa takeyi,Ba laifi ta cicciko a kwana ukun nan ,saidai har yanzu tunani biyu sun kasa fita daga ranta,tambayar ta shine mai tayiwa Gimbiya zulaikha ne har ta kasa ta tako sashenta tayimata barka da samun lafiyarta ,tareda yi mata barka da Arzikin jin labarin d'iyarta? Sai kuma tambayar ta na biyu sai zuwa yaushe ne za'a barta taje nemo d'iyarta ,sannan me yasa mai martaba da Gimbiya zulaikha sukeyi kamar da er tsami tsakanin su?
Taso taje da kanta 6angarenta ita ta gaisheta ,don a rabu a gana ma arziqine ,kuma kewarta take kamar mene tanaso taga fuskar abokiyar zaman ta koda ita batazoba, saidai kafin tayi yunqurin zuwa mai martaba ya takawa abun burki,yace bai yarda ta taka sashen zulaikha ba matsawan ba itace ta tako wajenta ba.sosai tayi mamakin yanda akayi yasan batazo ta dubata ba,Ashe abunda bata saniba ,mai martaban yazo wucewa ta windon sashenta dake liqe da sashenshi yariski muryarta tana zazzagawa jakadiya bala'i yaso ya wuce tunda yaji duk akan ya kashe ta kashe ne, yasan ba huruminsa bane wata qila labarin horror film take bata,tunda yasan halinta ko magana takeyi haka take yinsa fad'a fad'a,Abunda ya tsinkar masa da zuciya ya kuma sashi cikin kogin tunani jin furucinta na qarshe "muje zuwa ,badai taji sauqi ba yanzu za'a fara wasan ,kuma ni in taka sashenta da sunan naje mata barka da Arziki saidai ta mutu!.." Rumtse idonsa yayi da Sauri ya bar wajen ba tareda ya bari yaji qarashen fad'an ta ba. Wannan furucin nata ya dokesa yasa masa qarin tsanarta fiyeda na da,yayi kukan takaici da tausayin Diyanah ,yanzune ya yardarwa kansa wannan ciwon cikin d'ayan biyun,amma da sa hannunta a ciki ,don tunda suka iya sheqewa da wazirinsa bayan tulin yardan da ya basa ,yasan zata iya komai. Don haka yanzu dukkan idanuwansa suna kanta da motsinta kuma ya lashi takobin har Abadan ba mu'amala ta sunnan aure da zata had'asu yabarta matsayin albarkacin iyaye ,kuma a tsarin fada sarki babu saki!
Don haka yanzu ya ajiye Gimbiya zulaikha ne,matsayin su d'aya da barorinsa da yike ciyar dasu sadaka ,itace take kidin girbinta don harta Abincin ta ya dainaci saidai yaci 'ya'yan itatuwa drinks da sauran su ,don haka yau a dokance yike yasan zaici abinci mai gishiri mai dad'i daga hannun masoyiyarsa,dama haka Allah ke ikonsa bazaka sama mata na gariba sai a ta biyu ,Amma banda haka saidai ya biya buk'atarsa a wajen qwarqwarorinsa,yafi mai sauki da ya biya bukatar sa wajen gimbiyarsa..lolx
Qarfe Tara na dare ta nufo sashensa tana tafe tamkar wacce qwai ya fashe mawa a cikinta ,wai yau itace zata dakin mijinta bayan tsawon shekarun da tayi cikin hauka,da lalurai nau'i nau'i,Sam bata da desire din having sex dashi,saidai ya zatayi dole taje hakkinsa yike Nema a wajen ta ,nacin kiran yayi yawa.
Sanye take cikin doguwar rigar barci fari tar da adon yellow din furanni maras hayaniya ,mai taushin gaske ya lafe a jikinta ,saita saka doguwar hijabi iya gwuiwa a sama,ta dauko tray din shayin larabawa a cikin dan butan shayi mai kyau, da d'an ficilin tambulan, da ada take had'a masa duk dare ,kafin ta kwanta ciwo,hannunta na dama yina kalmashe da casbiha dinta na lazimi,harta isa d'akin,saida tayi sallama ta nemi izini kafin ta shigo dakin sosai,yina kwance akan wata irin kujera faffad'a shiba gadoba ,kuma shi ba doguwar kujera ba ,bayida hannu d'aya,zuwa gabansa tayi ta russuna "Barka da hutawa jarumi ,sadaukin mijina ,Alfaharin yankinsa " murmushin yabawa ya jefeta dashi "Barka da isowa Gimbiya ta,a wajen mutane Nike da sarauta amma a wajen sahibata sarautata akeyi,bakiga yanda Nike jero kiraba ba qaqqautawa amma saida aka kintsa sannan aka ji qaina aka taho" "Afiwan ranka shi dad'e, a gafarceni" "bakya laifi amaryata tashi miko tebur ki aje kayan hannunki,don nasan in ban fansaba to a hakan zakiyi ta tsugunu" "Godiya Nike" ta mike ta miko wani dan ficilin tebur da yike a tsakanin kujera da kujera ta aje a gabansa ,tana zuba masa a dan tambulan din sannan tadan sunkuya ta mika masa "A gaisheda Gimbiya ta" ya fada ya kamota ya aje agefensa kafin ya tashi zaune,itakuma a hankali ta cire hijabin ta ninke a gefe,Kur6a d'aya yayiwa shayin ya lumshe ido "Hmm nasha kewar wannan shayin naki ,nayi cigiyar masana sirrin shayi suyimin irin wannan in biya amma na Gaza samu,Nagaisheda matata Aljannahta mai dubun basira Allah ya baki aljannah" "Nagode mijina da duk kokarin da ka yimun tsawon ciwona ,ka cancanci in maka jinjina samun miji na gari kamarka cikin wannan duniyar rabone ,Allah yabani dukkan damar da zan saka farinciki a iya tsawon zamanmu kar Allah ya bani ikon sa6a maka ,ka bani farinciki ka daukakani cikin tsararraki ka daga martabar zuciyata a burnin zuciyarka har ta azalzali bakinka da furtawa,batareda duba da matsayina na er ba kowaba,to dame zan iya saka maka?....saidai inyi maka addu'a Allah ya bayyanar maka da qwanka da zakayi Alfahari da ita a doron duniya kaima kace ga d'iyarka,,😭sosai ta e da kuka harda shesheka.
Bugun bayanta ya ringa yi a hankali bayan ya aje kofin shayin da ya zuqe
" Kukan ya Isah haka nan diyanah ,badon ki tunamun abunda ya faru a baya ko kiyi kuka na kirakiba ,A'ah na kirakine don in maki kyakyawar Albishir ,ammafa sai bayan kin farantamun ,mun jiyarda juna farincikin da muka kwashe shekaru bamujiba....kinkosan yanda nayi kewarki diyanah,nakasa sabawa da rashin ki,duk wata d'iya mace ina fara tarayya da ita a shimfida zata zamar mun lami ,tamkar dusa,ke kadaice sha'awata akanki Alkalamina kad'ai yike jin ta6i harya motsa ba tareda An ta6asaba,kice Wanda tunanin ki kad'ai yikansa inyi inzali toh akan mene zaki rusamun tanajina,zo mujiyarda juna dad'i in nuna maki irin kewar da nayi naki"
Oh ni Oum Aphnan ,rubutu nikeyi ina nad'o maku rahoto ,banji ban gani sai girgiza kai,da dan murmushi a fuskata,tambaya ta shine waidama sarakuna suna da feelings? Ban auneba saidai naga mai martaba ya kwasa mun wata bahagon kallo daga inda Nike lafe aiko da gudu na kwasa takarduna nayi waje,na ciji yatsa,amma xakuga naci don sainadawo jin albishir na barku kushana kusha soyayya girmankune,ba tona sirri Allah ya nuna mana nasu su'adah wannan dolene ayi komai akan eyes dinmu😂💃
**
Ban samu zarafin dawowa ba sai wajen ukun dare,suna kwance cikin wani farin bargo maras nauyi, ta d'aura kanta akan kirjinsa suna magana k'asa k'asa yina shafa suman kanta.
"Kinaji na ko? Wato jiya su wambai da ciroma sunje gidan harsu shi yaron yusuf ashe ma dan gidan marigayine sule ngwandu mai rasuwa ,yanzu haka shine maiba mataimakin shugaban kasa shawara ,wato Ahamadu yaron mu, dan wajen ubaida yayata kina ciwo ya zama VP to shine suka so jin ta bakin en gidan nasu gameda 6atar yarinyar ,To a gaskiya andai shaida masu tabbas ba d'iyar sa bace a gidan marayu suka d'akko ta amma cikakken bayani yina wajen uwar Yusuf ,itakuma tana burnin tarayya taje jinyar d'an tan din ance tunda ta 6ace yake jinya,kinga wannan ya nuna yarinyar mu ta fada kyakyawar hannu kafin fad'awar wannan ibtila'in.
To ni yanzu shawarar da na yanke gobe zanyi kiran shi Ahmadun(yina nufin VP) zan shaida masa inason ganin yusuf tunda yina matsayin me basa shawarane,sai muje har gida a kwakwafesa kuma aji ta yanda akayi ta 6atan sai a San yanda za'a samota,don a jikina nikeji tabbas zamu samota nan kusa"
"Bakomai yalla6ai duk yanda kukayi daidai ne,yanzu su baba ciroman zasu tafi abujan wajen VP din ko ko yaya? Hmmm ikon Allah amadu dai da nasani ne ya zama VP? Koba Wanda ya ta6a rasa babynsa ba sanadiyyar matarsa?
" shifa Ashe dai qwalwarki ta dawo zam" dukule hannu tayi ta sakin nasa dukan wasa.
Tasoma masa magana cikeda shagwa6a....
Hello🙋♀️Inada tambaya
Wai wannan wata masarauta ne,a wani gari take,sannan meye tarikhin wannan masarautan?
Kuma dama VP da PA sunada alaqane da fadar ko ko gayyar masarautane kurum ,dasuka saba kar6an kowa nasu?
Muje zuwa a next episode
[7/27, 5:29 PM] Bamalli✌️: *JNS 2*
26-30
Dr.Khalid yina sauka daga airport wani sanyine ya lullu6esa yau dai gashi a Egypt kwana ya tashi a cikinta ,zaiga masoyiyarsa a koda yaushe yaso acikin Asibitin ,rataye yike da jakar baya a 6angaren hannunsa na hagu ,yina sanye cikin wasu ji6a ji6an kaya masu kamada track suit ash colour da ratsin fari ,yasaka cambas ma Ash da yarfin ja da fari, gashin kansa ya dauki sheqin mai ,an yankesu tsawo daidai kufkuf dashi gwanin ban sha'awa,shine matashi na farko da naga ya Tara gashi kuma yayi masa kyau ,Wuyarsa rataye da wani roba kamar na headphones da yayi attaching da tabarau din idonsa ,Wanda gilas din ya ciresa a fuskarsa ya sakko masa a saman qirjinsa ,a nutse yike gangarowa zuwa inda zai samu taxi da zai kaisa asibitin,A tashin fari bazaka ta6a kiransa JININ SARAUTA ba saidai kace masa matashi maiji da quruciya da tarin miskilanci,gaban taxi din airport din mai sunan airport d'in a baya ya hau,sukayi reverse suka fita filin jirgin.
Sanda ya shiga dakin bai tadda kowa ba sai Saudah dake yiwa su'adah alwala cikin wani roba mai fad'i tana bata labarin wani comedian kiddy buk da ta karanta ,ta apple dinta
"Aminiya akwai wata app wattpad suna saka littafin tsofaffin turawa masu yawan gaske ,inkin gama zan maki download din app din a tablet dinki da zan siyo maki yau in mu shiga suq(kasuwa) da ummah" "hmm lovely nagode, but still banida ra'ayin karanta Littafi Sam ,na d'auke sa 6ata lokacine,karki yaudara kanki wai ai na turancine,zaki qaru,aah duk d'aya ne,just muyi focusing a karatun ,there is yet time for that..." Qiyyy ya bud'e qofar yina sakar mata murmushin da akanta kad'ai yike iya yinsa ,karaf idonsu ya had'u "Oyoyo yayanahhhh" kallon tsaf ta bisa dashi kafin ta juyarda qwarar idonta a kan Su'adah cikin sigar tambaya da son qarin bayani "kin sanshi ne?" Jinjina mata kai kurum tayi,kafin tace "yayah qaraso daga ciki mana" murmushin jin dadin yanda ya ganta yayi kafin ya sako jikinsa duka ya samu kujeran d'ayan gefenta ya zauna..."Welcome yaya" Saudah ta yi masa barka da zuwa cikin nuna kara ga Su'adah dukda batasan kowayeba tanajin wanine da yakeda muhimmanci a rayuwarta .Nunata yayi da yatsa"Saudah Aminiyanmu ,if I guesss"
Gyada masa kai tayi da Sauri fuskarta da murmushi "yeah yeah" ,"sannu da qoqari Aminya ya jikin mai jikin" gatanan taji sauki sai rigima wai bazata motsa hannun nan ba sai bayan wata guda ,wai karya goce asake gyara mata shi taci wuya...ko sallah a kwancen nan takeyi" tsamm yayi da ransa "Lallai su'adata akwai raki amma kinsan inba'a motsa wa zaki samu skin ulceration? Damukafi sani da pressure sore? Dole ana motsawa ana massage dinshi ,ko so kikeyi ,ki gama jinyar karaya ,kuma a dawo ana jinyan ciwo?" Tale bakinta tayi tana girgiza kai "uhm uhm yayahna" ta fada cikeda shagwa6a,tamkar ciwonma ya futo tana shhhuuu da baki,tana Jan yaji tana yarfe hannu ,idonta ya fara Tara qwalla . Dariya dukansu suka fashe dashi "wooo raguwa ,nafada maki twiny wallahi nafiki qwarin zuciya ke harma qarfi kawai ke babban kawai ne" naqe ido d'aya Dr Khalid yayi cikin sigar zuzzurfan tunani ,don ko sauraron shirmen su ya daina yi "twiny? Yana nufin itadin er uwar tace ta jini,kumadai nasan Saudah yarinyar VP ne,kenan akwai danganta ka na jini tsakanin familyn VP da itah ,shi vpn yace masu ko qaqa? Nidai nasan ,Su'adah ba d'iyar VP bane ,saidai in akwai wata kitimirmiran da ake 6oyewa yaran nan
" yayah ka ganta ko? Ta kwalla qara tana kawo masa qarar Saudah
"Uhm me ya faru?" Saka dariya sukayi duka "hium yayah Dr tunanin me kakeyi haka?" Saudah ta tambayesa with kin. Ajiyar zuciya yayi "this girl is sharp" ya raya a ransa ,da Sauri ya kauda zancen da cewa "help me with wora(water) plz " ya tambayi Saudah da American English dinsa.... Had'e hannunsu sukayi suka tafa "Humm wora English dinka akwai ban dariya" murmushi yayi yaran nan basu San kwa6o ba. Ana haka sai sukaji 6ud'e qofar,mumy ce,bayanta dady da wasu mutane mace da namiji.
Da gudu Saudah taje ta fad'a jikin Abbahnta "Oyoyo Abbahna ".Shouting din murnar da tayi shi yayi drawing attention din su'adah da ma Dr. Khalid, zumbur Dr ya miqe cikin alaman girmamawa da mamaki.qyam ya qame hannunsa a baya kaman na soja ,har saida suka shigo suka Nema waje suka zauna fuskar Gimbiya diyanah fal murmushi, mai had'e da kwalla ta kalli dukkansu to wa zata fara yiwa magana?
Kawai saita fashe da kuka "Yaro? Khalesah na?" Da gudu Dr Khalid yazo ya fad'a jikinta ya fashe da kukan da baisan na farinciki bane ko menene,sun rizgi kuka ,Abun duk sai yaba En d'akin mamaki kowa yayi tsit sai mai martaba dake harde a kujera yina baza sarauta kamar yina kan kujeransa ,ba Wanda ya keda zarafin tankasu ,abun ne ya ishi qwalwar Su'adah cikin cuno baki da sangarta tace "Yayahh" a hankali ya waiga ya zuba mata rinannun idanuwansa, still yina lafe a jikin Gimbiya diyanah "Yayahna kazo nan inason magana dakai? Ko ka sansu ne,kuma ma meye na kuka" ta fada muryarta na rawa kafin ta fara alamun kuka itama.
Gyaran murya Excellency yayi "Ya Isah su'adah ....Ranku ya dad'e marabanmu da zuwa" ya fada cikin sigar martabawa ,itakuma umman Saudah ta fara hidimar kawo masu abun sha.
A hankali Dr Khalid ya hau shafa kuncinta "Nannah ta yaushe hakan ta faru ban saniba? Alhamdulillah nannah " murmushi tayi ta lakuce masa hanci "Nayi lafiya a lokacin da kazo ka tare a wajen qanwarka mana,mun kira layinka bai tafiya,kai kuma kayi fushi damu" ta fada tana nuni wa su'adah dake kan bed.
Su'adah kam bata damu da furucinta ba a tunanin ta ai dama yaya take ce masa,Shi kuwa rikicewa yayi ya mike tsaye "Nannah ,karki cemun su'adah itace khalisat? "
"Qwarai kuwa khalisat gatanan kwance akan bed under your care amma kai baka sani ba" bakinsa rawa ya kamayi ,kawai saiya ruga da gudu ya qanqame Su'adah akan bed din yina kukan farinciki "Su'adah dama ke din bloody dita ce,shiyasa na gaza sukunin rai har sai na saka rayuwar ki cikin walwala? Su'adah dama kece khalisat dina danike gani cikin barci na? Su'adah innalillahi wa innailaihir raji'un" kawai saiya Fara sambatun godiya ga Allah ,qwalwarta ne ya tsaya cak da aiki ,batasan sanda ta daka masa dukaba a baya "kai yayah ka daina wannan dramar ,karku haukatani kunji,wannan yace ni ersa ne gobe ya yadani ,jiya mummy tace ni twin sister din Saudah ce ,saida na fara murna ,ina farinciki na samu sauyin rayuwa kuma sai kurum ka bijiro da wata magana ,kun nemo wain su mutane da ban sansu a rayuwa ta ba ,claiming that wai su iyaye nane,to duk kuje na yafeku,Ku barni Allah zai fitomun da iyayena na haqiqa inma ban samuba na dangana,nabi shawarin maaiki (s.a.w) dayace idan masifa ya same ka kace innalillahi wa inna ilaihi rajiun,nayi kuma ina jiran sakamako don fadin Allah ne ,innallaha la yudi'u ajral muhsinin "
Tuni dakin suka rushe da kuka ,dady yusuf (PA) da ya kafe a bakin qofa akan shi lallai bazai shigoba,zuruf ya shigo dakin ,yaje ya fincikeshi a jikinta ya maye gurbin wajen sa da kansa "twinkle kinga yanda na koma ko? Farida ta cuceni tayi nasarar koranki a rayuwa ta, na zawwace akan Neman ki ,saidai kash a lokacin da naji labarin samuwar ki,sai iyayenki suka bayyana maki,twinkle yanzufa so suke su rabani dake ,nikuma bazan iya rayuwa in babu keba,kice su kyalemu mu koma gida mu cigaba da rayuwarmu na baya,muyi wasanmu tare,ki mun kwalliya in baki shawara koba haka ba?" Tsinkewa tayi da kuka "dadynah inason ka ,kuma bansan kowaba saikai don haka kai zanbi na yafe duk Wanda zasu biyo bayan kai matsayin iyayena ,koda sune na gaskiyan na yafesu tunda sun hofuntar dani lokacin da Nike bukatar tallafinsu ,kai kuma sai ka maye mun gurbinsu,akan me yanzu ga kai sai in koma ma wasunka ,ina ,,,,aima sai hakkinka ya kamasu"
Tasowa Gimbiya diyanah tayi ta saka gwuiwoyinta a qasa tareda kamo hannun su'adah "khalisat karki yimun haka ,kinsan ko ke wacece? Kinsan waye mahaifinki?