Showing 42001 words to 45000 words out of 50778 words

Chapter 15 - KISWA Book Complete Document by Chuchujay.txt

29 Nov 2024

2568

ya ƙarb'a yayi sipping kaɗan kafun yace"Ummi,Baba Kiswa ta b'ata,babu wanda yasan inda take dan family ɗinta ma basu damu ba dan sune suka koreta cikin dare babu koda suturar kirki,gashi ina kiranta wayarta a kashe,I'm doom dan wallahi idan wani abu ya sameta ban san yaya zanyi surviving ba".


Cike da mamaki Baba yace "Abunda ban gane ba,mai yasa zasu koreta cikin dare babu wani dalili?""Uhum nima abunda nake san sani kenan ,babu yarda za'ayi su koreta babu dalili".Ummi ta faɗa tana mai shafa kan Haidar.


Kamar yarda mai gadi ya basa labari shima haka ya labartawa musu,salati Ummi ta saka yayin da Baba yayi shiru cike da mamakin inhumanity irin na Mother ,Kallan matar sa da tayi narai naraii da ido yayi yace"Madam ku ƙwantar da hankalin ku,za'a ganta,yanzu zanje na samu IG za'a ganta ne ,im sure tana guri mai kyau".cike da karaya tace"my dear ina zan kwantar da hankalina Na Haidar ba a kwance ba,ka kalli fa yarda yake kuka kamar ƙaramin yaro",dan Allah kayi wani abu a gano inda take i cant stand this,ana ganin ta kuma a ɗaura musu Aure gwara idan tana ƙarƙashin kulawarsa hankalin mu zai fi kwanciya.


Haidar yaso yabi mahaifin nasa amma Ummi ta hana dan haka yayi mata karyar zaije ɗaki ya zaga da taimakon Tasleem ya fita dan bazai iya zama gida ya nannaɗe hannu ba baiyyi wani abu ba dole yaje nemanta shima.


**************


_______yarda Mother ta cukumi wuyan Doctor Ben abune wanda kana kalla kasan magana ce ya faɗa mata mara daɗi musamman da ya kasance tana kuka tana mai ce masa ƙarya yake sakamakon da ya faɗa dangane da Sagir,


Samir dake ta faman ƙokarin rabata da Doctor ɗin ne Yace"Mother mana please control Your self ,mu godewa Allah abun ma a haka ya tsaya bai yi gaba ba ,dan ai we learnt from our mistake,shi nashi ƙadarar kenan,gobe zai kiyaye".


Kuka ta fashe dashi sosai tana mai cewa"yanzu sameer kana nufin ƙaddarar Sagir kenan bazai ga jinin sa ba,to mene yayi zafi haka,wallahi bazan yarda ba,sai na kashe Kiswa da hannuna zanji daɗi."


Zage Zage take ɗugunzumawa Sameer na Kamota har suka fito daga ofishin likitaan,kukan suka tarar da Farry nayi gefen gadon Sagir wanda ya ɗan samu bacci,kamar wata kamun hauka Mother taje ta zauna gaban sa ta kama hannun sa tace"indai nice na haifeka Sagir ,yarda Kiswa ta ƙwace maka farin cikin ka na zama uba sai na ƙwace mata nata farin cikin na zama matar wani balantana ta zama uwa,sai na mayar mata da rayuwarta cikin rayuwa mafi muni da ƙasƙanci,wallahi sai taji dama baka kanta Tayi cikin ruwan sanyi babu gardama,abunda ta hanaka sai na saka maza goma sunyi amfani da ita a lokaci guda,bazan huta ba sai wannan alwashin nawa ya cika '".


"Wow Mother wow,Wallahi kinsaka ina jin kunyar wani ya wuce nace masa ga mahafiya ta nan,ina jin kunya da ƙyamar abunda kuka aikawa Kiswa ,yarinyar nan cikin dare kika koreta babu koda suturar arziki,baki san Wane hali zata shiga ba ko wanne hannu zata faɗa,idan da ace Farida ce fa,koda baki tausaya mata dan komai ba zaki tausaya mata for the sake of humanity,amma abun kunya da takaici kece zaune kike alwashi munana akan yarinyar da ɗanki ya nemi ya ƙetawa haddi,ai koda kashe sa tayi Batayi laifi ba,ya godewa Allah a nan abun ya tsaya,Good for nothing bastard".yaya Sameer ya faɗa babu koda guntun tausayin Sagir a ransa.


Tasowa mother tayi ta tako gaban sa ,sai da tazo daf dashi ta ɗauke sa da mari mai zafin gaske ta nuna sa da yatsa tace"kaine Good for nothing bastard ba yaran da ya nemi tsayar da hawayen dake bin kuncin mahaifiyar sa da ƙanwar sa ba,sannan kaje ka faɗawa duk wanda zaka faɗawa abunda nace sannan ka ƙara da cewa nice nan na bawa Sagir goyan bayan haike mata,duk inda kuma take idan ka nemota ka faɗa mata ta shirya tarbar fushin uwar da akayiwa ba dai dai ba,sannan kar tayi gangancin dawowa gidan mu ta cigaba da buya domin duk abun nan da kaji na furta sai ya faru da ita,wutar tsanarta tana yi mun rurin da babu mai iya kashewa sai biyan buƙatar fansa ta,bari kaji koda hakan yana nufin zan rasa aure nane,abu kuma na ƙarshe da nake san ka sani Shine ,idan ka sake goyan bayan Kiswa a gabana ban yafe maka nono na da Kasha ba."


Wasu irin hawayene suka fara zarya akan kuncin samir yana mai jinjina tsantsar jahilcin dake cikin maganar Mahaifiyar sa ,bai ce komai ba ya juya ya fita a ɗakin,kai tsaye motar sa ya shige ,cikin rashin tsammani ya tsinci kansa da fashewa da wani irin kuka mai cin rai,tunanin sa halin da Kiswa take ciki da wanda Mother ke neman saka ta nan gaba,tun da ya tsinci labarin abunda ke faruwa yake gwada layinta amma baya samu,tunanin sa kuma da inda zai sameta baki ɗaya ya gushe,yasan a duk inda take tana buƙatar ɗan uwanta,numbern Appa ya sake nema a karo na babu adadi dan so yake ya zamana a bakin sa ya fara jin labarin nan,amma still a kashe bai sameshi ba,abokinsa masu binciken boye ya kira dan su fara cigiyar inda take,baya sun gama waya kai tsaye ya wuce gurin sa Ayi binciken dashi.


Bangare Haidar kuwa babu inda bai duba ba akan neman Kiswa ,Baga asibitoci,Sashen aje gawa da duk wani guri da tunaninsa zai bashi amma bai ganta ba,abinci kuwa bama shi da lokacin tunawa da yanajin yunwa tun safe har dare baici ba,tracking layinta shima yaje a ayi a kashe wayanta amma suka tabbatar masa da zasu cigaba da gwadawa har Allah yasa ta kunna wayarta ,karshe dai da kyar ya iya komawa gida dan kanshi sakamakon zazzabi mai zafi da ya rufe shi.


Shin ina labarin Kiswa kuwa?






CHUCHUJAY ✍️


08130229878
[5/31, 11:42 PM] Chuchujay✍️: 💥KISWAH💥


(Surrogacy was the cause)


Na


CHUCHU JAY ✍️


Book1⃣


Page1⃣9⃣


________Da wani irin matsanancin ciwan kai Kiswa ta tashi washe gari sakamakon irin kuka data raba dare tana yi,babu abunda ke damun ta idan ta tuna yarda tsakaninta da Yaya Sagir yake,they were this close da take jin babu wani abu da zai kawo mata matsala muddin tana dasu,babu abunda yake da ciwo sama da buɗe ido ka wayi gari ace yau family ɗinka sunyi back stabbing ɗinka saboda kawai wani selfish abu nasu na san zuciya wanda bai chanchanci yaudara da lalata zumunci ba,Baccin da tayi baifi na Awa biyu ba wanda Shima tana farawa zata tashi a firgice wanda cikin deren anxiety ya ziyarce ta,yanayi na tsoro da kuma tunanin abunda yafaru zai sake maimaita kansa.


Bayan tayi sallar asuba bata iya komawa ba,tana jin Saleek na mata knocking kan ta tashi lokacin sallah ta sanar dashi idanta biyu ta tashi,bayan nan bata iya komawa ba ta zauna tana neman Allah ya kawo mata ɗauki ya saka mata hannu a rayuwarta,gari na fara haske ta shiga wanka tana tunanin sake mayar da bathrobe ɗin dake jikinta dan da ita ta Ƙwana ,locker ɗin da aka tanada domin aje towels a bathroom ta buɗe ta gansu jere tsaf dasu ,guda ɗaya ta jawo ta ɗaura kafun ta fito ta zauna kan gado ta ɗauki wayar ta tana tunanin kunnawa ,tasan mutum uku sun nemeta basu sameta ba,Haidar ɗinta da yaya sameer sai Appa idan ya san labarin ko 'ya dawo,amma ta shirya saka idanunta cikin nasu?,bata san mai zata fara faɗa musu ba domin kuwa mayar da zancen kawai sakata yake ta jita cikin wata irin matsananciyar kunyar da ba'a saka mata rana,san kiran Mamanta ne ya faɗo mata amma bata shirya tada mata hankali ba domin tasan Mama najin maganar nan zata taho Abuja ne wanda tasan abun babu kyau,hakura tayi da kunna wayar ta koma ta kwanta tana mai jiran tashin Saleek ta ari wayarsa ta kira Baba Baraka ta kwaso mata wasu kayan ta a boye da jakar ta boye dan koda zata koma gida ba yanzu ba sai abun nan 'ya sake ta.


Tunanin abun ya cigaba da dawo mata da yarda Baba baraka bata kwana gidan ba,ta yarda sun gama shirya abun su ne Allah ya nuna musu bai yarda abu ya samu bawan sa ba muddin ba Shine yaso ba.


Ƙwanƙwasa mata ƙofa da ake ne ya fito da ita daga dogon tunanin da take,daga inda take tace "wanene"?


Saleek dake tsaye bakin ƙofar ne yace "Nine,Saleek na kawo miki kaya ne and breakfast is ready".tashi tayi ta jawo Hijab ta saka kafun taje ta buɗe kofar ,da murmushi ɗauke a fuskarsa ya nuna mata ledar yana mai faɗin "Good morning"


Murmushin itama ta mayar masa kafun ta karbi ledan hannun nasa tace "Good morning and thank you".ɗan sosa gefen safen fuskarsa yayi yace "well ban san 'ya zanyi dake da godiyar nan ba,imagine da sanyin safiyar nan,well get dressed ki fito mu karya,and i hope komai na ciki is to Your liking na saka An siyo ne anjima idan na fita zan shopping miki kaya da abunda zaki buƙata".


Dan buɗe kayan tayi cikin ledan ta ɗan kalla kafun tace"Well wannan ma na gode anjima zan saka a kawo mun kaya na office ka taho min dashi ,but bari na shirya na fito".kaɗa mata kai yayi kafun ya Bar gurin yana faɗin yana jiran ta.


Kulle ɗakin tayi ta juye kayan kan gado,doguwar rigace ta material ready made sai inners,wani irin kunyace ta kamata ,thank God bashine yaje ya siya ba,pant ɗin baiyyi mata kaɗan ba baiyyi yawa ba amma Bra ɗin ya ɗanyi mata kaɗan,haka na ta saka ta ɗauki JC veil ɗin dake ciki ta ɗaura,Room Slipper ɗinta wanda dama dashi ta fito ta saka ta fita .tana fitowa ta hango shi zaune kan dinning table gefe guda kuma mace wadda bazata wuce 35 years ba tana jera abinci kan table ɗin,karasa tayi nervously tayi sallama ,ɗagowa yayi ya sauke idanun sa akanta ,wani irin santa yaji yana yi masa yawo a cikin zuciyarsa musamman yarda ya ga tayi masa kyau ɗin nan,kome ta saka kyau yake mata, she's Just pure and natural,saurin saita kansa yayi tunawa da yayi akwai neman wani akanta sannan yayiwa kansa alƙawari zai tsarkake Alaƙar dake tsakanin su,zama tayi tana mai faɗin"barka ".murmushi yayi yace"barka and Guess What? you look Good"yauwa zarah je ki kira mun kowa ,"To yallabai"


Bayan wucewar Zarah ta kallesa tace"hope bazan zamar maka damuwa ba dan ina so nayi koda sati biyu ne out of any matsala and ina san kamun alfarmar kar ka faɗawa wani inda nake,i need a break for this madness,and ina san kiran Mai aikin gidan mu zata kawo min wasu kayan ka taho mun dashi,and ina san ka ara mun wayan ka,sai na kira ta".


Kaɗa kai yayi yace"baki tunanin ita bazata fitar da maganan ba,i mean do you trust her"


100%" ta bashi amsa tana mai yi masa murmushi da ƙara ganin girmansa musamman da bai tambayeta abunda ya faru ba,matar da ya aikace ta dawo tare da mata uku,ɗaya zatayi tsarar zarah ɗaya kuma dattijuwa ce sosai dan Aƙalla zata daki hamshin,cike da mutuntawa bayan isowarsu yace musu"Good morning and na saka kuzo ne dan na gabatar muku da baƙuwata Kiswa,she's a family and tazo ne zata ɗan zauna annan dan haka yarda zaku bani service haka zaku bata bana san naji complain,kallan babbar yayi yace "Mama asabe dan Allah a kula da ita idan bana nan".murmushi matar da ya kira dan Mama asabe tayi tace"Insha Allahu yallabai,sannu da zuwa Hajiya,sunana Asabe,nice kuma nake kula da gidan nan bisa umarnin Yallabai Babba da ƙarami,ga Zarah ita ke kula da kitchen ga kuma Jamila Ita ke kula da shareshare ".gaishe da Kiswa sukayi cike da girmamawa wadda ta tsinci hakan weird dan bata san taga babba yana nuna mata girma tana ƙasa dashi,bayan sun bar gurin Zarah tayi serving nasa kafun itama ta wuce. A hankali ta fara cin abincin tana mai kallan Saleek wanda shima abincin yake ci kafun tace"baka tsoran ko na kashe wani ne aka koreni daga gida ka bani masauki,what if ni wanted killer ce,atleast ka tambaye ni."


Murmusawa yayi yace"nasan ko mene zaki aikata akwai dalili sannan idan baki faɗa mun ba akwai dalili,bazan tab'a miki dole ba ki faɗa mun abunda ke damunki,kilan ba abune wanda zaki iya faɗa ba and i understand,ina san kisan abu ɗaya ne,a kowanne hali ina tare dake kuma zan baki goyan bayana ɗari bisa ɗari,zan saurare ki zan taimaka miki idan iyuwar hakan ta tashi".


Goge ƴar ƙwallar dake ƙokarin zubo mata tayi kafun tace "kamar yarda ka sani gidan su Farry gidan yayan Mama nane ,ya dawo dani gidan sa ne lokacin mahaifina ya rasu so nida Farry muka girma tare kamar yan biyu,duk da na girmeta amma ƙawa na ɗauketa kuma ƴar uwa,haka zalika yayyunta guda biyu,Sagir da Sameer ,they are my everything ,so jiya yaya Sagir yayi kokarin yi mun fyaɗe ,ni kuma a kan cetan kaina nayi masa rauni shine Mother ta koreni a gidan,she never likes me,and worst thing Shine da Haɗin bakin ta yaso yayi raping ɗina,she knows.


Wani irin ɗaci ne ya tsayawa Saleek a maƙogaro,tunanin abun kawai ya sakashi jin baki ɗaya yayi losing apetite,tasowa yayi daga kujerar da yake ya dawo ta kusa da ita gannin tana hawaye,shafa kansa yayi cike da damuwa yace"look babu wanda ya ke da ikon nuna ki da ɗan yatsa,kilan ban san yarda zan comforting ɗin ki ba saboda ban ƙware a nan ba,amma ina so ki sani abunda kikayi dai dai ne,Idan nine a madadin ki ma zan iya abunda yafi haka,im so sorry to hear this sannan ina san ki sani ina bayanki ɗari bisa ,sannan kamar yarda kika yanke shawara hutawa daga madness ɗin nan is a Good thing amma baki tunanin ya kamata Haidar yasan inda kike?i mean man nasan a irin san da yake miki yanzu haka damuwar da yake ciki bazata misaltu ba."


Ɗan Ajiyar zuciya tayi tace,well ina tunanin hakan amma ina san na ɗan huta kaɗan daga kowa ,hope zan iya Ɗaukar 1 to 2 weeks break daga aiki CEO Sir?


Dariya yayi a karo na farko kafun yace"kar ki manta idan Kin dawo ki shirya amsa query amma for now zan kulle ido nayi kamar Bansan baki zuwa aiki ba,".a Haka ya ringa kwantar mata da hankali har taci abinci shima ya samu ya ɗanci,.kamar yarda tace zata kira Baba Baraka haka ne ya faru koda ta kirata kamar zatayi mene saboda murna tana tambayar ta inda take.


Saƙo ta bata na duk abunda take so takawo mata office ɗinta sannan kar ta faɗawa kowa ta kirata.bayan sun gama waya Saleek ya wuce bayan ya tabbatar da babu abunda zata buƙata..






CHUCHUJAY ✍️


08130229878
[6/2, 9:02 PM] Chuchujay✍️: 💥KISWAH💥


(Surrogacy was the cause)


Na


Chuchujay ✍️


Book1⃣


Page2⃣0⃣


_______Kiran Samer da Appa yayi ya saka shi ji kamar an tsundu ma shi Aljanna,cikin sauri ya shirya an zuwa Airport duk da Appa yace yazo wurin ɗaya na rana ne amma tun goma yaje yana jiran saukar sa domin he cant wait ya faɗa masa abunda yake faruwa da wanda yake Shirin faruwa,ya kamata wani ya tsaida Mother kuma yasan Appa ne kawai yake da wannan power ɗin.ille kuwa gaisuwa kawai ta haɗa Appa da sameer ya fara zayyana masa abunda ya faru ba tare da ya rage ko kaɗan ba.


Yanayin da Appa ya shiga ba ƙarami bane musamman da yaji ko inda Kiswa take ba'a sani ba,yasan Mother zata iya komai wa ƙiyayyyarta amma bai san rashin imani yana ɗaya daga ciki ba,Asibitin ya nemi kai tsaye Samir ya kaishi domin ya kamata yayi wa tufkar hanci,yana isa kai tsaye ya shiga ɗakin bisa jagorancin Samir inda suka tarar da sagir yana faman wa Mother kuka tana taya sa Farry na gefe itama kuka take tana lallashin su,kuka sagir yake sosai yana cewa"yanzu Mother bazan ga yara na ba kenan fa,Mother please ki taimaka mun ,nasan akwai asibitocin da suke nan a ƙasashen turai da zasu iya mun aiki na iya haihuwa,this cant happen To me Mother ,no now,wallahi bazan taba barin Kiswa ba sai ta gane ni tayiwa haka".


Kafun mother tace wani abu Appa ya sanar da zuwan sa ta hanyar faɗin"sai dai in kai ka gane ita kayi wa haka,sannan duk wani asibintin da zaka je ya kasance da sa hannun uwarka amma ba da nawa ba,ya kamata kuma ku sani ko Wane Aiki yana da kamashu naku sakamakon kuwa Shine bani babu ku,daga nan ki san inda zaki kaishi amma ba gidana ba,idan kuma kina san ganin tashin hankali ki dawo gida na juwairiyyah,sannan kafun nan ina san ki sani na datse igiyar Aurena guda Ɗaya daga kanki,kinga ina da babban dalilin da zai saka na hanaki shigar mun gida,shi kuma na yafe miki shi domin ni ban haifi ɗan da zai yiwa ƙanwarsa fyaɗe ba wallahi sai dai in kece kika haifa tunda gashi nan maganar ki yake ɗauka,sannan wallahi na rantse da Allah idan wani abu ya samu Kiswa Na rantse da Allah sai na ɗaure ku".


Ya juya zai fita Mother tace"Amma dai idan baka manta ba kana da ƙanwa wadda ta haifi ɗa a waje,ita dame tafi Sagir".


Sosai maganar ta daki Appa da mamaki ya juyo ya kalli Mother, ƙaramun murmushi yayi yace"Uhum ina da ita sannan ba sai na faɗa miki ba ta ko ina ta fiki ,tarbiyya da komai ta fiki,domin nayi imani da Allah bazata bada goyan ba ayiwa Faridha fyaɗe ba,haka tasan darajar ɗan Adam,tana da imani sannan tana da taƙawa da tsoran Allah,idan kuwa duk tana da wannan abun kinga kuwa tafi mace Jahila ,ɗakikiya ,mai halin dabbobi kamar ki,nayi dana sanin mayar dake matata juwairiyyah na cutar da yara na da ban nema musu uwa ta gari ba,nayi dana sani sosai".yana kai ƙarshen maganar sa ya fita yayin da Farry ta fashe da wani irin kuka,sameer ya juya zai bishi ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login