Showing 33001 words to 36000 words out of 125146 words

Chapter 12 - MIJIN MALAMA BOOK 1 Complete.txt

23 Nov 2024

9050

ta faɗa da mamaki domin bata gane ba. Majeederh ta kwasu chocolate guda uku a hand bag ɗin jakarta, ta farke guda ɗaya ta ajjiye, kana ta ajjiye guda ɗaya wacce bata farke ba. Sauran ɗayar ta riƙe hannunta. "Ɗauki ɗaya na baki" Aaliyyah ta dinga kallon chocolate ɗin daga ƙarshe ta saka hannu ta ɗauki wacce ba a buɗe ba. "Me ya sa ita?"
"Sbd ita ce a leda, kuma yadda ledar ke ƙyalli ta ban sha'awa" Majeederh ta harɗe hannu a ƙirjinta ta jima kafin ta ce
"Duk iri ɗaya ce fa?" Aaliyyah ta tura baki gaba ta ce "To ni dai Anti Jeederh wannan ta fi" Murmushi kawai ta yi ta ce "Wannan shi ne illar mace mai kyau, ta na saurin jan hankalin namiji sosai, da yawa sbd kyanta suke so sai an yi aure a fara samun matsala, shi kuma kyau sam baya tabba ranar ɗaurin aurenki ma mijin da zaki aura zai iya ganin wacce ta fiki kyau, to da ga nan yabar ganin na ki kyan sai na ta, duk wanda yake so na tsakani da Allah ko ban buɗe fuskata ba dole watarana ya bayyana a gabana da soyayyar shi, aure kuma lokacin ne let them do, idan sun samu ma su auren su ok" Aaliyyah ta sauke numfashi sbd samun kwanciyar hankali da bayanan Majeederh, ko babu komai ta san cewa ba baƙin jini Anti Jeederh ta yi ba kawai lokacinta ne bai ba.
“...Ya Allah..” Ta ce tana duba tsantsar kyan da Ubangiji ya yi mata, fara ce tas irin farin Fulanin Usul, gashin Idanunta dogwaye sun kwanta luff har saman fatar Idanunta, girar fuskarta har haɗewa take sbd tsabar yawa kuma bata askewa. Gashin kanta jaa bashi da duhu sosai kuma ƙaƙƙarfa irin na cikakkun Hausawa. "No"
Ta ce sanda Idanunta ya sauka a ƙirjinta domin duk wata baiwa a nan Ubangiji ya gama sauke mata su. Ita kanta mamaki take balle kuma ɗa namiji, ta riƙe jikinta sosai jin tsigar jikinta na tashi akwai abin da take tsananin so da ƙauna tun kafin ta kai wannan matakin, a lokacin bata san mene ba har ta dawo ta sani ta fara yin azumin kare kai. Misalin 8:30 na dare bayan idar da sallar Issha duk suna zaune a parlour suna cin abincin dare. Tuwon samo bita ne, da miyar kuɓewa wacce ta ji bushasshen kifi ƙamshi sai ta shi yake. Abbu ya gyara zama bayan ya wanke hannunsa ya ce "Rumana ki mini Hawwa'u"
"To Abbu" ta miƙe tare da shigewa Bathroom ɗin Majeederh ta sameta zaune saman ladduma hannunta riƙe da azkar tana dubawa ta yi murmushi ta ce "Malama Uwar malamai, don Allah ki taimaka ki samu mijin aure domin mu dai ba zamu jiraki ba" ko motsawa Majeederh ba ta yi ba balle ta ɗaga kanta. "To kyakkyawar gidanmu Abbu na kira" ta juya bayan ta sanar mata. A hankali ta rufe azkar ɗin ta miƙe tsaye hijab nata har ƙasa kai tsaye main parlour ta nufa duk suna zaune. "Abbu, Mami barka da dare" Mami ta ce "Ai na ɗauka waya kike sai na yi tunani baki da wanda zai kira, ashe ɗan gado ake"
Ita dai Majeederh couldn't speak. Abbu ya ce "Ki fara shirye-shirye scholarship ɗinki ya kusa fitowa zuwa Al-Azhar University" Ta ɗago kai da sauri gabanta na faɗuwa ina take jin Al-Azhar University? Ita yanzu gabaɗaya ma at her age ba karatu take buƙata ba, ta samu iya wanda ko wacce mace take burin samun wanda zai riƙe ta har zuwa gidan mijinta. "Hawwa'u"
"Na'am Abbu" "Ki na ji na ai ko?" Ta jinjina kai alamar eh kafin ta ɗago kai kaɗan ta ce "Abbu Al-Azhar fa a Egypt take, Abban Latifa ya ce aure za tayi, Abbu ni ma ka barni na yi...,"
"Na barki ki yi me?" Ya tambayeta a ɗan hassale. "Ina jinki" ta yi shiru Mami ta ce "Tana nufin kabarta ta yi aure ita ma, wanda ba shi da ko saurayi shi ke maganar aure", Aaliyyah ta ce "Ai wani ya zo zai auri Anti Jeederh Abbu yana ya kore shi wai ba yanzu za ta yi aure ba sai ta gama makaranta, kuma ina ta yi candy" Mami ta riƙe baki ta ce "Aaliyyah Uban naki kike so ki ce yana kurarwa Majeederh samari?" Aaliyyah ta girgiza da sauri ta ce "A'a Mami ba haka nake nufi ba, su Anti Ruma ne suke mata gori wai bata taɓa yin saurayi ba, kuma ai Abbu ke cewa samarin nata sai ta gama makaranta har su Master su P.h.n.d"
Abbu ya yi gyaran murya tare da cewa "Haka na ce, tsarina kenan ba ita kaɗai ba har ke" Ya juya kan Majeederh dake tsugune kanta a ƙasa ya ce "Karatun iya secondary bai isa ba, idan kuma kina da wanda yake son ki da aure ki sanar masa gobe ya zo ya saman sai na yi miki auren idan shi kike so" ganin ran Abbu ya ɓaci sosai ya sa Majeederh cewa "Ka yi haƙuri, Abbu to ka kai Raihana kaga ita akewa refitin a ss 1 take na bar mata scholarship ɗin" da sauri Mami ta ce "A'a, Raihana da Rumana duk aure za su yi, idan da rabo sai su yi karatun a ɗakin mazajen nasu" Abbu ya kaɗa babbar riga yana cewa "Shawarar da na yanke kenan, idan har ta kawo mini wanda zata aura gobe ni kuma zan aurar da ita" Ya yi waje abinsa. Majeederh ta miƙe tare da shigewa bedroom tana zuwa wayarta ta ɗauka ta kasa zama ta shiga lalubar number waya da ƙyar ta iya gano number kira uku ba a ɗauka ba, ta ƙara kira ana biyar aka ɗauka. Ajjiyar zuciya ta sauke mai ƙarfi kafin a hankali ta ce "Assalamu alaika"
An ɗauki tsayin daƙiƙo kafin ace "Wslm, lafiya?" Ta zare wayar ta duba number data kira. Imran dai tasa sani wanda yake mutuwar son ta shi taga sunan shi raɗau a saman screen ɗin wayar. Jin shiru ya sa Imran ya ce
"Majeederh ina da abin yi please, lafiya? Me ki ke da number ta?" A diriri ce sbd rashin sabo da magana ta ce "Uhm Abbu ya ce ka turo wai"
“.... Na turo me...” ya faɗa was abin da ta ce. Ta san ya gane rainin hankali ne, ko kuma har yanzu yana jin zafin kurar karen da Abbu ya yi masa. "Am listening"
"Magabata" Imran ta tuntsire da dariya sosai ya ce "Goodness, ni aurenki? For God sake?" Ya tsaya da dariyar da yake ya ce "Majeederh ai ni bana da burin auren mace mai shekaru ashirin ko sama da haka, kwanaki ma da na ce zan aureki sbd kina cikin age ɗin da nake son amaryata ta kasance, amma gsky yanzu kin mini tsofa" tunda ya fara maganar Idanunta akan Madubi yake kasancewar ba a jima da kawo nepa ba, tana jiran taga ta ina ta fara tsofa a shekaru ashirin shi ne har mace ta fara tsofa?. Imran ya ce "Oh baki samu labarin Raihana nake so zan aura ba? Ko ɓoye miki suke? Ai kullum sai na zo wajanta zan ce kuma ina gab da shirin turo iyaye, am sorry Majeederh Abdul'aziz Khan, amma akwai solution idan zaki amince muna haɗuwa tare da ɗaukewa juna sha'awa da kewa sbd wallahi jikinki ba ƙaramin ruɗata yake ba, ina aurar ƙanwarki ke kuma ina keɓewa dake.....




MIJIN MALAMA
Paid book ne.
Book 1 and 2 1kne
0811923761616
Maganganun Imran su ka yi wa Majeederh dirar mikiya a kunne. Duk yadda take so tayi shiru ta kuma daure amma har zuciyarta ta kasa yin hakan gani take da zarar Imran ya fasa aurenta babu wanda ya yi saura zatai ta tabbata a gida. Majeederh ta runtse Idanunta a hankali cikin muryar dake nuna zallar abin da zuciyarta ke buƙata ta ce "Imran ba tsofa na yi ba, am just 20, na fi kowa kyau a gidanmu" ta ƙare maganar tana sanya duka hannunta tare da dafe kanta dake juya mata tana ganin komai bibbiyu. Imran ya miƙe ƙafafuwan a saman office ɗin shi idanunsa buɗe cikin isgili ya cewa Majeederh. "Tsari na ne haka, ina son auren macen da bata haura sha bakwai zuwa takwas ba, lokacin da na zo neman aurenki wanne irin rashin mutumci ne ba a nuna mini ba? Ko an faɗa miki ke kaɗai ce mace Majeederh, ki je kici karatu daman ni wayewar ki tsoro take bani karatunki ya yi yawa" ya juya kaɗan sbd ya ƙara sanyawa zuciyarta dafi, dafi irin wanda ta sanya masa, domin har ranshi yana ƙaunar Majeederh a shekaru biyun da suke shige "Ki roƙi Allah kada ki tsofa a gida, domin darajar mace gidan mijinta gadai ƙannenki....,"
“....Stop it, ya isa..”
Ta kashe wayar da sauri tana zubewa a gefen gado, ta kasa tantance wanne kalar yanayi zuciyarta ke ciki, da gaske ta tsofa ko kawai faɗar Imran ce? mene abun iliminta na addinin? Ta kifa kanta a tsakanin cinyoyinta tana ambaton sunan Allah. Aure take so da gaske yanzu ta fahimta kuma shi ne dalilin da yake sawa tayi azumi domin riƙe kanta.
Tana jin wayarta na ƙara ta shareta domin babu wanda zai kirata idan ba Latifa ba, mai kiran nata al'amuran bikin Widad ya sha kanta. Sai da ta kwashe adadin mintina kusan goma kafin ta ji sauƙin zuciyarta, ta miƙe a hankali tana cire kayan jikinta kai tsaye bathroom ta nufa ta yi wanka tana fitowa ta goge jikinta tare da zura night wear masu ɗan kauri sbd sanyin hadarin dake fusawa, ciwon Limoniyarta yana ƙoƙarin tashi, bata jin daɗin komai rayuwar tayi mata juyin wainar tan da wannan shi ake kira da gwara na yi bara a bulayi yin bara a kofai.
Jikinta sai fitar da ƙamshin Nivea men active clean shower Gel yake. Ta juya kaɗan tana jan pillow ƙarar ƙofar da ta ji ya sa ta yi saurin rufe Idanunta tana jiran ta ji wannan karan kuma mene? Waye kuma?.
Mami ta dubi Majeederh tana sakin murmushi ta ce "Hawwa'u shiru ke ɗaya? Sau zan faɗa miki ki daina zama haka, bakya gudun abin da zai taɓa lafiyarki 24hrs kowa na shira banda ke rayuwa za tayi haka?"
Majeederh ta lumshasshun Idanunta kamar tana jin bacci so romantic domin gabaɗaya idan bata yanayi na jin daɗin zuciya shagwaɓewa take kamar ba ita ce babba ba, bata taɓa riƙe da nuna shagwaɓarta ga abin da take so. "Ina magana ki na ji? Oh! Ni Asabe Allah ya ye miki wannan miskilanci maza tashi ki kwashe kayan dinner ɗin can" da tsananin mamaki wanda Majeederh ta kasa shanyewa ganin ita ko hannu bata saka cikin abinci ba. A hankali cikin jan idanunta tana lumshewa ta ce "Kaya? Dinner?" Ta furta cikin sanyin murya wacce take always cool and so romantically.
"Eh, abincin da su Rumana da Raihana suka ci, naga gabaɗaya suna wajan fira sun yi baƙi ke kuma babu abinda ki ke sai zaman banza, to tunda suna wajan mazajen da za su aura ai ke sai ki yi aikin gidan"
Tunda Mami take magana Majeederh ta zuba Idanunta wanda suke farare tas kamar madara. Rayuwa kenan! Zamani riga duk shekaru data bawa su Ruma amma yau ita ake cewa ta kwashe kayan abincin da suka ci sbd suna wajan samari duk sanda su kai aure bata san mene zai iya faruwa da ita ba. Bata ce komai ba ta miƙe tare da ɗaukan hijabi ta saka Mami ta ce
"Allah dai ya yanke kazar wahalar nan, ya kawo ƙarshen zamaninki bana iya bacci sbd tausayinki yanzu ke babu wani daya taɓa cewa yana son ki da aure?" Ba tare data kalli Mami ba tayi gaba tana cewa "Babu"
Washegari da wuri Majeederh ta tashi sbd daman tun Subhi idanunta biyu dalilin azumin data ɗauka ta gyara gidan bakiɗaya, tana cikin haɗa breakfast Aaliyyah ta fito tana murza Idanunta ta ce
"Good morning Anti Jeederh" bata kalleta ba sai data gama haɗa kunun gyaɗar ta juya tana harɗe hannu a ƙirji tana juya idanunta da suke ɗauke da ruwa kamar mai shirin kuka. Sai kawai ta girgiza kai tare da juyawa tana faɗin
"Ki haɗa a parlour" she said. "Ok Maah"
A parlour Majeederh ta samu Ruma na waya tana ganin Majeederh ta ce "My Imran ga Anti Jeederh ku gaisa"
"Antynmu, ok give her the phone" Imran said.
Ruma ta miƙe tana bawa Anti Jeederh wayar ta ce "My Imran zai magana da babbar yaya, yama ce mini wai zai haɗaku aure da ƙanninsa idan Muzayyid ya amince"
Majeederh tayi jim she was so speechless.
Sai kawai tabar parlourn Idanunta rufe zuciya babu daɗi. Kaya ta sauya cikin Nidha abaya dark blue tayi rolling da babban vail kafin ta ɗauki kyakkyawan liƙab ɗinta ta sanya, gabaɗaya yau ta kasa jurewa dole ta isa gare shi, shi ke ɗauke mata kewa. Ta samu Abbu a parlourn shi ta tsuguna har ƙasa ya amsa yana cewa.
"Ya maganarmu dake?" Ta yi shiru ta kasa cewa komai. "Zan iya ɗaukar shirunki matsayin amsa"
"Abbu ka zaɓa mini ko waye, na amince zan aure shi" “…. Karatu na zaɓa miki, ki je nan da shekaru uku zuwa huɗu sai ki aure kafin nan kin kammala karatu"
Ta runtse Idanunta bata san amsar data bawa Abbu ba sai tsintar kunnenta tayi ta jin yana cewa "Allah ya yi miki Albarka, su dai bar su suyi auren tunda shi suka zaɓa"
Fitowa tayi bayan tayi sallama da mutanen gidan kanta a ƙasa tana rungume da ƙirjinta tafiya take a hankali mai cike da nutsuwa da kamala, ilhamarta ta gama bayyana gidan karamcin data fito, tare da tarbiyyar da take da shi. Napep ta tsayar ta shaida masa inda zata, tunda suka shiga kanta ke sunkuye lokaci zuwa lokaci mai napep ɗin ke kallonta ta cikin madubi har ya isa bakin gate ɗin data shaida masa. "Mun iso" ya ce yana karkaɗe kujerar da yake kai da dosta. Shirun da ya ji yasa ya juya mamakin yadsuta zuba tagumi Idanunta rufe yake yatsun hannunta kawai ya kalla yasan za a zuba kyau kuma Ubangiji ya gama tsara halittar shi a jikinta. Ya ce "Malama mun iso" Majeederh ta yi saurin buɗe Idanu, domin sunan da ɗalibanta na makarantar Ahlul Madar suke faɗa mata kenan Malama Majeederh Abdul'aziz Khan!
Ya saki murmushi ta cikin liƙab tare da fitowa tana ɗaukar jakarta ta bawa mai napep ɗin guda ɗari biyu. Ya ɗauki hamsin ya bata ta kalli hamsin ɗin ta ce
"100 ne" "Tab,Yoo maganar da kike wazai kawo ki nan a ɗari inda aka ƙarawa litar mai kuɗi" bata iya musu ba ta juya tare da nufar gate ɗin da aka rubuta.
*"An orphanage for young children"*
Ta faɗaɗa murmushinta tare da ɗan ƙarawa tafiyarta sauri zuciyarta sai janta take Idanunta ya kwaɗaitu ta son ganin abin da su kayi kewa. Kewarta ya yi mata jagora har zuwa office ɗin Akeeth. Yana ganinta ya miƙe tsaye with so much respect na tarin iliminta bawai don ta girme shi ba ya ce
"Your wlcm Majeederh-khan" ta jinjina kai tare da zama kan kujera tana rarraba Idanunta dake cikin liƙab, Akeeth ya ce. "Bar gaigaye za kici tumu ne"
"Uhm" ta furta ta ɗauki Wayarsa ringing ɗin farko aka ɗauka Akeeth ya ce "Come with him"
Ya kashe kiran yana kallon Majeederh yadda take kallonsa yasa ya fahimci me take nufi ya ce "She's goode, but she's trouble Maker very stubborn boy" "....Am very sorry for that"
Majeederh said. Tana haɗe hannu waje guda alamar ban haƙuri.
Akeeth ya watsa hannu baya ya ce "Is there nothing serious, kawai har yanzu bai sauya ba"
Ya gyara zama sosai cikin fahimta ya ce "Baya jin magana, ya yi ƙanƙanta da irin trouble ɗin da yake haɗa mana, he just Five years amma fitar shi ne sai shi, baya ɗaukan karatu da muhimmaci" Majeederh tayi shiru kawai domin bata san me zata ce ba, bawai don ta rasa ba, sai don bakinta ya yi mata nauyi harshenta ya harɗe bakiɗaya. Tun kafin ya shigo jikinta ya bata yana tsaye a ƙofa ta juya da ɗan sauri ganinsa tayi tsaye daga shi sai gajeren wando na Adidas sai wata ƴar shirt mai photon lion a gaba wacce ka yaga masa ita ta baya, jikinsa futu-futu.
Kan nan na shi gabaɗaya a cure fatar shi haƙa ƙarin, ta dube shi suka haɗa idanu da gudu ya ƙarasa wajanta cikin farin ciki da murn ya faɗa jikinta yana cewa
"Mamina, ƴar madara"
Faɗa zata yi masa amma jin yadda yake sauke ajjiyar zuciya a jikinta ya yi lamo tare da ƙanƙameta ya sa rauni ya bayyana a tare da ita, rauni irin na uwa da ɗanta ta lumshe idanu tana shafa sumar kan shi "Little" "Ƴar Madara"
Ya ce yana rufe Idanu tasan tunda ya ce Ƴar madara bai ce Mamina ba to fushi yake da ita.
Akeeth ya ce "Majeederh ni banga cancantar riƙe shi a wajanki ba, duba da cewa ke ba aure gareki ba, kuma idan kika duba yanayin society ɗinmu akwai wasu abubuwan da idan mutum mara aure ya yi shi musamman ɗiya mace za a fara yi mata wani irin kallo nada ban, tunda mutane basa buƙatar bincike kafin making decisions zuwa zatar da shi, kawai the only thing da suka iya yaɗa jita-jita da ƙanzon kurege, You have to be very careful"
"I'll, but" ta yi shiru daga maganar. "But what? Open your heart Mrs Khan" Majeederh ta ce
"About his family?" Akeeth ya ce "Oh Yes! Babu wata amsa gamshasshiya wacce bincikenmu ya nuna, na faɗa miki a bakin masallaci aka tsince shi a shekaru uku da suka gabata,zan ci-gaba da bincike komai ake ciki I'll let you know" ta jinjina kai Akeeth yana ta son ko sau ɗaya ne yaga fuskar Majeederh amma ina. Ta miƙe tsaye tana riƙe da hannun Little.
"Thank you!"
"Always Wlcm" fita su ka yi har bakin gate tana kallon yadda Little yaƙi ce mata komai, alamun ya yi fushi sosai ta duba hamsin ɗin da tayi saura a hannunta sai kawai ta bawa mai ice-cream na kan hanya ya bata na hamsin ɗin ta kalli kyakkyawar fuskar shi wacce ta kasa bayyanar da asalin yare ko ƙabilar daya fito ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login