Showing 18001 words to 21000 words out of 21599 words
kyawun d'akin babu abunda yafi daukan hankali na irin lafiyayyen abinci dake shak'e kan wani gold glass tebir. Ajiye kayan nayi na zauna gaban abincin ina tunanin yanda zan deba naci ba tare da an gane ba. Gefe-gefe na dinga bin ina daukan snacks, pie,cakes ,fruits, kaza da sauran su ina ci saida nayi kat na miƙe da sauri don shimfiɗa zanin gadon kan tafkeken gadon dake tsakiyar dakin an kewaye shi da net kaman labube tsakiyar cikin net din kuma wata dankareriyar chandler ce ta gold.
Dole a shagala da duniyar kuwa. Hannuna na sule na juyo don fara aiki. Wani irin bugawa k'irjina ya yi na k'ame gurin a tsaye na kasa motsawa. Ido na kyefta na k'ara Kyefta wa don tabbatar da abunda nake gani. Hak'ika kuwa dai-dai na gani ba gamo bane. Tsaye yake a gabana daga shi sai tawol d'aure a kungunsa ruwa nabin jikinsa tun daga gashin kansa har zuwa fatar cikin sa. Kutt na had'iye yawu nabi wani ruwa daya tawo daga wuyansa a hankali yana gangarowa har zuwa bakin tawol d'in sa .
Wani yawun na k'ara had'iyewaa ina kallon yanda ruwan ke bin Abs dinshi a mugun hankali suna shigewa cikin tawol nashi dake daure kan kugunsa. Baza kuso kuji matsanancin bugun da k'irjina keyi ba.
'Me ki ke yi haka Nadine kin kafe shi da ido salon yace your a creep and a Pervert?"
Da azama na d'aga ido na na mayar kan fuskarsa da babu emotion. Girar nan a had'e ya daga guda d'aya . Ido cikin ido muke kallon juna ya buɗe baki a hankali lebbansa kawai suka yi motsi badan ina kallon saba bazanji mai yace ba
"Are you done?, Pervert "
Cike da burin kamani da ya yi ina kallon sa na sunkuyar da kaina katsa. Takunsa kawai naji banyi aune ba sai ji nayi kawai ya fisgo ni na fad'o jikinsa babu zato. Wani irin shock ya tsarga jikina a rude na fara k'ok'arin kwacewa ya rike hannu gam yana cewa
"Don't you want to see me naked?, I will show you"
A firgice nake girgiza masa kai kuka na shirin kwacemin gashin na k'asa bashi hak'uri kaman wadda aka d'aure bakin. Jana ya fara yi ina turjewa ganin ya nufi makeken gadon. Me yake shirin faruwa ne? Ban fargaba sai da naga ya fisgoni da mugun k'arfin ya jefa kan gadon. Laushin gadon baisa na manta tashin hankalin da nake ciki ba na tashi da mugun gudu na wuntsula d'aya b'arin. Tsayawa ya yi riƙe da kugu yana kallona da wani expression dana kasa ganewa wa. Shar naji hawaye sun biyu kuncina. Wace irin rayuwa ce wannan? Raping d'ina yake son yi saboda yaga ni ba komai bace bafe baiwar sa?
Tsawan minti biyu muka d'auka a haka nida shi. Yana kallona ina kallonsa hawaye na gudu kan fuskata. Duk irin d'aci da tsanarsa da nake ni bazan bashi damar da zai samu galaba a kaina. Yunkurawa ya yi kaman zai tawo na kawa a guje nayi kofa. Ko tsakiyar d'akin ban jiba naji ya fisgoni yana cewa
"Ina ki ke tunanin zuwa?, do you think you will get away with what you have being doing?, you must be punish for your wrongs doing "
Jana ya cigaba da yi ina turjewa .ganin da nayi ya kusa cimma galaba a kaina mun kusa bakin gadon naga babu sarki sai Allah na haushi da duka da cizo ina kokawar kwace kaina ga wani irin kuka da nake mai gunji. Yanda kasan dutse nake duka harta zafin a jikina nake jinsa. Bai daina jana ba saida ya kaini bakin gadon ya wani fisgoni gaban sa sai a lokacin na samu damar ganin irin matsanancin b'acin rai dake kwance kan fuskarsa har wasu jijiyoyi ne suka fito raɗau kan goshin sa.
"How dare you?, ni ki ke duka harda cizo? ,ni Azrah?"
Hannuna dake ciki nasa ya k'ara matsewa kaman zai balla. Tuni wani fitsari ya kawomin ziyara kafafuwana suka fara saboda azaba. Da k'araji ya cigaba da magana
"Tambayar ki nake ni ki ke duka?, do you think am nice?"
Ya wani lankwasa hannun nawa kashin ya bada kara kass kaman wanda aka balla. Lu na tafi zan fad'i saboda azaba ya riƙe ni. Duk nayi jage-jage da ruwan hawaye da majina ga uwar zuba ta wahala dana had'a.
Ganin ina neman sume masa ya wani wulli da hannun nawa ya kama gashin kaina da k'arfi ya d'ago kaina ina fuskantar da. Badan halin da nake ciki ba da tsab zan iya cewa bakin mu saura kiris ne bai had'e ba saboda yanda bakin nashi ke dabda nawa har ina jin hucin numfashin sa da kamshin mint breath nashi. Dishi-dishi na fara gani saboda matsar da ya yiwa gashin nawa kaman zai cire fatar kan gaba d'aya. Saman lebena na fara jin hucin maganan sa
"Don't you dare repeat the same mistake. Am not nice. Next ki ka k'ara gigin abu makamancin haka I promise you sai kin kwammace mutuwar ki"
Wani irin hankad'ani ya yi na tafi taga-taga zan fad'i Allah ya taimake ni na dafe kujera. Hannu dake uban zugi na tallafe da sauri ina kuka mai cin rai.
"Get out of my sight"
Yace da k'araji. A guje na juya na fice talleb'e da hannu na da nake tunanin ya karya. Ji kawai nayi naci karo da mutum .saboda k'arfi had'uwar tamu duk muka zube a k'asa. Da sauri na dago dan naga ko waye naga. Wata kyakkyawar yarinyar da bata wuce shekaru gona sha takwa ba. Sanye take da doguwar rigar da akayiwa surfani da gwal. Sai kanta data saka d'an k'aramin crown na DAIMON. Kallo d'aya zaka mata kaga KING AZRAH. A take na gane kanwar sace PRINCESS SOPHIE. Ance ta jima bata k'asar tun tana k'arama tana can UK. Ta dawo kenan?..
Miƙewa nayi cikin azama na wuce ta a guje ina kuka sosai.
✿︎✿︎✿︎✿︎
Da ido Princess Sophie ta bita. Wacece wannan kuma? Me ya same ta ta fito daga d'akin Brother tana kuka haka?. Kai ta girgiza ta shigo d'akin kaman koda yaushe tana nan bubbly baka tab'a ganin bacin ranta. Kullum fuskarta dauke yake da murmushi.
Tsakiyar d'akin ta same shi riƙe da kugu ya juyawa k'ofar baya hannun sa d'aya rike da goshin sa. Da sand'a ta k'arasa inda yake tayi tsalle ta d'ane shi tana dariya. Groaning ya yi yace
"Baby get off"
Kafad'a ta mak'ale kaman yana kallon ta tace
"Sai ka gayamin Wacece wannan kyakkyawar da naga ta fito daga d'akin ka yanzu"
"No one, get's off"
"No one fa kace, amma me yasa na ganka cikin damuwa?"
Da sauri ya sauke ta daga jikinsa. Yasan halin Sophie da shegen bin kwakwaf. Banɗakin daya fito ya koma ta bishi da kallo tana wani irin murmushi da ita kaɗai tasan ma'anar sa.
✿︎✿︎✿︎✿︎
A guje na shiga b'angarenmu ina mahaukacin kuka. Da Mamee naci karo tana tambaya ta meya faru ban bi ta kanta ba na kwasa da gudu na shige d'aki na banko k'ofar. Zamewa nayi na jingina jikinta ina kuka sosai. Tsanar sa tayi min wani irin katutu a kahon zuci. Hannuna dake zugi na kalla . Runtse ido nayi na kama gurin da nake tunanin gocewar k'ashi ce na lankwasa yace bas alamun ya koma dai-dai. Kad'an ne ban saki fitsari a zauna ba sai gunji dake fita daga bakina dana datse da hak'orana saboda matsanancin azaba.
A yau d'innan zan bar cikin masarautar nan koman dare inshaAllahu . Bazan zauna yaci galaba a kaina ba. Tunda ya kwantanta yimin fyade to tabbas duk lokacin daya samu dama zai iya kwatanta hakan saboda yana da ikon yin hakan. Kamar wadda aka tsikara na tashi da sauri na d'auko jakata na had'a kayana cikin bako na tura k'ark'ashin gado na zauna ina zaman jiran lokaci na aiwatar da kudurina.
TO FA. NADINE ZATA CIMMA NASARA KUWA?
WANDA BASU BIYA BA SU FARA HANZARIN BIYA DON MUN KUSA IDA BOOK 1 INSHAALLAHU!
♔︎ ♔︎
𝕊𝕌𝕃𝕋𝔸ℕ𝔸𝔸ℍ
𝒕𝒉𝒆 𝒖𝒏𝒌𝒏𝒐𝒘𝒏 𝒑𝒓𝒊𝒏𝒄𝒆𝒔𝒔
Ashanty love.
☆
☆𝐈'𝐌 𝐀 𝐒𝐓☆𝐑☆
Chapter
46/50.
Har bayan isha ina jin Mamee da Layher nata buga k'ofa ta amma nayi mursisi naki buɗewa dole suka hak'ura suka kyale ni. Tunda nayi sallan ishan na had'a kai da gwiwa ina zaman jiran lokaci. Haka na zauna nayi ta zuba ido da wasi-wasi ta yanda zanyi na fice ba tare da wani ya ganni ba. Kai ita kanta k'ofar da zata fiddani daga cikin masarautar ban sani ba. Tsawon shekaru nayi cikin ta ban taɓa taka k'afata waje ba.
Da wannan tunane-tununanen barci ya kwashe ni ban fargaba.
A firgice na farka sakamakon mafarki da nayi mai ban mamaki. Cikin mafarkin na ganni cikin wani d'aki mai masifar kyau da akayi shi da gwala-gwala. Kuma abun mamaki kaina nake kallo zaune kan gado kaman yanda itama ke kallo na. Murmushi tayi ta miƙo min hannu kafin naji ta kira sunana 'SULTANAAH'. A firgice na farka ina maida numfashi bakina d'auke da Addu'a. Wane irin mafarki ne wannan kuma?. Gani a zaune gani kuma a tsaye?. Kai na girgiza na yunƙura da sauri na tashi saboda jin yanda masarautar ta d'auki shiru alamun dare ya tsala sosai.
Zama na gyara sosai ina tunanin ta inda zan fara. Ajiyar zuciya naja mai k'arfi na yunƙura da sauri na d'auki bakkona na mak'ale shi cikin k'irjina na nufi k'ofar a hankali ina Addu'a. Turus naja na tsaya bak'in k'ofar na kasa buɗewa saboda zuciya ta data ce 'idan ki ka tafi wane hali ki ke tunanin Mama Maria zata shiga?' .wannan tunanin ya kashemin gwiwa matuƙa na kasa motsi. Hak'ika idan na samu nasarar fita daga nan bansan inda zan fad'a ko hannun wanda zan fad'a ba. Duk rashin dad'in nan yafi dana fad'a hannun wani mugun da ban sani ba. Ko ba komai ina ci ,nasa sutura da gurin kwanciya.
To idan na fita kuma fa?. Numfashi naja mai k'arfi na juya a sanyaye na koma na zauna ina tunanin Mama Maria. Inama dai ina da halin da zanje naga yanda take. Da na samu nutsuwa ko ya ya ne. K'ofar d'akin nawa naji an tab'a kaman ana laluben sai kuma naji an d'an bugata a hankali. Da sauri na miƙe tsaye ina kallon k'ofar. Waye kuma cikin daren nan? Ban gama tunanin ba aka bugu k'ofar a hankali amma sai gata ta balle . Ga dukkan alamu wanda ya daki k'ofar maji k'arfi ne duk da cewa k'ofar dama ba wata k'ofar kirki bace.
Wasu mutane suka shigo cikin bak'aken kaya sun rufe fuska da bak'in abu. A razane na ja baya na buɗe baki zan kwala ihu d'aya daga cikin su ya k'araso cikin hanzari ya toshemin baki da hankici. A take naji numfashi ya d'auke na tafi lu na zube a k'asa.
ANONYMOUS POV.
Baya suka ja suna kallonta kafin d'aya daga cikin su ya fito waje ya yi fito. Saiga wata mace ta bullo daga mab'oya sanye cikin bak'aken kayan kaman nasu ta rufe fuska da mask. Tana shigowa d'akin kallo d'aya tayiwa Nadine dake yashe a k'asa tace
"Ku fito da ita"
Wani irin k'amewa suka yi ta juya zata fice daga d'akin har ta kai bak'in k'ofa ta juyo.
"Ku had'o da wannan tsummar jakar ta ta"
Baki suka had'a wajen cewa "aye captain "
Juyawa tayi ta fice ta barsu suna kici-kicin d'auka Nadine. D'aya d'aga cikin su ya sab'ata a kafad'a D'aya kuma ya d'auke ki kayan nata. A biye suka fice da ita kaman yanda suka shigo a b'oye. Wata hanya dake k'arkashin k'asa suka bi mai tsayi sai gasu sun fito daga cikin masarautar ta can k'ofa baya. Dankareriyar motar da yarinyar ke jiransu suka jefa Nadine bayan booth da kayan ta kafin su buɗe motar su shiga baya . Matar dake ciki taja motar da mugun gudu suka bar gurin.
NADINE POV.
Ruwan sanyin da aka kwaramin shi ya yi sanadin farkawa ta na tashi firgice ina ihu amma baya fita saboda manne bakina da sukayi da salatif. Ban gama farfaɗowa daga sumanmen ruwan da suka shekamin ba naji an d'auke ni da mahaukacin mari da saida naga wuta a take habo ya b'allemin. Gashin kaina aka fincika da mugun k'arfi aka dago kaina. Dishi-dishin da nake gani baisa na gane wake tsugunne gabana ba saida na runtse ido na da k'arfi na buɗe sannan ganin nawa ya fara dawowa daidai. Fatar bakina na furta sunan Anita da babu sauti.
Wani murmushi tayi mun na tsananin mugun da samun nasara
"Me nace miki idan har ki ka sake yin abu da zaki ja hankalin Azrah kan ki?,yau Azrah saboda ke ya yiwa baiwa dana sata aiki hukunci?. Duk irin abunda nake bai taɓa d'aga kai ya nuna ba dai-dai bane sai a kan ki. Wacece ke? Ke ba kowa bace face baiwa kaman sauran bayi. Aina gaya miki idan hakan ta kasance sai kin kwammace mutuwar ki"
Sosai hawaye ke gudu kan fuskata da nake jin b'arin data maren ya kumbura sumtum dan ido na guda d'aya bana gani dashi sosai. Bayan rufe min baki da sukayi harda hannu na da k'afafuwana suka d'aure. Wace irin kiyayya ce wannan? Me yasa ta kasa gane cewar King Azrah babu abunda ya had'ani dashi face tsantsan kiyayya?. Me yasa ta kasa gane kishin da take a kaina duk aikin banza take. Nikam me yasa bani da sa'a a rayuwata ne?. Had'uwa ta da KING AZRAH babu abunda ya jefani ciki sai masifa da tashin hankali.
Lokacin da baisan da zamana ba ina rayuwa ta cikin kwanciyar hankali aikin da nake ba komai bane kan masifar da nake had'uwa ta dashi. Duk abunda ya sameni saboda shi ne. Miƙewa tayi tsaye tana murmushi sai a lokacin na samu damar ganin inda nake. Bakin teku mu ke. Yau garin babu haske ki taurari babu bare hasken wata. Ruwan ya yi bak'ikki'rin baka ganin komai yanzun ma saboda y'ar torch da suke haskawa ne yasa naga fuskarta.
"Ku yi abunda nace daga bisani ku jetafa cikin tekun"
A razane na ke kallonta ina girgiza kai ko zataji tausayi na amma sai ta juya abun bayan ta bini da wani last kallo ta wuce ta barni da wad'annan kartan mazan. Tana b'acewa suka juyo kaina suna wani sinister smile da mummunan fuskar su. Tuni na k'arawa kuka na gunji na fara Jan jiki nan k'asa. Ina jin dariyar su suna bina harda tafawa alamun hakan ya yi musu dad'i. Saida suka bari na wahala duk na kurje ciki da k'afafuwana sannan suka kama k'afata kee suka jani zuwa bakin tekun inda ruwa ke haurowa.
Juyo dani sukayi d'aya ya hau kan ruwan cikina irin ya sani tsakiyar sa bawai zama ya yi ba. Kici-kici na fara ina gunjin kuka sosai sai dariya suke ya kawo hannu kan mad'aurin rigata zai warware. Sosai nake girgiza kai ina kuka na fitar hayyaci. Kiris ya rage ya kai hannu wata irin iska mai k'arfi ta kad'a sai wuff ta d'auke shi tayi jifa dashi can gefe. A rude na d'ago ina kallon d'an uwan nasa daya kai masa d'auki shima iskar ta d'auke sa tayi jifa dashi gefe.
Da wani irin tsoro da firgici suka tashi da mugun gudu suka bar ni nan kwance ina neman d'auki. Innalilllahi wa Inna'ilaihi raji'un. Allah ka kawomin d'auki kaga halin da nake ciki. Ka tseratar da rayuwata daga nan. Wossh naji iskar ta kad'a saman kaina kafin naji sunana saitin kunne na dama
"SULTANAAH "
A guje na runtse ido ina kuka sosai . Na shiga uku ni NADINE. Flash rayuwata tamin sanda ina yarinya da nayi experiencing irin wannan abu na d'auka ba komai bane yarinta yasa naji kaman hakan ne.
"SULTANAAH, kar ki damu ina tare dake a ko da yaushe. Buɗe idon ki bazan cuce ki ba"
Maimakon nayi abunda naji sai na k'ara runtse ido ina furta duk Addu'ar data zo bakina. Tabbas yanzu na yarda nayi gamo tun ina yarinya wanda yarinta yasa na kasa gane hakan. Ji nayi kaman anyi sama dani cikin iska kaman hannu yasa ya d'auke ni. Jikina in banda kakkarwa babu abunda yake kafin naji an kwantar dani cikin zunzurutun yashi. Shiru ban k'ara jin wani motsi ba bayan hakan har wajen sakan uku. Jin babu wani motsi kusa dani na fara k'ok'arin buɗe ido.
Kan wata kyakkyawar fuska mai tsananin kyau na sauke kwayar ido na dake durkushe kusa dani. Ido na zaro sosai ina k'ok'arin ja da baya. Wannan idon nasan wannan idon. Idon da nagani a bak'ar ranan da bazan tab'a gogewa a rayuwata ba. Ranan da narasa komai nawa na rasa farin ciki na . Ranan data janyo na shiga cikin k'angin rayuwa. Tsananin firgice yasa na sume.
✿︎✿︎✿︎✿︎
THE PALACE.
A zafafe ya juyo kan dakarun sa dake tsaye tsakiyar fada sun durkushe kansu a k'asa.
"What did you mean she's gone?"
Murya na rawa d'aya daga cikin su yace
"Mun duba kaf cikin masarautar nan bamu ganta ba. Har can b'angaren da take muka je suka ce rabun su da ita tun ranan da aka d'auko ta daga can. To sai kuma wata take ce mana ko taje wajen Maria ne duk da bata tab'a fita ba. Muka je gidan Maria dan mu duba itama bata can"
Da wani irin zafin rai ya sauko daga kan karagar Mulkin sa da yake zaune. Kaman dai koda yaushe fararen kayane a jikinsa riga da wando sai ya dora wata shegiyar