Showing 1 words to 3000 words out of 50778 words
[5/1, 10:07 AM] Chuchujay✍️: https://chat.whatsapp.com/DgTUlodRcp2AHM4rmfKTqK
KISWAH
(Linked through surrogacy).
Na CHUCHUJAY ✍️
Book 1⃣
Episode 1⃣
◼
A/N
Assalamu Alaikum masoyana abun alfahari na,Fatan na sameku cikin koshin lafiya ,
Ina kaunarku a koda yaushe kuma bazan daina ba domin kuwa Allah ne ya haɗa ni daku wanda ba yine 'na mutum ba,
Ina rubutu kuna kaunarsa sannan kuna bani kwarin gwiwa wajen so da yaba abunda 'na rubuta,😪ni ba kowa bace idan Babu ku ❤.
So yarda Allah ya bani ikon haɗa Littafin AURE UKU da AHALINA ina Addu'ar 'ya ara mana rayuwa da lafiya domin kawo muku wannan littafi nawa Na KISWAH(Surrogacy was the cause ) amma a wannan zagayyen tafiyar ta dabance domin kuwa littafin 'ya kasu kashi biyu ma'ana book 1&2
,book 1 zai zo maku kyauta ne book two kuma na kuɗi,kamar yarda na nishaɗantar daku a series biyu da 'ya gabata ina fatan nima zaku nishaɗantar dani da beautiful sales na wannan littafin Na KISWA,kilan kin taba ko ka taba jin story line ɗin kilan kuma wannan ne na farkon ka,abu guda ɗaya na sani wanda shine ,insha Allahu zai ilimantar,zai nishaɗantar .
Na sake faɗa Book two 'na kuɗi ne kar ki fara karantashi ya katse kiji haushina akan bance 'na kuɗi bane saida mutum ya fara' thats what happpend a Abla Adnan amma insha Allahu zaizo muku akan farashi mai sauki cos biyan zai zo da tsari,iya kudinka iya shagalinka❤
TSOKACI.
◽Surrogacy Wani method ne da turawa suka kirkira wanda idan ma'aurata biyu na san haihuwa misali idan ɗaya daga cikin ma'auratan bazai iya haihuwa ba ko kuma matar bata san ta haihu ɗin sai su samo wadda za'a sakawa Maniyi na mauratan biyu,da taimakon technology zasuyi developing ciki jikin Matar da wannan halittar samun ciki na Ma'aurata biyu,
Surrogate mother ɗin zata masu rainan cikin ta haife ta basu abunsu wanda shi yasa a kasashen yahudu surrogate mothers suna nan aikinsu ne iyakacin su haifa maka su baka abunka aikinsu 'ya gama kenan,wannan kana ji aikine na nasara domin kuwa Musulunci yayi Allah wadai da wannan tsari,sannan baya da gurbi ko waje ko wata ɗauraya a addinin Islama.
Wannan kenan.
DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN KAI.
Ko wanne ɗan Adam dake numfashi a rayuwa An haliccesa ne sannan aka rubuta masu ƙaddararsa sai dai yiyuwarta da wanzuwarta a lokacin rayuwa domin kuwa sai tazo kuma sai ta faru jira ne kawai bawa ke yi,
A haka rayuwa da ƙaddarar KISWAH UBAID ke tafiya a rubuce cikin tsari da godiyar Allah domin kuwa duk wani musulmi na ƙawarai yana daga cikin Imaninsa 'ya yarda da ƙaddara wala mai kyau ko kuwa akasinta ,
Iyayen KISWA biyu Malam UBAID da Zubaida ,Mutane yan asalin jihar Bauchi,a rayuwar Aurensu sun jima basu samu rabo ba domin rabon nasu na chan nesa,Zubaida bata samu ciki da mijinta ba har sai da suka shekara huɗu da Aure ,a lokacin kuwa da sanin cikin ya ziyarci Malam UBAID ba ƙaramun mirna yayi ba da farin ciki domin kuwa yana mutuƙar kaunar Ace yau zubaidarsa ta basa Farin cikinsa wanda shine ganin yaronsa ko yarinyarsa a hannunta.
A lokacin da Ya samu labarin cikin kamar ya zuba ruwa a ƙasa yasha dan murna,idan kuwa ka haɗu dashi a wannan rana To tabbas sai yayi maka ihsani saboda wanda ubangiji yayi masa.
Mutane da dama kan faɗi masa maganganu iri iri akan rashin samun cikin Zubaida dan harda masu ce masa rashin haihuwa Ya saka mijinta na farko sakinta domin bashine Ya fara Aurenta ba a bazawara Ya Aurenta,
Dukkan wata magana Da wani zai faɗa masa zata shiga ta kunne guda ne ta fita ta guda dan Babu wadda ke tasiri akansa,abu guda ɗaya ya sani wanda shine yana san matarsa sannan itama tana sansa sannan mahaifansa basu taba masa ƙorafi akan rashin haihuwar matarsa ba sannan ya sani da samu da rashi duk na ubangijine wanda a lokaci guda ya azurtasa a lokacin da bai tsammani ba,
Lokacin da Matarsa ta isa haihuwa ta zanƙado masa yarinya mace mai kyau wadda yana kallanta yace Allah ya basa KISWAH (Madubi,Rufi na Ka'aba)ya bata sunanne saboda Itace madubinsa na farko gurin sanin menene jininka,yana kuma fatan ta kasance mai tsarki da purity kamar irin na gold and Black lullubi na Ka'aba domin kuwa yan representing unity irin na islama.
Ranar sunan KISWAH kuwa ba ƙaramun bajinta yayi ba dan idan ka gani zakayi tunanin dukkan wata dukiyarsa yake ƙoƙarin ƙararwa a wannan rana,
Yana samu domin ɗan kasuwa ne wanda Allah ya bawa nasibi a kasuwancin nasa,
A lokacin da Zubaida tayi Arbain ya biya masu saudiyya domin kai KISWAH ya shafa hannunta akan KISWAH.
Lokacin da KISWAH ta shiga shekaru huɗu a Duniya Allah ya jarabci Malam UBAID da larura wadda tazo da ajali,bayan Kiswa basu sake samun wani rabon ba ashe ita ɗin ita kaɗaice rabo tsakaninsu.
Sosai Lalurar ta far masa wadda likitoci suka kasa gano bakin zarenta yayin da a bangare guda kuma ciwan ya ringa tafiya da dukkan arziƙinsa da tanadinsa wajen nema masa lafiya inda daga bisani Allah yayi masa cikawa ,
Bayan rasuwarsa a hankali Zubaida ta fara shiga chakwakiya ta rayuwa domin kuwa komai nasa ya kare sai gida wanda suke ciki inda shima ya shiga cikin gado,iyayensa da basu nuna masa san zuciya a fili ba lokacin rayuwarsa sai suka Nunawa Zubaida da ɗiyarsa KISWA domin kuwa ana saida gida suka karbi gadonsu suka sallama mata KISWA,itama iyayenta ba masu ƙarfi ba amma a haka ta cigaba da rayuwa da daɗi ba daɗi karkashinsu inda daga bisani lokacin da KISWA ta isa shiga makaranta Yayan zubaida ,Aliyu dake da Hali ya ɗauketa ya kaita gidansa domin sakata makaranta wanda ya shaida mata shine kawai abunda zai iya mata domin ba wani shiri suke ba amma sai Allah ya ɗora masa san Kiswa ,daga bisani kuma miji ya fito mata mai mace biyu ta Aura a nan cikin bauchin inda a gefe guda ta kama sana'ar abinci.
***
24 YEARS LATER
ABUJA NIGERIA!
Zaune ƙyakƙyawar budurwa take kan gado a wani ɗaki dake ihun Naira,komai na cikinsa princess like ne cikin color na pink and white,ɗakin na ɗauke da gado guda biyu wanda zai ɗauki mutum biyu each,a hankali take taba tab ɗin dake hannunta cike da siga ta mayar da hankali,ba fara bace irin matan nan ne da ake ma ikirari da black beauty wadda a kalo ɗaya idan kayiwa fatarta tabbas kasan ta samu kulawa,tana wannan zaman aka turo kofar ɗakin ,wata budurwarce da bazata wuce tsarar ta ba,Babu sallama a bakinta ta shigo ta na mai jefar da jakar hannunta kan gado na biyun a yayin da ta zauna tana mai cire takalminta wanda Ya gaji da tsini,
Kallo ɗaya budurwa farkon tayi mata ta dauke kanta,ƙaramun tsaki ta biyun tayi tace"Wallahi KISWA kina da matsala ba kaɗan ba ,kina jina na shigo Ai ko sannu ne kya faɗa mun amma dan tsabar bakin nukuburci kinyi kamar bama kisan na shigo ba,tsaki ta kumayi tace "today was beyond stressful ".
Murmushi kawai KISWA tayi sanin halin mai magana,tana so a koda yaushe kasan da ita ka bata attention,
FARIDHA ALIYU kenan wadda ake wa laƙani da FARRY ɗiya mace tilo a gurin ALHAJI ALIYU yayan zubaida mahafiyyar KISWA da Matarsa Barrister JUWAIRIYYAH ,yarinya wadda a kayiwa rainon gata da sangarta,yarinya wadda aka raina kamar ɗiyar sarki,Yarinya mai taƙama da ita ɗin yar gatace gurin Yayyunta guda biyu maza SAMEER da SAGIR wadanda basu san laifinta,
Bata da kara bata kuma gudun nuna maka kaiɗin ba komai Bane,duk da Halinta a bangare guda tana mutuwar san Kiswa duk da kuwa yarda mahaifiyarta ke mutukar nuna tsanar Kiswa ɗin tsantsa 'dan a cewarta tana neman kwacewa yayanta gida ne duba da yarda mai gidanta ke nuna kulawa ga Kiswa ɗin bugu da kari kuma yaranta maza dake faman mata shishshigi ,tsoranta guda kar wani cikinsu yace yana so,
Sau da dama Kiswa ke bin mess ɗin Farry tana gyarawa 'dan ita ɗin bata ji a yayin da gefe guda kuma Kiswa tasan ta duk wata hanya da zata bi ta kare Farry ɗiin.
Aje tab din nata tayi ta kalli Farry wadda ke ƙokarin Ɗaura towel tace "last da na tuna lokacin da zaki shigo bakinki babu sallama so mene zai dameni akan kulaki,and Yes maganar guy ɗin chan dake stalking ɗinki is all done and Abeg Farry ki barni haka nan na huta i have a life too"
Da sauri Farry ta dawo inda Kiswa ke zaune ta kama hannunta tace"God ina mutuwar sanki yar uwata ,na gode and anjima kaɗa zakiji alert na 500k "
Kallanta da kyau Kiswa tayi tace "you must be Nuts,wai sau nawa zance miki idan abu haka ya faru tsakanina dake ki daina ƙokarin biyana bana so abeg ,idan kina san ana miki aiki ne kina biya ki samu masu aikin a waje wanda irin aikinsu kenan mana."
Saurin kama hannunta Farry tayi tace"Chill girl calm down ba ina nufin wani abu haka ba wallahi,kawai ihsani ne and Yes nasan you're doing Okay financially amma aibu ne dan na maki kyauta?"
Kinsan im off better financially ki kalla fa ina hawa Landcruiser kina hawa 306 so girl i mean no harm,Tashi tayi tana mai gyara towel ɗinta ta nufi bathroom ɗinsu,har zata shiga ta juyo ta kalli Kiswa dake kallanta tace "500k im sending it idan kinga dama ki kyautar"Tana kai aya ta faɗa.
'dan murmushi Kiswa tayi a fili tace "im also doing well cos ina da savings na wajen 5 million and ban raina ba cos i earned it and motana i bought it my self"
Daga cikin bayin Farry tace "'dan kina da 5 million doesn't mean zaki saka kanki cikin millionaires ,you have alot way To go,so idan zakiyi quiting wannan kamfinin da kike ma aiki ki dawo na Daddy kiyi cos chan zaki samu kuɗi ba inda wani zai biyaki ba trust Me zan biyaki da kyau,yes im enjoying daddys money wanda kema ke kika hana kanki,cos motar nan Ya siyan miki kika ƙi karba.
Tashi Kiswa tayi tana mai sake gyara gadonta tace "nasan dai kinyi karatun addini sannan a cikinsa kinsan surutu a bayi haramun ne ,so ki bari idan kin fito sai ki bani wannan lecture ɗin."
Haka nan Farry take,idan magana tazo bakinta bata tunanin saka mata filter idan zata faɗe ta sannan duk abunda tayi niyyar faɗa shi take faɗa bata damuwa da abunda kai zakaji as far as ita ta futar da ta cikinta,haka nan take koda kuwa da Kiswa ne amma idan abu ta bangaren Kiswa ne bata wasa dashi komai ƙanƙantarsa,koda zuwan Kiswa gidan afafur ta ki yarda da a raba masu ɗaki duk da wadatar hakan ,duk nacin mahaifiyarta dole ta barsu.
Dauke takalman da ta watsar Kiswa tayi tana mai jadadda mitar ta daina aje masu takalmii a ko ina,
Kafun Farry ta fito ta gama gyara ko ina tana mai haɗama kanta cornflakes ɗin da tasa akawo mata,tana cikin ci Farry ta fito Babu wani tambaya ta kwace cup ɗin Ta fara ci tana mai cewa"ki haɗa wani"
Tsaki Kiswa tasa tace "wata rana sai kinci abu mai guba".
Zama gefenta tayi tace"indai a gurinki ne sis nasan bazan taba cin guba ba,kinsan dai kin bani wata ɗaya dole ne kina Cin girman,yauwa ina ma san tambayarki Ina Haidar ɗinki,
Ɗan ƙaramun tsaki Kiswa tayi tace "rabu da wannan yana tunanin bazan iya rayuwa babu shi ba shine yake faman shan ƙamshi a faɗan da ba laifina ba,well muje zuwa wanda Ya fasa gajiya."
Yar dariya Farry tayi tace "ke dai faɗanki da Haidar ɗinkin nan bamu shiga muji kunya,ina,ni 'fa shi yasa da kika ganni Babu ruwan da wani relationship' kuɗin dai da power ɗin tukunna .
A tare suka saka dariya 'dan a kullum furucin ta kenan a yayin da Kiswa kan faɗa mata bai zo Bane shi yasa.
Share fisabililahi
https://chat.whatsapp.com/DgTUlodRcp2AHM4rmfKTqK
CHUCHUJAY ✍️
https://whatsapp.com/channel/0029VaRpQeUHwXb52H0abb05
Join my Whatsapp channel
[5/1, 7:01 PM] Chuchujay✍️: https://chat.whatsapp.com/DgTUlodRcp2AHM4rmfKTqK
KISWAH
(Linked through surrogacy)
By
CHUCHUJAY
Book1⃣
Page 2⃣
◼
MONDAY MORNING.
Cikin gidan Na Alhaji Aliyu kowa ka gani yana sauri ne da kimtsawa domin tafiya aiki
,Kiswa wadda idan tayi sallar asuba bata iya komawa ce ta kamawa Baraka mai girkin gidan duk da kuwa yarda bata san Kiswa din na zuwa taya ta aiki amma nacin Kiswa ya saka ta barta dan Babu yarda zatayi da ita tun kafun ta kai haka.
Zazzaune suke baki ɗaya kan teburin cin Abinci suna jiran Kiswa wadda bata kai ga ƙarasowa ba ,rules na gidan bai barka kaci abinci ba tare da kowa ya hallarci gurin ba ,idan kana saurine to ranar sai dai kaci abincinka daban,wani irin tsaki Barrister JUWAIRIYYAH taja tana mai kallan mijinta tace"wai kai Alhaji mene damuwarka da sai anjira kowa za'a karyane?wannan yarinyar sanin haka ya saka take miƙe kafafu a ɗaki sai lokacin da taga dama zata fito ,gaskiya abinci zanci dan ina da abunyi a court haba."
Cup din dake gabanta ta ɗaga dan haɗa tea,Alhaji Aliyu bai tankata ba har ta fara haɗa tea ɗinta sanin koda yace ta yi hakuri bayi ɗin zatayi ba,sameer da maganar mahaifiyar tasu bata gamshe sa Bane yace "Amma Mother jiya Sageer yafi kowa fitowa latti and we waited Babu wanda yayi complain,after all Babu mai latti tunda baifi mu ɗauki minti talatin ba wajen karyawa kowa ya kama gabansa,its 6:30 am saboda Allah.
Cike da masifa ta kalli Sameer tace"zaneni mana Sameer sai nasan kana shigar wa uwarka juwairiyyah faɗa,bana san iskanci fa Zan bata maka fiye da yarda baka zato,"kafin wani yayi wata magana Kiswa y
Ta fito cikin shirinta Na zuwa aiki tana mai faɗin"kuyi hakuri na saka ku jira ,Im sorry da kun fara without me"
Tsaki Mother tayi tace"su da zasu iya jiranki ai gashi nan suna jiranki tunda basu da abunyi ,Ina ga zubaida ta sassaƙasu"
Da ƙarfi Alhaji Aliyu ya daki table din wanda da bashi da girma da yayi Bari,cikin yanayi na karsashi yace"sau nawa zanna faɗa miki ki cire zubaida daga fitinarki Barrister,ya isheni fa bana san kina saka ƙanwata a al'amarinki na rashin kirki na faɗa miki ba yau ba ba jiya ba "
Kallansa tayi narainarai da ido ganin yarda yake mata tsawa gaban yaranta which is not like Him,aje spoon ɗin ta tayi tace"Its okay ka cigaba da mun tsawa gaban yara amma hakan bashine zai boye gaskiyar cewa ƙanwaka Zubaida is a disappointment ba,sannan hakan bazai taba chanzawa ba so kama daina pretending caring brother cos kasani na sani its a pretence ,quit it already,excuse me"tashi tayi tana gama maganarta ta ɗauki jakarta ba tare da ta tsaya kula Sageer dake faman kiran sunan ta ba ta fice ,a hankali Kiswa taja kujerar kusa da Farry ta zauna tana mai faɗin"Im sorry about that,ba niyana nayi causing matsala ba ,na cire kayan da zan saka ne tun jiya so dana saka yau da safe yaki shigana since dama na daɗe ban saka ba so dole na sake neman wasu and i had to look responsible cause yau muna da baƙi masu muhimmanci and nice host dinsu sannan..."
Dariyar da suka saka ne a tare ya katse ta,dan taune lebenta tayi tace"well i didn't think i sounded funny,"Sageer dake gefenta ne yace"Aikin jarida ne kawai ya dace dake mai ya kaiki karanta Public relation?,".
Ɗan murmushi tayi tace "dalilin da yasa Appa karantar Kasuwanci sannan abunda yasa Farry karantar kasuwanci,abunda ya saka Mother karantar Law,abunda ya saka Ya Sameer shiga Immigration da abunda ya kai ka Ya Sageer karantar Accountancy which is Passion "
"Case closed"Alhaji Aliyu wanda suke kira da Appa ya kara yana mai jin Kiswa har ransa,She's smart beyond expectation,yaso tayi aiki karkashin kamfaninsa amma taƙi wanda take ganin kamar alfarmace inda shi kuma ya rabu da ita dan baya san takurata amma ko yaushe idan ta shirya dawowa Akwai gurbinta.
A Haka suka fara cin abinci har suka gama Babu wanda yayi maganar Mother domin abune wanda aka saba duk da kuwa tsawar Appa gareta shine abu na farko a gurinsu,amma ina zasu shiga gurin da bana su ba,duk da kuwa rayuwar gidan free rayuwace ta yan boko amma ko wanne yaro yasan limit ɗinsa da iyayensa.
Ko wannensu ya shige arniyar motarsa a yayin da Kiswa ta shiga cikin 306 ɗinta wadda take alfahari da ita ba tare da tana jin wai ita ɗin bata kai ba.
A parking space wanda aka tanada domin ma'aikata ta faka motarta a katafaren Building na Ma'aikatar ta AYZEL FOUNDATION,kamfanine wanda ke harƙalla da abubuwa daban daban wanda ya danganci kayan zaƙi,kamar su sweets,chocolates,ruwa,drinks,food stuffs ,sutura da sauransu wanda yake karkashin jagorancin Founder kuma chairperson na Group ɗin wato Alhaji Basil Madugu Dattijo mai fitarwa da ma'aikatan sa hakkinsu sannan mutum mai kirki na gaske,idan kana san shiryawa dashi to tabbas ya zamana kana san aikinka sannan kana cikin masu maida hankali akan aikinsu,wannan dalili ya saka yake mutuƙar ƙaunar Kiswa matsayin PR officer ɗin sa domin kuwa tasan aikinta yarda ya kamata.
Tunda ta shiga cikin ma'aikatar Take gaisawa da abokanan aikinta cikin mutunta juna domin kuwa ita d'in She's frndly ƙaryarka kace yau kuna zaune ga matsalarta,
Kai tsaye ofishin chairman d'in ta nufa domin shaida masa shigowata dan koda bata je ba zai nemeta ,gaisawa tayi da sakatariyarsa wadda ke faman yamutsa fuska dan bata ƙaunar Kiswa ko kaɗan Ganin Yarda chairman ke ji da ita kamar ya maida ta ciki dan haka duk wani chance da zata samu wurin bata Kiswa a ma'aikatar bata rainasa dan har rumours ɗin cewa Kiswa mistress ɗinsa ce ta assasa a kamfanin ,amma mey babu wanda ya isa 'ya tunkari Kiswa da maganar ko ya yaba mata Ya jawa aikinsa.
Cike da mutunci da girmamawa Kiswa ta Gaida Alhaji Basil wanda yana ganinta ya washe baki yana mai faɗin"yarinyar Albarka yanzu nagama maganarki da manager akan