Showing 39001 words to 42000 words out of 50778 words
sai na samu abunda nake so a gurinki koda kuwa da ƙarfine,domin masu cetan naki basa nan,Appa yayi tafiya,shi kuma wanca mai kankanbar shi yayanki ne nasan yanzu haka yana Chan ya baje kan gado dan maganin baccin da yaci a abinci nasan ya Fara aiki"
Babu abunda take karantowa a zuciyarta sai"lailah'ailla anta subhanaka inni kuntu minza'zzalimin"tayi yafi ba adadi dan tasan Allah kaɗai zai ƙwaceta hannunsa musamman da hasashenta ya bata cewa haɗakar ba tashi bace shi kaɗai har da Mother da Farry,baya ta cigaba da ja har sai da takai ƙarshen bangon kusa da bed side drawer ɗinta yayin da ya mara mata baya yayi mata cage da jikinsa,rufe idanunta tayi tsam lokaci da taji hannu sa a wuyanta yana shafawa ,rumtse idanunta tayi sosai hawaye na fitowa ta cikinsu kafun tace"Yaya sagir kaji tsoran Allah,duk wani abu da kake tunanin zakayi mun yanzu Allah yana kallanka kuma bazai barka ba domin zalunci ne ,ba zai tashi tambayar ka ba sai lokacin da ka manta ka sakankance , ka tausaya mun ko dan maraicina,babu abunda nake binka dashi a rayuwa sai alheri,dan Allah kada ka bini da sharri".
Dukan ginin gefenta yayi ya damƙe hannunsa cike da bacin rai yace"kar ki Fara faɗa mun wannan a wannan gejin da nake wanda bazan iya huƙuri dake ba,please Kiswa na roƙeki,kar ki bani wahala,kiyi mun wannan alfarmar ko dan yan uwantakar dake tsakanin mu,wallahi na miki alkwarin cikin satin nan zan Aureki, kinga babu wani tunani na zaki fuskanci wulaƙancin Namiji,after all Nine na sanki ƴa mace kuma zan riƙe miki sirrinki.
Abubuwan da suka haɗar mata sun haɗo ne da ƙyama,takaici da baƙin ciki,yawun da ke mata ɗaci a bakinta ta tattaro ta watsa masa a fuska tana mai faɗin"Allah ya tsinewa Aurenka da rufun asirinka ,To hell with you ."da wani irin zafin yanayi ya ɗauketa da mari ya Fara ƙokarin cire bathrobe ɗin dake jikin ta,kuka take sosai tana ihu wanda yaci ace wani a gidan ya farka ya kawo mata ɗauki,kokawa suka fara inda take mayar masa da iyakacin ƙarfin ta,kamar ance ta kalli Kan bedside ɗinta lokacin da yake faman sunsuna mata wuyanta,fitilar kan bedside din ta ƙarfe idanunta suka sauka akai inda take wata idea ta faɗo mata,cikin zafin nama ta saka hannunta ta ɗauko ta buga masa akai,wata wahalaliyar ƙara ya saki ya ja baya dafe gurin yayi yaga jini,gadan gadan yayi kanta yana mai fadin"wallahi sai kinci ubanki,kafun ya ƙaraso ta sake ɗaga lantern ta saita gaban shi da ke jansa yayi iskanci da ita ta buga masa iya ƙarfinta,wata iriyar azababbar ihu ya saki wanda ya dau ƙuwa a gidan,gefe Kiswa ta tsaya tana kallan yarda ya riƙe gabansa yana ihu ga jini da take gani yana fita,ko kaɗan bata ji tausayin sa ba,cike da ƙarfin hali ta ɗauki wayarta tana mai ƙokarin kiran layin Appa amma bata shiga,ƙarar ƙwankwasa ƙofarta ya saka ta rab'ewa ta buɗe jikinta na ƙyarma ƙaɗan kaɗan,mother ta shigo da saurin ta tana mai cewa "me kika yi masa ni juwairiyyah "kafun tace wani abu sai ga Farry ma tazo da gudun ta tana mai cewa "lafiya?"turus tayi lokacin da idanunta suka sauka kan sagir wanda ke faman ihu hannunsa bisa gabansa wanda ke faman jini,kafun kuma kace mene sai dif ya ɗauke a sume.
Wani irin ihu Mother ta saka tana mai cewa ta kasheshi Faridha ta kashe mun ɗa maza ƙira sameer,cikin kuka Farry tace"mother Kin manta ɗazu ƙinyi drugging abincin sa ,babu abunda zamuyi ya farka a yanayin da yake bari na kira Mai gadi ya taimaka mu kaishi asibiti"fita Farry tayi da gudu yayin da mother ta taso kan Kiswa wadda babu dana sani ko tausayi a zuciyarta face mamaki tunda ai yaci ace ihunta ya kawo su amma basu zo ba sai da yayi nashi ,hakan ya tabbatar mata da cewa tare suke.
Mari mother ta ɗauke ta dashi tana mai cewa"ke azzaluma ce,ke muguwa ce kiswa tuntuni na sani amma yau kika tabbatar mun,amma anzo ƙarshe ,kama hannunta tayi tace "zo ki bar gidan nan,wallahi sai Kin tafi,sannan idan Sagir ya mutu wallahi kema sai Kin mutu"hanunta ta fara ja zuwa hanyar waje ,tirjewa Kiswa ta fara ganin ko ɗan ƙwali babu akanta,cikin muryar rashin nadama tace "Mother ki bari na ɗauki mukullin motata sannan nasaka kaya mana,ki kalleni 'fa babu ko ɗan ƙwali kaina".
"Wallahi tunda na jawoki ko babu kayane a jikinki sai kin bar gidan nan,sannan a duk inda kike ki shirya ƙarbar shammaci dan wallahi sai na kulleki"mother ta faɗa yayin da ta cigaba da jan Kiswa wadda a wannan gejin idanunta suka fara zubar hawaye sakamakon rashin imanin da Mother ke gwada mata.
Koda suka isa bakin gate Mai gadi ma yana ƙokarin shiga ciki domin taimaka musu a fito da sagir a kaishi asibiti,buɗe ƙofar gate ɗin mother tayi ta watsa Kiswa wadda taji abun kamar a mafarki,kallan kanta tayi daga sama har ƙasa ,bathrobe ɗinta iya gwiwace sannan kanta Babu ɗan kwalli ,wanne hotel zata fara nufa a haka ?ita ba mai ƙawaye bace domin a rayuwarta Farry ta ɗauka ƙawarta yanzu kuma ga inda takaisu,Haidar ya faɗo mata,kallan kanta ta kumayi tayi saurin kaɗa kai,bazata taba bari ya ganta cikin yanayi irin wannan ba ,maƙiyinta ma bazata so taganshi haka ba,tana tsaye tana wannan jimamin ga waya dai a hannunta tarasa wanda zata kira,SALEEK?Shine mutum na farko da ya faɗo mata ,kira ɗaya tayi masa ya ɗaga,rasa abun cewa tayi kawai ta fashe masa da kuka,cike da tashin hankali yace"Kiswa lafiya?"cikin kuka tace "ina buƙatar taimakon ka idan zan samu please,zan kunna maka location kazo inda nake indai ban taƙura maka ba,and idan ba damuwa ka sama mun koda hijab ne.
Cikin tashin hankali ya tashi daga kwancen da yake ya ɗauki mukullin motar sa yace"gani nan yanzun nan ,im coming."tana kashe wayan ta kunna masa location ta kuma gefe ta rab'e tana mai jin tsoro ganin yarda garin yayi shiru ga dare , dama koda rana unguwar na da ƙarancin Mutane,addu'a kawai take a zuciyarta Allah ya tsareta daga sharrin wajen da take,tana wannan tsayuwar Su mother suka fito inda Aka kulle gidan baki ɗaya gudun kar ta shiga,haka nan tana wannan tsayuwar Jiran Saleek motar sa ta danno gurin,wani irin ajiyar zuciya ta sauke tana mai hamdala ,da mutuƙar damuwa ya fito a motansa hannunsa ɗauke da Hijab ɗin Maman shi cos Amatul'islam bata da hijab a gidan tunda bama ta gidan bai ɗaya,kafun ya fara tambayarta me ya faru hijab ɗin ya miƙa mata ya juya baya ,Bayan ta saka tace masa ta gama sai lokacinne ya juyo yana tambayar ta lafiya?mene yafaru?
Mai kike yi a waje ?talk to me kiyi mun magana.
Share hawayenta tayi tace"just take me out of here ,bana san na sake minti ɗaya anan i feel suffocated .bai sake cewa komai ba ya buɗe mata gaban motar sa ta shiga,key yayiwa motar bai tambayeta inda zai kaita ba ganin yarda take sheƙa kukan da sai a lokacin yadawo mata,tuƙi kawai yake bai san inda zashi ba,sai da tasha kukan ta mai isarta kafun tace"idan bazan takura maka ba ka kaini hotel mana zuwa safiya na saka a kawo mun jakana cos ina samun matsala da bank ɗina Ƙwana biyu gashi cards ɗina duka suna jakana."
Bai ce mata komai ba ya ɗauki hanyar guest house ɗin su,tafiya ce mai ɗan tsayi dan har bacci ta samu ya fara ɗaukarta wanda tana farashi take farkawa,unguwace mara hayaniya kamar dai tasu wadda ke ɗauke da gidaje na gani na faɗa,horn yayi bakin gidan ,sai da yayi wajen sau huɗu kafun gate man ɗin ya fito dan ganin wanene domin baya tsammanin kowa ,ganin motar Saleek ya sakashi komawa da sauri dan buɗe masa gate.
Yana shiga yayi fakin a gurin adana motoci kafun ya maida kalansa ga Kiswa wadda idanunta ke rufe,haka nan ya tsinci kansa da jin yana da gurbi mai muhimmaci a gare ta ,koda bata faɗa masa ba abun cikin gida ya fito da ita kuma ya tabbata abunnan ba mai daɗi bane,sannan kiran sa da tay ya nuna masa irin adadin yardar da ta bashi wadda ya ɗaukarwa kansa alƙawarin bazai bata damar yin dana sani na yardar da tayi masa ba.
A hankali ta buɗe idanunta tana mai gyara zamanta da ta kula da ƙarfin halinta na baccin da tayi a motar sa,murmushi yayi ganin yarda take kallan window ɗinta dan tabbatar da inda take,cikin sigar kwantar mata da hankali yace"hajiya calm down ba sace ki nayi ba ,nan guest house ɗin Abba ne dake ALI AKILU estate,its safe sannan ki ƙwantar da hankalinki bazan taba cutar dake ba,naga da kije hotel gwanda ki zauna anan ɗin yafi,sannan ba ke kaɗaice cikin gidan ba akwai mai gadi da masu aiki mata uku,ɗaya na girki ɗaya na shara da wanke wanke,ɗaya kuma itace ogansu wadda ke kula da gidan baki ɗaya,suna gidanne kuma saboda yawan amfani da gida da nake domin Abba ma zan iya ce miki ya manta da gidan dan kulawarsa a hannuna take.
Shiru tayi tana kallansa kafun ta buɗe bakinta tace"nagode Saleek bazan taba mantawa da abunda kayi mun ba yau ɗin nan".murmushi kawai yayi ya bude side ɗinsa ya fita kafun ya zagayo ya buɗe mata gefen ta.
A baya take binsa suka shiga tamfatsetsan gidan yana maiyi mata jagora,duk da dare ne an rage haske gidan hakan bai hana kaga yanayin tsarin sa ba,staircase ɗin dake cikin falon suka haura inda ya buɗe wani ɗaki guda ya kalleta yace "bismillah".
Babu musu tabi bayan sa bata jin wani ɗar zuciyarta domin kuwa tayiwa Saleek yardar da bai kamata ace tayi masa ba,amma a hakan nan zuciyarta bata dana sani da yardar da tayi masa ko kuma tunani na zai cutar da ita duk da kuwa hakan ta miƙawa ɗan uwanta Sagir amma ya nemi ya ƙeta mata haddi.
Queen sized bed ne cikin ɗakin mai kyau wanda yasha farin bedding yayin da komai na ɗakin yake white and ash gwanin burgewa,juyowa yayi ya kalleta yace "kiyi amfani da ɗakin nan,Abba yayi sa domin Amatul'islam ne ,duk da kuwa bata ƙasa amma ya yarda yaran sa can be rebellious kinga kamar ni gidan nan Na mayar dashi gidan zuwa na dan nan na wuni dana kiraki ɗazu Kin fita ,so feel at home,kina jin yunwa ba? Bari naje na taso cook ta sama miki wani abun".
Saurin taresa tayi ta hanyar cewa"im not hungry,bana jin yunwa ,sannan na gode sosai "shafa kansa yayi yace "godiyar nan ce bana so please ki daina yi mun,ina da damar nayi miki ne shiyasa nayi miki,ban san godiyar nan,ina ɗayan ɗakin dake jikin wannan Just Call me idan kina san wani abu".
Kaɗa masa Kai tayi tana mai yi masa murmushi kafun ya juya ya fita shima yana maida mata fara'arta.
Yana fita ta cire hijab ɗin jikinta ta cire ta ninke a gefe ta buɗe kofar da take tunanin bayi ne ta shiga domin watsa ruwa.
***********
__B'angareen yaya sagir kuwa Kai tsaye suna zuwa asibitin da suke da insurance aka fara attempting masa ,babu abunda mother take sai kaiwa da komowa hankalinta a atashe musamman ganin yarda ɗanta ke bleeding sannan baya cikin hayyacin sa,
Farry dake zaune itama cikin tashin hankalince ta kalli Mother tace "mother ki kwantar da hankalinki babu abunda zai same shi amma Mother ni abunda nake san sani mai Yaya sagir yake a ɗakin Kiswa babu kaya? "
Wani irin kallo Mother ta bata kafun tace"ke damuwar ki yana ɗakin Kiswa babu kaya ko?,kina tunanin a banza ne na miki alkwarin tashi da farin ciki yau?To ba komai yaje yi ɗakin ta ba,yana da buƙatar ta ni dake muna da buƙatar kaita ƙasa , wane opportunity' ne yafi wannan?amma da yake yarinyar nan sheɗaniyace shine ta nemi ta kasheshi"
Shiru Farry tayi tana neman gasgata maganar Mother,ganin yanayin fuskarta ya saka Mother cewa"kada kice mun tausayinta kike?Bari kiji idan ma shi kike to ki daina,'dan wallahi idan baki kashe Kiswa ba zata kashe ki sannan duk abunda kika ga inayine domin farin cikin kine "
Shiru Farry tayi tana sauraran mother yayin da wata zuciya ke faɗa mata hakan ba dai dai bane inda wata ke faɗa mata dai dai ne,ita a nata tunanin zasu koreta a gidan ne shiyasa koda tana jin ihun ta bata kawo komai ba,illa tunani Chan daban amma bata kawo fyaɗe ba tunda ba'a faɗa mata ba,shima wai yaya sagir.
Suna wannan tsayuwar doctor ya fito yace ma mother ta sameshi a office,
Koda taje bayani likitan ya fara mata kan ya zubar da jini da yawa ,ana buƙatar kara masa ,sannan yana buƙatar surgery saboda raunin da yaji a gabansa sosai ne ,amma a wannan lokacin su tsayar da jinin an saka masa ruwa da alluran da zasu taimaka masa wajen farfadowa ,sauran bayani kuma sai babban likita yazo da safe amma a yanzu dai babu wani abu da zasu iya cewa bayan he is out of danger.
Hawaye kawai mother take tana Adduar kar abun ya haifa masa matsala,idan kuwa ya samu complications To tabbas ita zata zama ajalin Kiswa wannan alƙawari ne ta ɗaukawa kanta.
08130229878
CHUCHUJAY✍️
[5/31, 7:29 PM] Chuchujay✍️: 💥KISWAH💥
(Surrogacy was the cause)
CHUCHUJAY✍️
Book1⃣
Page1⃣8⃣
__________Bayan rabuwar Haidar da Kiswa ba ƙaramun damuwa ya shiga ba domin maganar da yayi da yanayin da ta bar motarsa yasan cewa abun bata ɗaukesa ƙarami ba,bayan dawowar Ummi kamar yana jira ya tareta yana mai faɗin"Ummi Kiswa fa"?
Kallan sa tayi tana mai murmushi tace "baka tunanin san Kiswa yayi yawa a gurinka wanda yake san zama ba lafiya ba,kasan dai ba zan siyar da ita ba dan haka na kai ta gida and fita da ita was fun dan tun yanzu na fara tunanin fixing mana wani date cos ina faɗa maka ina kallan idanun hajiya Aziza kishi na ne ƙarara a fuskarta".
Yar dariya Haidar yayi yace "Ummi namu,well im glad kinji daɗin fita da ita and ina fatan itama bata damu ba"
Takawa Ummi take dan shiga sashenta yana biye da ita a baya tace"idan ma da damuwa zata saba ne".
Bayan ya raka mother ya koma ɗakin sa 'ya dauko wayarsa ya ƙurawa numbernta ido kamar ya kira amma yana tsoro,sanin sab'ani irin hakan bai saba faruwa tsakanin su ba ya saka ya yanke shawarar barinta ta huce zuwa safe yaje har gida ya sameta,a hakan nan yayi bacci duk da jikin sa yana basa wani irin yanayi dangane da ita amma sai ya bar hakan kan tana cikin damuwar maganar da ya faɗa mata ,haka nan ya lallashi zuciyarsa yayi bacci da niyyar washe gari da safe zaije ya sameta,ille kuwa tun asuba ya fara kiran layin ta amma baya samu,Har Allah Allah yake gari yayi haske ya tafi gidansu,duk yarda Ummi tayi dashi ya ƙarya ƙiyayi sai ce mata yayi yana da abu mai muhimmaci ne a asibiti amma zai ci abinci a waje.
Koda ya isa gidan cigaba yayi da kiranta amma still a kashe,fitowa yayi a motan ya isa bakin gidan ya ƙwanƙwasa ƙofa,sai da ya buga sau uku kafun mai gadin gidan ya buɗe,yana ganin Haidar ya dashe baki dan yana yi masa alheri sosai,cike da girmamawa suka gaisa kafun haidar Ya nemi da yayi masa isoo gurin Kiswa,kamar kuwa yana jira ya tambayesa yace"aikuwa ranka shi daɗe hajiya Kiswa bata gida,dan In taƙaice maka jiya ba gidan nan ta Ƙwana ba.
Cike da damuwa Haidar yace"To fatan lafiya dai ko,sannan ina taje dan bana samun wayarta".
Ajiyar zuciya mai gadi yayi yace"bazan boye maka ba yallabai jiya dai gidan nan Babu daɗi domin kuwa hajiya Babba korar kare tayiwa hajiya kiswa dan isasshen kaya ma babu jikinta a lokaci ga dare,sannan a tawa fahimtar duba da yarda muka ɗauko yallabai Sagir tsindir babu kaya daga ɗakinta yana ta ambaliyar jini ina kyautata zatan yaje mata da lalatane ita kuma ta ƙwaci kanta ta hanyar yi masa rauni,yanzu haka ma yana asibiti ita kuma Hajiya Kiswa Allah kaɗai yasan inda take dan kaga Chan ga motarta cikin gida ko ita ba'a bari ta ɗauka ba dan rashin imani,Ga dare,ga Yallabai mai gida baya gari ,yallabai sameer kuma Bansan mai ya faru ba dan duk abunnan da ake bai fito ba har mukaje asibiti to sai da safen nan shima nake bashi labari da ya tambayi hajiya Kiswa".
Wani irin yanayi na jirine ya ziyarci Haidar yayin da wani irin tsoro da fargaba da bai tab'a ji ba suka ziyarce sa,Hailala kawai yake iya furtawa ,juyawa yayi bai kuma cewa da Baba mai gadi komai ba ya shiga motarsa yayi mata key ,idan da zaka tambayeshi inda zaije shi kansa bai sani ba,dumin da yaji na bin hawayen sa shi ya tabbatar masa da hawaye yake ,shi mutum ne mai rauni indai akan abunda ya shafi Kiswa ne,magana ake fa ta fyaɗe sannan bama asan inda take ba duba da korar da akayi mata cikin dare ,tsoron sa kar ace tana hannun banza duba da yarda baya samun wayarta,Kai tsaye gida ya wuce bayan ya gama lalabansa cikin duhu,yana isa gida ya fara ƙwalawa Ummi kira wadda ta fito a kiɗime kanta ko ɗankwali babu,cikin tashin hankalin ganin sa yana kuka ya saka ta zuwa gareshi tana faɗin"Haidar lafiya?Wane ya mutu".
Faɗawa yayi jikinta kamar ƙaramin yaro ya fashe da kuka yana cewa"Ummi gwanda ma ace mutuwa mutum yayi da abunda ke faruwa".
"Mene kenan yake faruwa my Son,lafiya haka?"Alhaji Tukur Bula ya faɗa yana mai saukowa daga sama jin kukan ɗan nasa,
Haka nan Tasleem ma wadda ganin yana kuka itama ta fashe da kukan domin sosai zuciyarta ta karaya ganin Haidar na kuka.
Kamosa Ummi wadda itama idanunta ya ciko da ƙwalla tayi tace"oya zauna ka samu nutsuwa tukunna,Tasleem maza kawo masa ruwa".
Zaunawa yayi Mahaifin sa ma ya zauna Gefen sa yana san yaji abunda ya saka jarumin ɗan sa kuka haka,Yasan abunda zai saka Haidar kuka ba ƙarami bane,.ruwan da Tasleem ta kawo