Showing 24001 words to 27000 words out of 50778 words

Chapter 9 - KISWA Book Complete Document by Chuchujay.txt

29 Nov 2024

2565

bana tunanin komai ba muddin wani abu akace ya sameki"Serious face yasa yace "yauwa Girl we need to talk idan zaki iya idan kuma You cant talk much just tell me na bari other time.


Kallan sa take cikin ido tana mai san gano maganar da yake san mata amma ta kasa gano komai,murmushinta ta Faɗaɗa tace "na warke fa na faɗa maka Ina sauraran ka.


"lasar leben sa na ƙasa yayi Kafun yace "ban san ta ina zan fara ba and i wish baza kiyi fushi dani ba,im Just curious ina san nasan ya yanayin zaman ki yake da Mother cos im not understanding it ,bana san na boye miki saboda tsakanina dake bana fatan boye boye ya shiga tsakanina dake ,ummina ta kira Mother akan maganar mu so Mother take faɗa mata cewa ke ɗin ba da Aure aka sameki ba sannan mama zaman kanta take which im sure ba haka bane ,na kasa haɗa maganar guri ɗaya sannan im confuse akan mai yasa Mother zatayi hakan ,hope banyi mata ko Kin mata wani laifi ba cos im sure akwai wani abun a ƙasa."


Cikin wani irin siga da yanayi Kiswa ta tsinci maganar wadda tayi mutuƙar bata mamaki ,yar dariya Tayi tace "for real ?Mother tace ni bada Aure aka haifeni ba sannan idan na fahimta tana nufin mama ma karuwa ce,wata Dariyar ta kuma sakawa Kafun kuka ya kwace mata,bata san lokacin da ta kama hanunsa ba ta saka kuka sosai tana mai faɗin"Baby i swear To God wallahi Mama ba karuwa bace koda kuwa a baya bata taba karuwanci ba sannan ni ba yar zina bace idan Ummi bata yarda ba kuma ta saka ayi mata bincike,mahaifiyata da Aure ta Haifeni sannan bayan rasuwar Mahaifina bata zauna haka nan ba sai da ta sake wani Auren inda ta haifi Khalel da Rabiatu wallahi ba ƙarya nake maka ba ,idan ma baka yarda ba bari na kira maka yaya sameer kaji a abakinsa ,zumbur ta tashi dan zuwa kiran Yaya sameer,da hanzari ya saka hannunsa ya jawota ta zauna,tana zama ta fashe da wani irin Kuka mai ban tausayi tana mai faɗin"ban san mai na tabawa Mother a rayuwa ba da take san kushe Asalina ta lalata mun soyayya,idan ban Aure ka ba zan iya mutuwa saboda dukkan wata soyayyata na dauka na baka,bazan boye maka ba ,a soyayyarka baki ɗaya na zira jikina saboda na gama yarda da cewa naje destination ɗin karshe ,Babu wani gurbi dana ajewa wani ɗa namiji a wannan rayuwar,dan Allah Haidar kar ka rabu dani duk runtsi duk wahala".


A wannan gejin ji yake kamar ya jawota 'ya rungumeta jikinsa har sai hawayen dake zuba a idanunta sun daina zuba ,jin dumi a kuncinsa ya saka shi ɗora hannunsa inda ya tabo hawaye,kokarin gogewa yayi domin kuwa baya san ya zama mai rauni a lokacin da Abar kaunarsa ta kasance a raunace,dolene ya nemo dukkan wani ƙwarin gwiwarsa ya bata karfin gwiwa,saita kansa yayi yace "Baby its okay ki daina wannan kukan cos idan kina yinsa jina nake kamar zuciyata zatayi bindiga ta fashe ,Bansan mai nan gaba zai haifa mana a rayuwa ba saboda ban san abunda Zai faru gaba ba sanin wannan sai Allah amma koma mene ina san ki sani,Ina miki san da bana kallan komai da kowa face ke,ina maki soyyayar da bana iya gane dai dai da kuma abunda ba dai dai ba,ina sanki to the extent that zan iya sadaukar da dukkan wani abu da na mallaka domin na mallakeki,Baby i love you to the very last extent that i don't give a shaking damn about how you were born,abu guda ɗaya na sani an halliceki an Haifekii sannan Allah ya haɗani dake,nasan waccan maganar ba gaskiya bace cos bayan kowa maganarki ce gaskiya,a rayuwata Babu wanda zai faɗa mun abu mara kyau akanki na dauka,koda ace maganar ma gaskiya ce Babu abunda zai sauya yarda kike a zuciyata so calm down ki kwantar da hankali Haidar naki ne da yardar Allah koma mene ke faruwa it will get over saboda insha Allah cikin satin nan Baba zai zo suyi magana da Appa ,magana ce ta bincike ko wanne side yayi then bayan nan cikin wata jikina ya ma gama bani Zanzo na daukeki na maidake gidana karkashin kulawata ,'dan haka ki goge wannan hawayen naki mai tsada kinji yar tsana ta"


Tsintar kanta tayi da yin dariya tana mai faɗin Wane ƴar tsana,murmushinsa mai kyau yayi yace "ke mana abar kauna,you look like a barbie doll bakiga ba da kikayi Dariyar nan kamar na saceki mu gudu,"


Hannu ta saka ta rufe idanunta,tabe baki yayi yace "aw kunya come on jo yanzun nan ko tashi ba'ayi ba kika gama fallasamun sirrin zuciyarki Shine kike mun wani kunya yanzu ,im very sure baki ci komai ba so yanzu ki tashi na kaiki wani sabon gurin cin abinci mai kyau "


Binsa tayi da kallo tana mai jin daɗin idea ɗin Kafun daga bisani tace"Aikin naka fa i mean bana san kayi late"ɗaga gira yayi yace "well im the Ceo ,d king and the founder Babu mai bani query,shall we?"


Tashi tayi tana mai nuna masa farin cikinta tsantsa tace "bari naje na chanza kaya"


Kafun ta kai ga takawa yace "Why?,kinyi mun kyau a haka so muje kawai sai dai in zaki dauki wani abu ne kuma".


Kallan kanta tayi Kafun tayi murmushi tace "okay bari na ɗauko wayata Just a moment"bayan mintina Kaɗan ta fito bayan ta sanarwa da baba Baraka cos yaya sameer ma ya fita.


*******


________________"Sageer magana mai muhimmanci nake san nayi da kai matsayina na mahaifiyar ka "Mother ta faɗa tana mai bin Sagir da kallo wanda ke zaune kan stool a bedroom ɗinta.


Nutsuwar sa ya bata yana mai faɗin"Ina sauraran ki Mother"


Gyara zamanta tayi tace"well a matsayina na mahaifiyar ka kasan cewa Babu wani abu da zakayi yayi skipping ɗina sannan babu wani abu da zaka so na gagara ganewa ,after all i gave birth to You,lokuta da dama idan iyaye suka fuskanci abunda ɗan su yake so sai su zauna su duba suga yanayin kyan sa da rashin kyan sa,a wannan zagayen ni dana duba kyansa na gani sabida zamu jefi tsuntsu biyu da dutse ɗaya,ni mahaifyarka ce dan haka ba sai wai an faɗa mun kana sha'awar Kiswa ba"..


Da saurin sa ya zabura yace "Mother ni kuma,wallahi..…"saurin katse tayi da hannu tace "uhm uhm kar Kafara mun rantse rantse Ina sane da irin yarda kake kallan waɗan nan manyan mazaunan nata da kallo, so cut it ni ba wani abu zanyi maka ba ,im fighting for Your sister sannan nasan ko wanne abune zaka iya yi Muddin Faridha zata samu fari ciki dan haka wannan karan zumuntar ka da tausayin ka zaka bada 'na ɗa wani lokaci,so nake kayi wa Kiswa fyaɗe sannan Ina san ka ɗauko mun ita wasu hotuna na Nudes ɗinta,zan baka dukan goyan baya daga baya Babu wani abu da zai faru "


Wani iri sagir ya tsinci maganar musammman da ya kasance da mahaifiyarsa yake wannan maganar,sosa keyar sa yayi yace"Mother kin san Idan Appa ya kamani na mutu sannan this is a sin in the other hand"


Tsaki ta buga tace"amma lokacin da gabanka ke tashi idan ka ganta baka taba tunani sin ne ba ko,kalli nan Sagir Allah gafurur rahim ne Mai yafiya ne zamu nemi gafara daga baya"shiru yayi yana nazari yayin da a lokaci guda shedan ya cigaba da assasa mishi sha'awar Kiswa wanda a lokaci guda ya amince,daɗi kuwa a gurin Mother ba'a cewa komai domin kuwa ta kai wani guri da ake cewa ba gudu ba ja da baya musamman da ya zamana a ranar farko saboda Kiswa mijin ta mai kaunar ta yayi mata barazanar saki gaban yaranta,wannan abune wanda bazata taba yafewa ba har sai taga ta lalata wa Kiswa rayuwa ta yarda Appa zai ƙwashe ta ya mayar da ita inda ya ɗaukota.






TBC


I miss you guys,


Do you miss me?


Chuchujay ✍️


08130229878
[5/14, 10:34 PM] Chuchujay✍️: 💥KISWAH💥


(Surrogacy was the cause)


Na


CHUCHUJAY ✍️


Book1⃣


Page 1⃣2⃣


__________Washe gari cikin wata irin walwala Kiswa ta tashi,dan haka tayi shirin office ,bata da Niyyar yin wani breakfast dan haka tacewa Baba Baraka idan an tambaye ta inda take tace tana azumi ,ille kuwa Appa ya tambayi Baba Baraka ganin kowa yazo banda ita,Kafun ya rufe baki daga tambayar da yayi Farry ta cabe inda take cewa"Appa we are complete here tunda dai dama ai ba ƴarka bace Ko Mother Why bother?"


Wani irin kallo Appa ya bata Kafun yace"sai dai in ba ƴar maman ki ba amma ni Kiswa tawace domin kuwa yarda nake jinta a raina ma bana jinki sannan idan na sake jin wata maganar banza a bakin ki zaki zauna a gida ki bani kujerar office ɗina dan bana tunanin zaki iya girmama ma'aikatana yarda ya kamata duba da yarda respect ɗinki yake neman ƙarewa ".


Dif kake jin Farry kamar anyi Ruwa an ɗauke,duk da yarda bakin ta ke ƙyaiƙayi akan tayi magana ta ƙwabesa dan tasan halin Appa.


Fitowa Kiswa tayi cikin shirinta tsaf tare da wani vibe Energy da ta samarwa kanta dan tayi Alƙwarin sauke nauyin Saleek dake kanta a yau wanda take ganin Shine best solution,at least bazai kashe ta ba haka zalika bazai daketa ba,ganin yarda suka zauna suna cin abinci zuciyarta taji tana mai bata taje ta zauna musamman yarda taga seat ɗinta empty ,Allah ya sani tana san su tana ƙaunar su saboda sune family ɗin da ta sani sannan ta shaƙu dasu tun yarinta bata fatan ace yau sabani mai girma yana shiga tsakanin su amma Mother is hellbent taga ta b'ata mata abunda take so da sunanta dana mahaifiyarta ,dan haka itama ta ɗaura ɗamarar kare duk wani bullet da zata jefeta da shi,Takawa tayi dan zuwa gaisawa dasu Kafun ta wuce,tana isa gurin Appa ya Faɗaɗa fara'arsa yace "har na fara tunanin fushi Kike damu da yasa ba zakici abinci da mu ba "cike da ƙaunarsa tace "Appa ni ina zan fushi da family na mai kyau,na tashine da azumi ,ina ƙwana"ta faɗa gudun zama taci abincin dasu duk da ba azumin take ba.


Cike da jin dadi ya amsa mata gaisuwarta yayin da ta gaida mother da yayyinta amma su kadai suka amsa banda mother,ba tare da ta damu ba ta tashi tayi musu sallama ta fita..


**********


Ta daɗe cikin motar ta tana tunanin yarda zata fuskanci Saleek kasancewar sa mutum mai murɗaɗen hali,ta iya iyuwa jira yake tazo tayi confessing ya ɗauki wani matakin akanta amma hakan bai dameta ba domin kuwa ta shirya daukar consequences na abunda ta aikata at least ta fito masa da gaskiya kuma zata basa hakuri hukuncin da zai ɗauka ya rage nasa ,wata irin kunyarsa take ji musamman da ya kasance irin sunayen da ta kirasa dasu waɗanda ba hallayarsa bace sharrin Farry ne ,ajiyar zuciya tayi ta dauko Jakarta ta fito a motan ta kulle ta nufi cikin company ɗin,straight office ɗin Saleek ta nufa Kafun kwarin gwiwarta ya ƙare dan a yanzu ta shirya fuskantar sa da karfinta ,koda ta isa bakin ƙofar sa tsaye tayi tana cije baki Kafun tayi karfin hali wajen ƙwanƙwasa masa ,knocking ɗaya tayi ya bata izini da ta shigo kamar barauniya haka ta shiga bakinta ɗauke da sallama,kamar an mitsinesa haka ya ɗago ya kalleta dan baya expecting ɗinta ,jingina bayansa yayi da kujerarsa yana kallanta Kafun ya Amsa mata sallamar ta ya ƙara da cewa"lafiya dai Ko? dan duk wani document, da nake bukata yana kan desk dina sannan duk wani meeting schedule ɗina Khaleefa yayi arranging mini so a yarda nake tunani abu daya ne zai kawoki inda nake wanda Shine ƙarya da rashin kunya domin kuwa idan akwai abunda kika ƙware akai Shine wannan abu guda biyun bayan aikin ki dan haka bismillah nasan duk wata hanya da zanbi dake in dai Nine have a seat ".


Zama tayi tana mai saukar da kanta ƙasaa cike da jin kunyarsa sosai,kula da yayi da kunyarsa da take jine yasaka shi kwashe wa da wata irin dariya har yana mai fito da ƙwalla yace"kaji mun yarinyar nan fa,nine kike jin kunya Ko kuma wani sabon salan munafurcinne kika shiryo da safiyar Allahn nan kika zo ki sauke mun ita dan bana tunanin Ko office ɗinki Kin shiga,Allah yasa ba wani bacin ran kika kullo mun ba domin kuwa Dariyar nan da kikaga inayi akwai wani abu a bayanta idan aka tunzura ni dan haka karki fara.


Ajiyar zuciya tayi ta ɗora hannayen ta dukka kan desk ɗinsa tace "Sir bana zo bane nan domin aiki ba, nazo ne domin confession wanda nake fatan zaka karbi ban haƙurina in the process ,ni mutum ce mai rauni idan abu ta shafi Family na wanda wani lokacin bana tunanin menene zai fito sakamako saboda wannan mistake din nawa,haka akan ka i made a huge mistake wanda ya sakani nake jin mutuƙar kunyar ka a yanzu haka ,kayi hakuri dangane da hallayyata dana nuna maka mara daɗi sannan da ɗabi'un dana danganaka dasu waɗanda ba naka ba,it was all my idea bana Farry ba kar kace zaka ɗauki wani mataki akanta ,ta nuna mun bata san Alliance da iyayen mu ke san haɗawa tsakanin ku ,a yanayin yarda ta nuna mun rashin san abun yasa na kawo idea ɗin wanda na tabbata Babu wadda zai so ya Auri mace kamar wadda na nuna maka a ranar ,nasan ban kyauta ba and it was very stupid of me ,dan Allah dan Annabi ka samu wani guri da gurbi a cikin zuciyarka ka yafe mun ,idan kuma kace zaka dauki wani hukunci ne bazan yi ƙorafi ba ,hakkin kane kuma a shirye nake domin na ɗauki wani hukunci da zaka mun amma ina neman alfarmarka da kayi hakuri kar ka saka Farry Ko mahaifan mu a ciki dan idan Appa yaji maganar nan wallahi bazamuji daɗi ba shi yasa nazo na sameka..


_Ya ɗauki lokaci kaɗan yana kallanta tare da hango tsantsar nadamar abun a tattare da ita sannan a ɗayan bangaren abunda yake hangowa a idanun Kiswa baya tunanin haka yake a bangaren Farry domin shi mutum ne mai gane mutane cikin lokaci mara tsayi sannan selfishness da ya hango tattare da Farry ba wai gizo ne yake masa ba gaskiyar al'amari ne.shafa sumar kansa yayi yace"so idan Babu hannun ita waccan sister taki a wannan babban plan naku mai yasa a office ɗinki ta nemi da nazo mu sasanta bayan ga dama tana da ita tun farko taƙi amfani da ita ,Ko hakan yana nufin ke kina sona ne kuma kina san ki mallakeni a maimakon ta dan haka kika kawo waccan shawarar after all nasan wancan likitan ba fina komai yayi ba and ke kuma you're not bad zan iya maneji dake duk da kuwa you're not my type.


Tsintar kanta tayi da murmusawa kafun tace "Sir with all due respect relationship ɗina bai shafi laifin da nayi maka ba sannan idan zaka mun alfarma bana san ka sakashi cikin maganar da muke yanzu domin kuwa Haidar rayuwa ta ne bana jin kuma a rayuwa zan iya bawa wani ɗa namiji gurbinsa koda da wasa ne shi yasa ban saka hannu akan waccan takardun da ka bani ba na zabi da nazo na faɗa maka gaskiya domin kuwa soyayyata ita ce rayuwa ta babu kuma abunda zan iya trading ɗinta akai,haka ƙarfin ta yake gareni,Farry kuwa akan maganar da tayi maka ta iyu kayi mata ne a yanzu wanda da nasan zaka mata wanchan act ɗin ma bazai samu gurbi ba,and ka yarda dani When i said this Sir Farry yarinyar Kirki ce duk da kuwa ɗan Adam yana da wani guri a gefe guda na rayuwarsa wanda bai cika ba, amma idan kaga Its okay zaku iya sasantawa kamar yarda nace dama abunda iyayenmu ke so kenan,bazan dai daina baka hakuri ba dan Allah kamun afuwa.


Murmushi ne kwance a fuskarsa yana mai yaba wautarta a soyayya Kafun yace"hala wannan soyayyar first love ce,kinsan akanta Babu gangacin da mutum baya aikatawa ,akan maganar ƴar uwarki kuma She's definitely not my type ,sannan ki ƙwantar da hankalin ki kamar yarda kika buƙata bazan saka sister ɗinki a ciki ba sannan maganar nan zata shafe kamar ma ba'a taba yinta ba,kinsa ni family man ne ina mutuƙar san naga mutum na da dedication akan danginsa dan haka zan yafe miki komai ya wuce amma fa cikin sharaɗi guda ɗaya.


Saurin gyara zamanta tayi tana mai san jin menene wannan sharaɗin,ganin yarda ta zama restless tana san jin mai zai faɗa ya saka yayi waving hannun sa yace "calm down ba wani abun tashin hankali bane kike wani zazzare mun ido ,im not a bad person,ba komai kuma ne zai zama hukuncin ki ba face zama abokiya ta sannan mai tayani office work ɗin daya kakare mun ,.wayar sa ya cire a key ya tura mata gaban ta yace idan muna da deal ki saka mun numbern ki cikin wayana daga yanzu kuma Kin zama friend ɗina.


Jin maganar tayi kamar wasa dan ba abunda take tsammani daga tare shi ba kenan,haɗe hannayen ta tayi guri biyu tace "Sir im sorry ban gane ba".


Ƴar dariya yayi yace "na faɗa miki ni ba mutumin banza bane sannan bana nufinki da cutarwa ina sone kawai mu ƙulla abota wanda Shine hukuncin ki so zabi ya rage naki sannan na baki assurance bazaki samu aboki kamar Saleek ba and yauwa bana san Kina kirana Sir ɗin nan sunana Saleek kuma dashi nake san ki kirani ba wani Sir ba"


Kallan sa take cike da mamakin juyin halayyar sa inda shi kuma yayi mata alamu da ido akan ta ɗauki wayar ta saka number ta.cikin nutsuwa ta ɗauki wayar tasa ta rubuta number ta ta miƙa masa,faɗaɗa fara'arsa yayi sannan yayi dialing ,ringing wayar ta tafara cikin Jakar ta ,daukowa tayi ta kalle shi,shima ɗin ita yake kallo Kafun yace"oya save my number sannan ina mai tayaki murnar zama abokiyar Saleek ina kuma san na tabbatar miki kamar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login