Showing 18001 words to 21000 words out of 125146 words

Chapter 7 - MIJIN MALAMA BOOK 1 Complete.txt

23 Nov 2024

9081

da ƙasan bindiga. Da ace babu Majeederh wajan ko kalamanta ba su yi tasiri a zuciyarsa ba da tuni dambe ake da shi. Ana dukansa yana kallonta. Ya miƙe tsaye tare da ɗaukan hijabinta yaje har gabanta ya sanya mata, shi kansa bai san dalilin sanya mata hijabin ba, amma yana lura da idanun Abu-turab akanta. Wani securities ya sakarwa Abraham ƙasan bindiga akansa nan take kan ya fashe, Majeederh ta runtse Idanunta.
Daidai kunnenta ya ce.
"Jee kin jima da sanin Abraham baya giving up, azabar nan babu inda zata, idan baki yafe mini mun daidaita har mun yi aure babu shakka zan baki ciki na biyu, i don't care" "take him out"
Cewar Abu-turab, Hammad tausayin Abraham ne ya kama shi.
Da ƙyar yake jan numfashi sbd wahala amma bai fasa kallonta ba, har suka isa bakin ƙofa za su fitar da shi idanunsa ya kawo ruwa sai kuma ya yi dry domin ya hango rauni a cikin idanunta kawai bata sani ba ne, da ƙarfi ya ce
"I love you Malumana, I'll be back"


Not editing.
Littafin MIJIN MALAMA na kuɗi ne, kuyi magana a wannan number domin biyan kuɗin 08119237616... Na kusa gama free pages






*Ina Mata 'yan gayu masu son kayan gayu kuzo ga dama ta samu*. _BY JAY_ *ta kawo maku Kayan masu kyau da inganci indai mace tasan gayu to* _BY JAY_ *ne gurin siyayyar ta.*
We have
*Laces* _(Dubai laces, london laces, Switzerland laces,)_ dan uban su
*Atampha of all kinds*
*Veils*
*shadda*
*shoes*
*qualitative handbags*
*Jewelries* etc
Abun sha’awa ana shine Kayan mu ba a jikin kowa zaku gansu ba dan kaya ne unique na mata yan gayu da suka san kan gayu ku dai kawai ku mana magana ta Wannan no din *09060450181*
Ko kuma ku danna Wannan link din domin samun damar ganin kayan mu


https://chat.whatsapp.com/IBD74Cka3X2E2AqZyg0Nfo*🌈MIJIN MALAMA🌈*


Nimcyluv Sarauta
*9......*
Yadda suka ɗaure Abraham a jikin sarƙa zaka ɗauka wani tantirin ɗan fashi ne ko kidnaper, ko irin mutanen nan masu muyagon harƙalloli. Suna zuwa suka cilla shi a mota tare da yiwa motar key.
"Ku daka ta" P.a Hammad ya faɗa yana ƙara sawa inda suke ya dubi Abraham wanda kansa yake sunkuye jini ya ɓata masa fuska.
"Mene matsayina?" Kai tsaye Captain ya ce "Kai P.a ne a wajan His Excellency" Hammad ya jinjina kai ya ce "Good, kamar matsayin P.a ya fi na mataimakin Gwamna, idan ya tabbata haka ne la shakka zaku bi nawa umarnin" suka kalli juna
cikin kuma rashin fahimta Captain ya ce
"Me kake buƙata?"
Ya ce "Ku kai Abraham gidana, ya zama sirri ni da ku kada ku kuskura akai shi Prison idan ba haka ba, ku ne zaku tabbata a can har ƙarshen rayuwa"
"Cin amana?" "Shi ma ita ya yi" cewar Hammad. Captain ya ce "I can't, dole mu kaisa prison kamar yadda ya umarta"
"Nawa ya baku?"
"Mu ai ma'aikatan gwamnati ne, wannan shi ne aikinmu" Hammad ya yi murmushi mai kyau kafin ya ce "Mu ne Gwamnati ai, baka san inda rana zata faɗi ba gobe" "Kowa ya san ta yamma take faɗuwa" Captain ya tari numfashin Hammad da faɗin hakan.
"Zan baka 10Ms, zan faɗa maka yadda za kayi" ya yi shiru alamar tunani kafin ya ce "Sauran securities ɗin fa?" Hammad ya watsa hannu ya ce "Ɗauke shi, lokacin ya fara" Captain ya dubi abokan aikin nasa, ganin sun yi nesa da su hakan ya tabbatar ba su ji abinda suke tattaunawa ba. Tunaninsa ya rabo gida biyu shin ya amshi kuɗin? Idan ya amsa kuma ya ci amanar Gwamnansa, da ƙasar shi da kuma aikinsa. Amma miliyan Goma ai ba nan ba ce, babu wanda kuma zai sani.
Ya shiga motar, sauran securities ɗin ma haka kai tsaye suka fita daga cikin keɓantaccen gidan na His Excellency Abu-turab.
Hammad ya yi murmushi a fili ya ce "Kaci amnar maci amana kamar babu laifi? Ba zan jure ganin hakan ba, am sorry Best friend"
Abu-turab ya na tsaye da hannunsa wanda aka karya ya dubi Majeederh dake zaune tayi shiru ta sanya hannunta tsakanin cinyoyinta hakan na nufin tunaninta ya girmama har ya kasa ɗaukan ƙwaƙwalwarta. Abu biyu ya fi tsaya mata, kalaman mahaifinta Abbu, da kuma kalmar Abraham "I am the who raped her" hakan na nufin Abraham yaga surarta na ɗiya mace? Ya gama kallonta. Ta rutse idanu tana kiran sunan ALLAH. Yaron cikinta? Ɗan data raina? Ya yi mata Fyaɗe? Ya samar da cikin Khalil, ta ya ya hakan ya faru? Rabonta da shi shekara biyu, shin ciki yana shekara biyu ne? Ya akai har ya yi mata Fyaɗe bata sani ba? Yaushe hakan ta faru.
"Jiddo" Abu-turab ya kirata a ruɗe ganin yadda jikinta ke rawa kamar wacce take shirin yin jijjiga. "Ka da ki sawa kan ki damuwa wani ciwon ya kama ki, don Allah Jiddo listen to me ki bani dama, ki bani dama just one chance, please Jiddo Give me one chance"
Ta ɗago kai a nutse ta faɗaɗa kyakkyawar fuskarta speaking calmly ta ce "Your Excellency"
"Yes, Jiddo"
"Don Allah ka bani waje" ta faɗa murya can ƙasa idanunta na lumshewa.
Ya jinjina kai ya ce
"Zan fita,idan zaki farin ciki" yana faɗin haka ya yi waje yana zuwa wajan ƙofa ya juya ya kalleta sai kawai ya fice yana rufe ƙofar bedroom ɗin. Yana fita ta zame ƙasan lallausan carpet na ɗakin, zuciyarta tayi mata zafi ƙirjinta na ɗagawa sama. Tsoron t ɗaya kada bakin mahaifinta ya kamata ya sanya ta lalace kum ta bi duniya kamar yadda kalamansa suka bayyana haka, mene ya sa ya kasa yarda da ita ya kasa fahimtar ba zata taɓa aikata zina ba, ya kasa amincewa ƙaddara ce ta faɗa mata.
Kuka take son yi ku zuciyarta za tayi mata sanyi amma ta kasa sai ma wani abu daya tsaya mata a ƙasan maƙoshi da ƙyar take jan numfashi. A raunace ta ɗaga kai sama ta ce
"Allah na gode maka, Allah na gode maka da wannan jarrabawa, yadda kayo ni a Musulma mai yadda da ƙaddara Ubangiji ka sanya na cinye wannan ƙaddarar, zuciyata ta kasa jurewa Allah kai kasan abinda yake ɓoye Ubangiji idan rayuwata a wannan duniyar shi ne alheri ka tabbatar dani a raye ka bani haƙurin jure ƙalubalen cikinta, idan mutuwata ita ce hutu a gareni Ya Allah ka ɗauki raina a wannan lokacin, ka yafe mini kurakuraina ka kula mini da abinda na haifa" Ta rufe idanu tana ƙanƙame jikinta tana jan numfashi da ƙyar ta ce
"Asstagafirullah Ya Allah, Asstagafirullah, Asstagafirullah Ubangiji kana kallo,kana ji, kana gani albarkacin imanin da nayi da kai, albarkacin kare addininka da nayi, Ya Allah ka bani haƙuri kwatankwacin haƙurin da Annabi Luɗ ya yi da mutanensa, ka bani ikon jure yanayin rayuwa kwatankwacin juriyar da Annabi Yusuf ya yi, Allah ka bani ƙarfin zuciya wacce zan fuskanci ko wanne ƙalubale, kwatankwacin Yadda ka bawa Annabi Sulaiman ƙarfi ikon, Allah ka kula dani kwatankwacin kulawar daka bawa Annabi Musa a cikin gidan Fir'auna... Ya Allah Asstagafirullah!"
Jira take taga ta inda mutuwarta zata fara, amma shiru hakan na nufin rayuwata ita ce alheri a gareta.
Abu-turab na zaune ƙasan carpet ya sanya Mama a gaba hannunsa naɗe da bandeji cikin kulawa ta ce "Abu-turab me ka ke so?"
"Majeederh nake so Mama" ta ce "Nemi Soyayyarta idan ta amince ba zan hana ba"
Ya yi shiru ta ce "Idan baka da abun faɗa jeka, ka sani a gaba" ya kalleta ya ce "Kamar ba zata amince ba" Mama ta dube shi sosai tana duba yanayinsa ta ce
"Idan har baka sanya son zuciya cikin lamarinka ba babu shakka zata amince, ka yarda da kan ka shi ne kawai" tana kallon T.v ta ce
"fight for the truth, fight for your love, idan har ka faɗa mata wahalar daka sha akanta Majeederh zata ji tausayinka, sai dai bana son ta aureka don jin tausayi sai don cewa tana Son ka"
"Tausayi yana zama so"
"Inji ku Hausa ba, babban kuskuren da kuke kenan, gurbin tausayi daban na So daban go and search"
"Mama please ki....,"
Cikin faɗa ta ce "Abu-turab ba zan tilasta ƴar mutane ba, fita ka bani waje" ya miƙe jiki a sanyaye yabar bedroom ɗin, Jidda na nufar inda yake ya daka mata tsawa. Mama ta ce "Na gode Allah tunda ƴarka ce" yarinyar ta fashe da kuka sosai da gudu kuma ta nufi bedroom ɗin Majeederh ta sameta zaune inda take..
"Mami" Majeederh ta zubawa yarinyar idanu sai ta ɗan saki fuska ta ce "Call me Jidda"
"Dady ya ce Mami" Majeederh ta jingina da bed ta kallon yarinyar sosai tayi kama da mahaifinta. Jidda ta ce
"Ina son Daddy, kema kina son shi?" Majeederh shiru ba amsa ta ƙara cewa "Zaki zama Mamina?" Sai a lokacin ta ce "Ai ni Mamin kowa ce come here"
Barrister na zaune looking so worries ya ƙara ramewa ya yi baƙi kamar ba kyakkyawan matashin nan ba mai jini a jika. "Aliyu Meke damunka?" Ya dubi Hajia ya ce "Me kika gani Hajia?" Ta haɗe rai sosai ta ce "Why are you asking my question with a question?"
"Ɗan Najeriya ne fa?" Almustapha ya bada amsa yana hararar Bar Aliyu Sufyan Alhassan. "Lafiya nake" "ƙarya ka ke, na san halinka dole da abinda yake damunka" Aliyu ya rasa me zai ce, ya faɗawa mahaifiyarsa damuwarsa tamkar ya tona sirrin aurensa ne, kuma zata tsani Matarsa Latifa Omar, amma seriously yana cikin damuwa ya mance when last da ya yi mu'amalar aure da Latifa, ya manta rabon da ya ji ƙamshin girkinta kullum abinci da ƙauri ya manta rabon da yag kitso a kanta, ya mance rabon da ya ji kalmar adawo lafiya daga bakinta. Yana buƙatar kasance da matarsa haƙurinsa ya fara gazawa.
Ya riƙe kansa, da mutuncinsa sbd gudun faɗawa halaka, amma irin su Latifa sune suke sanya maza neman mata da aikata zina.
"Ni banga abinda ka rasa a gidanka ba, amma ka sanya wa kanka damuwa akan wata ƴar iska haba Aliyu" Barrister ya kalli Almustapha ya ce
"Mai ɗaki ai shi yasan inda yake masa yoyo, ba zan hana ka aibata Majeederh ba amma ba kowa ake halinsa ba" Almustapha ya kalli Aliyu sai kawai ya miƙe tsaye. A tare suka fice daga cikin gidan nasu, Bar Aliyu ya yi Lodge Road wanda dalilin Majeederh ya kama haya a unhwhaty, shi ma Almustapha ya nufi hanyar gidansa. Maimoon na zaune ita da ƙawarta wacce suke neighbor da ita. "Maimoon kin ji daɗi, Allah ya baki miji wanda yake wada taki da komai na rayuwa" Maimoon tayi dry sosai ta ce "Allah sarki, wallahi bani da matsala da mijina saɓani bai taɓa haɗani da shi ba, yana da haƙuri sauƙin kai, sometimes na fisa rikici ma, gaskiya samun miji kamar Almustapha da wahala, yana da kare hakƙin aure da nasa, kullum cikin kyautatawa iyalansa yake" Maryam tayi murmushi ta ce
"To Allah ya bamu irin taki" "Haba ya bawa ƴan gaba dai, ke kina ɗakin mijinki ai ki ce kawai Allahamdulillah,kin san duk wani kwanciyar hankalin aure shi samun daidaito tsakanin ma'aurata, yarda da juna, haƙuri, tausayi. Ni kam i trust my husband" Shira suka ci gaba da yi. Suna zaune Maimoon ta ji anyi horn ta miƙe da sauri ta ce "To ga ɗan halak nan" Maryam ta ce "A'a zama bai ganni ba, lemme have my way" sukai dry kana sukai sallama.
Maryam na fita compound na gidan Almustapha na fitowa ya dinga kallonta domin bai taɓa ganinta ba. Ya shafa kai lokacin da take cewa "Sannu da zuwa"
"Thank you, can i know you?" Ta ce "Matar maƙocinka ce Habib"
"Oh, you're too beautiful" Mamaki ya kama Maryam sai tayi ɗan murmushi ta ce "Harna kai Matarka Maimoon?" Ya yi murmushi yana kashe mata idanu guda ya ce "Haba waccar Dabbar?" Maryam ta zare ido ta ce "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un Matarka ka ke kira da Dabba?" Ya watsa hannu ya ce "Yes, Kinga bani number ki please" Number ta bashi ta shige tana Kaɗa masa jiki, ji ya yi kamar ya bi bayanta domin ya tabbatar mijinta baya gari.
Cikin dare Abu-turab na zaune ya samu sanarwar gaggawa an samu motar jami'an tsaron shi a wani gefen hanya, gabaɗaya jami'an sun mutu guda ɗaya ya yi saura Captain shi ma yana gadon asibiti. Misalin 2 na dare Uncle Isma'il na harabar gidansa yana duba jaridar ranar inda yake ganin cewa Governor yana asibitin Cameron domin duba lafiyar shi, kamar yadda aka samu sanarwar ta bakin mai kula da lafiyarsa. Ji ya yi an tsaya gabansa ya miƙe da sauri da ƙarfi ya ce "Abraham innalillahi,mene ya sameka...


MIJIN MALAMA
Book1 500
Book2 500
Mutum zai iya biyan book1 kafin a fara book2... Idan kuma yana da hali zai iya biyan 1k ɗin bakiɗaya. 08119237616 kuyi magana ta nan.*🌈MIJIN MALAMA🌈*




Nimcyluv sarauta
*10...…*


Masu Arewabooks follow my account👇🏾 akwai gift ga wanda suka fi kowa share da comments acan
https://www.arewabooks.com/u/nimcyluv




Abraham ya zube gaban Uncle Isma'il ya ce "I want to convert to Islam, I want to become a Muslim, how much will I give" Uncle Isma'il da mamaki yake kallon Abraham ɗin, Yaushe ya dawo? Mene ya same shi yaga jikinsa da wannan raunin? Mene ya ja hankalin shi zuwa ga addinin Musulunci duk da sauri irin na mahaifinsa Denial, duk da kasancewar Kakansa Pasto a church ɗin da tafi ko wacce girma.
"Lafiyarka ɗaya? Mene yaja hankalinka zuwa ga Musulunci? Yaushe ka dawo?" Uncle Isma'il ya jerawa Abraham tambayoyin cike da mamakin domin kansa ya riga cushe. Abraham ya kasa cewa komai domin bashi da kalaman da za su iya fahimtar da Uncle halin da yake ciki,
But speaking the truth, he wants to be a complete, pure Muslim. Na gartaccen mutum mai tsafta. Al'amarin daya wakana akan idanunsa sun bashi malam tsoro da tu'ajujji wani abu mai sunun tsoro Abraham bai sani ba. that is the first way he will take to surprise Majeederh.
Uncle ya kalli ko'ina kafin ya tattausa murya ya ce
"Ka bari zuwa gobe sai muyi magana mu shiga ciki" Sai a lokacin cikin gurɓatacciyar Hausar shi ya ce "Uncly, Jee"
"Jee?" Uncle Isma'il ya maimaita kenan bai mance da ita ba?
"Abraham Maminka Majeederh bamu san inda take ba, we lost her" Ya faɗa cikin damuwa. Abraham ya ɗago kansa tare da saka hannunsa ya dafa cinyoyin Uncle Isma'il ya ce
"She slapped me, insulted me, said she hates me, babu ni rayuwarta abada" Baki sake Uncle Isma'il ya ce
"Ita Majeederh? Wait a ina ma ka ganta? Mene ya sanya harta mareka?" Ya ɗaga gajiyayyun idanunsa wanda babu ladama ko kaɗan a cikin su ya ce "Tana wajan Governor na garin, his prvt house" Uncle Isma'il ya dinga jinjina kai yana tunanin abinda ya kai Majeederh wajan His Excellency, mutum mai tsananin karamci da tausayin naƙasa da shi Al'ummar shi yana da tabbacin ba zai taɓa cutar da Majeederh ba. Ya duba agogon hannunsa yaga lokacin ya ja, gashi ance ma baya ƙasar yana Cameron. "dare ya riga da ya yi, gashi His Excellency ɗin ma baya ƙasar da nayi masa waya ina so contact nasa kai tsaye ba shamaki"
"Liar, yana nan infact shi ya sa a kai ni prison, a gabansa Jee ta mareni" Uncle ya yi shiru yana son fahimtar wani abu kafin ya ce "Me kayi mata?" Abraham ya ce
"Wai don na ce ni na bata ciki, am the father of her son, am the one who raped her, na rantse" maganganun Abraham su kayiwa Uncle girma a kunne ya fahimci akwai buƙatar neman Majeederh domin bai taɓa ji Abraham ya yi ƙarya ba, He is a man who stands by his words.
Uncle Isma'il ya ce "Amma me ya sa kayi haka Maminka ce fa?" Ya haɗe rai sosai yana ɓata fuska ya ce "Ni yanzu ban son Mamin, she's my wife to be pls Uncle I need your help, Dadyna baya understanding my feelings, Jee bata duba feelings nawa" ya faɗa cikin damuwa da murya mai rauni.. "Ka aikata babban kuskure acikin tsarin addininmu na Islam, wanda ya sha bamban da naku Addinin na Christianity mabiya Yesu, a tsarin dokokin Muslunci role and regulations ga duk saurayin daya aikata Fyaɗe bulala ake masa, mai aure kuma jefe shi ake, wannan abin ƙazanta ce ma fi muni, ba zan goyi bayan haka ba Abraham, Maminka?"
Uncle ya faɗa rai ɓace. Abraham was just looking into uncle's eye's ya kasa bambance fari da baƙi, yana son fahimtar mene abin kuskure a tarayya da mace? Koda yake shi addinin musulunci ya sha bamban da sauran, komai nasu sai sun kawo hujja, A strong argument.
Ya dubi Uncle a lokacin baka iya gane mai idanun Bad boy ke faɗa sbd launin da suka sauya a taushashe ya ce.
".... I Just gave her i kissed, i Little kissed on her neck, duk abinda ya faru it was a mistake"
"Mistake?" Uncle asked.
"I.... I... I am sorry Uncle"
Was the first time daya bawa wani haƙuri saɓanin Jee, yana mata abu immediately yake cewa "Sorry Malumana"
"Help" "Sai nayi bincike, idan ya tabbata dole ka amshi hukuncin Islama, bi ma'ana bulala, kuma na kafa maka sharuɗa"
"Accepted alrdy"
Uncle ya ce "Tashi muje, zan kira Dr ya duba ka"
Sai a lokacin ƙarfi yazo masa, da ƙyar ya miƙe kansa na juyawa. Cikin gidan shiru kowa ya yi barci Uncle ya nunawa Abraham wani bedroom, ya shiga ya haɗa masa warm water kana ya ɗakko masa wata jallabiya tare da barin bedroom. A daren Uncle ya kira Dr, kana ya kira Uncle Bello akan yana neman sa gobe by 11Am, daga nan ya turawa Abbu message akan umarni yake bashi gobe yazo yana nemansa.
Daga nan zama ya yi tare da buɗe system nasa ya shiga Gmail ya turawa zuwa ga email ɗin Governor Abu-turab Alƙasim na sirri akan yana buƙatar magana tare da full address da muhimmacinsa wajan Malama Majeederh Abdul'aziz Khan.
Washegari Abraham na zaune watching TV daga shi sai 3gauter da Armless mara nauyi wacce ta haska baƙar fatar jikinsa, gashin kansa sai ya yi kamar an gyara shi yadda ya cukurkuɗe kamar indomie, duk wajan ciwon anyi dressing nasa, idanunsa wanda suke always a haka He is so genius, and so romantic. Kana ganinsa kasan bashi da haƙuri zafin rai da taurin kansa, musamman physquie. Ba komai yake ɗauka ya zuba a brain nasa ba, amma ƙwaƙwalwarsa ta kasa mance ranar, komai ya faru cikin tsautsayi.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login