Showing 51001 words to 54000 words out of 125146 words
na samu jika da yawon zawarci?" Ta ja numfashi ta sauke ta ce "Allah yana gani na fara gajiya yana neman shafa mini baƙin fenti" Murmushi kawai Majeederh ta yi ta ce "Ba komai"
"Da gaske babu?" Ta jinjina kai ta ce "To Allah ya iya mana, ko can ɗin kika je kiyi ta addu'a, ki riƙe mutumcinki har zuwa shekaru takwas ɗin" Kanta a ƙasa ta ce "Na gode" Mami ta miƙe tsaye tana cewa "Maza ki tashi ki shirya wani sa'ilin ke kike mai da kanki baya ayi mace ba kwalliyya? Ba kwalli ba powder, fuska kullum a rufe da wata ƴar malafar uban duguwar riga, kamar matar mamaci ko wacce aka koro daga Saudiya? Fuska a maiƙaci sai farin bala'i kamar an kwara miki man ɗanyar gyaɗa haba Majeederh? To ai shikenan" ta saka kai ta fice abinta.
Majeederh ta sauke ajjiyar zuciya, wai ta yi kwalliyya? Ai bata da wata sauran dama ta riga ta sallama, ta yarda ta amince domin ta yi ilimi da bautar Ubangiji take raye, ta yarda ita ta rako mata duniya ko me za ta yi a rayuwa ba zai taɓa sauya abin da zuciyarta ya yarda da shi ba, ko fata za a sauya mata ba zata taɓa samun mijin aure ta yarda za ta yi karatu zata zama cikakkiyar Malamar addinin Musulunci zata fafata da duk wanda zai ja da wata ɗiyya mace zata zama jaruma mai yarda da suke abin da Ubangiji ya zo mata da shi, yarda da ƙaddara ta zama feminist. Ta buɗe wayarta tare da kunna network ta shiga facebook, abin ya bata mamaki ganin ta samu mabiya da yawa sosai kamar jira ake ta buɗe. Ta shiga wajan timeline ta yi rubutu ta ce “ITA MACE, BA BAIWA BA CE, KO A GIDAN MIJI" tana gama rubutawa hannunta na rawa ta yi posting ɗinsa, Just now amma over 100 comment ta duba sunan wani Bilal-Habib ya ce
“Uhm ke ba aure ba, kuma zai kashewa wasu? Shi aure ne ba bauta ba? To uwarki ne?" Tana gama karanta idanunta ya sauka akan wani da ya rubuta.
"Malama Majeederh ki bari ki fara auren ko? Ai wannan maganar bata yara ba ce" Da sauri ta yi wurgi da wayar bayan ta kashe datar zuciyata na harbawa. Ta daɗe kafin ta samu nutsuwa. Mami da maƙociyyarta na zaune suna hira Latifa Omar ta yi sallama ta shigo cikin wani lace mai kyau ta sha kwalliyya ta ce "Ina yini Mami?"
"Lafiya lou Latifa ya Maman taki?" Ta ce "Ta ce a gaisheki, Majeederh fa?" Da hannu ta nuna mata hanyar ɗakin Majeederh ta shiga da sallama ta sameta zaune ta ce "Ya naganki zaune ba kyan gani? Kamon ba?" Ta yi shiru idanunta akan waya tana da Research more than 2hrs tana abu ɗaya "Amma dai baki isa ki ce ba zaki ba ko? Bikin Widad ƴar uwarki ni ma zani balle ke?" Ta ce "Mene amfanin zuwa? Ana zuwa domin farin ciki ni raina ke ɓaci Latifa Omar ki bari kawai karatu zan yi" Latifa ta zauna ta ce "Mene ya faru?" In brief ta faɗa mata komai, Latifa ta yi jigum ta ce "Kamar wata mujiya, Majeederh anya lafiya?" Majeederh ta yi murmushi ta ce "Lafiya lou, i believed Ubangiji ke komai i trust ni mutum ce ba Aljana ba....
MIJIN MALAMA
0811923761624
Latifa ta kalli Majeederh ta ce "Amma ba zaki gudu ba kowa? Ki bar gidan kawai idan a kaga babu ke dole a haƙura" Majeederh ta shanye mamakin da Latifa Omar ta bata, she just staring at her kafin ta girgiza ta ce "Kina nufin na gudu na bar gidanmu? Sbd buƙatar mahaifina?" Latifa ta ce "Yes, that's what i mean, idan kika ta fi after a month or a year sai ki dawo nasan babu abin da zai ce, sai murnar ganinki Majeederh" Tunda ta fara Maganar Majeederh ke jin zafin zuciyarta na ƙaruwa ta ce "Anya ke ƙawar arziƙi ce?" Latifa ta ce "Haba Majeederh? Is just a suggestion bawai dole sai kin aikata hakan ba, kawai gani na yi kina cikin takura na mahaifinki by the way ga rashin saurayi da baki da shi balle mijin aure"
"Kuma ɗan ƙaramin tunaninki ya baki na gudu? Kina gidan iyayenki,ni ki bani shawarar na yafi yawon duniya? Na taɓa ce miki Abbu ya takura ni?" Latifa ta yi shiru, Majeederh ta haɗe fuska babu alamar her heart stopped beating, ta ce "Ban so, a gaban saurayinki kin zauna kina zayyana masa Abbu faɗa zai mini idan ban amshi form, mene nashi? Ko halin ubana kike faɗawa wani? Ba ruwana da wanda kuke tare ki daina faɗa masa wace ni ko ya nake" Latifa da mmkin maganar Majeederh ta ce "Ba dai wata manufa kika juya zancan ba?" "Ban ji daɗi ba" Majeederh said quietly. Kana a raunace ta ce "Na yarda ni macace mai tarin buƙatu, ina sane da abin da ke yawo akaina, amma Latifa ban taɓa cewa ki bani ko biyar ba, na yarda Allah ke yi, na riƙe aikina da albashina nake komai, na taimaki mahaifina, kun fimu wadata amma Allhamdu lillahi, ina da wadatar zuci kuma yanzu na fahimci maganar Abbuna, to ki daina tunani komai mahaifina ya yi zan iya barin gidan nan, ya zama first and last time da zaki bani wannan shawarar" Ta faɗa cikin daɗin zuciya tare da miƙewa zata bar wajan, Latifa Omar ta riƙeta ta ce "Ki yi haƙuri Majeederh, i don't mean to hurt you, ba zan sake ba" Ta jinjina mata kai alamar babu komai ta ce "And yana da kyau ki kwanta ki huta, naga bacci da ciwon kai a idanunki sosai" Majeederh ta harɗe hannu a ƙirji tana kallon Latifa Omar kamar me nazartar wani abu kafin ta ɗauke kai tana duba littafin hannunta ta ce “Ok Dr Latifa Omar.”
“You need as much beauty sleep as you can get.” Latifa ta faɗa tana dry ganin yadda Majeederh har yanzu ranta ke a haɗe alamar dai sam bata ji daɗin shawarar data bata ba, kuma ita ma ɗin ta fahimta Majeederh doesn't deserve that, Ta gyara zama ta ce "Amma bakya tunanin farinki ya yi yawa? Shi yasa ake zaton wani abu daga gareki, ni a tunanina ki zauna yau na miki make up a shafa miki baƙi a fuska kiyi duhu wa'allah sai kiga an dace idan muka je wajan kamon Widad" Majeederh ta ajjiye littafin hannunta ta yi shiru alamar tunani speaking calmly ta ce "bleaching?” Latifa ta ce "Wanne irin bleaching ni ƴar nan, kin taɓa ganin farin mutum na bleaching?? Kawai baƙi zan shafa miki a fuska" Majeederh bata sake magana ba, ta shiga ta yi wanka ta fito ɗaure da towel wani irin kallo Latifa ke binta da shi, zata iya cewa tunda suke bata taɓa ganin Majeederh haka, tafi ganin ta gama shiryawa tana saka kaya ko tana zaune, ko aiki, ko kuma dai tana karatu domin ko bacci bata fiye samu taga tana yi ba. Ita da kanta zata iya cewa Majeederh ba Mutum ba ce, in her whole life bata taɓa ganin mace mai kyau da tsarin halitta kamar Malama Majeederh Abdul'aziz Khan ba. "kallon fa?"
"No, na fara missing ne" Bata ce komai ba harta gama zaro abaya zata saka, Latifa ta ce "Yau ɗaya sai kin kafa mana tarihi a ƙasarmu Nigeria da jiharmu Kano" wata atamfa ta ɗakko tun wacce matar Uncle Isma'il ta bata, ɗinkin riga da skirt, atamfar Golden ce mai blue sai ɗaukan idanu take, daman tun tuni Latifa ta kwaso kayan make up. Majeederh bata san meke damunta ba, amma zuciyarta ta amince da buƙatar Latifa Omar, ta zauna akan stool Latifa ta shiga yi mata kwalliyya ita dai idanunta rufe ta tafi wani tunani nada ban, wanda sam bai dace da ma'aunin iliminta ba. harta ɗaura mata head bata buɗe Idanunta ba, Latifa ta ce "Wow, wallahi kin yi kyau kalli kanki fa" slowly kamar mai tsoran ganin kanta ta buɗe Idanunta, tare da kafe kanta da kallo ta cikin madubin, gabaɗaya ta tashi daka baƙa, fuskarta sai azababben maiƙo take na baƙin kwallin da Latifa ta shafe fuskar da shi tas, sai fararen Idanunta wanda aka shafa musu kwalli ga wanin jambaki tun na iyaye da kakanni da aka lafta mata a lips ɗinta, ko ita ɗin ɓaka ce da wahala a nan a samu mai irin baƙin ta, amma har zuciyarta ta ji hankalinta ya kwanta da ganinta a haka fiye da ganinta a fara, sai taga baƙin ya mata kyau ta juya ta kalli Latifa ta ce "To ba zan iya baka Black gabaɗaya ba?" Latifa ta ce "how? Baƙin mutum zai iya bleaching ya dawo fari, fari kuma no way sai haƙuri" Ta yi jim ta ce "What about my hands? Legs, da wuya"
Latifa ta ce "Ki saka Safa, ƙafa da hannu, wuyanki kuma ki rufe da mayafi" haka ta yi ta ɗauki babban mayafi ta rufe jikinta ruf sai baƙar fuska kamar bayan tukunya a waje tana da ƙyalli. Ba kowa a gidan suka rufe jawo gidan tare da ficewa, yammaci ne kusan duk samarin unguwar na nan, suka dinga bin Majeederh da kwallo suna mmkin inda Latifa ta samu mahaukaciya domin duk mutum mai hankali ba zai taɓa irin kwalliyyar da Jiddatul-khairy ta yi ba, ganin kallon na yawa kuma Latifa bata son su fasa zuwa gidan bikin a haka sai ta tsare napep ta masa kwatancen gidan Uncle Isma'il..... Compound na gidan ya zama kamar hall event yadda aka tsara akai komai, ga manyan mutane ƙawayen amarya da sauran family. Bugawar kiɗan ya yi daidai da bugawar zuciyarta, ta sako ƙafa a hankali kanta ƙasa musamman da taga mutane kamar furanni sbd tsabar kyau da iya matching colour na dress, Hajiya Luba ce ta shige Majeederh tana sauri ganin Latifa ya sa ta tsaya ta ce "A'a zuwan yaushe Latifa? Ina babar taki?" Latifa ta ce "Yanzu na zo, wallahi bata jin daɗi ta ce ayi muku Allah ya sanya alheri" Hajiya Luba ta ce "Allah sari, Allah ya bada lafiya Majeederh bata zo ba ko?" Latifa ta ce "A'a, gata nan tare muke" Baki sake Hajiya Luba take bin wacce aka ce Majeederh ce da kallo with shocked ta ce "Malama Majeederh tamu nake magana, wannan ai na ɗauka wata mata ce mai taɓin hankali dake kusa damu" Latifa ta zare idanunta ta ce "Wallahi Malama Majeederh ce Anty, kalli cikin Idanunta zaki yarda" Hajiya Luba ta riƙe haɓa ta ce "Jama'a mun shiga uku, Majeederh lafiyarki ɗaya kuuwa? Kinga kalli kanki" Ta ƙare haɗe rai ta ce "Shawarar wace a cikin ku? Yin kwalliyyar?" Da sauri Latifa ta nuna Majeederh ta ce "Ita ce"
Sosai ran Anti ya ɓaci ta ce "Tsaya a nan ina zuwa" Tana barin wajan sai ga amarya Widad da friends ɗinta suka gaisa da Latifa tana ta mata complain bata zo da wuri ba, gashi Anti Jeederh ita ko zuwa ba ta yi ba. Ta juya ta ce "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un, wacece wannan waye ya ƙara barin wannan mahaukaciyar ta shigo?" Majeederh ta runtse Idanunta ganin yadda ake haɗata da mahaukaciya bata ji ba bata gani ba, kafin Latifa Omar ta yi magana ta sulale da sauri tabar wajan. Tun daga nesa wasu tawagar maza suke dariya ɗaya hadda ɗakko waya yana danna vedio yana cewa "Lallai bikin Widad da Mansur ya yi albarka, hadda su mahaukaciya a wajan?" Ta ƙarawa tafiyarta sauri harta shigewa bayan ƙofa ta shiga gidan Uncle Isma'il tana dafe ƙirjinta. Her heart broke, she hugged her knees even righter. She felt warm tears running down her cheeks, nothing hurts like they words, ta wulaƙanta kanta akan neman mijin aure sai gashi buƙata bata biya ba mazan ma kallon mahaukaciya ce suke bata, a wancan karan ance Aljana yanzu kuma suna kiranta da mahaukaciya. Ba abinda ke bata tsoro ganin hatta Aaliyyah da suke ciki guda bata ganeta ba. Ta ƙara ƙanƙame jikinta waje guda.
Hannunsa duk biyun ya sa ya rufe kunnenshi wanda sautin kiɗan ke neman fasa masa dodon kunnen, a hankali ya juya yana buɗe idanunsa cikin sauri kuma ya sakko daga kan gadon yana jan tsaki, gabaɗaya ƙaddara ce ta kawo shi gidan Uncle Isma'il ya ɗauka a gidan Uncle Bello za su yi Shirman abun nan, gashi daga dawowarsa garin ba a bar kunnenshi ya wuta ba, idanunsa sun ƙanƙance sbd bacci ya buɗe ƙofar ya fito daga shi sai wani 3gauter, tunda ya fito ta tsora masa idanunta da suke ɗauke da jiƙaƙƙun hawaye tana mamakin yaushe ya dawo shi kuma? Harya gama watannin kenan, yana zuwa ya fice ta gefen ƙofar kai tsaye kuma wajan M.c ɗin ya nufa "Hi" M.c ya ce "Hi" Ya kame fuska sosai ya ce "Kwashe kayanka kabar wajan nan yanzu, duk wanda ya yi magana ka ce Alpha Bello khan ya saka ka ok" Yana faɗin hakan ya juya, Ruma ce ta fara magana ta ce "Kai Dj ya haka? Yanzu fa abokan ango za su zo, kawai sai ka shiga kwashe kaya" M.c bai magana ba sai Dj ne ya ce "Wa nine ya ce mu kashe yanzu" Ruma ta ce "Kan uba waye?" Ya ce "To gashi nan dai, amma kamar Soja yanayin jikinsa" M.c ya ce "Sunansa Alpha Bello khan" Da sauri Ruma ta rufe baki tana zare idanu daidai nan Widad ta zo tana complain me ya sa ta ji shiru, Ruma ta faɗa mata Alpha is back, wani irin rushewa da kuka ta yi shikenan ta shiga uku, yanzu dinner ɗin gobe hanata zai yi ta dinga kuka, Anty ta zuwa ta ce "What did i miss?" Sahar ta ce "Captain ya dawo, Alpha" Anty ta ce "Na gode Allah, ya dawo a daidai".... Majeederh na zaune ta ji an saka hannu tare da miƙar da ita tsaye da sauri ta buɗe ido ganinsa tsaye a gabanta ya harɗe hannu a ƙirji yasa ta haɗiye sauran hawayen, ya dinga kallonta frm head to toe ya girgiza kai ya ce "Follow me" Ya juya zuwa bedroom ɗin daya fito, a hankali ta tura ƙofar ta shiga yana zaune hannunsa riƙe da waya yana magana a hankali ya nuna mata toilet "Clean your face, now" Za ta yi magana ya haɗe dole ta shige, ya daɗe zaune kafin ta buɗe ƙofa ta fito a hankali take takawa zata bar bedroom ɗin ta ji ya ce "Come, Jiddatul-khairy" Ta juya tare da zubewa a ƙasa ya ce "Meke faruwa?" Ta girgiza kai, ya ajjiye wayar tare da juyawa gareta bakiɗaya ya saka hannu ya tallafo haɓarta ta yi saurin ja baya zai ƙara ta ɓata ta marairaice fuska cikin shagwaɓa wanda daman ita halittace a jikinta ta ce "Don Allah Yaa Alpha kar ka sake ta ɓani" ta faɗa har zuciyarta domin daya ta ɓata ji tayi kamar an watsa mata wani abu, tsigar jikinta ya miƙe, ya nuna mata ƙofa ya ce "Out" ta fice da sauri.... Bayan gama bikin Widad aka zauna family meeting amma rawar bata sauya zani ba, har su Uncle Isma'il suka zare hannunsu daga kan al'amarin Abbu, har lokacin Alpha bai san meke faruwa ba, shi ne babban ɗan Uncle Bello, daman jininsa bai haɗu da Mami ba shi ya sa bai damu da zuwa gidan Abbu ba, Ranar monday aka gama komai na batun tafiyar Malama Majeederh Abdul'aziz Khan, daman tana yin dashi kuma ita ce ɗaukan ƙarshe aka bata kuɗi ta siyi kayan sawa sabbi da taimakon Latifa, sosai ta yi mamakin yawan Abayas ɗin data tambaya sukai mata shiru kawai, ta siyawa Abbu buhun shinkafa, katan na tafiya dana makaroni, ta siya musu masara ta Tuwo, ta bawa Aaliyah kuɗi ta ce ta riƙe a hannunta kana ta bawa Abbu ya dinga murna yana cewa "To gashi ɗan ƙaramin albashi ya yi rana, ina ga idan ta fara aiki a Misira ai shi Allhamdu lillahi, Majeederh ta wanke masa zuciya" Kanta a ƙasa, a daren ta shiga sallama da ƴan-uwa Innati kuka sosai, Majeederh na zaune a gaban Anty tana mata faɗa suka ji an shigo ɗakin ganin yadda yake huci kamar an maciji yasa Anty jin tsoro ta ɗauka ko wani abun ya faru domin tasa duk wani soja kullum cikin shiri yake ta ce "Alpha lafiya??" Idanunsa jajur bai kalleta ba, ya saka hannu ya damƙi hannun Majeederh tare da janta zuwa ɗaya bedroom ɗin yana shiga ya juya ya sakawa ɗakin sakata tare da harɗe hannu a ƙirji ya shiga takawa zuwa inda take tsaye.....
MIJIN MALAMA
Paid book
08119237616
Na'ima Sulaiman Sarauta
Nimcyluv sarauta
Ba posting weekend, mai buƙata mu haɗu a arewabooks da special grp🤓🙏🏻25
Huce ta ya yi tare da neman waje ya zauna, a hankali kuma ya sake miƙewa cikin ƙasa da murya Alpha ya ce "Why Majeederh?" Majeederh ta yi shiru ya sake juyawa a fusace kamar zai daketa ya ce "Don't let me to repeat myself Jiddatul-khairy" Ya faɗa yana hargitsa sumarsa. Majeederh ta ɗago kanta suka haɗa idanu ta yi saurin yin ƙasa da nata idon, ya san halinta da kafiya da rashin son magana ga shegen zurfin ciki, ya saisaita murya ya ce "Yanzu kina jin tafiya wata uwa duniya ya dace dake a matsayinki na mace? Duk ilimin da kika samu baki gode Allah ba? Idan karatun kike so me makarantunmu suka rasa? Bakya tunanin aure Ke??" Baki ta buɗe za ta yi magana ya daka mata tsawa yana ɗaga mata hannu ya ce "You have nothing to say, Ai na je wajan Abbu ya faɗa mini komai everything, bai san lokacin da kika nemi scholarship ba, sai form kawai ya gani kina kuka kika bashi uzurin tafiya karatu wannan dalilin ya sa kika kuri wancan that stupid Imran, akan karatu? Me kika rasa?" Tunda Alpha ya fara magana Majeederh ta yi ƙasa da kanta amma jin abinda ya furta Abbu ya shaida masa ya sa ta ɗago kanta da sauri ta shiga kallon bakinsa dake motsawa yana mata faɗa da ihunsa na sojoji. Baya ta yi tana riƙe ƙirjinta tare da nufar hanya zata fice