Showing 27001 words to 30000 words out of 50778 words

Chapter 10 - KISWA Book Complete Document by Chuchujay.txt

29 Nov 2024

2575

yarda kike loyal a soyayyar ki,haka nake a abotata so lunch during lunch time and Its on me".


Murmushi kawai tayi tace "thank you"still awkwardly domin kuwa abun baki ɗaya sabo ta tsincesa,ta kasa yarda wannan arrogant man ɗin ne a gabanta haka,koma dai mene tasan she will need to be very careful,sallama tayi masa ta tashi dan fita,tana ƙoƙarin fita Khalipha yana shigowa,matsa mata yayi ta wuce tana mai gaida sa inda ya amsa cike da fara'a da sakin fuska,binta yayi da ido har saida ta b'ace Kafun ya kulle ƙofar ya shigo ciki yana mai faɗin"mutumina ka ƙyaleni na gwada sa'ata kan Kiswa dan Allah alaji,babyn nan ta kashe ni so nake koda ba Serious abu ba a ɗan wana".


Haɗe rai sosai Saleek yayi yace "a wana mene?bana san iskanci fa Khalipha,ba tun yau ba nake faɗa maka Kiswa ba Ko wacce irin mace bace kaje dai Chan ka nemo yan matan ka marasa nutsuwa amma banda wannan sannan idan baka sani ba na sanar da kai cewa She's in a Serious relationship sannan She's so loyal about it dan Ko kaje kace kana santa a banza dan haka ka riƙe sauran mutuncinka da take gani mu zauna lafiya.


Zama khalipa yayi kan desk ɗin sa yace "ita da take Serious relationship sai kayi yaya?"


"Nayi yaya kuwa?dame fa?"dariya Khaleepa ya saka sosai yace "mutumina kenan nasan dai akwai wata a ƙasa kuma idan tayi tsami zamuji "ƴar waƙa ya fara masa ta zolaya,jifan sa Saleek ya fara da files ɗin sa yana mai faɗa masa he's fired!


Dariya khalipa ya fita yanayi yana mai faɗin"mutu ka raba ɗan nan Koma bazan daina faɗa maka you're in love ba"


Hannu Saleek ya saka a baki yayi ƴar dariya yana mai shafa kansa yana maida maganar Khalipha a kansa,Kaɗa kai yayi a fili yace "No Babu ma yarda za'ayi haka ya faru no",files ɗin da ya jefi khalipa da ya kwashe ya fara duba su da kawar da tunaninsa.


Kamar yarda ya nemi suje lunch hakan ya faru inda baki ɗaya cikin rashin sabo dashi taci abincin yayin da shi kuma yake mata hira cikin san ta saki Jiki dashi,wayarta da tayi ringing ne ta saka ta dakatawa tana mai faɗin "excuse me "kafun ta kara wayar a kunne tace"Assalamu alaikum hayatee"


Take bite ɗin da Saleek ya saka a bakin sa yana tauna ya dakata,wata irin shagwababiyar murya da tayi magana da ita ce ta dake shi,he Just cant blv a gaban sa dan yarda ta cigaba da wayar kamar ma baya gabanta,cigaba yayi da cin abincinsa a hankali yana sauraran yarda take jefawa Haidar kalaman soyayya,ya kasa yarda wai Kiswa ce.


Sai bayan ta gama wayar ne tayi realizing wai a gaban Saleek take,take wata kunya ta lullube ta ta fara kame kame,murmushi yayi yace"yanzu ne kike jin kunya ta bayan Kin gama narkewa a waya,dole nayi jotting down friend ɗina idan babe ɗinta ya kira ta mantawa take da kowa a gabanta"


Sosai taji kunyarsa ta kamata dan kamar yarda ya faɗa indai akan Haidar ne ta wuce nan,haka suka gama cin abinci suka koma office a tare yana ta janta da hira wanda bata taba expecting yama iya ba.






Chuchujay


08130229878
[5/16, 10:55 PM] Chuchujay✍️: 💥KISWAH💥


(Surrogacy was the cause)


Na


Chuchujay


Book1⃣


Page1⃣3⃣


___________karfe biyar na yamma Haidar yazo suka wuce da Kiswa gida bisa umarnin Ummi tunda basu samu zuwa Boutique ɗin ba da rana,da fari taso tayi masa gardama akan zuwan amma da ya fita da baki ya lallabata ya kuma sake tabbatar mata da bazata samu matsala ba indai daga gurin Ummi ne,da haka ta yarda tabi bayan sa a motar ta suka tafi tare .


Koda suka isa gidan su Haidar Babu abunda gaban ta yake sai faɗuwa cos magane ne na zata ga sirikarta for the first time wanda abune take jinta very weird amma kasancewar Ummi ta saka tazo ya zama dole ta zo ɗin domin nuna girmamawar ta a gareta,rawar kan da Haidar yake Kiswan sa ta amsa kiran Ummi kuwa ba karami bane cos koda suka shiga Ummi bata falon ɗakin ta yayi Kai tsaye dan kiranta domin yasan tana ciki,ita dai Kiswa zaune tayi hannayen ta nata zufa yayin da a bangare guda kuwa kafun kace ƙwabo gabanta ya shiryu da kayan tabawa ,tana wannan zaman Tasleem ta shigo bakinta da sallama,da mamaki ta kalli Kiswa dan bata tsammanin ta sannan ba sai an faɗa mata ita bace duk da kuwa sau ɗaya suka taba haɗuwa,da fara'arta ta ƙaraso ciki tana cewa"wa nake gani kamar Auntyn mu"


Kallan ta Kiswa tayi inda itama kallo ɗaya ta gane ta,wata irin kunya ce ta kamata dan tun abunda ya faru tsakanin su basu sake haɗuwa ba,murmushin dole tayi tace "ina wuni"dariya Tasleem tasa tace "ina wuni ?"Kina matar yayan nawa to be kike faɗawa ƙanwarki ina wuni,apart from that nasan kilan ma kin girme ni!.ƙare maganar Tasleem tayi tana mai zama kusa da Kiswa.


Cike da fara'a Kiswa tace "well age never matters sannan bana tunanin gaisuwa tsakanin ƙarami ne zuwa babba,Babu laifi idan shima babban ya gaida ƙarami,thats exactly what respect mean"


"Exactly my dear"muryar Ummi dake fitowa daga ɗakinta ya karaɗe gurin,saurin saukowa Kiswa tayi daga kan kujera ta zauna a ƙasa ,da sauri Haidar ya zo gurin ta yana cewa"babe mene Hakan"?


Takowa Ummi tayi tana mai cewa "part of respect my dear"gaban Kiswa da ta kasa dagowa da idanta ta ƙaraso ta kama hannunta ta zaunar kan kujera tace "im not complaining Kiswa ki zauna kan kujera"


Murmushi Kiswa tayi tace"nagode ummi ,ina wuni".ɗaya gefenta Ummi ta samu ta zauna kafun ta kama hannunta tana mai cewa "ina wuni yarinyata ,ya aiki ya kuma fama da Handsome yarona dan Nasan anayi".


Murmushi kawai kiswa tayi ta kasa cewa komai saboda wani irin nauyin Ummi da take ji,itama Ummi ɗin ta fuskanci haka, haka nan taji Kiswa ta shiga ranta sosai dan ganinta ma yafi jinta ,kallan Tasleem da Haidar tayi tace "ku ɗan bamu guri mu gana da ƴarinyata,we need privacy"


Ɗaga hannu Haidar yayi yace"of course bari nayi using damar naje na ɗan watsa ruwa,Ummi ga amanar Kiswa nan na baki"dariya Tasleem dake ƙokarin boye kishinta tayi tana mai cewa"Brother yarda ka barwa Ummi ita ni dai nasan haka zaka sameta".dariya ya saka kafun ya nufi hanyar fita a falan Ummi domin zuwa ya watsa ruwa yayin da Tasleem ma ta wuce tana mai jaddadawa Kiswa kan idan tana bukatar wani abu tayi mata maganaa zata zo Babu bata lokaci,da ƙwarin Gwiwa Tasleem ta fita tana tsoran kar zuciyar ta ta karaya ta fashe da kuka a gurin ,kamar jira take kuwa tana shiga ɗakinta ta fashe da wani irin kuka Mai cin rai tana mai jin zuciyarta kamar zata fita a kirjinta ,a hankali ta fara shafa saitin zuciyar ta tana mai Addua a hankali tana mai cewa"'ya Allah help me ,ka taimaka mun ka cire mun san yaya Haidar indai babu alheri a cikinta,Allah 'ya sani ina san shi ba domin kuɗirin mahaifiyata ba sai domin Allah amma nasan jelar raƙumi tayi nesa da ƙasa Allah ka kawo mun ɗauki "a haka ta ringa lallashin kanta kafun ta gangara kan gadonta ta ƙwanta ta rumtse idanunta tana mai ambatan Allah,ba sai wani ya faɗa mata ba,Kiswa ta haɗu ta Ko ina ta yarda babu ma yarda za'ayi ta haɗa kanta da ita,She's not in her lane a kyau ,class da komai ma kuma tasan idan aka ajeta aka aje Kiswa to Kiswa zai zaba sau dubu,haka nan ta ringa bawa zuciyarta hakuri da addu'ar fin ƙarfinta.


**


__Bayan tafiyar Haidar da Tasleem sai ya zamana daga Kiswa Sai ummi,shiru Ummi na karantar ta yayin da ita kuma ta kasa haɗa ido da ita,murmushi ummi tayi da ta fahimci hakan,gyaran murya tayi tace "ni uwace mai san kanta muddin abu ya haɗa da Haidar,zan zab'esa fiye da komai a rayuwa sannan zanyi hakan over and over again koda kuwa abun zai zammar mun matsala,shi Kaɗai Allah ya malaka mun sannan wahalar da aka sha kafun samun sa abune wanda bana san maganar sa a yanzu ya zama labari,ina da san Kai yarda baki tunani akan haidar domin kuwa shi yasa na zabeki kan Faridha domin kuwa ke ya zab'a ba ita ba sannan ni abunda yake so shi nake sannan sai gashi nima kin shiga raina duk da ba wai muna status ɗaya bane,magana ɗaya cikin biyu nake san yi dake,ga Haidar nan please dont hurt or break his heart domin kuwa ya dauki soyayyar duniya ya ɗora miki,sannan abu na biyu indai pure kike ban damu da maganar wani ba a kanki musamman ita Aunt ɗinki da kike gurinta wannan matar mean no Good,bazan ce dole sai naji ya zamantakewar ku take ba dan nima ba mutum bace mai yaɗa sirrin gidana ga wani ba dan haka na wani bai dameni dole sai naji ba,but please be careful a duk inda kike domin kuwa in wani abu ya sameki zamu shiga matsala domin idan Haidar ya shiga daga ni har Baban sa mun shiga idan kuma kika shiga kinga dole shi ma ya shiga ,sauran magana kuma ta maza ce ,Baban Haidar zaije ya samu shi kawunki idan yaso duk abunda za'ayi sai ayi, but definitely zanyi binciken background ɗinki duk da nasa ko da negative abu aka samu kanki babu mai sakewa Haidar ra'ayi akan ki ,but still ina san nasan wacece ke its My right"gyara zama tayi tana mai mayar da hankalinta kan wayarta kafun tace "so wacce kala kika fi so"


Cike da confusion na rashin gane tambayar Kiswa tace "Na'am?"ɗaga gira guda mami tayi tace"Uhum ya kamata nasan likes ɗinki da dislikes ɗinki saboda idan ƙawayena na hirar taste ɗin sirikansu da siyan musu abunda suke so nima nayi bragging and hope kina da classy taste sannan bazan boye miki ba i dont like it yarda kike wannan sunkuyar da kan ni ba surukar da bace ta yanzu ce dan ni so nake matar Haidar ta zama kamar ƙawata dan haka already na siya miki VIP membership a Spa ɗin danake zuwa and nayi mana booking saturday make sure kinyi squeezing idan ma Kina da abunyi cos na riga nafara anticipating ma frnds ɗina zan kawo musu in Law na 9 sharp,wanne car kike driving By the way?


Cikin rashin sakewa da abunda Ummi ta faɗa na Tayi mata Register na membership tace "im driving 306 and Ummi please ba sai Kin mun reg na membership ba yayi yawa" kallanta Ummi tayi tana san maganar 306 ɗin da tace tana ja ya gama blending a kanta kafun tace"306? Kice mun ke Haidar ya gani da ita ya siya,Babu irin fadan da banyi ba akan ya daina embarrassing kansa da motar nan ,ga nan motocinsa worthing many millions amma ya aje su gida,but yea im not complaining dole idan kika shigo ki daina jan 306 dole kinga shima ya hakura amma yanzu bazan maku dole ba,zan aiko driver yazo ya daukeki ranar saturday wanda kinga yana nufin bana san gardama akan maganar ,"


Dole Kiswa ta bar mata ta cigaba da yi mata godiya yayin da ta dan saki jikinta da ita tana faɗa mata likes and dislikes ɗinta kamar yarda ta buƙata,suna cikin hakan Haidar ya fito cikin jallabiya Navy blue yana ta zuba kamshi,zama yayi yace "yauwa menene kyawawan yan matan da nake bala'in so guda biyu a rayuwata suke tattaunawa cikin nishaɗi Haka"?


Yar dariya suka saka a tare inda Ummi ta bashi amsa da"magance ta mata biyu dan haka baza kaji ba"murmushi yayi yana mai jin daɗi a zuciyar sa Ummi ta karb'i Kiswa hannu biyu biyu sannan Kiswa ɗin Ma ta fara sakin jiki da ita ,abu guda ɗayane zatayi fama dashi wanda Shine rich life style ɗin Ummi da yanayin yarda suke da rich ƙawayen ta kowa yana san yace shine na gaba.a haka ranar Kiswa ta shashance gidan ko tace Ummi ta riƙe ta har sai da taci dinner duk da kuwa hankalinta yayi gida although tasan ba wanda zai ce mata dan me ko daga ina take amma a hankalinta tasan tabbas bai kamata tana gidan ba har dinner amma ta kula Ummi mutum ce wadda bata san kace mata a'a dan haka ta yi hakuri har after Dinner ɗin wadda Baba ya hallarta yayin da Shima ya ringa yaban ta ta ko ina .


Lokacin da tazo tafiya baki ɗayan su suka rakota har compound inda Ummi ke sake jaddada mata fitar su nan da Ƙwana huɗu,


Fafur Haidar yaƙi barin ta ta tafi ita Kaɗai duk da kuwa ba a mota ɗaya zasu tafi ba,Baba ma ya saka baki akan lallai Haidar ɗin ya bita a baya,murmushi kawai kiswa take domin kuwa wannan soyayyar da suke nuna mata cikin ɗan ƙanƙanin lokacin nan bama tasan inda zata kaita ba,godewa Allah tayi a zuciyarta tana"Addu'ar kawar da fitina a cikin ta"har gida ya raka ta sannan bai wuce ba sai da yaga ta shiga gida tukkun ya juya motar sa ya nufi gida.


Tana shiga ta faka motarta ta shiga ta ɗauki system ɗin ta ta shiga gida tana mai jin duk wata damuwa tata ta yaye mata,Babu wata fargabar za'ace ina kikaje kika kai haka tunda normally bata Kai bayan sallar isha'i a waje sannan da Mama ke gidan dole zata yi mata faɗa akan taje gidan surukai ta zauna Babu kunya amma Mother kuwa koda ɗakin saurayi zataje ta kwana Babu Abunda zai dameta iya kace ma ta zama mutum ta farko da zata fara yayatata,tana shiga Falon dake na kowa wanda yake farkon sashen gidan tayi turus ganin Mother zaune a kan kujera ta kunna Tv tana kallo,sallama tayi tace "sannu da gida Mother ina wuni" ?


Wani irin banzan Kallo Mother tayi mata kafun tace"daga gidan uban wa kike karfe takwas na dare sannan zaki shigo gida Kina daga hanci kamar na ubanki,Kina san ki nuna ke kinfi uwarki ko"?


Da fari kamar ta wuce ta bata ce mata komai ba sai kuma taga Babu amfanin ta wuce ta ɗin gwanda ta bata amsa dai dai tata ,dan haka ta samu guri ta zauna tace "daga gurin Aiki Haidar yazo ya ɗaukeni akan Ummin sa na san ganina ,wurin yamma dai haka mukaje gidan ,baki ga irin soyayyar da suka nuna mun ba dan Ummi har Membership ta siya mun a inda take Spa ranar saturday za muje tare na tabbatar kuma gurine na mata masu aji da ji da kansu,sannan Ummi ta karbe ni hannu biyu yanzu haka tace magana ba za'a barwa mata ba ta maza ce,and Yes kafun na manta hakan yana nufin tayi rejecting offer ɗin ki ne ta zab'eni zabin ɗanta ,dan Allah Mother ba sai Kin kirata ba ta daina ganin sauran mutuncin mu ba,sannan kiyi hakuri nayi dare bazan Sake ba banyi tunanin zan saki rashin bacci ba saboda ban dawo ba,bari naje na watsa ruwa ,"tashi tayi dan barin gurin taji an kamo mata hannu,juyowa tayi taga Farry tana faman huci kamar wata zakanya kafun tace"how dare you kike faɗawa Mother magana haka".


Wani irin kallo Kiswa ta bata kafun ta kwace hannunta cikin muryarta Babu zafi tace"how dare you Ask me that stupid ,lame,idiotic ,useless question?"


Kama ƙugu Farry tayi tace"na tambaye ki ɗin sannan ki bata hakuri idan kuma ba haka ba wallahi ki gane kuɗar ki"


Kallanta Kiswa tayi tana san karyata Wai tare sukayi yarinta mai daɗi,ta rasa ina aka kai mata Farry mai nuna tana ƙaunarta sannan mai shigar mata faɗa muddin Mother nayi mata akan rashin Gaskia sai gashi a yau wai tare suka haɗe Kai ake mata cin kashi wanda bata shirya bar musu ba dolene ta ƙwatarwa kanta yanci kafun su ƙwace mata.bata Sake ce musu komai ba ta bar gurin tana mai jiyo Farry na fada mata maganganu mara sa daɗi,.kamo Farry Mother tayi tace "ki ƙwantar da hankalin ki Farry mana dani take maganar wallahi,na fita iya Shege sannan duk abunda take ji dashi nawa ya ninka"


Tashi sukayi kowa yayi ɗanƙin sa dan kimtsawa .


Kai tsaye Kiswa na shiga ɗakinta ta cire kayanta ta faɗa bathroom dan yin wanka,tana jin alamun mutum a ɗakin ta tunanin kila Farry ce tazo neman wani balain ya saka ta cigaba da wankanta,bayan ta gama ta sako bathrobe dinta fara ta fito tana tunanin da wadda Farry ta shigo amma ga mamakinta sai ganin 'Yaya Sageer tayi kwance kan gadonta daga shi sai boxers da singlet,wani irin faɗuwa gabanta yayi, mazewa tayi tana daga bakin kofar bathroom ɗin tace"yaya Sagir lafiya?,ko kayi batan hanya ne ka shigo nan i mean a kallan gadan ma zaka gane ba naka bane".


Tasowa yayi ya zauna yana binta da wani mayen kallo yayin da ita kuma ta Sake tamke igiyar bathrobe ɗinta ganin kallan da yake mata.


Duba agogon bangon ta yayi yace"well lafiya Baby sannan ba batan hanya nayi ba inda nake san zuwa hanya ta kawoni kuma ina fatan a bani hanyar da nake san bi nabi domin kuwa dole ne na samu,".ƙaramar dariya tayi tana san gane inda ya dosa wanda idan hasashenta yana kai mata dai dai lalata yake san yayi da ita ,waiyazubillah.riƙe handle ɗin bayin tayi gam tace"Yaya Sagir ban fahimci abunda kake cewa ba sannan bana fatan na fahimta,zanyi shiru Babu wanda zaiji zuwan nan naka amma fa sai dai in idan kaso haka ka fitar mun a ɗaki tun ina da sauran girma a gareka".


Dariya yayi yar ƙarama yace"Kiswa kenan,kinsan irin wahalar dana sha wajen danne duk wata sha'awa taki da nake ji? ,kinsa ya na danne na daure nake kiranki ƙanwata duk da yarda nake ji akanki,?kinsan ya nake ji idan naji Kina ambaton wani banza Chan har Kina wani faɗa akansa?duk baki da idea dan haka kar ki fara mun wasu maganganu yanzun nan,i will have sex with you idan kina so ko ba kya so,dole ne na sauke craves ɗina akanki yau ko me za'ayi ,and trust me Babu mai ji after all ni zan Aureki domin dare ɗaya bazai ɗauke mun buƙatata akan ki ba".






TBC


Chuchujay ✍️


08130229878


Kuyi hakuri kunjini sai a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login