Showing 42001 words to 45000 words out of 125146 words

Chapter 15 - MIJIN MALAMA BOOK 1 Complete.txt

23 Nov 2024

9061

bata da wani kuzarin yin magana. Ya juya a hankali da ɗan sauri kuma ya buɗewa Majeederh ƙofa ta shiga a nutse da addu'a bakinta. Ya buɗewa Latifa Omar gaban motar ta shiga. Tafiya suke a nutse ya gyara zama ya ce "Sunana Barrister Aliyu Sufyan Alhassan" "Nice" Aliyu ya shafa gemu ya ce "A gida more especially Hajia suna ce mini Zaki, am the second born of my parents, ina da babba yaya Almustapha, mahaifina sunan shi Sufyan Alhassan yana nan tare damu, ya su nayi aikin jarida na ƙi, to ya na iya abincina yana ga Shari'a, sai mahaifiyata we call her Hajiya, I love my mother more than anything dake duniyar nan tamu, na yi karatu mai yawa akan Shari'a now an working with Shari'a court of appeal ban jima da fara aiki ba" Tunda ya fara magana Latifa ta rufe Idanu sosai har cikin zuciyarta Aliyu ya kwanta mata irin mijin da take so daka gani zai yi haƙuri sosai. Har suka isa gidan Uncle Isma'il Majeederh ko tari ba tayi ba ta rungume Little kamar zata mayar da shi ciki, lokaci zuwa lokaci Aliyu ya dinga kallon Majeederh ta madubi, duk sanda ya kalleta sai ya sauke numfashi a ɓoye. Suna tsayawa ta buɗe ƙofa ta fita ta shige ciki, da sauri kamar wacce wani abu ya biyota. Innati dake maƙale a bayan labule ta buga tsalle tana faɗin "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un, wahala haula wala ƙuuwata, uban waye a wannan wajan?" Majeederh ta shiga tana sauke numfashi Innati ta ce "Amma dai Allah ya isa Kululu, Allah ya isa saura kaɗan na saki gudawa ɗaukan hakƙin nan har ina? Ashe ƙatuwar jahila muke zaune da ita kinsan alhakin da kika ɗauka? To wallahi ba wani yafewa nayi ƴar banza da fuska kamar karas" Majeederh ta tura baki tare da kwaɓe fuska ta ce "Ki barni" Innati ta riƙe haɓa ta ce "Na barki ba? Idan na barki a duniyar nan Kululu na kama ubanwa? Wa kike da shi daga duniya har lahira wanda ya shige ni?" Majeederh dai ba tayi magana ba ta ɗaga liƙab ɗin fuskarta Innati ta zabga sallati ganin yadda fuskar Majeed ta yi jajur kamar jini ya kwanta. Innati ta kwasa a guje zani na faɗuwa ta shiga faɗin "Muhammadur Rasulullah Sallallahu alaihi Wasallama, Isma'ila masifa ta faɗo mana uban kowa ya yi ta kansa Aljana mai kama da Kululu a ɗakina....




*A yi karatu a nutse, a fahimta a ilmance, a nishaɗantu. Muna nutsawa a labari zaku kasa bacci da sukuni. Soyayya ce mai wahalar gogewa, ƙaddara ce mai wahalar fahimta. Babu batun sadaukarwa faɗa ne akan Soyayya!*


Allah ya nuna mana Monday Lafiya, a yi weekend cikin farin ciki.... 08119237616




Nimcyluv20
"Masifa da bala'i, Kamarni har wata Aljana ta isa ta firgita? Ina Isma'ila ya zo ya yi mini iyaka da wannan Aljanar tun kafin raina ya ɓaci" Innati ta faɗi hakan jikinta gabaɗaya rawa yake na fargaba da tsoro, tuni ta yi wurgi da zanin jikinta sai ɗan tofin daya rage mata banda haka tsirara za ta yi.
Uncle Isma'il daya fito a hargitse sbd jin kiran shi da Innati ke yi ya sa yana zuwa ya ce "Innati lafiya dai? Mene ya faru?"
Ta girgiza kai ta ce "Lafiyar kenan, maza maza a haɗa mini kayana yau sai gidan Bello, ba zan zauna matarka da kasheni ba, ina sane ita take tura mini Aljanu" Uncle Isma'il ya kusan tuntsirewa da dariya amma babu hali duk abin da ya kuro ɓera da ga wuta, ya fi wutar zafi. "Majeederh ta ƙarasu?" Ta zare idanu ta ce "Wata abace haka? Ka je dai kaga turan da akai mini da wata Bafullatanar Aljana" Uncle Isma'il ya bar Innati a tsaye, tare da nufar ɗakinta. Yana shiga ya samu Majeederh durƙoshe a saman gwiwoyinta ta dafe kanta da hannu bibbiyu wanda yake bazaranar rabe mata gida biyu sbd tsananin ciwon da yake mata, ta rufe idanu sosai sbd komai bibbiyu take ganinsa a cikin idanun nata. Uncle Isma'il ya zuba mata ido cike da tausayinta yasan duk abin da zai sanya Majeederh cikin wannan yanayin ba abu ne mai sauƙi ba. Ya dubi Little dake tsaye ya ɗora kansa a bayanta ya saƙalo wuyanta tare da yin lamo, yanayin Mamin tasa ya taɓa kuzarin yaron. Ya nemi waje ya zauna saman kujerar dake ɗakin na Innati, cikin kulawa ya ce
"Hawwa'u!" Ta yi sauri ta ɗago kanta tare da ƙaƙaro murmushi ta ɗorawa fuskarta matsayin dole. Cikin sanyin murya kamar kullum ta ce "Ina yini Uncle?" Ya ce
"Lafiya" ya yi jim kafin ya ɗora da "Ke kika firgita mini uwata ko?" Ta ƙara yin murmushi kamar ba za ta yi magana ba ta ce
"Da Aljana take haɗani fa" Ya yi murmushi ya ce "Dole ta haɗaki da Aljanu, ni kai na mamakin kyan da Ubangiji ya yi wa ƴata nake, sai yanzu nake ƙara ganin cancantar suturta fuskar da kike"
"To ALLAH ya isa, Allah ya isa shi kaɗai zai isar mini idan ka yafe Allah ya tsine" Innati dake bakin ƙofa tana leƙowa ta furta hakan lokacin data tabbatar Jikarta ce Majeederh Abdul'aziz Khan! "Ki yi haƙuri Innati"
Innati ta fashe da kuka sosai tana face hanci ta ce "Wallahi ba dani kike ba, ba kuma ni ki kaiwa ba, Ubanki mai faɗin ran nan da manyan Idanu Audil azizu shi kika tsoratar" Majeederh dai bata kulata ba, domin tunaninta baya wajan gabaɗaya zuciyarta tana wani birgire wanda kullum take ganin kanta acan, a cikin mafarkanta na kullum.
"Majeederh wa kika bari a waje? Na ga mota" Uncle Isma'il ya faɗi hakan cike da zumuɗin jin Majeederh ta ce wani ne ya kawota, addu'a yake Allah ya sa nata rabon auren ne ya zo.
"Latifa Omar ce"
"Ayya to, Allah ya amfana" Ya gyara zama sosai ya ce "Hawwa'u ki faɗa mini gaskiya, mene hujjarki na barwa Rumana saurayin dake son ki yake son aurenki a lokacin baya, sai yanzu kwatsam! Reshe zai juye da mujiya wai kin fasa auren shi ya auri ƙanwarki Rumana anya akwai ƙamshin gaskiya? Domin na lura da rashin nutsuwarki, A can gidan" Ta yi shiru domin bata da amsar tambayar Uncle ɗin nata, ita yanzu a yadda take ji ko sa'an mahaifinta Abbu aka bata matsayin miji da gudu zata amsa, koda ha za ta yi farin ciki ba da zama da shi muddin zai ɗauke buƙatar ta, wacce ke damunta take sanyata rama da ibadar dole.
"Ina jinki, kin fi ganewa ki zauna duka ƴan-wanki su yi aure ke kina gida? Kin fi ganewa ki gansu da mazajansu gwanin sha'awa suna yin soyayya da rayuwar aure mai tsafta? Su haifi ƴaƴa wanda ko wanne mai rai yake muradi, inma namiji inma mace? Zuciyarki ta yi rayuwarki adalci? Anya Hawwa'u-Jidderh?"
"Ka yi haƙuri Uncle, Idan da rabo zan yi auren"
Maganarta ta narkar da zuciyar Uncle Isma'il, kalamanta sun nuna karaya zahirin fuskarta kuma ta amshi ƙaddarar tare da godewa Allah bisa tarin Ni'imar da ya yi mata, tasan yana sane da ita bawai barinta ya yi ba. "Shikenan, ALLAH ya yi miki Albarka ki je wajan Luba" caraf Innati ta ce "Wacce masifar ce Luba? Ka fita daka idanuna Isma'ila matar taka da ban gama sanin zuciyarta ba ita zaka turawa Kululu? Ƴar Gombe? Wato ta tsaface ta bayan kasan yadda Fulanin Gombe suke?"
"Allah ya baki haƙuri Innati, zan shige taron da ake yau babu mamaki na samu dacewa da aiki mai kyau" "A to! Ya dai fi maka, kamar tsiya akan ƴaƴana ta kare kowa fama yake da kansa da azababben talauci, In sha Allah tsalelen miji Kululu zata aura na tarkata na koma gidanta" Murmushi kawai Uncle Isma'il ya yi tare da shafa kan Little ya ce "Yau ba magana?"
"Mami kakewa faɗa"
"To ɗan Maminta Allah ya baku haƙuri kai da Mamin" Yana fita Innati ta yi ƙasa da murya ta ce
"Munafuki, ai duk tsinewa matarsa da nake to ta shi nake, daga shi har Ubanki Audil azizu sai na kai su hisba uban kowa ya huta, turmin atamfar ankon wannan yarinyar Wifat fa na ce ya siya mini wai bashi da shi?" Ta ƙara girgiza kai ta ce "Hoo! Ƙasa Ubangiji ya baki miji mai kuɗi wanda zai so ki"
Majeederh ta marairaice fuska sosai ta ce "Innati bar maganar auren nan"
Innati ta riƙe haɓa ta ce
"To ba zan bari ba, Annamimiyya ina nan watarana idan ban mutu ba sai mijinki ya sunkuya ya miki doki-doki dake da yaran da zaki haifa, wallahi ko bana raye sai kin tuna wannan maganar tawa, zaki haifi zuri'a mai yawa zuri'ar da babu Uban wanda ya taɓa haifarta a cikin ƴan-uwanki da iyayen naki" Majeederh ta lumshe idanunta a zuciyarta tana tona tsayin shekarun da zata ɗauka kafin tabbatuwar hakan! Innati ta fashe da kuka ta ce "Allah ba zai barki haka ba, wallahi halin Uwarki Fulani kika ɗauka, har tsinannen kyan da kike da shi duk nata ne, ki rubuta ki ajjiye watarana sai labari ni dai ki sani ina son ki ba zan baki gurguwar shawara ba, amma dai Allah ya yi ɗaiɗai da zuciyar Rumana" Surutun Innati ya hau wa Little ka, daman ba daɗi yake ji ba ta shagwaɓe fuska tare da fashewa da kuka ya faɗa jikin Majeederh ya ƙanƙameta "Mami gida"
Majeederh ta yi saurin rungume shi tana shafa kansa yau ɗin gabaɗaya ta rasa meke damunsa ga kanshi zafi kamar mai zazzaɓi. "Innati kin firgita mini yaro" Innati ta riƙe baki ta kasa cewa komai sai can ta ce "Ba zan ce komai akan yaron nan ba, amma dai a guji gobensa akwai abubuwan Al'ajabi cikinta" Majeederh ta ɗauke ɗan ta tare da rungume shi sosai a ƙirjinta tana ji yana sauke numfashi ya ƙanƙameta.
Latifa Omar ta yi murmushi mai kyau tare da kallon Aliyu ta ce
"Kana da abin dariya"
Aliyu Sufyan Alhassan ya ce "Uhm Latifa Ina son ki, bana son a ɗauki lokaci ki bani dama"
"Daka ganin sarkin fawa sai miya ta yi zaƙi?" Ya yi murmushi kawai kana ya ce "Bani labari"
"Na me? Akan wa?" Latifa Omar ta tambaya. Ya ce "Your friend"
Ya nuna ƙofar gidan da Majeederh ta shiga. Latifa ta juya idanunta ta ce "Oh, Sunanta Majeederh Abdul'aziz Khan! Iyayenta suna yawan ce mata Hawwa'u, ƙannenta musamman Aaliyyah tana ce mata Jeederh. Mun yi makarantar primary lokacin ɗaya, amma ta fini ƙoƙari ne sa ba kusa ba, da yawan lokaci ina hana kai na bacci ganin na zama ita, sai na fahimci iliminta baiwa ce, daga Allah. Biye ɗaya takewa ayar Alkur'ani ta hadda ce ta, tun muna primary ta rasa mahaifiyarta, she left her, at the same time ta yi saukar Alkur'ani, ni kuma na maimaita aji, a lokacin da ta zama hafiza a lokacin na yi sauka ta farko" Ta yi jim,tana rayuwa da step mother ɗin ta, kishiyar babbar ta, ilimin Majeederh ya sa Manyan mutane na primary school ɗin mu suka shige mata gaba wajan samun scholarship a matakin secondary school, ta samu makaranta mai kyau tun a lokacin Karatun ta a ɓangaren Islamic yake, yanzu maganar da nake maka ranar Candy ranar ta zama Gwarzuwa a ɓangaren musabaƙar Alkur'ani, wannan shi ne kashi na wajan uku na dai manta Makarantarmu Ahlul Madar tana bada sunanta matsayin wacce zata jagoracemu, yanzu haka sunanta yaje ko'ina duk wata gasar karatun Alkur'ani indai Kano zamu shiga to ita za ta yi" Ta ja aya tana sauke numfashi. Tunda ta farar maganar idanun Aliyu a rufe yake ruf ta ce
"Lafiya?" A taushashe ya ce "Ina jinki"
"Majeederh ta zama malama a Ahlul Madar duk wata suna bata albashi, da albashin take kula da yaron daka gani a wajanta" Ya ware idanu da mmki ya ce
"Yaro? I heard you kin ce single take, not house wife" ta ce "Eh, Tsintar yaron ta yi, kuma tana son sosai banda kada na yi maka ƙarya bayan iyayenta babu wanda take so kamar Little, tana iya haƙura da cikinta ta bashi ya ci, kuɗin Makaranta, kayan sawa duk da albashinta take masa, kuma a ciki take taimakon Abbu da abincin gida, by the way yanzu tana shirin tafiya ƙasar waje Africa, ta samu scholarship za ta ɗora University ɗin ta a can ɓangaren Islamic and Arabic studies"
Ta yi shiru ganin kamar Attention ɗin Aliyu baya kanta ta ce "Ya dai?"
"Wacce ƙasa?" Ya faɗa yana murmushinsa mai kyau da aji. "Misira"
"Ok Egypt, Allah ya taimaka" Latifa Omar ta ce "Amin".
A can cikin gida Hajiya Luba ta kalli Majeederh ta ce "Yanzu karatun zaki?" Majeederh ta sauke ajjiyar zuciya a fili tare da jinjina kanta alamar "Eh, Mama"
"To Ubangiji ya sa rabokin ke kiranki, Allah ya baki ikon cinye ƙaddarorinki mutane ne kawai da basu son zama lafiya gabaɗaya nawa kike balle ƴan-uwanki shekaru Ashirin bai ci har a fara gorantawa mutum bai aure ba"...
“...... Allah ya kyauta”
Ta ci-gaba da bata haƙuri da ban mamaki. Har Latifa Omar ta shigo suka ta fi gidan Yaya Bilkisu domin acan ake Sabgogin bikin Widad ɗin. Ko! Da ta je bata iya zama ba ƴan matan familyn Khan, suka shiga sauke magana. Kusan duk akan Idanunta aka haife su sbd rashin aure ya sa girmanta ya zube. Tana zaune kiran gaggawa ta sameta zuwa Orphanage for young children, kira ne daga kai tsaye daga Akeeth. Yaya Bilkisu ta bata kuɗin napep daman tuni ta ce Latifa Omar ta tafi kawai. Tana gab da zuwa ta sake kiranta.
"Assalamu alaika"
Majeederh ta furta cikin muryarta mai sanyi daɗi a kullum. Akeeth ya amsa ya ce "Am sorry Majeederh,na samu meeting na gaggawa idan na gama ko kiranki ne zan yi" Jikinta san yi ƙalou ta kashe wayar ba tare data ko amsa masa ba.


Unguwar Darmanawa
Idanunsa rufe yake kallon selling ɗin dake cikin bedroom ɗinsa, lokaci na farko a rayuwa da ya yi nauyin baki wajan furta abin da yake so. Ya juya kaɗan yana sake mirginawa hoton idanunta kawai suke gilmawa cikin nasa idon, ganin abin bazai goge ba sai ma ƙaruwa da yake ya sa a hankali ya miƙe ya shiga bathroom tare da sakarwa kansa shower yana riƙe ƙugunsa bugun zuciyarsa na ƙaruwa gabaɗaya Latifa Omar ba tsarin aurensa ba ce, me ya kai shi? “Density” Shi kansa bai adadin lokacin daya ɗauka a bathroom ɗin ba, sai da ya ji ana knocking ƙofar part ɗin shi ya fito ɗaure da towel a jikinsa.
"Meke damun ɗan autan Hajia yau da bai yi dinner damu ba?" Aliyu ya shagwaɓe fuska sosai autar ta motsa daman rauninsa da wuri yake fallasa asirin zuciyarsa. Ya ja baya yana zama kan kujerar dake kusa da gadon shi, ɗan ƙasar Turkiya. "Hajia"
"Na'am Autan Hajia" Hajia ta amsa tana jiran ta ji dame yau kuma ya zo, domin shi Aliyu baya rabo da issues sbd tsabar taɓara gashi kyakkyawan ajin farko sai ka ɗauka Half-caste ne. Looking so classic. "Aure zan yi, na samu mata" Ya faɗi hakan domin a tunaninsa shi ne mafita ga abin da yake ji, wacce zai aura daban, wacce ta yi zuciyarsa kamo daban. Ko mene hakan hakan? Only God knows.
Sosai Abbu ya yi wa Majeederh faɗa don me bata ƙarasa ta karɓo form ɗin ba? Ita dai bata ce komai ba ita kaɗai ta san abin da take ji. Yau ɗin ma sai da ta yiwa Little wanka ta sanya masa kaya masu ɗan sauƙi bata son ya kwana da zazzaɓi. Ta tsora masa idanu a hankali ta ce "Little zaka manta dani?" "Me?" Ta tambaya domin bai fahimta ba.
Ta ce "Idan na ta fi karatu, karka manta dani ka ji? Kada ka bawa wata matsayin uwa a zuciyarka idan ba Maminka ta gasky ba, ka da ka ci amana" Ita kaɗai take magana ita kaɗai kuma take fahimtar me take cewa. Ya shafa laɓɓanta da suke jajir ya ce "Mami ni ma irin naki"
Ta yi murmushi tana ɗaukar shi tare ta ɗora a cinyarta ta ce "Until you grow up" Ya shiga buga ƙafa da yarfe hannu shi a dole sai laɓɓansa sun yi irin na Maminsa Jee ta tura masa baki ta ce
"Ok Shafi kaɗan, da safe sai koma red" Ya yi murmushi yana tsalle ya ɗora bakinsa a nata ya shiga goga sai ta gaji ta ɗauke shi tana dungure masa kai, ƙara wayarta ta yi tana duba taga albashi akai mata sosai ta ti farin ciki gobe za ta yi masa siyayya. Tunanin yadda zata rabo da Little tsayin shekaru takwas shi ne ya bijiro mata, rabon da ta yi kuka ta manta sbd kansa cewar ta mace jaruma da zurfin ciki. Ta samu kanta da rungume Little ta fashe da kuka sosai, kukan da rabon da ta yi shi tun rasuwar Fulani. Wani irin kuka take da dukkan ƙarfinta wanda yake tasowa tun daga ƙasan zuciyarta. Ganin tana kuka ya sa Little fashewa da kuka sosai. Da ƙyar ta rarrashe shi suka kwanta bacci. Kiran sallarsa farko ya farkar da Majeederh daga bacci a hankali ta shafa tana son taɓa jikinsa ta ji ko da zafi. Wayam! Ta buɗe idanu taga babu Little a kan gadon ta miƙe da sauri idanunta ya sauka akan ƙofar ɗakinta dake buɗe bayan har rufewa ta yi. Da sauri ta ce "My Son, Little?....


Paid book
MIJIN MALAMA
0811923761621
Sosai Majeederh ke kuka kamar ranta zai fita har da shassheƙa Mami dake tsaye ta riƙe haɓa ta dubi Majeederh ta ce "Yanzu ke kina Ina yaron ya zare sakata ya yi nasa waje" Ta kasa cewa komai sai kuka gabaɗaya hankalinta ya ta shi ta zama kamar ƙaramar yarinya. Mami ta ƙara tafa hannu ta ce "Yaro ne mai shegen karambanin tsiya, ko gidan uwar wa ya sani wanne hannu zai faɗa ohho, ga yadda ƴan mafiya da ƴan kidnaping su ka yi yawa a gari" Majeederh ta ƙara rushewa da kuka ta ce "Little ba zai taɓa buɗe ƙofa ya fita ba, ina yaga tsayin?" Aaliyyah ta ce
"Kuma ko ya iya buɗe Ƙofar ɗakin ki Anti Jeederh ai ba zai iya buɗe ƙofar waje ba" Abbu wanda ya fito da shirin fita Masallaci ya gyara muryar kowa ya shiga hankalinsa kamar sun ga mala'ika ya dube su ɗaya bayan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login