Showing 69001 words to 72000 words out of 125146 words
haɗata da Allah magana ta ƙare, Majeederh ta ja gajeren tsaki kamar wacce akai forcing nata wajan magana ta ce "Kitchen"
A tare suka nufi Kitchen ɗin, Latifa na nuna mata ta dawo tare da zama kusa da Aliyu ya ɗan ja gefe da sauri ta ce "Me kuma?" Ya dubeta yana girgiza kai ya ce "Baki jin kunya?" Ta juya masa idanu alamar "Kunya? Akan me kuma"
Ya taɓe baki yana faɗin "Rayuwarki abar tausayi ce, ban yi zatonki haka ba gaskiya" Latifa ta ware Idanu akan Aliyu ta ce "Kayi mini bayani, bana fahimtar wannan zancen" Ya ce
“ina nufin ƙazantarki"
Latifa ta ce "Sbd ka ganta?" Cikin rashin fahimta ya ce "Wa kenan?" Ta yi masa shiru ya ce "Yanzu ke baki ji kunyar Hawwa'u ba? Riga daban, zani daban, abin kanki daban? Ƙamshin parlourn daban da warin da yake fitarwa daban? What exlty wrong with you Latifa? Haka zaki haifi yara kina wannan ƙazantar su tashi da abinda suke ganin kina yi?" Bakinta cike da yawo ta buɗe zatai magana ya yi saurin ɗauke kansa zuciyarsa na tashi.
"Oh! Daman fa haka ku maza kuke bazan kasan dalili banda cikin dake jikina har zaka ce haka?" Aliyu ya ɓata fuska ya ce "Sbd Allah duk matan da mazan su ke musu ciki haka suke wannan azababbiyar ƙazantar? Parlour warin yawo, part ɗinki haka nikam na shiga uku" Zata buɗe baki sai ga wayo zarara Aliyu ya yi saurin tashi ta juya kanta bayan kujera ta zubar da yawo ta ce
"Nikam ina yin iya bakin ƙoƙarina, baka da godiyar Ubangiji" Aliyu ya kasa cewa komai dan takaici can ya ce "Tun satin aurenmu ai haka kike, matsalolinki nada yawa idan zasu zan yi a zuciyata tsaf zata buga tunda na kawo abokaina suka ci abinci suka dinga amai na sare miki, ciki kuma wannan shi ne na biyu wancan ya zube wannan kuma sai ki kula zan kawo ƴar aiki kawai" Ta yi saurin miƙewa ta ce "Kan uban nan a wanne gidan zaka kawo ƴar aiki? Ai wallahi baka isa ba, tsohuwo ko yarinya bana mara ba da su, haka kurum a aure mini miji, matan yanzu da basu da mutumci kamar mayu haka suke akan mazajen wasu musamman yanzu da za a saka ƴan candy marriage, ina son ka ina Mahaukacin kishinka kai ka sani kuma......," Shiru tayi ganin Majeederh na shigowa cikin parlourn hannunta riƙe da wani kyakkyawan warmer wanda Latifa bata taɓa amfani da shi ba, Kullum a warmer ɗaya take zuba masa abinci idan tayi ma kenan. Latifa ta yi murmushi ta ce "Thank you Bestie sannu da aiki" Majeederh ta ɗora warmer ɗin akan table tana nuna tamkar bata jin Conversation ɗin su ba, Aliyu ya dinga satar Kallonta Majeederh na ƙoƙarin miƙewa Latifa ta ce "Ina zuwa"
Ganin ta nufi part ɗinta yasa Aliyu shafa cikinsa ya ce "Zuba mini please" Ta cikin liƙab ta harare shi sarai ya gani sai kawai ya shafa kansa yana jan plate tare da zubawa a ciki, sosai Superghgett take tashin ƙamshi gashi ta sha sadin, kasancewar kaɗan ta dafa kuma gas ne ga komai a zube ya sa cikin ƙaramin lokaci ta gama dafawa. Idanunsa ya rufe lokacin da daɗin abincin ya ratsa cikin kunnuwansa Gabaɗaya jijiyoyin da suke amsar saƙo zuwa ƙwaƙwalwar sun ɗauka tuni sun kaiwa tasa ziraya, cin abincin kawai yake hannu baka hannu kwarya har ya mance Majeederh ce gabansa, ya daɗe bai ci abincin mai daɗinsa ba. Ya goge bakinsa da tissue a hankali yana kallonta ya ce.
"Kin ceci rai" Ba tayi magana ba, ya saita murya ya ce "You're the best cooker Hawwa'u thank you" Miƙewa tayi bata jira zuwan Latifa ba tayi gaba abinta tare da ficewa daga parlour bakiɗaya... Shigowarta compound ɗin ya yi daidai da fitowar Abbu daga cikin mota, har zai tafi sai kuma ya tsaya yana Kallonta har ta ƙarasu, Majeederh na zuwa ta zube a ƙasa ta ce "Barka da dawowa Abbu, ina yini?" Ya dinga Kallonta kafin ya ce "Lafiya, daga ina?"
"Gidan Latifa..." Ta bashi amsa kanta a ƙasa tana wasa da yatsun hannunta ya numfasa ya ce "Ki sameni a part ɗina" Yana faɗin hakan ya juya cikin gidansa nasa wanda ya zama sai mai hannu da shuni ne kawai iya gina gida kamarsa, iya compound na gidan abin kallo ne balle kuma ciki wanda duk sanadin ƴar cikinsa Majeederh ya same su ta tara masa kuɗi na ban mamaki. Lokacin data shiga main parlour tuni Abbu ya shige ɓangarensa Mami ce kawai zaune tana kallon shirin Mata a yau, ta shiga da sallama tana cire liƙab ɗin fuskarta tare da zama, Mami ta kalleta ta ce.
"Sai yanzu?" Ta ce "Eh" Ta ƙara cewa "Zaman me ki kai a gidan ma'aurata?" Kamar zatai shiru sai ta ce "Latifa bata jin daɗi shi ne naiwa mijinta girki" Da mamaki sosai Mami ke kallon Majeederh ta rasa ma me zata ce kafin ta ce
"Ba kiji nauyin cewa Aliyu ki kai abinci ba? Ba kiji nauyin furta kalmar nan ba? Mijin Aminiyyarki ki kai girki? Ban taɓa jin haka ba ko da wasa na Asabe" Mami ta ƙara tafa hannu ta ce "Sai kika shige madafa kika bar miji da mata a parlour suna jiran abinci" Majeederh kanta a ƙasa ita sam ba taga aibun hakan ba, tunda taimako ta yi Mami ta ce "To liƙab kika cire?" Ta girgiza kai ta ce "A'a" Sai a lokacin Mami ta sauke ɓoyayyiyar ajjiyar zuciya kafin ta ce "Na gode Allah" Miƙewa ta yi ta nufi part ɗinta, bayan ta shiga ta nufi toilet tare da yin wanka ta ɗaura alwala wata jallabiya ruwan toka ta saka mai yafin farin duwarwatsu bayan ta idar da sallar Asr tayi azkar idanunta rufe ta shiga tilawar Alkur'ani ta yi hakan ne sbd rashin abin yi kuma bata son yin baccin Asr, tana nan zaune Mami ta murɗa handle ɗin bedroom ɗin Majeederh ta shigo daga tsaye ta ce
"Zaki mana dinner" A sanyaye Majeederh ta ce "Mami kai na ciwo yake, tunda na dawo ban yi bacci ba, can ma ba bacci nake ba" Mami ta saki ƙofar ta shigo tare da zama saman gado ta kalli Majeederh ta ce
"Kenan Raihana ko Ruma zan kira daga gidan mazajen su suyi mana ko?"
"Sun tafi ne?" Cewar Majeederh, Mami ta ce "Da ke zasu tsaya su taya zaman gida bayan su Allah yaye musu wannan ƙaddarar? Majeederh shekarunki nawa yanzu ne?" Kanta a ƙasa zuciyarta na bugawa ta ce "28"
Mami ta ce "To da kyau tunda har kina lissafe, Sahar a gabanki aka haifeta yanzu yaranta huɗu cif, Widad a gabanki aka haifeta haihuwa ta uku ta biyu za tayi a hakan ma don Allah bai bata da wuri bane, Raihana, Ruma duk akan idanunki aka haife su ita Ruma cikin ne baya zama, ita Raihana Allah ne bai bata ba, duk wannan ba zai sanya kiwa kanki karatun tanatsu ba Hawwa'u? Me kike nema a duniya, kina da kyau, kina da iliminki, kina da kuɗi mene ya yi saura?"
Majeederh ta kalli Mami jin ta ce tana da kuɗi, bayan ko ƙwandala bata da shi da sunan mallakinta, komai data mallaka a Misira ta sallamawa Abbu. Mami ta gyara zama ta ce
"To na fara gajiya nikam, gashi nan jama'ar gari sun fara zagina da ƙana nan gulmace-gulmace akan wai an tura ki neman kuɗi ba wani karatu da kike, wasu ma cewa suke neman maza kike gashi nan baki aure ba, kuma bama ta kuraki akan aure kina neman tsofe mana a gida" Tunda ta fara magana Majeederh ta kafe Mami da manyan idanunta wanda gefe ɗaya ya yi ja sbd ciwo Kallon nata kawai take amma tunaninta yana wani waje guda, kalmar neman maza ta girgiza Majeederh ta kasa fahimtar wake neman mazan? "Kina jina?"
"Wake neman maza?" Majeederh ta faɗa muryarta na rawa Mami ta bata amsa da "Ke mana, kuma dai bani da shaida akan ki ɗana ne ka haifa baka haifi halinsa ba, tunda gashi sam baki damu da rashin auren naki ba" Kalma “Zina” babbar kalma ce wacce a duniya ta tsaneta balle mai aikata yinta amma ita ake ƙoƙarin laƙabawa wannan muguwar kalmar? Bayan data aikata zini gwara ta kashe kanta kawai ta huta, da zina zatai ko yawan bin maza ai tun kafin tabar ƙasar zata fara sbd abinda ke damunta, sai yanzu ne da Allah ya ye mata dukkan wani abu da take ji zata fara zina? Bayan shi isn't interested at all! Ɗigon sha'awa yanzu babu a tare da ita, ta wannan ɓangaren har mancewa take ita ɗiya macace?... Kai ta ɗago ta ce "Allah ne shaidata"
"To Allah ya rufa asiri, kin tabbatar kafin shekarar nan ta ƙare kin kawo mijin aure, idan ba haka ba wallahi sai ranki ya ɓaci kinfiso muna jerawa a gida muna haɗa kafaɗa? Kuma daga yau duk wani aiki na gidan nan ke zaki nama sallami ƴar aiki, Aaliyah makaranta take zuwa" Tana faɗin hakan ta miƙe tare da ficewa daga ɗakin tana zuba kumfar baki... Majeederh ta bi bayanta da kallo, to ita yanzu za ta yi da ranta? Tallan kanta za tayi kenan? Ko kuma dai photo nanta zata raba masallatai? Wata zuriyar ta ce mata.
"Kin manta kenan ko Majeederh? Bayan mazan gudunki suke babu wani wanda zai ce yana son ki balle aure" Zuciyarta tayi mata nauyi da ƙyar ta samu ta ja numfashi kafin ta miƙe jiki a sanyaye ta nufi part ɗin Abbu. Yana zaune saman ladduma gabansa cike da kayan marmari hannunsa riƙe da jarida ya dubawa ta yi sallama, bai amsa ba sai gyaran murya da ya yi mata alamar ta shiga. Ta zauna a gefe cike da tsoransa ta ce "Ina yini Abbu? Na sameka lafiya?" Ya ce "Lafiya lou" Ya yi shiru ta ɗan ɗago kanta ta saci kallon Mahaifin nata, ba zaka ce shi ne ya haifeta ba, sbd ya samu duniya da abinda yake so wato kuɗi jikinsa ya murje alamun kwanciyar hankali sun bayyana a tare da shi. Ta sauke ajjiyar zuciya a hankali ta furta "Allhamdulillah na cika burin Abbu" Ta ɗauka zai tambayeta kalar rayuwar da tayi a Egypt ba tare da iyaye ko wani nata ba, ta ɗaukan zai sanya mata albarka bisa namijin ƙoƙarin da tayi na zama Gwarzuwa a musabaƙar Alkur'ani ta ƙasa, ta ɗauka zai albarkaci rayuwarta bisa burinsa data cika sai ta ji ya ce "Na haifi ƴar da bata san girma da ƙimata ba, na haifi ƴar da take son tuna mini asiri a cikin al'umma, na haifi ƴar da take son saka mini ciwon zuciya...,"
A gigice Majeederh ta dakatar da Abbu da faɗin "Me na yi Abbu, me aka ce nayi idan zuwa gidan Latifa ya ɓata ranka don Allah ka yafe mini" Jikinta duka rawa da ɓari yake sbd tsoran ɓacin ran mahaifin nata. Abbu ya dubeta sosai kana ya jawo laptop ɗinsa ya shiga Gmail ya nuna mata wani saƙo ya ce "Hukumar makarantarku ta ƙasar Egypt take ƙorafin sun nemi alfarmar ki zauna musu domin zama malama amma ki kaƙi bayan sun yaba miki ba za su samu wata ɗaliba data kai ki ba" Majeederh ta ce
"Ka yi haƙuri Abbu" Ya ɗaga mata hannu cikin tsawa ya ce "Haƙuri? Kin manta al'ƙawarinmu dake?" Ta ce
"Ban manta ba" Cikin zafin rai ya ce "Ok isa ce ban ba? Anya zaki albarka kowa Majeederh? Kina son wanyewa lafiya?" A ruɗe ta ce
"Ka yi haƙuri Abbu, rayuwata a wata ƙasar da bani da kowa akwai hatsari ba zan iya zama ba, na yi ƙoƙarin cika al'ƙawarin amma na kasa ka yafe mini, bana da kowa a Misira bana da mai mini faɗa, bana da wanda zai kalla a matsayin wani nawa, bana da wanda zan zauna nayi fira da shi" Abbu ya dinga kallon Majeederh cikin tarin tsana da ƙonar rai ya ce
"Shi ɗan uwanki Alpha ba mutum bane? Da yake tafiya cikin jeji sai ya yi shekara bamu sa shi a idanun ba, ba kuma mu san halin da yake ciki ba, gwara ke mun san inda kike...,"
Ta ce "Abbu taya zaka haɗa ɗiyarka mace da namiji? Namijin daya kusa tun karar shekaru arba'in? Kuma zai iya kula da kansa?" Ta ƙare maganar tana sakin kuka sosai. Abbu ya ce "Ok ke yarinyar goye ce kenan ba zaki iya kula da kanki ba? Kinga tashi maza ki bar mini parlour idan na ci-gaba da ganinki zuciyata bugawa zatai mu zauna mu cinye ƴan kuɗaɗen da suka rage kinga ma dawo gidan jiya talakawa" Zatai magana ya ƙara daka mata tsawa kamar ba Mahaifinta da take mutuwar so kamar rai ba ta miƙe jiki na ƙyarma da ɓari ko kallon gabanta ba tayi ta nufi waje ga idanunta da suke mata wani masifaffan ƙaiƙayi nan da nan sukai jajir ta shiga susawa tana yin main parlour kuka na cin ƙarfinta, karo tayi da mutum tsaye wanda shigowarsa kenan cikin garin Kano tana ƙoƙarin yin compound a tunaninta main parlour ne sbd idanunta rufe yake caraf ya sa hannu ya riƙo nata hannun....
*BOOK 1 PAGE 31*
MIJIN MALAMA
LITTAFIN KUƊI NE WANDA YAKE SO YA YI MAGANA 08119237616
Ina godiya bisa ta'aziyyar da akai mini ta babban rashin da na yi na wan mahaifina Alhaji Musa Zakari sheka ( Dagacin sheka) Na gode sosai Allah yabar zumunci marubuta da yawa wasu ma ban san su ba, sun nuna mini kara ƙwarai makaranta ina alfahari daku kune silar kai ni inda nake kune kuke goya mini baya ta hanyar siyan littafaina, ina fatan ba zaku gajiya ba🙏🏿🙏🏿32
Janta ya yi har tsakiyar main parlour yana zuwa ya saki hannunta yana binta da wani irin kallo kafin ya ce "Baki da hankali?" Ta buɗe idanu wanda sukai jajir ta ce "Me na yi?" Da idanu ya dubi shigar dake jikinta da kuma kallon fuskarta dake buɗe, itama tayi saurin kallon kanta tana ɗan marairaice fuska zuciyarta duk babu daɗi ta kasa cewa komai sbd yadda ƙirjinta ke ɗagawa ga zafin da idanunta suke mata duk ta sushe su. Ya gyara tsaiwa yana harɗe hannu a ƙirji shi ma nasa idanun sun yi ja sbd abubuwan da suke masa yawo a zuciya can ƙasa ya ce "Kuma da gaske fita zaki haka? Tsirara?"
“.... Tsirara!?” Ta faɗa da sauri cike da tsoro, Alpha ya haɗe fuska ya ce "Mene marabar dambe da faɗa?" Majeederh ta yi shiru domin ita sam tunaninta baya nan wajan, zuciyarta ta Kaɗaita da maganganun Abbu, lura da yanayinta ya sa Alpha bai ƙara magana ba ya bi ta gefenta ya shige ya zauna saman kujera yana harɗe ƙafafuwan. Majeederh ta shige part ɗinta not too long ta dawo sanye da rolling na vail a kanta, ta nemi waje saman kujera ta zauna, shiru ya biyo baya can ta ce "Ina yini?"
"Lafiya" Ya bata amsa a taƙaice. Majeederh ta yi ƙasa da kanta cikin sanyin murya ta ce "Ance an maka ƙarin girma congratulations" Alpha ya ce "Uhm" Yana ɗan kaɗa ƙafa kafin babu wasa idanunsa ya kira sunanta ya ce "Majeederh!" Ta yi shiru.
"Zabiya?" Ta kwaɓe fuska tunda bata son sunan ya ɗan shafa kai daman He just wants to tease her. Ta miƙe zata bar parlourn ya ce
"No, please" Ta zauna kamar zatai kuka ta ce "Tun ina ƙarama kake ce mini Zabiya Yaya, ni ban so idan kai ma da Aljanar nake maka kama to"
"Stop it Majeederh!" Ya furta a tsawa ce, domin ji ya yi kamar ta caka masa nashi a ƙahon zuciya, ya girgiza kai ya ce "Sorry"
Ta yi shiru speaking calmly ya ce "Sannu da dawowa ƙasa Nigeria, yanzu sai me?" Kanta a ƙasa tana wasa da yatsun hannunta ta ce "Sai abin da Abbu ya ce" Alpha ya watsa hannu ya ce "Kina sane da problem ɗinki, komai zaki ki fara tuna aure first" Kunya ta kama Majeederh sai yanzu take dana sanin sanar masa da matsalarta, kuma yanzu da baya ai ba ɗaya bane tuni Ubangiji ya ye mata "Kina ji?" Ta ce "Aiki zan nema" Da wani irin sauri ya ce "Aiki?" Ta ɗaga kai ya ce "Shi ma Abbu ne?" Tayi shiru cike da tausayawa ya ce "Am sorry, zan masa magana ya fara bari kiyi aure" Wani irin abu ne mai ɗaci ya tsayawa Majeederh a maƙoshi ta runtse Idanunta tuni ta ji rauninta na son bayyana muryarta na rawa amma ta dake domin tayi al'ƙawarin ko hawan jini zai sameta, ko zuciyarta ce zata buga ta mutu nan take ta daina yin kuka ta sauke ajjiyar zuciya ta ce "Idan ya amince nayi auren wa zai aureni?" Alpha ya zura mata manyan idanunsa ya ce "Kamarya? kina nufin tsayin shekarun da ki kai a Egypt baki saurayi ba?" A hankali Majeederh ta girgiza kai ta ce "Even friend ban ba, shekaruna ashirin da takwas 28 ban taɓa yin saurayi ba idan ka ɗauke Imran shi ma ya guje ni ba tare da sanin dalili ba, baƙin jini ne dani Yaya na zama mujiya a idanun mazan duniya, hatta soyayyar ƙuruciya ban san ya take ba, ban san daɗin soyayya da wahalar cikinta ba, ko saurayin da zai zo ya yaudareni ban taɓa yi ba, balle wanda zai ji muradin aurena a zuciyarsa....,"
Ta yi shiru sbd numfashinta dake fisga kaɗan kaɗan kafin ta ce "Duk son da maza suke wa farar mace, duguwa mai kyan fuska nawa ya tashi a banza, mummunar mace wada ta fini farin jini, to idan ban yi aiki ba me zan Yaya? Shi ma Abbu fahimtar hakan ce ta sanya ya zaɓa mini wannan rayuwar kuma ina farin ciki da ita" Duk rashin imanin Alpha kasancewar shi Soja, wanda yaga masifu da yawa ya kashe rayuka da yawa amma a yanzu a gaban Majeederh sai dai zuciyarsa ta karye ya miƙe tsaye ya shiga kaiwa da komowa yana bugawa hannayensa waje guda kafin cikin sauri ya tsaya a gaban Majeederh ya ce "Majee ki minin wani al'ƙawari, do me a favor please" Ta kasa kallonsa ya kai hannu zai riƙe nata tayi saurin janye nata tana ɗan yi murmushi ta ce