Showing 15001 words to 18000 words out of 50778 words
i swear bazai ci abincin dare ba ni kuma i cant sleep with that fact!"
"Inyeeeeh"muryar ya Sameer ta bayyana bayanta"wani irin kunya ce ta lullube ta dan da saurinta ta juya ta bar gurin dan bata san mai zata kuma cewa ba domin sai da ta gama maganar kunya ta kamata ,She's so much in love da take mantawa da kawaicii akan Haidar domin kuwa taga idan ta biyewa kawaici za'ayi mata sakiyar da ba ruwa .
Kallan Sageer sameer yayi yace "mai yasa zakace zaka hanata fita ,shes matured enough' sannan i trust Kiswa bazatayi abunda zamuyi Allah wadaran da ita ba,nasan abunda kake ma tarewa kenan,Chill and calm down dole wataran gidan wani zasuje and idan ba yanzu ba sai yaushe".
Dan murmushi sageer yayi yace "bro kasan mazan yanzu ne burin su su dauki advantage na mace ,ni kuma bana san wani abu makamancin haka yake samu sisters' ɗina ".dafasa Sameer yayi yace "insha Allahu sai dai Alheri bari na shiga ciki naga kamar zaka fita ne".
Wucewa Sameer yayi yayin da Sageer ya bi bayan motar Kiswa data fita da kallo yana
Mai jin wata irin fitina na dukan Ko wanne sashe na zuciyarsa dangane da ita.
********
Tsaye black BMW din mother take a bakin katafaren Boutique ɗin dake dauke da suna ZEE BULA Fashion House tana mai duba wayanta dan kar taran da take hari ta wuce bata gana da hajiya Zainaba Bula ba ,yau zata nunawa Kiswa mene ake kira da kuɗi da isa da kuma karfin burin Uwa,
Tana wannan tsayuwa kuwa motar Hajiya zainaba ta faka inda Bodyguards ɗinta suka fito su biyu suka buɗe mata ƙofar mota ta fito cikin shiga ta alfarma,yar gayuce mai harka da abunda ya shafi gayu shiyasa Mother ma ta kashe nata gayun dan zuwa ganawa da ita,sai da ta Bari Tayi wurin minti ishirin da shigaa ciki Kafun itama ta fito ta kulle tata motan ta nufi ciki ,bayan dan zagaye da tayi a ciki ta haura sama da taimakon ma'aikaciyar gurin domin ganawa da Md wato hajiya Zainaba,da fari basu bata dama ba amma da sales manager ɗin taga irin shigar jikin Mother sai jikinta ya bata ƙawar Hajiya BULA ce dan sukan yawan kawo mata ziyara shiyasa Mother na mata ihsani ta mata iso zuwa sama,bayan zuwan su PA dinta ta kira waya akan tayi baƙuwa,bata expecting kowa dan haka tace Ko ma Wane yayi booking appointment tukunna.
Nacin Mother da persistence ya saka Daga karshe Hajiya Bula tace a mata iso ta shigo ,kallan katafaren ofishin Hajiya Bula Mother ta fara Kafun ta fito daga wani daki da yake na hutawanta fuskarta Babu yabo Babu fallasa,zama tayi tana mai kallan Mother cikin kallan Ban sanki ba Kafun tace"barka Ina fatan dai wannan zuwan naki mai amfani ne a yarda na karbeki babu Appointment sai gashi kuma yazo da ban ma san fuskarki ba,hope im safe."
Murmushi Mother tayi Ta saka hannunta cikin jakarta ta ciro office card ɗinta tace"sunana Barrister Juwairiyyah ALIJUA,mijina shine Founder kuma babban shareholder na ALIJUA inda ni kuma nake babbar Barrister wadda ake damawa dani shekara talatin da uku kenan,bazan bata miki lokaci ba sannan bazan beating around the bush ba,wayarta ta kunna a dauko hotan Farry wanda ta gaji da haduwa ta miƙa mata tace"take a look wannan yarinya tace sunanta Fareedha ALIJUA sannan youngest CEo dake ruling babban FOUNDATION na ALIJUA da confidence' ,Nasan kina da yaro Haidar i mean Wane bai sani ba,sannan duk wanda ya sani yasan shine sanyin idaniyarki ,a matsayina na uwa na zauna nayi tunani a cikin society dinmu da status ɗinmu abune na kwarya tabi ƙwarya sannan na dauki step ɗin nan ne domin Farry dake crushing kan HAIDAR and matsayina na uwa kinga i can stoop to kowane level domin farantawa yarinyata inda nasan kema a gurinki haka yake,
Ina san mu kulla alaƙa ta hanyar Auratayya tsakanin yaranmu,ki daukesa proposal na ƙaruwa domin Farry bazata taba zama liability ba ga Haidar tunda itama ta da akwai,im Just looking out for us tunda koda Ban faɗa miki ba kinsan duk macen da zata bi Haidar kudinsa da kyansa ne,shine reality' ɗin mu a yanzu,shine dama abunda ya kawo ni har na zo Babu appointment ina fatan dacewa".
Shiru Hajiya Bula tayi tana kallan Mother tana jinjina guts ɗinta,wani dan madanni ta danna kan desk dinta wanda cikin minti ƙalililan PA ɗinta ta shigo tace"Yes ma"
Kallan PA ɗin hajiya Bula tayi kana tace ma Mother tea or coffee?
Murmushi Mother tayi tace"coffee ,"Kaɗa Kai Hajiya Bula taya tace"two cups please,"
Bayan fitar PA din Hajiya Bula ta kalli Mother tace"kinzo mun da magana mai kyau i must say sannan kina da yarinya mai kyau,ta shiga raina sannan straight forward halayyarki ta burgeni itama ,bazan watsi da tayinki ba amma ina so ki sani ,Haidar shine abu mafi soyuwa a gareni dan haka idan yacee yarki batayi masa ba babu abunda zan iya miki illa nace kiyi hakuri but kamar yarda na faɗa miki yarinyarki tayi mun zan gani"murmushi Mother tayi dan tasan Babu namijin da zaiƙi Farry ɗinta saboda tata ƴar farace tas ita kuma Kiswa baƙa sannan koda ace Haidar yasan Farry tasan bai taba kawo maganar nan a zuciyarsa ba and bata tunanin yasan cewa Kiswa yar riƙoce ba yar gida ba,tasha Alwashin Kiswa bazata Auri Haidar ba Shi ɗin tanadin Farry ne.
Bayan sipping coffee ɗin da Mother tayi tana mai sake shigewa Hajiya BULA sosai dan bazatayi ƙasa a gwiwa ba,sallama Mother tayi mata yayin da Hajiya Bula ke kan juya office card din Mother tana mai yin nazari akanta ,wani bangare na zuciyarta yana san gamsuwa da tayin Mother inda dayan ke mata wasiwasi,duk da haidar bai taba zama yace mata yana da budurwa da yake gani ba amma jikinta da abunda ta fuskanta akwai mace a rayuwarsa amma koma mene zata sani.
Da wuri hajia Zainaba ta tashi yau cos dama daɗewarta idan tayi sosai bayan sallar isha'i ne,Tana shiga shahararen falonsu ta tarar da Tasleem wadda ke aikin danna waya,Jakarta ta cilla mata tana mai fadin"aikin ki kenan danna waya kamar mai wani muhimmin kasuwanci a cikin"tashi Tasleem tayi tana mai Faɗaɗa murmushin ta tace"Ummi sannu da dawowa ,takowa tayi tana mai kama hannun Ummin tana matsawa Kaɗan tace"and Ummi nasan so kike na faɗa miki Me nake a waya to i will tell you,brother Haidar ya bani 1 million na fara business ɗin snacks ɗin da nace miki ina so na fara and i didn't even ask him,"
Takawa Ummi take Tasleem na binta gefe da gefe,kallanta Ummi tayi lokacin da suka iso Door step ɗin ɗakinta ta kalli Tasleem tace"i hope ba soyayya kuke ba?"
Dan turus Tasleem tayi jin yarda maganar Ummin ta fito da wani irin yanayi ,murmuswa tayi tace"ina ni ina soyayya da Brother ina sane Ummi da maganarki da kikace Brother Haidar sai Babbar mace ,nikam kuwa ai ina kan hanya ne wadda zaki mayar dani"
Dan kallanta Ummi tayi Kafun tace "better cos ke da Haidar yan uwa ne "Kafin Tasleem tace wani Abu Ummi ta shige ɗakinta,wata ajiye zuciya Tasleem ta Sauke,Allah ya sani tana mutuwar san Haidar amma yanayi na Ummi yasa take kama kanta gudun karta saita mata hanya tace ta tafi gida ,sau da dama idan ta zauna da Mamanta maganarta guda ɗaya ce"ki shawo kan Haidar"amma ita ta sakawa ranta bazata taba furta masa soyayya ba muddin bashi ne ya nuna mata ya furta mata yana santa ba ,ta sani a wannan geji kuwa Haidar baya ganin kowa bayan Budurwarsa Kiswa.
Tunda Ummi ta kankarawa Tasleem basu haɗu ba sai lokacin Dinner wanda dukkan su suka Halarta dan sau da dama tare suke Dinner dan ita kaɗai ce suke da lokaci,akai akai Ummi kan Kalli Haidar wanda ke ta santin Abincin musamman da ya zamana Tasleem tace masa ita ta girka ba cook ba,aje spoon Ummi tayi tace"Haidar what's so Good about abincin nan da zaka ishe mu ka hanamu ci cikin kwanciyar hankali ?"
Kallanta mijinta Tukur Bula yayi yace"sweet heart ya dai?mene aibu dan ya yabi abincin Tasleem When Its not a lie She's a Good cook"Kaɗa kai Haidar yayi yace "oho Baba tell her ,idan Ban yabi girkin ƙanwata ba Wane zai yaba?"kallan Tasleem wadda ke ɗan yaƙe yayi yace"girl you can cook for Africa Abincinki da daɗi amma kina da masu jealousing Ummi kuma tana ciki amma ni da Baba we have Your back".one spoon Baba Ya sake yace "For real Boy"
Ƙaramun tsaki Ummi tayi ta cigaba da cin abincinta ,bayan sun gama Ummi ta fara tashi tana mai cewa"Haidar ka sameni a falona zamuyi magana, bata jira mai zai ce ba tabar gurin yayin da suka cigaba da cin abincin su ba tare da kowa ya damu da sudden Halayyar Ummi ba idan aka cire Tasleem ".
Bayan gama cin abincin sa Ya nufi sashen Ummi dan jin kiran da take masa,zaune Ya tarar da ita tana Kaɗa kafa ɗaya,zama yayi gefenta yana mai kama hannunta yace"Ummi na wanene Ya taba mun ke aji kan mu a garin nan na Abuja"ƙaramun murmushi tayi ta kallesa tace"ai ka iya wannan dama and Wane kake gani zai tab'ani garin Abuja Ya kwana lafiya dama,"yar dariya Haidar yayi yace "Allah Ya jada ran Ummon Haidar "serious face ta saka tace "mene tsakaninka da Tasleem"?
Da mamaki yace"Tsakanin mu kuma Ummi ,ƙanwatace da nake Alfahari da ,kema Kin sani ina jin Tasleem kamar ke kika haifeta ba Aunty Maryama ba"
Da kyau Ummi ta kallesa tace "ka tabbata baka kallanta romantically cos bazan so hakan ba Ko kaɗan".
Dariya Ya saka lokacin da ta kai karshen maganarta yace "Ummi Tasleem fa?tayaya zan kalleta romantically?dariya Ya sake fashewa da yace"Allah yasa daga ni sai ke Ummi babu wanda yaji wannan maganar taki".
Yar Dariyar itama tayi tana mai jin daɗin yarda Haidar ya dauki Tasleem ,wayarta ta dauka ta shiga images ɗinta kana ta miƙa masa tace "oya kalli ka faɗamun ya ta jikin hoton nan take".hannunsa ya saka ya karbi wayan yana mai fadin "hope ba matchmaking zaki mun ba Dan im taking,"idanun sa ya ɗora kan hoton da mamaki yace"Farry"?Dago idanunsa yayi ya kalleta yace "Ina kika san Farry Ummi and mai kike da hotonta"?
Kallansa Ummi tayi da Mamakin jin ya ambaci sunan Farry wadda ga dukkan Alamu ya santa,cikin ƙaguwa tace"kasan ta ne?abun ma yazo da sauki kenan cos wannan yarinyar ina san nayi bincike mai kyau akanta kaje ku sasanta Dan a yarda na gana da mahaifiyarta na gamsu ."
Gyara Zama Haidar yayi yace"wait Ummi let me understand,Wane ya gana da Wane sannan Wane zai sasanta Dan Wane im lost".murmushi Ummi tayi tace"mahaifiyarta ta sameni yau a office ta kawo mun tayin Aurenta gareka so na zauna nayi tunani naga offer ɗinta is not bad cos yanzu duk macen da zatazo tana sanka dole She's after money and Your look amma wannan yarinyar atleast koda iyayenta basu kaimu kuɗi ba bazatayi ƙwaɗayi ba since itama shes loaded so na faɗawa mahaifiyar ta zan nemeta idan na gana da kai and of course Babu dole amma inasan ka bawa abun nutsuwa da tunani mai kyau sannan ka samu kaga ita Farry ɗin".
Wata irin gajeriyar dariya yayi yace "Ummi you cant choose yarinya for me Just Dan mahaifiyarta tazo ta sameki akan tana san ɗanki ya Auri ƴarta,bamafa ki sansu bafa Ummi,and Wane yace wai duk macen dake sona dan kuɗine,?
Gyara zaman sa yayi yana mai cewa"Ummi Wannan yarinyar da kike gani sister ɗin yarinyar da nake soyayya da ita ne for year and counting now "Da mamaki Ummi tace "ta yaya and how comes ita maman nasu bata sani ba take san ka Auri ɗayar?"
Tabe baki yayi yace "ga dukkan alama dai but Ummi Haidar dai Kiswa yake so sannan inata san na faɗa miki amma na shirya baki surprise ne amma abun yazo a haka,"wayarsa ya ciro ya shiga hoton Kiswa yace "kalleta nan Ummi wadda tayi gaba da zuciyar ɗanki".
Karban wayar Ummi tayi tana mai ɗora idanunta kan beautiful Black Queen ɗin Haidar ,Dan washe baki tayi tana mai fadin"kuma gata mai kyau da ita,to ai ba abun tada hankali bane,im sure maman bata sani ba but na tabbata zatayi farin ciki idan taji already ma kana tare da ƴarta,i will talk to her sannan yaushe zaka kawo mun ita na ganta cos na ƙosa naga wannan Yarinya da Haidar ɗin Ummi yake ikirarin ta tafi dashi"
Sosa kansa yayi yana mai murmusawa kafin yace "Soon ummi i will talk to her duk lokacin da take da free time zan kawota ku gaisa and im sure Ummi zaki sota cos Kiswa is a very lovely girl,cute and stunning".Kalllansa Ummi take ganin yarda yake faman koɗa Kiswa ba sai an faɗa mata ba yana santa and hes happy about that and farin cikinsa shine gaba cikin abinda ke sakata farin ciki,haka nan take jin kamar taje ta dauko Kiswa ta kawo ta gidan ta,shafa gashin kansa tayi tace"badan dare yayi ba ai yanzu zan kira Barrister Juwarriyah amma da yau da goben duk Na Allah ne tunda dare yayi bazan dameta ba,nasan itama zatayi farin ciki sosai idan taji maganar nan".washe baki Haidar yayi ya cigaba dawa mami waƙar yaban Kiswa.
TBC
CHUCHUJAY✍️
(Amina jamil Adam)
08130229878
[5/8, 12:13 PM] Chuchujay✍️: https://chat.whatsapp.com/DgTUlodRcp2AHM4rmfKTqK
💥KISWAH💥
(Surrogacy was the cause)
Na
CHUCHUJAY ✍️
Book1⃣
Page 9⃣
AL'HAIDAR PRIVATE HOSPITAL.
Cikin Yanayi na nutsuwa Haidar ke takawa domin isa office ɗin sa inda yake mai karban gaisuwar ma'aikatan sa yana miƙa musu cikin girmamawa , yana isa bakin office din sa Ya saka key domin buɗewa amma ga mamakin sa yaji kofar a bude ,turawa yayi yana mai tunanin Ko jiya bai kulle ba Ya wuce,turus yayi lokacin da Ya shiga office ɗin ,roses ya ganin an cicire su an rubuta Good Morning love da kuma tambari na heart,kan desk kuma dauke da food pack wanda ba a bude ba ,dan kalle kalle Ya fara dan ganin Ko zaiga giftawar wani ,a hankali Ya taka dan sake dubawa,kofar shigowa da yaji an buɗe ne Ya sakashi waigawa,Kiswa ce tsaye bakin kofar hannun ta dauke da leda yayin da fuskar ta ke dauke da babban murmushi,dafe fuska Haidar yayi yana mai sauke ajiyaar zuciyar ganinta Kafun Ya ƙarasa gareta hakoran sa washe kamar anma yaro kyautar candy.
Ledan hannunta Ya karba yana mai fadin"Good morning my romantic heartrob to what did i owe this?"
Faɗaɗa murmushinta tayi ta shigo ciki tana mai cewa"to love masoyi,i woke up naji yau ina san ka fara sakani a idanun ka idan kazo office ɗin nan and of course i made you breakfast dan na sanka da rashin san karyawa idan zaka fita office which you will have to work on dan idan mukayi Aure bazan dauka ba,yanzu abunda za'ayi ka zauna nayi serving maka breakfast Then na wuce aiki cos kar ka manta i work for someone and i cant afford being sacked".
Cike da wani irin santa dake faman fuzgarsa ya zauna inda ta masa nuni yana mai binta da ido fuskarsa dauke da wani irin murmushi na farin ciki da ya kasa cirewa ,.
Buɗe food pack din tayi ta ciro Kulan dake dauke da plantain mossa,sannan ta dauko plate ta saka masa guda uku manya a kai Then cutleries Kafun ta aje a kan cinyansa then ta ciro Cup ta buɗe karamun flask ɗin dake dauke da kunun gyaɗa a ciki ta zuba sannan ta dawo Gefensa ta zauna tace "bismillah hero and mind you sai ka cinye mossa ɗinn nan da kunun gyaɗan nan,"rufe idanunsa yayi ya buɗe yana mai shaƙar kamshin abincin dake gaban sa Kafun yace "my favourite,ya akayi kika sani ban taba faɗa miki ba idan Zan tuna"
Haɗa hannayenta tayi guri ɗaya tace "well idan ban san favourite abunda mijin da zan Aura nayi rayuwa ta har abada dashi ba mai ya kamata na sani?,well just eat already"
"What about you?"ya tambaya yana mai zuba mata ido.
Wani fari da ido tayi Kafun tace "well ni a ƙoshe nake burina kawai kai ka ƙoshi,"murmshi yayi yayi bismillah ya fara cin abincin Cikin nashaɗi, bayan ya gama Ya kalleta da soyayya yace"Allah yayi miki albarka Kiswa,Allah ya mallaka mun ke a matsayin matata uwar ƴaƴana wallahi ina sanki da yawa sannan a kullum sake sanki nake sosai ba wai so na wasa ba,dan Allah ki dage da yin Addu'a kema Allah yasa mu mallaki juna kafun mu koma ga mahaliccin mu".
Tashi tayi ta fara haɗa kwanikan kafun tace"na faɗawa Mama maganar ka jiya da mukayi waya and ta ƙosa na kawo ka Bauchi ta ganka,i can tell tun Kafun ta ganka kayi mata already"
Cike da zumuɗi yace"OmG Baby i love you ,dan Allah ki samu free time muje cos ni kaina yakamata na ga macen da ta haifa mun macen da bana da nutsuwa idan akanta ne"dan shiru yayi kafun yace"Yea kafun na manta ina ganin ya kamata ace by this time Mother ta san dani a rayuwarki sabida rashin sanin yasa ta samu Ummi jiya a office tana san haɗani da Farry na Aura and im sure dan bata san muna tare bane ,but i told Ummi jiya about us and tayi farin ciki sosai dan idan da dan ranta ne yanzu ma na kaimata ke ta ganki,ba kiga yarda take murna ba".
Jin maganar mother ta je gurin mahaifiyar Haidar tayi kamar almara,bata taba sunanin san zuciyar Mother ya kai har inda bata zato ba,kallan Haidar tayi da kyau cikin sigar boye abunda ke ranta ta saka wata dariya tace "so mother did that,gaskiya ya kamata yau na shigar da kai gida a samana rana dan yanzu mother taje cikin rashin sani gobe wanine zai je ."
Dariya ya