Showing 30001 words to 33000 words out of 50778 words

Chapter 11 - KISWA Book Complete Document by Chuchujay.txt

29 Nov 2024

2567

hankali makaranta ta buɗen wuta,kun dai san watan karshe kafun grad akwai wuta.


Xx❤
[5/19, 11:45 PM] Chuchujay✍️: https://chat.whatsapp.com/DgTUlodRcp2AHM4rmfKTqK
💥KISWAH💥


(Surrogacy was the cause)


Na


Chuchujay ✍️


Book1⃣


Episode1⃣4⃣.


_________Takowa Yaya Sagir ya farayi zuwa gurin ta yayin da take jikinta ya fara rawa,ganin da gaske gurin nata yake nufowa ya saka ta buɗe ƙofar bayi ta faɗa da wani irin zafin Nama ta kullo tana ambatan Allah wanda tasan shine zai kawo mata ɗauki ba mutum ba,Takowa yayi bakin kofar bathroom ɗin ya murɗa handle ɗin cike da baccin rai yace"ki buɗe kofar nan Kiswa domin kuwa idan kika kuskura na b'allata baza kiji daɗin ba wallahi dan haka tun muna mu biyu ina lallab'aki ki fito muyi abunda zamuyi na wuce ,ina da aiki kema Kina dashi da safe"


Ƙaramar dariya tasa cikin kuka tace"you're far beyond a devil yaya Sagir,you're evil sannan Allah ba zai tab'a baka dama akaina ba wallahi domin ni na rigaka nace Allah,duk wani mugun nufin ka da kake dashi akai na wallahi sai dai kayi ka gama Allah bazai tab'a baka dama ba,im disappointed in You sannan yau ka tabbatar mun ni ba taku bace tunda nayi imani da Allah bazaka tab'a neman Farry ba,sai ni zaka wulaƙanta?"


Cije leben sa yayi yana mai shafa ƙansa cike da takaici kafun yace"Kiswa idan kin ɗauki wannan mugunta so be it amma ni nasan ba mugunta bace ,We are two adults for God sake,muna da buƙata kin fi sone naje waje na biya buƙata ta da ƙazaman mata na samo wa kaina wani ciwo bayan gaki wadda nake so a gida clean and pure haba mana Kiswa ki tausaya wa yayanki."


Sanin bashi amsa bata da amfani duba da yarda yayi wannan maganar ya saka ta furta "mahaukaci,daƙiƙi,jahili".cike da wani irin fushi da ya taso masa jin kalmomin da ta kira shi dashi ya daki kofar bayin yace"ni kike zagi?"


"An zage ka ɗin, kayi abun zagin wanda da akwai dama jefe ka ya kamata ayi "useless dog sannan kayi mun alfarma ka cigaba da dukan ƙofar bayin nan yarda mutanen gida zasu gane kana nan su zo"sanin abunda ta faɗa gaskiya ne ya saka shi cije lebensa yana mai nuna ƙofar da yatsa yace"zamu haɗu Kiswa sannan idan na tashi dawowa baza kiji daɗi ba dan ashirye zan zo and na maki rantsuwa sai na sameki"


Yar dariya tayi daga ciki tace"yayi,sannan nagode da kayi pointing mun kanka kaga kuwa yanzu na gane ɗan akuyan da ke zaune gidan nan sannan ranar da zaka dawo nima ashirye zaka sameni wallahi concerning my dignity i can hospitalize you Just dare me and See kuma ,Try me you dog".ƙwafa yayi ya juya ya fita da ƙudirirka masu yawa akan ta,sai da ta tabbatar ya fita tukunna ta buɗe a hankali ta fito ,zazzare idanu ta fara tana mai san tabbatarwa bai boye a wani gurin ba,ajiyar zuciya ta sauke sannan ta fito ,direct ƙofarta ta nufa ta sakawa key sannan ta dawo ta zauna kan gadonta ta rushe da wani irin kuka tana addu'ar dama ace mumunan mafarki ne wannan tasan dole wani zai tashe ta ,amma kash gaskiya ce mai ɗaci da rashin daɗin saurare ,babu abun da yake damunta kamar irin yardar da ta basu,shin wane kuma zata yarda dashi gidan nan bayan hell ɗin da tayi facing cikin satin baki ɗaya,tana wannan zaman Haidar ya ƙirata cos yana jiran kiranta dama amma ganin bata kirasa ba ya sakashi gazawa da jiran kira nata shi ya kira ,Kamar zata ɗauka Amma sanin shi mutum ne mai saurin gano damuwa a muryarta ya saka Bata ɗauki wayar ta ta saka ta a silent,ganin kukan bazai mata ba ya saka ta tashi ta shiga closet ɗinta domin saka kayan bacci,dama already ta yi sallah gidan su Haidar dan haka kawanciya kawai tayi tana saƙa da warwarar yarda zata kawo karshen wannan sabuwar ƙaddarar da ke tun kararta kamar guguwa,ita dai bata da wata hujja sannan babu wata mace da zata goya mata baya gidan ,Appa kuma ba magana ce wannan wadda zata iya yi mata ba ,Amma Ya sameer fa ,shin shima yana mata irin kallan da ya Sagir yake mata ko A'a domin yanzu bata san inda zata kama ba bata san wa zata tunkara ba saboda shima yaya Sagir ɗin bata tab'a tsammanin zai bijiro mata da wannan badaƙalar ba ,a haka tana waɗanan tunanuka bacci ya ɗauke ta wanda zata kira da barawo domin kuwa baki ɗayanta a tsorace take.


****


Washe gari koda ta tashi tayi sallah da asuba kasa komawa bacci tayi,Qur'ani ta ɗauko tayi ta muraja'a har sai da gari ya fara haske,wanka ta shiga ta yi kafun tazo tayi shirin tafiya office ,tsaye tayi bakin mudubi lokacin da ta gama tana mai duba kanta a mudubi,ita dai mutum ce wadda bata tab'a mantawa da ita ba muharrramar mazan gidan bace wanda hakan ya saka duk lokacin da ta saka kaya zata duba ta kalli kanta da kyau ta tabbatar da cewa Batayi shigar da bata dace ba,amma duk da haka sai da ya zamana Ya Sagir ya ɗauke ta ta hanyar banza wanda tunanin abunda ya faru kawai zuciyarta kan mata ɗaci taji baki ɗaya bazata iya yafe abunda ya faru ba,haka nan take ji kamar idan ta fita wani zai gano wani abu wanda bata fatan kowa ya gane hakan, tana so ya zamana ita zata yiwa tufkar hanci,ta shirya kanta ,ta shirya zama Mai dauriya juriyar da zata yiwa kanta faɗa,gyara tsayuwarta tayi tana mai Sake kallan kanta da kyau kafun ta ɗauki hand bag ɗinta ta fita dan bazata dawo ɗakin ba after breakfast wucewa kawai zatayi,a da tace bazata tsaya breakfast ba gudun haɗuwa da yaya sagir amma tunawa da tayi kunyar mara kunya asara ya saka zata tsaya,sannan tana san ta kalli fuskar sa ta tabbatar da cewa shi ɗinne yazo keta mata haddi,?shi ɗinne ya faɗa mata maganganun jiya?shin zai iya haɗa ido da ita?koda ta isa table shi Kaɗai ke Kai wanda ya tabbatar mata cewa ya fito da wuri ne yana jiranta ba sai an faɗa mata ba,ajiyar zuciya tayi ta taka zuwa dining table ɗin ta zauna hannunta ɗauke da wayarta ,kujerarta ta jawo ta zauna ta cigaba da danna wayarta ,tunda tazo gurin yake kallan ta, sanin yana Kallanta ya saka ta haɗe ranta sosai ,yar dariya yayi yace "Kiswa kenan,babu sallama Babu gaisuwa?mene yayi zafi?"


Yi tayi kamar bata ji sa ba dan kula sa ma bata tunanin yana da amfani tunda ita dai a gurinta yanzu baya da wani mutunci ƙwataƙwata ,dariya ya kuma yi kafun yace"ina fatan baki shirya faɗawa wani little encounter ɗin mu ba domin kuwa babu mai yarda dake,kowa zai ɗauka sharri kike mun musamman yarda dukkansu suka yarda im decent ,and abunda baki sani ba my mom will die backing me up so ki rike sirrin ki a bakin ki kar ya kaiki ga tushen dana sani dan Wallahi idan kika zabi buɗe wannan bakin wahala ta ganki".


Ɗauke idanunta tayi daga kan wayar tana mai kalllansa a karo na farko kafun tayi wata irin dariya kafun a cigaba da danna wayarta Kamar bata ji abunda yace ba wanda yin hakan ya Sake tunzursa ainun.tana Danna waya ne amma a bangare guda tana tunanin maganar da yayi na Mother zata goya masa baya,a nata tunanin da yarda duk tsanar da Mother tayi mata baza ta taba bada goyan baya a keta mata haddiinta ba tunda ita uwa ce mai ɗiya mace wadda bazata so hakan yafaru da tata ƴar da ta haifa ba,it would be ridiculous ,tasan duk tsanar da tayi mata idan taji maganar nan bazata taba ragawa sagir ba ,haka nata tunanin yake bata,amma koma dai menene magana ce ake ta bai samu nasara akanta ba a tayin farko sannan ya bata hint na sharrin da yake binta dashi so next time he wont like her ,sai a yanzu maganar Baba Baraka ta fara dawo mata da kuma nacin maganar da yake mata na tayi masa wani taimako,a haka suna wannan zaman sauran mutanen gidan suka hallarta inda kowa ya gaida da kowa wanda yin hakan ta b'angaren Mother ya mutuƙar bawa Kiswa mamaki ganin yarda Mother ke amsata faran faran,Kai bama ita ba kowa abun ya bashi mamaki ,hakan yasa Kiswa ta fara zargin wani abu ba dai dai yake ba a wannan fara'ar ta Mother.


Kiswa na ƙokarin aje Cup ɗinta da ta shanye tea ɗinta Appa ya jefeta da maganar da ta daɗe bata ji mai daɗin ta ba inda yake cewa"nayi waya da Costum Bula, and labari mai daɗi,ranar sunday zasu zo tambayawa Haidar Auren Kiswa kuma ina san Auren kar ya ɗauki lokaci,ba kuma shawarar wani anan nake nema ba,naga ya kamata ku sani ne duk da wasu cikin ku ba san Auren suke ba"hankalin sa ya mayar ga Kiswa wadda take ƙokarin boye ihun murnar dake neman san ya ƙwace mata yace"dota what are Your prayers?".


Kasa rufe bakinta tayi ,gyara zaman ta tayi tana mai kallan Appa tace "Appa burina guda ɗaya ne wanda bai wuce ina san a saka dangin Abbana ko guda ɗaya ne a cikin maganar Aurena after all nasan ba dukkan su ne na banza ba ,ga kawu Halilu kawun Abbana he is very kind to me and a sau da dama yana yawan kirana yaji lafiya na,and yace mun idan har na tashi Aure kar a cire sa,and Appa nima ina san haka musamman da ya zamana akwai masu tantamar ko ina ma da uban nan ina ganin hakan zai wanke zarginsu ,sannan nasan Kai Kaɗai zaka iya yiwa Mama magana yarda ta ɗauki zafin nan da su. "


Cike da yaba hankalin Kiswa sameer yace "nima dai Appa ina tunanin maganar nan ta Kiswa abun a duba ce at least Sun chanchanta"ajiyar zuciya Appa yayi yace"well banyi Alkwarin zama da Zubaida akan yi mata wannan maganar ba domin bana fatan zama ni da Zubaida dan na faɗa mata wani abu da zummar ta jini domin da Zataji maganata shekaru da yawa da taji amma zanyi wa Dada da baffan mu magana tunda dai ni da Zubaida sune iyayenmu,Dole zata ji maganarsu, sannan da yardar Zubaida da rashin yardarta babu abunda zai sake na cewa Dangin mahaifin Kiswa sun fimu karfi a abunda ya shafi Aurenta duk da muma zamu iya Aurar da ita basu amma hakkin su ne sannan suma masu tantamar mahaifin Kiswa a wanke musu doubts ,shi yasa na tambayeki ,what are your prayers domin kuwa abunda kike so shi za'ayi "


Godiya tayi ma Appa kana ta tashi tana Mai satar kallan Mother wadda tunda Aka fara maganar bata saka baki ba hankalinta na kan arish ɗin da take ci,fita Kiswa tayi tana Mai yi masu sallama wanda tana tashi Farry ma ta tashi ta musu sallama,Kiswa na ƙokarin buɗe motarta taji an riƙe mata hannu,juyowa tayi cos already tasan Wane,haɗe ranta tayi tamau tace"yanzu kuma Waccece matsalar ki Farry?"


Haɗe rai itama Farry ɗin tayi ta saka hannunta cikin jakarta ta ciro check book ta cike komai banda amount ɗin kudi ta mika mata ta tace"ga blank check nan ki saka duk wani amount da kike tunanin zai miki zan biya In dai zaki bar mun Haidar ."


Kallan check ɗin Kiswa tayi sannan ta kalleta tayi ƴar ƙaramar dariya tace"so yaushe wannan dramar karyar san na bar miki Haidar ta fara?i mean are you Nuts or you're just trying to deny the fact that you have lost it?kina hauka ko?bari kiji na faɗa miki wani abu,A gurina Haidar ya wuce duniya da abunda ke cikinta har su ƙudi da kike ɗaga kafaɗu dasu kina thinking Kin wuce kowa a rayuwa,when wanda ya tarasu from scratch bai ɗaga kafaɗa ba,See Farry ki shiga hankalinki tun wuri ki rabu dani da wannan shashancin 'dan wallahi idan kika sake mun wannan iskanci i wont mind beating you blue black"tsaki taja tana Mai tureta gefe ta shiga motanta ta tada.


Bin ta Farry tayi da kallo har ta figi motar,kwafa tayi tace "wallahi idan ban samu Haidar ba bazaki sameshi ba,im tired na gaji da nuna mun da Appa yake Kin fini,abunda yake taƙama dashi wanda yake sakawa yake maganar gwara ke akaina zan ƙwacesa sai naga kuma sai mene,Haidar dole ya zama nawa kuma ni zan Mai dashi nawa ko Kin so ko kinƙi,that i promise."motarta ta nufa tana Mai yiwa gate man jaraba akan ya buɗe Mata gate.


Bayan kowa ya fita Ya rage daga mother sai sagir wanda dama space suke jira,washe baki mother tayi tace"uhumm Sagir ka bani labari mai daɗi na tabbatar duk strong shit ɗin nan da take forming pretending ne,Mai yasa kaga tunda Aka fara maganar Auren ban saka baki ba?saboda nasan na saka hannuna a kan abunda bazai taba barin wannan Aure ya wakana ba so ina abunda na saka ka?".


Shafa kansa yayi yace "akwai matsala fa dan abun bai iyu ba cos she was fast ta shige banɗaki sannan tayi warning ɗina akan zata yi ihu kuma kinga tana Yimun ihu game over ,na mutu shi yasa na fita a ɗakin,worst abun kuma yanzu tasan mai nake so akanta"


Shiru Mother tayi tana Mai jin wani irin baƙin ciki kafun ta kallesa tace"its okay kar dan wai ba'aci nasara ba yanzu abun ya karyar da kai,next time zamu gwaɗa amma muje a shirye dan na fahimci wannan yarinya tayi fukafukai waɗanda idan ban balle mata su ba zata fara tashi sama,and trust me wannan yaran Haidar mijin faridha ne,yanzu ka tashi ka wuce gurin aiki zamu san abun yi,nima ina da appointment da client bari na wuce kar nayi latti".


Haka nan Mother ta fita zuciyarta baka wuluk ,koda ta isa firm ɗin su client ɗinta ma haka nan ta gana dashi sama sama kafun ta ɗaga haɗuwar su domin bata da nutsuwar ganawa da shi ta fahimci case ɗinsa yarda ya kamata ,aminiyar ta Brrst Salamatu ce ta matso inda take tace "ƙawata wai menene damuwar ne ,kar dai akan wannan yar riƙon ne kike nema ki sakawa kanki hawan jini."


Ajiya zuciya Mother ta sauke ta kalleta tace "ki barni kawai ƙawata wallahi al'amarin Kiswa yana nema ya saka zuciyata ta buga,baki ɗaya yarinyar nan na nema ta zamar mun karfen ƙafa,na rasa yarda zanyi na cire ta,yau kina ji maigidana maganar Aurenta da Haidar yake,na rasa abunda zanyi gashi duk abunda na shirya sai kiga ya lalalce".dafata Barr Salamatu tayi tace"yo Allah na tuba idan duk wani makirci yaƙiyi menene amfanin Malaman garin nan,kinga akwai wani malami na babu bata lokaci idan yayi aiki,abu guda ɗaya zamuyi wanda Shine sakawa ya farraƙa su wallahi idan yayi miki aikin nan ba wasa,dan aikinsa yafi na wannan malamin da ya baki mallakar Appan su sameer.


Shiru Mother tayi tana nazari kafun tace"ke ni rabani da wannan harkar tukunna shi kanshi Appan nasu kaɗan ya rage wanda Shine na rashin kashewa iyayensa unnecessary kuɗi amma tsakanin sa da wannan yarinyar yaƙi kamuwa ,nima nan kina ji ranar abunda yayi mun i told you ai ,dan haka ni kawai ki barni na buga tugguna dan yanzu card d'in da nake bugawa zai baki mamaki sannan jikina yana bani zanyi nasara ".


Kaɗa Kai Brr Salama tayi tace "ai shikenan idan uwar bari ta kamaki zakizo ai ni dai a ko yaushe ƙofata ta taimaka miki a buɗe take"


"Ƙofar ki ta kaita wuta dai"Brrs Hafsat wadda take itama ƙawarsu dan duk tare suka shigo firm ɗin ta faɗa tana Mai sake maida hankalinta kan system ɗinta,bayan ta gama ta ɗago ta kallesu tace"wallahi juwairiyyah ki guji biyewa Salamatu Kin san dai Halin ta,idan kuma kika ce ke Abunda Allah ya tsara bai miki ba to Kina daf da kalmashe dana sani babu wanda ya sani,and after all yarinyar nan fa babu abunda ta tsare miki,kamfaninku kanshi taƙi karban aiki a gurin,koda kuwa mijinki ne 'ya mutu Bata da gado so mene na cutarawar har tana alfaharin tuna miki ta kaiki gun malami 'ya raba mijinki da danginsa yo boka dai sannan abunda kashuka shi zaka girba dan Allah mu gujewa yin abunda zai faɗa kan yaran mu da basu ji basu gani ba".


Tsaki Brr salamatu tayi tace"says someone who had an abortion When she was 16 ,abeg my frnd idan zaki saurara ki saurara idan kuma bazaki iya ba kar ki damemu da wani kinibibinki after all we are all sinners".


Murmushi Brr Hafsat tayyi tace"well naji i had an abortion da shekara sha shida ,kuskure nane wanda ɗan adam baya wuce sa amma kar ki manta at that sixteen i was raped ba karuwanci nayi ba sannan Alhamdulillah ban taba siyar da imanina ba dan zuwa gurin wani mushiriki 'ya biya mun buƙatar duniya ba kinga kuwa shima abun buga ƙirji ne,duk kuma abunda kuka ga dai dai ne kuyi dan Allah wanda baiji bari ba...... "Ita dai Mother bata ce komai ba dan bata san musu da Hafsa ta nemi ta chanza mata kuɗirinta Akan Kiswa wanda bata nemi ta sauke makamai ba sai taga ƙarshen yaƙi ,amma magana kuwa ta malam dama bata ma sakashi a ranta ba.


**********


Delay a update bashi na shirya muku ba a littafin Kiswa,but ina da alot a plate ɗina wanda nake dealing da within lokutan nan,but i will be trying my best naga koda book one ne na gama muku update da wuri tunda wancan book two dama kuɗinka karatun ka and like i said its affordable,ku dai ku cigaba da kasancewa dani a tafiyar labarin Kiswa ❤❤


Xx


Chuchujay ✍️


08130229878


Yar arewa 1&2 N500


Abla adnan N500


They are still on my paid book shelf Come and purchase 🥰❤
[5/22, 10:10 PM] Chuchujay✍️: 💥KISWA💥


(Surrogacy was the cause)


Na


CHUCHUJAY ✍️


Ku bi whatsapp channel ɗina domin karatu cikin nutsuwa.


https://whatsapp.com/channel/0029VaRpQeUHwXb52H0abb05


Book1⃣


Page1⃣5⃣


________Murmushi Shine kawai abunda ke kwance akan fuskar kiswa yayin da a lokaci guda idan ka kalleta zaka gane tana cikin farin ciki ne , hannun ta guda ɗaya riƙe yake

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login