Showing 45001 words to 48000 words out of 50778 words
buga masa wata irin tsawa tace"zo nan dan ubanka".
Rumtse idanunsa yayi kafun ya juya yana mai takawa gareta,nuna sa tayi da Ɗan yatsa tace "ni zaka yiwa munafurci,ni uwarka da na haife ka,To sai mene dan Aliyu ya sake ni ina ce na faɗa maka sai naga karshe Kiswa koda hakan zai sanadiyar mutuwar Aure na?bazan maka baki ba amma zaka ga muhimmancin uwa ga ɗanta ,kaje kamar yarda ya sallama mun Sagir nima na sallama masa kai kaje Chan ku ƙarata sannan ku fara irgen ƙwanakin da suka rage mata na jin daɗi a duniya,sai na ɗai ɗai ta ta ,sai na saka Kiswa abincin da zataci tayi barar sa ,sai na saka duniya ta tsaneta ,sai na saka duniya ta tsine mata,sai na tozartata,idan banyi haka ba darajar Aurena da narasa bata da amfani,ka fita ka vani guri bana san ganin ka ,kuma koda na mutu ne ban yarda kazo kan gawata ba".
Durƙusawa Sameer yayi akan gwiwowin sa ya fashe da wani irin kuka mai cin rai,cikin kukan yace"Mother dan Allah dan darajar Annabi Kar ki lalata rayuwarki ki lalata mana tamu,Farry har yanzu bata yi Aure ba nima haka kina tunanin idan abun nan duniya taji mutane zasu so haɗa jini damu?all this bitterness and hatred is for what?yarinyar nan Kiswa babu abunda ta tab'a yi miki na sharri iyakaci ma a kullum burin ta taga ta saka ki jin daɗi,babu abunda ta tab'a yi miki na sharri wanda zai saka ki na nementa da wannan bala'in,zamu iya gyara komai Mother we can talk to Appa together muddin zaki yarda makaman yaƙinki ki tuba a kullum Mother zaki iya faɗuwa ki mutu mai zaki cewa ubangijin mu dangane da ba dai dai ɗin ki ba?dan Allah Mother ki duba magana ta.
Wata irin dariya ta saka kafun tace"tashi ka bace mun da gani samir kafun raina ya b'acci na rasa gane abunda zanyi maka dan wallahi zan sab'a maka Sosai,get out babu kuma wani munafurci da zaka sake faɗa mun,banza mara kishin uwar sa da yan uwan sa".bai kuma cewa komai ba ya tashi ya fita a ɗakin,zama Mother tayi tace "sakaran banza,kai kuma Sagir ka ƙwantar a hankalinka koda komai nawa zai ƙare zan bayar dan ka warke"juyar da kansa yayi ya cigaba da kukan sa inda a bangare guda yake jin wata irin tsanar Kiswa sosai tana huda mada zuciya.
Kallan Farry Mother tayi tace "nasan kina tare dani a duk abinda zanyi after all dama ai komai domin ke ne sannan ina mai tabbatar miki zaki Auri Haidar ko anƙi ko anso So ki ƙwantar da hankalin ki".
Goge hawaye Farry tayi tace"amma Mother yaya sameer bai san dani a wannan abun ba after all dama Mother ai ba karya bane ban san dan cewa Yaya Sagir zaiyyi wa Kiswa fyaɗe ba "..wani irin kallo Mother ta bata kafun tace"ban fahimci inda kike Son dosa ba,Eh baki san zai mata fyaɗe ba amma dan ubanki dan Wane na bada goyan baya"
Ganin kamar Mother na neman daukar zafi ya saka Farry saurin cewa"bafa wani Abu nake nufi ba Mother ,ina so ne na koma gida ,ba yarda za'ayi na biku keda yaya Sagir After all kina buƙatar mai kawo miki rahutan cikin gidan wanda kin san Yaya sameer bazai baki ba,sannan Mother bana san na rasa aiki na amma ba wai da wani Abu ba,kinsan Appa na sanin wani Abu koda babu saka hannuna zai kwace matsayina ne a company shi yasa yanzu nake san naje gida na nuna tare nake dasu amma kamar kina da spy ne a ciki,after all kina san ki san Kiswa ta dawo ko bata dawo ba."ƙarasa maganar Farry tayi tana Addu'ar Allah yasa kar Mother ta b'ata matsala.
Shiru Mother tayi tana nazarin abun kafun tace"oya maza tashi kije gida ,ya kamata kiyi welcoming Appa ɗinki properly ."murmushi Farry tayi fahimtar abunda Mother ke nufi dan haka ta tashi ta ɗauki jakarta ta fita tana tunanin yarda zata gamsar da Appa da yaya sameer kan cewa ba'a bayan su Mother take ba..koda ta isa gida ganin motar Yaya sameer ta tabbatar mata sun dawo gida,tana shiga taci karo da Baba Baraka na arranging dining,kamar wadda tayiwa sarki ƙarya ta shiga tace "ina wuni"da mamaki Baba Baraka ta kalleta dan sabon abune wannan tsakaninta da Farry,amsawa tayi tana mai cewa sannu da zuwa,ɗan yaƙe Farry tayi kafun tace"yaya sameer fa?"
"Yana sashen sa"ta bata amsa ta cigaba da abunda take yi ,kai tsaye Farry ta nufi gurin samir dan shi ya kamata ta kama tukunna, tana shiga Kamar munafuka tayi masa sallama,yana zaune ya rufe idanunsa abun duniya duk ya ishe ta,jin muryarta ya saka shi buɗe ido ya kalleta kafun yace"Na yi imani da Allah duk wani Abu da Mother zatayi da saka hannun ki,uban mene kuma ya kawo ki inda nake?wallahi Kin bani kunya da Mamaki Farry,akan duniya da abun duniya kike Name ki zama abun tsoro.
Zubewa tayi kan gwiwowinta ta saka kuka tace"Wallahi yaya sameer ni ban da masaniya akan abun nan,na yarda muna da matsala tsakanina da Kiswa amma tunda aka saka bikinta na janye,ka tambayi Mother ɗin kaji,koda wasa basu sakani cIkin wannan abun ba dan da ace sun sakani baza'a zo nan ba,im also disappointed yaya sameer sannan na kiɗime da ban san cewa Mother ta kori Kiswa ba sai bayan na dawo nake nemanta ban ganta ba"
Kallanta da kyau sameer yayi kafun yace"ki tabbatar wannan abun ba wani game ɗinne kuka haɗo ba,domin wallahi idan na kamaki da rashin Gaskiya Faridha kiyi kuka da kanki,'dan da kaina zan miki hukunci mumuna ba sai Appa ya saka baki ba.suna cikin haka Appa ya shigo yana mai cewa"Sameer zamu iya tafiya ."ganin Farry ya saka shi cewa "Allah ya saka tunani na n cewa dake ba gaskiya bane"
Kuka ta sake rushewa dashi tana mai yi masa rantse rantse,haka nan dai shima yayi mata gargaɗi kafun suka wuce shi da samir domin sake saka cigiyar Kiswa.
*********
____________wasa wasa jikin Haidar yaso yaƙi hannu amma kasancewar sa likita ya saka bai bari sun gane ba domin kuwa shi yanzu zama bai ganshi ba,fitowar sa daga wanka kenan guy ɗin da yasaka yayi masa tracking wayar Kiswa ya kirasa ya shaida masa labari mai daɗi inda yake sanar masa da cewa sunyi tracking layin ta amma cikin minti talatin ta kashe wayarta amma kuma duk wani bayani na location ɗin ta da suke san sani sun samu.
Jikinsa har rawa yake yana shiryawa domin sun tura masa address ɗin da zai ga Kiswa,bai fadawa kowa ba ya fita domin zuwa gare ta ,mamakin da yake kai Shine wanda ta sani a gurin domin gurine mai nisa kuma downtown ,dama 'ya sani jikinsa kuma ya bashi a duk inda take zai ganta duk kuwa nisan gurin da taje,a haka ya isa Unguwan cike da zumuɗi yana mai duba address ɗin da suka tura masa, he blv sun san abunda suke a aikinsu sannan shima ya ware bakin aljihu wajen neman ta ,baga gidaje radio da tv's ba baga trackers ba,he is just meant to find her.
Yana cikin motar sa yana san gano gidan motar Saleek ta wuce sa and for real Saleek ya gani sannan ya tabbata hakan ba coincident bane,ganin yana horn bakin gate ya saka shi saurin fitowa a motarsa ya isa gurin motar tasa da gudu gudu sauri sauri,yana zuwa ya ƙwanƙwa sa masa glass,wani irin faɗuwar gaba ce ta ziyarci Saleek lokacin da idanun sa suka saka kan Haidar,tambayar da ya fara yiwa kansa ita ce"shin Haidar binsa yake?amma saboda mene?fitowa yayi domin yi masa wannan tambayar amma ga mamakinsa kafun yace wani abu Haidar ya kai masa naushi mai kyau a fuska yana faɗin"ina ka boye ta".yana ƙokarin sake kai masa wani ya riƙe hannunsa ƙam yace"kar ka kuskura,'dan mene daga ganina zaka fara kaimun duka,sannan lafiya Why are you stalking me?
Cike da fushi Haidar yace"A for Audacity ,Just the temerity And the fucking guts,ni kake tambaya ko ina stalking ɗin ka ne,nasan kasan da b'atan Kiswa sannan nayi tracking ɗinta tana nan dan haka kada ka bani wani act din banza i know kayi kidnapping ɗinta ne and im calling the police yanzun nan ".
Ɗaga kafaɗa Saleek yayi yace"suit Your Self amma kasani ni banyi kidnapping kowa ba had it been ka bini da sauki da na tausaya maka amma tunda ƙarfi zaka nuna mun ga fili ga mai doki saura sukuwa,motan sa ya buɗe zai shiga Haidar yayi saurin kama hannunsa desperately yace "kana nufin Kiswa na cikin gidan nan?"please kayi hakuri Just let me See her dan Girman ubangiji.
Kallan sa Saleek yayi lokaci guda yana mai jin kishin sa inda bangare guda kuma yake mutuƙar tausayin sa ,ya tabbatar Haidar na mutuwar san Kiswa sannan ba ya so ya zama third wheel akan abunda bazai samu ba,kallan sa yayi a karo na biyu kafun yace"bismillah ".
Buɗe motar Saleek yayi ya shiga inda ya sake horn aka buɗe masa tare suka shiga Saleek na mota Haidar wanda kejin kamar anyi masa babbar kyauta yana biye dashi a a baya yana Allah Allah yaga Kiswa ko zai ji daɗi a rayuwarsa.
Chuchujay ✍️
08130229878
[6/4, 11:01 PM] Chuchujay✍️: 💥KISWAH💥
(Surrogacy was the cause)
By
Chuchu jay
Book1⃣
Page 2⃣1⃣
__________Koda suka shiga ma'aikatan gidan ne kawai a falo waɗan da suka gaida su cike da girmamawa,kallan Haidar dake raba ido yana neman inda kiswa zata fito Saleek yayi kafun yace masa"ka zauna bari nayi maka magana da ita ko zata gan ka cos kasan nayi gaban kai na ne babu yardar ta,idan kuma baza ta ganka ba babu abunda zan iya sai dai in na baka hakuri..murmushi Haidar yayi yace "i doubt if she will reject me".kallan sa kawai Saleek yayi ya juya dan zuwa yi mata magana duk da yasan yayi mata laifi tunda ta roƙe sa kar wanda yasan tana nan,but its not his fault Haidar yazo ne using his own method wanda koda Shine a stead ɗin sa shima haka zaiyyi ,Allah kaɗai yasan abunda guy ɗin yayi going through saboda soyayyar sa is Top notch..tsaye Saleek yayi a bakin ƙofarta yana debating da zuciyarsa kafun yayi ta maza ya ƙwanƙwasa mata,Knocking ɗaya yayi tace Wane,amsata yayi yace Shine,jin muryarsa ya saka ta kimtsa kanta tace"Bismillah".
Kamar yayi wa sarki karya haka ya shiga ɗakin ,gaishe shi tayi ya amsa mata yana mai tunanin yarda zata dauki maganar kafun yace "na dawo kawo miki kayan ki ne da Baba Baraka ta kawo mun office so ina tunanin ko zaki buƙaci wani abu shi yasa nazo sannan in the process nayi miki laifi hope za'a yi mun afuwa,ina dawowa na tarar da Haidar bakin gidan nan and i swear bani na faɗa masa kina nan ba,nima i Just saw him ina shirin shigowa and he look Like a mess ,a yarda na ganshi kuma i had no option dole na bar shi ya shigo,but idan kince baza ki ganshi ba bani da matsala dama i told him idan baki yarda ba zai haƙuri ne".. Shiru tayi tana kallan sa kafun tace"yana ina yanzun?"."yana falo"ya bata amsa yana addu'ar Allah yasa kar tace bazata ganshi ba,it shouldn't be Like that,dan Shiru tayi kafin tace"its okay muje na ganshi".
Koda ta fita ya juya baya yana Kallon ta inda zata fito,gyaran murya Saleek yayi yace"oga sir ga Madam ɗin ka fa"juyowa Haidar yayi da sauri take idanunsa suka cika da hawaye lokacin da ya sauke su akanta,bai san lokacin da ya ɗaga kafafun sa ba ya isa gareta kafun tayi Aune ya haɗe ta da jikin sa cikin runguma wadda yake ji kamar za'a ƙwace masa ita,ba tayi zato ba Batayi tsammani ba haka zalika Saleek wanda abun yazowa a bazata,tana ƙokarin kwacewa ya riƙeta yace"please Just a Moment ,"Ajiyar zuciya ya sauke kafun ya raba jikin sa da nata ya kalleta yace "mai yasa kika yi mun haka?,kinsan Wane irin hali na shiga da ban ganki ba,i know kina fushi dani Shine ya saka baki kirani ba,im sorry about abunda na faɗa miki ,sharrin shaiɗan ne and na miki alƙawari bazan ƙara miki zargi irin wannan ba so please kar ki bani wahala irin wannan.kallan sa take wani irin san sa na fizgar ta,ganin yarda baki ɗaya ya rame dare ɗaya kawai ya bata tsoro,ɗan murmushi tayi tace"ka zauna muyi magana"babu musu ya zauna,ganin cewa Haidar da Kiswa sun manta da Saleek ya na Falon ne ya saka shi jejely barin Falon wani Abu nayi masa yawo a ƙirji,sunnan Allah kawai yake kira domin wani irin kishin ta ya tsinci kansa ciki ,ji yake zuciyarsa nayi masa wani irin suka,amma sanin baya da hurumin da zaiyyi wannan kishin a kanta ya lallashi zuciyar sa ya roƙi Allah ya sassauta masa kishi akan abunda ba nasa ba.
Zama Haidar yayi yana mai jin kamar zai buɗe ido yaga mafarki yake,zama itama tayi tana kallan yarda baki ɗayan sa ya kasa nutsuwa,Ajiyar zuciya tayi tace"yarda kazo and da yarda nake kallanka a yanzu nasan kasan komai da ya faru and im sorry ban kira ka ba domin bana fatan ka ganni cikin halin da nake ciki,and ban kira ka ba bayan nan saboda bana san na tada maka hankali"."ai rashin kiran Shine yafi komai tada min hankali baby cos gwanda nasan inda kike da ace Kin boye ban sani ba ,im sorry about komai sannan ina san a Rayuwar nan ace na zama a gefen ki a yanayi mai kyau ko mara kyau domin kuwa Alaƙa na dake is for better and worst ,don't do this to me ever please,nasan kuma abunda na faɗa miki kan Saleek ne yasaka, kar ki ga laifina kece burina ,duk wani ɗa namiji da zan gani a tare dake zuciyata sai tayi skipping beat musamman kuma namiji kamar Saleek,ta ko ina haɗaɗan gaye ne wanda mace zata ji a kallo ɗaya yayi mata Why wont i be scared.ɗan murmushi tayi tace"tsakanina da Saleek Pure relationship ne wanda babu wani tunani mara kyau a cikin sa,yana da kirki he is just very kind to me sannan mutum ne shi wanda na ɗauke sa kamar ɗan uwa haka zalika shima ya ɗauke ni haka,kai ma ka sani i will never be moved By any man When i have you,kai nake so kai na zaba idan kuma za'a sake dawo da hannun agogo baya i will still choose you,you're my muse in love and everything,i will never abandon Your love for another ya kamata ace tuntuni ka san wannan,so please ka daina sakawa kanka insecurity akan abunda ba haka yake ba,sannan da kake cewa kallo ɗaya mace zatayi wa Saleek ya tafi da ita kai kuma fa?ka dai san Saleek ba kyau ya fika ba iya kaci ace ya fika kama da play boys,you're so Handsome My Sugar"ƙarasa maganar tayi tana mai kashe masa ido guda ɗaya.
Haɗe lebensa yayi guri ɗaya kafun ya sake su ya Faɗaɗa fara'arsa yace"dont do that gaban wasu cos you look cute,so yanzu dai kije ki ɗauko belongings ɗin ki mu tafi dan daga nan gidan mu zaki je,ba zaki koma gidan nan ba".ɗan shiru tayi kafun tace "bazan bika gidan ku ba gaskiya ,idan Mama taji ma raina zai b'aci i will be okay here"....kafun ya sake cewa wani abu sukaji ana buga ƙofar falo,tana ƙokarin tashi Saleek ya fito yana mai faɗin"i will get it".
Koda yaje ya buɗe mai gadin gidan ne ya duƙa cike da girmamawa yace"Alhaji kayi baƙine nayi tunanin ma na Alhaji babban ne to amma sai suka ce kai suke nema".da mamaki Saleek yace ni kuma?
"Eh kai kuwa muke nema"muryar Appa da ya kasa hakura ya tako ta karaɗe kunnuwan su,wani irln faɗuwar gaba ne ta ziyarci Kiswa ,tashi tayi daga zaunen da take tace "Appa?"jin tace Appa yasa Saleek cewa "bismillah ku shigo,"babu musu Appa ya shigo bakin sa ɗauke da sallama yayin da yaya sameer ke bayan sa shima yana mai yin sallama ɗin,muzurai Kiswa ta fara da ido tana mai cewa"sannu da zuwa Appa,durƙusa wa tayi domin gaida shi,saurin binta yayi ya ɗagota yana mai kaɗa mata kai yace"No my daughter ina mai mutuƙar jin kunyar abunda ya faru dake amma ina mai jin babu daɗi daya kasance bani kika fara kira kika sanar wa ba duk da ina matsayin mahaifinki".kallan Haidar yayi yace "tana gurin ka kenan,kaima baka kyauta ba domin ni ya kamata ka kira".duƙar da kai Haidar yayi yana mai gaidashi kafun yace"nima Appa zuwa na kenan dan sai da na saka ma a kayi mun tracking ɗin ta,amma wanda ya taimake ta gashi nan,Saleek ogan ta gurin aiki".Gaida Appa Saleek yayi inda Appa ɗin ya bisa da kallo domin yau ne ya fara ganin sa duk da kuwa mahaifinsa abokin sa ne,koda suka so haɗa alaƙa tsakanin yaran su shi baisan Saleek ba amma yana da yaƙi nin duk ɗan da za'ace daga Alhaji Basil yake to mai tarbiyya ne wanda dalilin da yasa yaso su haɗa Auratayya.cike da mutunci Appa ya amsa mishi kafun yace"nagode sosai da abunda kayi wa Kiswa im so glad hannunka ta faɗo thank you Allah yayi maka albarka,muma tracking ɗin nata mukayi,ina gayyatar ka gidan mu for saturday lunch ina fatan kuma baza kaƙi amsa gayyata ta ba".murmushi Saleek yayi yace"insha Allahu Appa ,"kafun ya juya suka gaisa da yaya sameer inda Haidar ma ya miƙa masa hannu suka gaisa.
Duk yarda zuciyar Kiswa ke assasa mata ƙin komawa gida kasa nuna wa Appa tayi lokacin da ya mata izinin ta ƙwaso kayanta su wuce,kula da Appa yayi da rashin jin daɗin komawa gidan ya saka shi cewa"ki ƙwantar da hankali ki ,Mother da kika gani bata gida dan Aure na da ita ya ƙare,shima babban shaɗanin yaran na sallama mata shi dan haka ki saki jikin ki,gida na mahaifin ki ne kuma zanyi waje da