Showing 114001 words to 117000 words out of 125146 words
furucin akan Abraham shi me ya yi masa zafi? Mutumin da yake da zuciya na ci, da taurin kai ka zafin rai, baka tunanin kalamanka su haifar da wani abu? Kai fa uba ne komai ka faɗa akan ƴarka Immediately Mala'iku za su amsa su rubuta, idan Allah ya ƙaddara Abraham mijinta sai kaga ya musulunta kuma ya aure ta" Abbu ya ce "Har abada ba zan taɓa bawa lalataccen yaron can auren yarinyata ba" Uncle Isma'il ya ce "Idan da rabo mai zafi sai kaga ya kashe ka, rashinka a duniya babu abinda zai hana, ka karɓi ƙaddara a yadda tazo domin allon lauhil mahfuz baya rubuta abin da ba daidai ba, komai ta faru da sanin Ubangiji, zanen ƙaddararta kenan"
After 2 yrs. Lokacin Majeederh nada 33yrs a duniya Abraham kuma 18 Abubuwan sun faru, tashin hankali fiye dana baya, Majeederh ta gujewa Abraham ya haukace baya iya ci baya iya sha duk wani abu da ta hana shi baya yi amma ya fita daga hayyacinsa, ganin hakan yasa Abbu barinta tafiya aikin Hajji bayan an kammala Azumin Ramadan. Fitowarta kenan daga bathroom ɗaure da towel duk ta rame tana daga tsaye taga kamar gilmawar shadow da sauri ta ɗauki hijabi ta saka tana juya idanunta ya sauka cikin na Abraham wanda ya sauya mata ya ƙara yin wani girma na ban mamaki kamar ana ƙara shi kyansa na baƙin ɗan America ya sake fitowa a fili. A kallo ɗaya da tayi masa ta fahimci bashi da cikakken nutsuwa walking slowly ya nufeta da sauri ta ce "Karka zo nan" Ya yi mata banza kamar ana jansa haka ya nufeta kafin ya ƙarasa ta ɗauke shi da mari ta ce "Mahaukaci, to addinina ba irin naku bane, ɗabi'ata tasha bambam da taku kada ka sake mafarkin taɓa jikina, ni ba Maminka bace ok fine ni ma ban haifeka ba, ba zan taɓa haifarka ba ka fice mini daga....," Caraf ta ji ya cafke lip's ɗinsa da bakinsa tare da manneta da jikin bango ya shiga....Zare idanu tayi alamar ya haka? Banda bugawa kuma babu abinda zuciyarta take. He was kissing her passionately, the kiss coming from the land of his heart with all love and affection. Takaici ya sanya Majeederh runtse Idanunta wani irin hawaye mai zafi ya shiga gangaro mata ta gefen idanunta, jikinta ya saki ta kasa koda motsa hannunta, tunda ta zo duniya bata taɓa jin wani abu mai kama da wannan ba, ji tayi jikinta ya shiga rawa da ɓari kamar ana kaɗa mata gangi, wani abu ke tsarga mata tun daga kan babban yatsar ƙafarta har tsakiyar kanta. Tsigar jikinta ya shiga tashi yana zubewa ganin yadda jikinta ya ɗauki rawa da ɓari numfashinta na neman ɗaukewa sbd kawai yana kissing ɗinta ya sanya Abraham buɗe idanunsa da sukai jajur yana jin kansa na masifaffen sara masa sbd baƙon lamarin daya ziyarce shi ba tare daya shirya zuwansa ba.
This is the first time in his life that he kissed a woman and the woman he looked upon as his mother. A hankali ya zame bakinsa ganin tayi baya zata faɗi ƙasa ya yi saurin saka hannu ya dawo da ita saman chest ɗinsa hannunsa ɗaya a waist ɗinta, idanunsa ya ware sosai cikin mutuwar jiki ya kasa cewa komai yadda take sauke numfashi haka shi ma yake ganin babu mai ƙauri a cikinsu ya sanya ya ƙara riƙeta sosai a jikinsa yana riƙe kansa da ƙoƙarin ganin ya dawo cikin nutsuwarsa. A hankali ya zame daga inda take yana matsawa ta yi baya zata kifa sbd ta gama tunanin tana jikinsa ta gama sakin jiki bakiɗaya, cikin sauri ta riƙe kanta da kyau tana jan breathing ɗinta da saukewa a hankali, har lokacin jikinta kuma bai gama daidaituwa ba rawa yake still. Idanunta ta buɗe da son nuna masa ko a jikinta ta ce "Ka fita daga cikin bedroom ɗina" Ta faɗa ba tare daya kalli direction ɗinsa ba, shi kuma ya zubawa yatsun ƙafarta idanu yana karantar yanayin da kike ciki, a hargitse ta ƙara cewa "Khalil get out of my room,i Said" gently ya ɗaga kai ya kalleta da rikitattun idanunsa wanda sukai laushi calmly ya ce "Bayan kasancewata Christa mene hujjarki?" Wani irin murmushi ta yi ta ce "Waya faɗa maka sbd kai ba musulmi bane ya sa naƙi amincewa? Da ace ina sonka da na ja ra'ayinka kan musuluncin ai" Ta gyara tsaiwa ta ce
"Ba zan taɓa son ka, ba zan taɓa son yaron cikina ba, ba zan taɓa auren under age irinka ba, kayi mini ƙanƙantar da ba zan iya cewa kai mijina bane, infact i don't love you, wani gwanini da kai a gabana" Tunda ta fara maganar yake kallonta da wani irin yanayi wanda ba zaka iya tantance shi akan fuskarsa ba, ya nufeta da niyyar riƙe hannunta ta yi saurin matsawa ta ce
"Ya zama last time da zaka ƙara gigin riƙe wani sashi na jikina, addina da naka akwai tazara mai yawan gaske" Rai ɓace kamar Mahaukaci! ya ce "Wanne irin addini ne wannan for God sake? Komai ba kyau" ta fizge hannunta, kau! Ta ɗauke shi da mari ta ce "Mahaukaci, addinina ya fi ƙarfin cin mutuncinka sai a yanka wuyan wanda duk zai aibata Musulunci" idanun Abraham sukai jawur ya ce "Shi addinin ya haramta auren macen data girmeka kenan? Shekaruna 18 mene abun yarinta a jikina? Me ya sa ki ka raina ni? Kawai saboda ni yaro ne, saboda kin girmeni da shekaru goma sha biyar?" "Kai yaro ne"
"Zan wadataki da komai JEE, don kin rai ne ni a lokacin dana rasa iyayena bashi ke nuna ba zan iya zaman aure dake ba, ina soyayyar da kika nuna mini ina yaro? Okay fine, i have a solution! Your father doesn't like me kawai muyi auren Choci ko kuma wallahi mu haifi ƴa ƴan banza kuma shegu, ko kuma na wulaƙanta addinin Musuluncin naku" Yana faɗin hakan ya fice daga cikin bedroom ɗin. Zubewa tayi saman gado tana riƙe kanta wanda yake juyawa mata, tama rasa wanne irin tunani za ta yi da matakin da zata ɗauka, Abraham na neman zame mata ƙarfe ƙafa. A hankali ta lumshe idanunta da sauri ta buɗe jin tsigar jikinta na tashi har yanzu while bakinta na mata wani iri, Abraham ya bar mata wani irin moment da memory mai wahalar mantawa a zuciya, ya yi abinda babu wani namiji daya isa ya yi shi ya kafa tarihi a rayuwar Majeederh. Shuɗaɗɗan abinda ke damunta shekara da shekaru wanda tayi maganinsa ya dawo mata sabo fil. Gabaɗaya ta hargitse tare da yin luf saman gado ta rungume pillow addu'a take Allah ya kawo mata ko tsoho ne wanda ya girmi Abbu ta aura ku ta samu sauƙin maganganun jama'a ta kaucewa rashin kunyar ɗan cikin nata.. Uncle Isma'il ne zaune a parlourn baƙinsa ya dubi Pasto David kana ganinsa kaka cikakken Christa gaba da baya. Uncle Isma'il ya yi murmushi ya ce "Sir Please ga ruwa nan" Grandpa ya yi murmushi ya ce "My pleasure sir"
Uncle Isma'il ya gyara zama cikin nutsuwa da harshen turanci ya ce "Kafin na ce komai zan su nasan waye kai, kuma na yi maka some of questions akan Abraham" Grandpa ya jinjina kai yana yaba nutsuwar Uncle Isma'il kafin ya ce "David sunana, shugaban church, business man with experience, sai wani secret aikina, kuma Abraham's Grandfather" Uncle Isma'il ya watsa hannu ya ce "That's good and i like it, amma Sir daman can Abraham Christa ne?" Kallo Uncle Isma'il kawai Grandpa ke yi kafin ya ce "Maybe, Abraham gaba da baya Christa ne kamar yadda ka ganni ɗin nan, muna ganin kima da matar tabar addininmu kamar yadda kuke ganin naku, muna ƙarfafa al'adunmu mun san muhimmancin hakan sosai, sai dai Abraham rayuwarsa ta samu bambanci da tamu kasancewar a nan Naija aka haife shi tun yana da 3yrs baya ƙaunar zama cikin gidan iyayensa, akwai wasu Neighbor ɗin su da suke Musulmi kullum yana gidan, yana da masifar wayo na ci da taurin kai, idan su kai alwala haka shi ma zai yi, ko sallah sukai haka shi ma zai. Bayan mahaifinsa ya fahimci hakan ya fara dukansa san bai gwadawa Abraham tausayi ba, ya tashi cikin mugunta yau zai dake shi ya fasa masa jiki haka zai wayi gari babu shi ya koma gidan Musulman nan, daga bisa ni ya kulle shi a wani ɗakin duhu babu abinci ya gana masa azaba sbd kawai ya daina zuwan gidan mutanen, kai har farcen ƙafa dana hannu Denial ya cire Abraham yana ɗan ƙaraminsa, shi yasa zuciyarsa ta ƙeƙa shi bashi da tsoro ko kaɗan, watarana kawai aka wayi gari babu shi neman duniya, shi kuma Denial ya yi tafiyarsa tunda daman ba a ƙasar yake ba, bai damu da ɗan ba ya ce watarana dole zai dawo gare shi idan har yana raye shi kuma daya haifi musulmi gwara ya kashe ɗan da hannunsa ya wuta" Wani irin tashin hankali ya bayyana akan fuskar Uncle Isma'il, da wani irin Expression yake bin Grandpa da kallo kafin ya ce "To mahaifiyarsa fa?" Ya ce "Ta mutu tun yana ƙarami ai, amma bai san da hakan bai kuma taɓa tambayar wani abu daya danganci mahaifiyarsa, Abraham bai taɓa zama da mace na minti ɗaya da sunan kulawa da bashi tarbiyya ba, mace ɗaya ta fara ƙoƙarin saita shi da ganin ya dawo hanya ita ce wacce yake kira da Mami, ur daughter Malamar nan" Uncle Isma'il ya ce "To ya akai ya dawo gare ku bayan ya ɓata? Tunda mun zauna da shi shekaru 2" Grandpa ya ƙara yin murmushi ya ce "His father, shi zuba private Investigators everywhere domin hankalinsa ya dawo kan shi, cikin sa a kuma aka same shi daga nan ya ɗauke shi zuwa wata ƙasar" Mamaki fal ya cika Uncle Isma'il sbd yasan cikin dare aka nemi Abraham aka rasa. "Waye mahaifin nasa? Yanzu yana ina? Me yasa kuma basa tare" Grandpa ya ce "You can ask him by yourself" Uncle Isma'il ya jinjina kansa kana ya yi murmushi ya ce "Yanzu ga abinda jikan naka yake ƙoƙarin rikituwa, kana ganin zai iya musulunta" Grandpa ya jima yana kallon Uncle Isma'il kafin ya ce "Har abada, ku gaggauta yiwa yarinyarku aure, idan kuma zaku bashi aurenta haka to, kai ko zaku bashi mahaifinsa ba zai taɓa yarda y auri musulma ba kuma ba wacce ta girme masa ai tayi tsofa da yawa gsky" Ran Uncle Isma'il ya fara ɓaci sosai kafin ya ce "Kai kake ganin tsofanta, bamu zamu gaggauta mata aure ba ku ne zaku jawa naku ɗan kunne akan ya fita harkar yarinyarmu ko kuma duk abinda ya same shi shikenan, ko hukuma ta rabamu da shi" Miƙewa Grandpa ya yi da sanda a hannu irin tsofaffin attajiran nan masu arziƙin gaske ba muna kuɗi ba ya ce "Hukuma? Waya faɗa maka Abraham na tsoran hukuma bayan shi ne hukumar kansa? Abraham babu wanda ya taɓa zama ya ce masa wannan abinda kake ba daidai bane ga wanda ya kamata ka yi, Abraham ko yini guda ya yi bai kai abinci bakinsa ba babu wanda zai ce masa ɗauki abinci kaci, irin wannan wanda bai san bambancin fari da baƙi be kake tunanin zai fahimci wani ya daina kula muku ƴa?" Grandpa ya girgiza kai kawai kafin ya ce "Sbd karamcinta ya sa nace kuyi nesa da ita daga idanunsa, Abraham ne yaro ne mai naci da taurin kai, tun yana ƙarami idan yana son abu kansa yake bugawa a ƙasa ba zau taɓa bari ba sai an bashi, Have a good day!" Yana faɗin haka ya fice daga cikin Parlourn ya nufi compound da sauri driver ya buɗe masa bayan mota ya shiga.
Anti dake shirya Lunch ta kalli Uncle Isma'il ta ce
"Ya akai kai jarumin namiji?" Ya nemi waje ya zauna tare da rufe idanu ya yi shiru. Ganin yanayinsa ya sa ta nemi ruwa mai sanyi a cup ta miƙa masa tana zama kusa da shi, bai musa ba ya amshi ruwa ya sha sosai yana sauke numfashi. Ganin bai ce komai ba itama Anti ta yi shiru da bakinta, har ya je sallar Asr ya dawo ya zauna cikin iyalansa idanunsa akan Jawaad ya kasa cewa komai, tunani fal ya sa yana sanya Jawaad matsayin Abraham taya zan iya sanwaltar da rayuwar ɗan shi ya bawa duniya ajjiyar shi? Ba dole ya kan gare ba. "Abba" Jawaad ya kira sunan Uncle Isma'il ganin kallon da yake masa kafin ya ce "Abba ruwa zan baka?" Ya girgiza kai kawai ya ce "Allah ya yi maka albarka Jawaad" Ya ce "Amin Abba" Sona ta ce
"Jawaad kaɗai Abba?" Ya haɗe rai ya ce "Sona dake da Jawaad waye babba?" A hankali ta ce "Shi ne" Ya ce "To ya zama last day da zan ji bakin ki ya ce Jawaad ki bi bakin Majaufiarki na Fulanin Gombe ki ce Hamma, ko ki ce Brother da turanci ko Yaya da Hausa" A hankali ta ce "Am sorry Abba" Ya ce "Bashi haƙuri" Ta kalli Jawaad ta ce "Am sorry Yaya" Jawaad ya yi murmushi ya ce "No bad my dear" Bayan sun kammala cin abinci Uncle Isma'il ya zayyane wa Anti yadda sukai da Grandpa. Anti ta yi shiru zuciyarta fal tausayin rayuwar Abraham ta ce "No wonder sweetheart, ka duba Abraham sosai wallahi kallo ɗaya nayi masa nasan babu kulawar uwa a tare da shi ita kuma ya yi missing, duk lalacewar yaro idan har a gaban mahaifiyarsa yake wlh zai samu nutsuwa da sauƙi wani abu, shi yasa a kullum muke addu'a Ubangiji ya bamu tsayin rai mai amfani mu rayu tare da yaranmu" Ta girgiza kai ta ce "I felt sorry for the boy, his life is full of challenges, wallahi ya bani tausayi yanzu da babarsa na duniya taya zai dinga garari? Ba sai dai su shiga duniyar tare ba?" Uncle Isma'il ya ce "Ƙaddara" Wani irin kuka Anti ta rushe da shi ta ce "Wallahi tallahi na ji gwara ɗana ya mutu ya barni da ace na mutum na barshi ban san wacce kalar rayuwa zai yi ba, ban san waye zai kula da shi ba, Innalillahi wa'inna ilahir raji'un Ubangiji kayi mana tsayin rai mu rayuwa da yaranmu cikin kulawa da amincinka ya Rahamanu ya Rahimu" Uncle Isma'il ya ce "Ke fa daman haka kike babu dama ki ji abu sai kuka haba" Ta girgiza kai kawai wani kukan na kwace mata ta ce "Yallaɓai baza ka gane ba, don Allah ka jawo Abraham jikinka plx" Ya yi shiru for good 3 minutes kafin ya ce "I'll think about that dear" Abraham na kwance saman 3 sitter a haɗaɗɗan parlourn shi kwana uku kenan cif babu inda yaje, duk ya fita daga cikin hayyacinsa. Taj ya kalle shi ya ce "Wani ya yi mini maganar zanen gida da kukai da shi, gashi har time ya shige" Abraham ya yi shiru idanunsa buɗe yana kallon sama alama ya lula duniyar tunani. Taj ya ce "Ina ta magana?" Sai a lokacin ya ce "Ka tura masa kuɗin shi ba zan ba" Taj ya ce "Nawa ne kuɗin?" Shortly ya ce "3M" Joshua ya girgiza kai ya ce "A'a ba za a mayar ba, a bashi haƙuri zuwa wani week ɗin kafin nan sai ka yi" Taj ya ce "Ya ce a mayar kuma daman shi zai aiki tunda ba zai ba bashi kenan ba?" John ya ce "Taj kada a mayar plx mu yi tunanin wani abun" Duk sukai shiru. John ya ce "Kunga news guy's?" Taj ya ce "What news? What's happening in the world?" A hankali ya ce "Wai President ɗin Germany aka kaiwa hari za a kashe shi" Da wani irin Mamaki Taj ya ce "Kashe kuma? President ɗin guda? Kuma a hospital?" Join ya ce "Daman wai jinya yake fa bashi da cikakkiyar lafiya, to a hospital ɗin akai attempting kashe shi amma ya kuɓuta, irin haka dole akwai haɗin bakin wani na kusa shi" Taj ya saci kallon Abraham da idanunsa ke lumshe yana jin duk abubuwan da suke cewa ya ce "Ayya! Shi bashi da ɗa ne wai?" A hankali Abraham ya miƙe ba tare daya kalli kowa ba ya nufi cikin part ɗinsa ya kwanta saman bed, haka kawai ya ji bashi da nutsuwa gabansa sai faɗuwa yake, ya runtse idanunsa sosai a hankali ya ce "Daddy"
Majeederh ta kalli Latifa a sanyaye ta ce "Yanzu Latifa ya zan yi? Wanne irin baƙin jini ne irin wannan? Kamar wata mujiya" Latifa ta girgiza kai ta ce "Ki daina cewa haka komai lokaci ne, ƙaddara ce kuma tana da nata lokacin" Ta goge hawayenta tare da yin shiru a hankali ta ce "Surutun jama'a ya fara damuna ana son mini sharri" Cike da tausayawa Latifa ta ce "Duk yadda kake kare kanka ba zaka taɓa hana jama'a faɗar abinda su kai niyya ba, wani ma bai san waye kai ba labari kawai zai ji yaje ya ɗorar ba zaki taɓa yiwa kowa daidai ba rayuwa kawai ki tsarkake zuciyarki" Latifa ta ce "To yanzu da Uncle ya kira Abraham gidan nan parlourn Abbu me zai masa?" Ta girgiza ta kasa cewa komai. Uncle Isma'il ya kalli Abraham ya ce "Khalil me ya kawo ka bedroom ɗin Mamin take few days ago?" A hankali ya ce "Matata dai not Mami" Uncle Isma'il ya jinjina kai ya ce "Ohk me ya kawo ka?" Ba tare da damuwar komai ba ya ce "Just to see her, sai kissing ɗinta da na yi" Uncle Isma'il ya saki baki dan ya san da gaske anyi hakan tunda har ya faɗa don baya ƙarya. Abbu ya runtse idanunsa sosai yana jin kamar zuciyarsa ta fita. Uncle Isma'il ya ce "kiss fa kace Ibrahim?" Abraham ya ɗan kalli Uncle I sai kuma ya kwaɓe fuska ya ce "A small kiss, kaɗan na yi fa" Uncle Isma'il ya ce "Tab ɗin" Uncle Bello shi abin dry ya bashi yana kallon Abraham cike da birgewa ganin baya ƙarya ko kaɗan kuma