Showing 3001 words to 6000 words out of 21599 words
kawai naga kaman mutanen sun zube k'asa suna kururuwa daga nan ban k'ara sanin komai ba ido na ya rufe ruff.
βοΈ βοΈ
πππππΈβπΈπΈβ
πππ πππππππ ππππππππ
ASHANTY LOVE.
β
βπ'π π ππβπβ
Chapter
5/10.
β€οΈ EID MUBARAK β€οΈ
18YRS LATER.
EGYPT.
Bazan iya ce muku ga yanda aka yi muka tsinci kanmu cikin wannan k'asa ba k'ark'ashin wannan masarauta ta zalunci. Mun farka ne kawai mun ganmu anan kewaye da masu tsaro(Gaurds). Tunda muka shigo wannan masarauta aka rabamu kowa da b'angaren daya ke aiki. Tun ranan kuma ban k'ara saka Julde da Azima a ido na ba da sauran yaran da muke tare. Uwar d'akina da nake gurin ta Mama Maria ita ke cemin suna can wani b'angare cikin masarautar saboda girman ta da kuma rashin y'anci da bayi basu dashi basu isa su fita ba sai in aiken su aka yi. Yau tsawon shekara goma sha takwas ban taΙa fita daga masarautar nan ba bare nasan ya rayuwar waje take. Muna can b'angaren bayi dake k'arkashin k'asa. Bamu rasa ciba bare sutura don nikam Allah yaso ni da arziΖi uwar d'akina wato Mama MARIA ita keda ragamar girkin Sarki da sarauniya da y'ay'an su. Ita ke musu wanki da sauran wasu abubuwa daya dangance su.
Babban abun mamakin shine tun ranan da muka tsinci kanmu cikin wannan k'asar na daina wannan ganin da nake cikin duhu. Har zuwa yau kuma na kasa tantance abunda na gani ranan bakin teku kafin na suma. Shin idon da na gani da kuma sillin gashin da naga yana kad'awa cikin iska gaskiya ne ko kuma imagination d'ina ne?. To amma kiran da naji ana munfa da sunan da babu wanda ya san shi sai iyayena fa?. Allah ne kad'ai masani. Nima kuma tunda na mallaki hankalin kaina na watsar da komai bana son ma na tuna wannan bak'ar rana da baza ta tab'a gogewa a kwanyar kai na ba sai ranan da zan koma ga mahallicina.
A yanzu bani da komai sai wannan sarkar da Abbu ya bani. Duk lokacin da nake begen su zan d'auko sarkar ina kallon ta ina kuka. Ganin yanda sarkar ke sani cikin damuwa sosai Mama Maria ta sani na cire sarkar na ada nata. Ta hanani daukan ta sai dai in babu idon ta. Kuma hakan da tayi ya yaye min damuwar rashin su matuΖa.
Mama Maria babbar macece balarabiyar Egypt. Tana da aure da yara biyu, halin rayuwa yasa ta karb'i aiki cikin masarautar kuma Allah ya taimake ta macece ita mai gaskiya da amana ,dalilin da yasa sarki da sarauniya suka yarda da ita d'ari bisa d'ari. Duk irin wannan bauta da take musu basu amince da fitarta daga masarauta ba sai lokaci zuwa lokaci. Wato sai idan abu mai muhimmanci ya taso. Tace hakan ya yi mata matsawar mijin ta da yaranta zasu ci, su sha su kuma saka sutura mai kyau.
Babu laifi gaskiya ana bata albashi mai tsoka. Har mamaki nake idan naga yanda take yin komai saboda y'ay'an ta. Wata rana haka zan zauna nayi ta kuka idan na tuna Abbu da Innati. Zamana da Mama Maria yana d'an debemin kewar rashin su dan ta d'auke ni tamkar yarda ta haifa. Ta koyamin larabci duk da nima ina ji amma ba sosai ba. Yanzu idan na juye harshe baza kace nasan wani abu waishi hausa ba. Kusan mutanen da muke wannan b'angaren d'ai-da'i kune ban koyawa hausa ba. Wasu sun d'an iya wasu kuma har yanzu sun kasa cikin su harda Mama Maria da bata iya sosai ba harta sunana NADEEYAH bata iya furta shi sai kawai ta samin NADINE da harshen su.
Duk wanda ya sanni anan da sunan da yake kirana dashi kenan. Bayan wannan kuma sai harshen nasara da muke makaranta shi nan b'angaren mu akwai dogari (Gaurd) na musamman dake koyar damu turanci don ya zama kaman doka ne mutum ya koya saboda gudun had'uwa da wani daga cikin masu Mulki.
A yanda nake ji sunfi yin turanci a kan harshen su mai dad'i yaran Manzon mu Annabi Muhammad (S.A.W) saboda y'an boko ne. Kaf cikin su jinin sarautar basu cika zama ba a nan sai kasashen waje. Shi yasa ma ilimin addinin ya yi musu k'arancin.
Ina da shekara goma sha bakwai cikin masarautar Egypt KING SAIFULMULK da QUEEN AIRA suka sauka daga kan kujerar Mulki suka d'ora d'ansu da naji anawa lak'abi da EZKE'IL wasu suce AZRAH. A yanda naji ana labarin sa mutum ne shi mai masifar had'arin gaske. Bashi da imani bashi da tausayi. Maganan Mama Maria a koda yaushe nayi hankali koda wasa kar na bari hanya ta had'ani dashi. Kai ko hanya nabi naji ana labarin sa tace na chanza wata.
Ranan nad'in nashi kaf cikin mu babu wanda ya runtsa. Yanda muka ga rana haka muka ga dare. Wuni mukayi muna aiki babu kama hannun yaro. Musamman ma mu da muke b'angaren girki. Mama Maria har ciwo tayi saboda gajiya ga kuma girma dake k'ara kamata. Da yawa wasu abubuwan nike yinsu nace ta huta. Shi yasa aikin ya zame min jiki, Idan ka cire ciwon jiki da kai babu wani bayan hakan. A ranan ne zan iya cewa muka fito daga b'angaren mu ,muka mik'a abinci wajen da ake ajiyewa a shiga dashi cikin masarauta.
Tunda ake fita dashi ban taΙa karb'a na fito da dashi ba hasalima nan gurin mu dogarai ke shigowa su kwasa suyi waje da su. D'ai-da'i kun rana ne Mama Maria ke fita da abincin da kanta bata tab'a cewa nazo muje tare ba. Wajen had'a kayan ne muka had'u da Fahima. Rungume juna muka yi cikin matsanancin farin cikin ganin juna. Harna fidda ran k'ara ganin ta sai gashi Allah ya had'amu. Tun daga ranan muke d'an satar jiki muna haΙuwa.
Ita tana can b'angaren masu wanki.
βΏοΈβΏοΈβΏοΈβΏοΈ
Yau ya kama ranan weekend. Tun dare Mama Maria ke kwance zazzabi mai zafi ya rufeta. Da kyar ta iya yin sallan Asuba don ko karatun Qur'ani da take koya min duk bayan sallan asuba kasawa tayi yau. Na shiga cikin matsanancin damuwa da ciwon nata hankalina duk ya tashi. Idan itama ta mutu bani da kowa yanzu a duniya sai ita. Ina yin salla na miΖe da sauri na fito katon kitchen d'in dake nan kaman gari masu aiki nata kai kawo sai kayi tunanin kasuwace. Da sauri na fara bin kayan ganye dake ciki kwanduna ina dubawa har Allah ya taimake ni na samo ganyan lemon. Shayi na had'a mata da ganyen da y'ay'an coffee.
Cikin y'ar k'aramar butar shayi ta silver na juye na d'ora kan plates da d'an k'aramin kofin butar. Ragowar abincin da aka kawo daga masarauta nabi da sauri ina d'an duba abu mai dan ruwa-ruwa. Kayan abinci ne gasu nan sunfi kala ashirin. Nama ne , kaza ce ,kifi ne, snacks ,kayan ganyayyaki ,fruits ne gasu dai bila adadin dan wasu ma ko tab'asu ba'a yiba. Haka kullum zamu dage mu girka a dawo da rabin abinci ba'a tab'a ba. Shi yasa babu yunwa mukam a gurinmu kaman sauran b'angarorin. Dan muna ci mu koshi har sai mun ture.
Kaza na hango katuwar gaske kan wani plate an shak'e da abubuwan ci wasu ma baka sanin mene. Da sauri na d'auki plate na yanka k'azar na d'ora a kai na kwashi romanta da yawa na zuba na hada da d'an snacks na koma d'akin mu da sauri.
A tsaye na tadda Mama Maria tana ta rawar jiki da babban d'anta da kanwar sa dake binsa. Huzaifa da Jalila. Kaya suke sa mata suna ganina fuskarsu su ta cika da fara'a. Ajiye kayan nayi cike da farin cikin ganin su nace
"Huzaifa , Jalila. Marhabanbikum, kaifal hal?"
A tare suka bani asma " Alhamdulillahi, kaifa Anty?munzo tafiya da Mama ne saboda yanayin jikin ta, zata koma gida ta d'anyi jinyar ta acan har Allah ya bata lafiya"
Ido na zaro tuni ruwa sun fara cika su. Idan suka tafi da ita zanyi zaman kad'aici. Babu yanda zanyi haka na taimaka musu muka shirya Mama Maria ina k'ok'arin hana kaina kuka. Duk abunda nake nasan Mama Maria na kallo na tasan kuma dakiya ce kawai nake saboda babu yanda zanyi. Muna gama shirya ta Jalila ta kwashi kayanta suka rik'e ta zasu fita da ita. Hannuna ta kama ta tallafo fuskata. Hawayen da nake ta k'ok'arin riΖewa suka tawo shar kan kuncina. Murmushi ta yi na wanda ke jin jiki tace.
"Ki kwantar da hankalin ki Nadine, da zarar na warke zan dawo kinsan babu yanda za'ayi nayi nesa dake sai in ta kama dole ne. Yanzun ma naso tafiyar dake ban samu wannan alfarmar ba saboda King SAIFULMULK da QUEEN AIRA basa k'asa sai EZKE'IL. Kinsan wane AZRAH yanzu ma da kyar ya amince wa Huzaifa da Jalila su d'auke ni saida ya ganni cikin matsanancin hali tukun. Nadine ki kula da kan ki har sanda xan dawo kar kiyi wani abu da zai jawo hankalin EMPEROR AZRAH kan ki don Allah Nadine"
Ina kuka na d'aga mata kai. Ba yau ta saba tafiya ta barni ba. Duk inda zata je kuma bata wuce kwana biyu ,yau d'inne kawai nake jin kaman wani abu na shirin faruwa idan ta tafi ta barni. Huzaifa da Jalila suka hau dariya suna tsokana ta dole na ware muka fito nayi musu rakiya har bakin k'ofar mu. Ban bar bak'in k'ofa ba saida suka b'acewa ido na na sauke ajiyar zuciya mai k'arfi na koma ciki.
Ranan wuni nayi babu kuzari. Harta Fahima data saci hanya tazo muyi hira sai gajiya tayi ta tafi dan duk abunda tace sai dai na bita da eh,ko A'a.
Kwana biyu da tafiyar Mama Maria na kasa warware wa. Duk abunda nake ina yinsa babu kuzari. Wajen la'asar yau na fito dauke da kwando dana zubo kayan ganye daga lambu dake can bayanmu. Azeemah dake aikin Mama Maria duk lokacin da bata nan ta aike ni na deb'o mata. Tafiya nake ina y'ar wak'a ta larabci da Mama Maria ta koyamin duk kewar ta ta dame ni. Bansa ya akayi ba na fito wani katon Garden dake nan gari guda ga wasu irin bishiyu masu masifar kyau da suka k'awata gurin an kuma kewaye gurin da kujerun glass da aka yiwa ado da furanni masu kyan gaske. Turus na tsaya ina kallon aljanna duniya. Ban taΙa sanin da akwai gurin nan ba sai yanzu. Can gefen sa wani irin kwami ne dake zubda wani irin ruwa mai shegen haske kaman madara ga wasu irin fulawoyi dake zuba cikin sa da wani irn kamshi da kukan tsuntsaye masu masifar kyau dake shawagi a gurin.
Nikam ya aka yi bansan da wannan aljannr duniyar ba duk tsawon zamana cikin wannan masarautar?. Dube-dube na fara ina tunanin hanyar dana biyo ta kawo ni nan. Chak idon nawa ya tsaya kan wata hallita mai masifar kyan gaske. Tubarakalla MashaAllah, hak'ika babu abun yabo da bauta sai Allah. Bayansa kawai na gani nasan cewa koma wane wannan ba k'aramin kyakkyawan mutm bane.
Dogone mai faffaΙan kirjin duk da bayan nasa kawai nake iya gani yanayin zubin halittar sa ya nuna shi d'in maji k'arfi ne. Gashin kansa dake tufke tsakiyar bayan sa nabi da kallo baki sid'ik dashi har tsakiyar bayansa duk da ya tufke shi. Wata irin tsayuwa ya yi bak'in kwamin dake zubda ruwa hannun sa goye a bayan sa ga wata irin tsuntsuwa mai masifar kyau kan k'afad'ar sa. Kayan jikinsa riga da wando farare kaman na Pakistan mara nauyi nabi da kallo da basuyi nuni da shi ko wani mai muk'ami bane cikin masarautar. Murmushi nayi a raina nace ai dole ma na kulla k'awance dashi kodan saboda kyansa duk da ban taΙa ganin sa ba cikin masarautar. Wata kila sabon d'auka ne cikin bayin da aka d'auka satin daya wuce.
A hanzarce na k'asara inda yake tsaye cikin sand'a . Ashe yaji ni dan a wani irin slow ya juyo inda nake. Kalu'innalillahi. Chak numfashi na ya d'auke sanda nayi arba da kyakkyawar fuskarsa. Tunda na taso tsawon rayuwa ta naji yanda ake zuzuta kyau na, amma wannan bawon Allahn ni ba komai bace a kansa. Ban taΙa ganin mutum mai tsananin kyau kaman sa ba ,duk da ba fita nake ba nasan ko na fita da wuya a samu mutum mai masifar kyan sa. Wata kila ma yafi EMPEROR EZKE'IL kyau kaman yanda naji ana zuzuta kyawun nasa.
Murmushi nayi mai kama da yak'e nayi tsuru-tsuru dani kaman wadda aka kamata tana sata. Kwayar idansa dake bak'a sid'ik da ita ya zubamin ya d'aga cikakkiyar girarsa guda d'aya da suka kusa had'ewa . Cikin inda-inda da rashin sanin abun fad'a nace da larabci.
"Assalamu'alaikum. Ya kke?, hala kai sabon d'auka ne anan?"
Shiru bai bani amsa ba sai idon sa daya zubamin ga uban kwarjini da yake dashi kaman na zura a guje amma na dake don ina son gwada damata. To ko bayajin larabci?. Kai na gyad'a na juya harshe da turanci nace.
"Hey are you knew?"
Nan madai shiru bai bani amsa ba. Na fara tsarguwa da kallon da yakemin zuciya ta tace ki kama gaban ki Nadine. Shawarar zuciya ta na d'auka na juya da sauri zan tafi sai kuma wata zuciyar tace ki gargade shi ya yi hankali cikin masarautar nan ya iya takun sa. Juyowa nayi da sauri na fara magana ina yi da larabci ina had'awa da turanci kai harma da Hausa tsabar yanda na rud'e da kwarjinin sa.
"Kayi hankali cikin masarautar nan idan kai sabo ne. Tunda har ka shigo masarautar nan nasan kasan wane KING AZRAH. Ba sai na tsaya ina maka dogon bayanin rashin mutuncin sa da rashin Imanin saba,amma dai kayi hankali da takun ka dan mugun mutum ne mai kan agwagwa, mummuna mai katon ciki. Nasan yanda ake cewa yana da kyau ko yatsan ka bazai kama ba...."
'NADINE ' Zuciya ta ta kirani da k'arfi. Chak na tsaya da b'ab'atun da nake Ina zare ido. Wani irin kallo naga yana min da naji hanjin cikina sun kad'a. Shikenan na b'ata damata nasan zama abokiyar sa. Nasan yana min kallon mahaukaciya na tsaya ina ta b'ab'atu bana ko Jan numfashi daga haΙuwa da mutum bansan waye ba?.A guje na juya a sittin na bar gurin cikin matsanancin kunya.
βοΈ βοΈ
πππππΈβπΈπΈβ
πππ πππππππ ππππππππ
ASHANTY LOVE.
β
βπ'π π ππβπβ
Chapter
11/15.
Ban tsaya da gudun ba don burin kunya saida na tabbatar na sadu da sashen mu. Kitchen na nufa kai tsaye na ajiye kayan lambun dana deb'o kan kanta na durkusa ina haki hannuna dafe da k'irjina dake bugawa. Muryar Mama Azeema naji a kai na d'ago da sauri ina kallon ta da murmushi kan fuskata dani kaina na rasa dalilin sa.
"Ina ki ka shiga tun d'azu ki deb'omin kayan lambu kawai?"
Y'ar dariya nayi mai kama da yak'e nace
"Yi hak'uri Mama Azeema bansan zan dad'e haka ba. Na tawo ne na kauce hanya na b'ata "
Ido ta zubamin tana jiran k'arin bayani. Idan nace mata na had'u da wani hanyar dawowa ta zata ce babu wani b'ata da nayi da sani na ne. Ni ko yama sunan sa? Allah yasa gobe mu had'u na tambaye shi. Kai na sosa nayi saurin kawar da kaina daga kallon tuhuma da takemin.
"Wlh Mama Azeema b'ata nayi. Gani kawai nayi na bulle wani Garden mai shegen kyau. Ban taΙa sanin da akwai shi ba ,koda