Showing 15001 words to 18000 words out of 21599 words

Chapter 6 - SULTANAAH Book 1 by Ashanty love.txt

27 Nov 2024

1662

da ihu nayi magana murya ta a shak'e. Na tsane shi, na tsane shi


"Mugu Azulumi. Me ka ke so a tare dani?. Ka kyale n..."


Maganan ta mak'ale saboda wani barin makauniya daya d'auke ni dashi saida naga wuta. Kunnena ya bada wani shuu naga wani duhu ya kaure kwayar ido na.
D'akin gaba d'aya ya amsa k'arar marin. Hannu na mik'a zan dafe kuncina ya kama hannun nawa da k'arfi ya fisgoni na miƙe tsaye kafafuna na rawa. Yanda ya matse hannun nawa kaman zai K'arya yasa na k'ara sakin kara na dago da idona da hawaye ke ambaliya cikin sa na d'ora su kan fuskarsa da manya deep black eyes nashi suka fara jaa tsabar b'acin rai.


"Don't you dare raise your voice at me, I'm your KING remember that. I cannot wait to make you my personal slave to boss around."


Wani smirk ya saki ya hankad'ani na zube a k'asa . Na shiga uku ni NADINE. maganan Mama Maria a koda yaushe ita ce


' kiyi hankali karki kuskura koda wasa Azrah yasan da zaman ki cikin masarautar nan. Sai gashi banji maganan ta ba na kasance mara sa'a duk haɗuwa ta dashi babu sa'a a cikin ta'


Maganan ta dawo dani daga duniyar tunanin dana lula na d'ago da sauri ina kallon sa


"Ki fara barci da ido a buɗe miss Nadine. Baki da masaniyar abunda zai same ki ,because this is just the beginning "


Yana dasa aya ya juya da tafiyar nan tashi ta izza ya fice daga d'akin.


Hannuna daya murd'e na d'ora a ka na rushe da matsanancin kuka ina kiran MAMA MARIA.




✿︎✿︎✿︎✿︎




OMAN.
MIDDLE EAST.


THE PALACE.


KING AL'HUSSAIN CHAMBER.




"uhhhm, uhmmm"


Sautin dake fita kenan cikin tafkeken d'akin daya karad'e ko ina. Magidancin balaraben mutum ne da a kalla zai haura shekara hamsin da biyar da magidanciyar mace da za tayi talatin da takwas zuwa da tara. Yanda suka yi nisa cikin wata duniyar daban baisa sun kula da zoben shi na gwal dake kan wani k'aramin tebir na zinare ya d'auki wani irin haske kaman fitila. Sai kuma diff ya d'auke a take zoben ya yi bak'ikki'rin kaman gawayi. Baza ka tab'a cewa zoben gwal bane.


Can sai d'akin ya kaure da wata irin iska kaman guguwa. Za kayi mamaki idan nace komai a rufe yake rufe. Babu ta inda iska zata shiga. Wannan ne yaja hankalin King Al'hussain da Kuyangar sa ya tashi da sauri yana bin d'akin da kallo kafin idansa ya fad'a kan zoben da ya yi baki kaman bak'in murhu.


Wani irin wuntsulawa ya yi ya fad'o daga kan gadon ya d'auko zubon cikin matsanancin mamaki yana duban sa. Meke nan yake gani?. K'afad'ar sa Aina ta dafa ta bayan sa sakaye da zanin gado kan k'irjin ta . Kafin ta kaiga magana ya buga mata tsawa.


"Get out"


Sanin halin Al'hussain dan haka bata musa ba ta tattare zanin ta cukwukuye a k'irji tayi waje abun ta. Tana fita ya koma kan gadon ya zauna yana duba zoben dake hannun sa zaman keda wuya iskar ta tsaya chak sai ga magana mai amo cikin d'akin.


"Your highness"


Bai daina kallon zubon ba ya fara magana


"Me nake gani ? Mene amsar hakan?"


Muryar ta bashi amsa da


"Hak'ika abunda ka ke gani ya shugaba gaskiya ne. Wannan shedace dake nuni da cewar akwai jinin Al'HASSAN a doron k'asa, amma mun kasa gano inda Wannan gudan jini yake. Kaman yanda muke baka kariya haka zalika Wannan jinin na Al'HASSAN yana samun kariya daga irin mu. Kuma irin namu masu tsananin k'arfin Mulki . Dalilin da yasa mun kaso gano inda Wannan gudan jini yake bare mu gano mab'oyar sa"


Wani irin tsawa Al'hussain ya daka cikin d'akin da k'araji yace


"Wannan bashi ne damuwa taba. Taya aka yi jinin Al'HASSAN ke raye bayan an shedamin mutuwar su?. Hakan na nufin akwai wanda suka ha'inceni kenan?."


"Tabbas haka ne ya shugaba, babu kuma wanda zamu tuhuma don gaba d'ayan su basu wanda ke raye cikin su. "


Miƙewa ya yi cikin zafin rai ya hau safa da marwa tsakiyar d'akin kafin ya tsaya gaban wani katon enlargement hoto da aka rufe da glass. Za kayi matsanancin mamaki idan kaga hoton da suke su biyu. Tsananin kamar da suke babu ta yanda zaka banbance su. Komai nasu iri d'aya ne tun daga kan bak'in gashin su dogon fuskarsu da kuma kwayar idon su dake nan GOLDING BROWN.


Hannu ya kai ya dora kan d'aya daga cikin su ya shafa kaman mai jimami can kuma ya dunkule hannu ya kai masa naushi. D'agowa ya yi ya zubawa hoton ido kaman yana magana da hoton.


"Brother " ya kira sunan da wani irin disdain. Kaman wanda aka d'urawa kashi a baki.


"Babu wani blood naka da zaiyi numfashi a doron k'asan nan matsawar ina raye. Duk abunda zai shiga tsakanin soyayya ta zanga bayan sa. NEELAM is mine. Zan cigaba da ganin bayan duk wanda zai rab'eta matsawar daga tsatson ka ya fito"


A fusace ya juya yana kallon tsakar d'akin cikin karaji yace


"Ku nemomin su duk inda suke a fad'in duniya "


Iskar ta kad'a da k'arfi kafin kuma ta b'ace kaman an d'auke ruwa. Juyawa ya yi saman hoton ya mik'a hannu ya danna wani abu kaman mukunni fitila. Sai ga bangon ya rabe kaman kofa ya kutsa kai ciki. Ashe wani irin boyeyyen d'akine da yaci uwar wanda ya bari. Komai na d'akin da gwal aka yishi. Can saman makeken gadon na hango mace a kwance. Jin motsin yasa ta d'ago a hankali kafin ta juyo gaba d'aya wajen k'ofar.


Hasbunallahu wa ni'imal wakil. Me NADINE keyi a nan tambayar da nayiwa kaina kenan?🤣. In banda shekaru da zata nunawa Nadine to da tabbas sai nace rufa ido tayi ta rigani zuwa.🤣


Babu abunda ta bari na Nadine in ka cire kwayar idon ta . Ita wannan kwayar idon ta bak'ace wuluk sab'anin Nadine nata kwayar idon Golding Brown ne kaman na Al'hussain .


Tsakiyar d'akin ya tsaya rike da kugu yana kallon ta kaman yanda ta zuba masa. Sai a lokacin na samu damar k'are masa kallo. Duk cewar shekaru sunja amma lifayeyyen mutum ne mai tsananin kyau da kwarjini. Da alama yana kula da kanshi sosai don kyawun jikinsa ko wani saurayin Albarka.


Komawa tayi ta kwanta ba tare da tace komai ba. Wani irin murmushi ya saki ya nufo gadon da sauri . Har ya d'aga k'afa zai hau gadon sai kuma ya tsaya kaman wanda ya tuna wani abu. Da sauri ya juya ya shige wata k'ofa . Bai jima ba ya fito d'aure da tawul a kugunsa yana goge lallausan gashin kansa daya sha gyara. Duk abunda yake bata juyo ba sai ma runtse idon ta da tayi.


Feshe kanshi ya yi da turarurruka kafin ya afka kan gadon da saurin sa ya jata kaman wani maye ya matse cikin k'irjin sa yana shinshinan wuyatan kafin ya fara lashen wuyan kaman ya samu sweet. Wasu hawaye masu zafi suka biyo kuncin ta ta k'ara k'ank'ame ido. Tanaji yana juyata kaman waina babu alamu dake za tayi wani attempt na kwace kanta da alama kaman abune data saba dashi. Tayi-tayi iya yanda za tayi don kwatar kan nata amma babu nasara shi yasa ta fawwala Allah ya kawo mata agaji.


A b'angaren Al'hussain ba'a cewa komai , bai damu da kukan da take ba sai ma zuba uban sumbatu da yake yana furta mata irin matsanancin son da yake mata zai iya yin komai indai a kanta ne. Wannan kalaman nasa suka k'ara sata rushewa da matsanancin kuka. Baibi ta kanta ba ya cigaba da bugunta kaman doki yana sakin layi.








♔︎ ♔︎
𝕊𝕌𝕃𝕋𝔸ℕ𝔸𝔸ℍ
𝒕𝒉𝒆 𝒖𝒏𝒌𝒏𝒐𝒘𝒏 𝒑𝒓𝒊𝒏𝒄𝒆𝒔𝒔




Ashanty love.












☆𝐈'𝐌 𝐀 𝐒𝐓☆𝐑☆








Chapter
41/45.






Washegari na fito ina taya Mamee da Layher aiki da k'arfina. Sam ban bari maganganun sa sunyi tasiri a kaina. Shi ai ba Allah bane babu kuma abunda ya isa ya yimin sai abunda Allah ya rubuta zai same ni. Wanki na taya su muka yi sosai har wajen azahar. Muna gamawa muka yi alwala muka yi salla kafin mu nufi tebir d'in abinci. Kaman dai koda yaushe kowa ya d'auki plates nashi zuba cimar da babu sauyi. D'an kwana biyun nan da nayi ina cin abinci mai kyau yasa na manta da wannan cimar. Sai yanzu na tunama to daga ina wancan abincin ke zuwa?. Da kyar na iya d'aukan plate na kai hannu zan debi waken mai tsaron abincin tayi saurin tare ni. Hannu ta d'aga da sauri tace


"A'a ke akwai naki abincin da aka ce na baki"


Wani irin dad'i ne ya ratsa ni domin nayi tunanin abincin da ake kawomin ne. Sunkuyawa tayi ta d'auko plate k'ark'ashin gurin ta mik'o min. Harna miƙa hannu zan karb'a na tsaya ina kallon ta cike da mamaki. Ni take so naci wannan abincin?. Abincin ne aka barshi ya lalace don waken har wani irin doyi yake shinkafar kuwa da gani tayi yami su kansu ganyan dake kai sun yamushe. Gira ta d'aga tana kallo na ganin ban karb'i abincin ba ta saki murmushi mugunta.


"Ki karb'a mana kinja kin tsaya kina kallo .umarni ne daga sama kin san kuma illar karya doka"


Muryar Mamee naji da Layher kusa dani.


"Haba ke kuwa .Ya zakice wannan abincin za taci?, abinci ya lalace ace shi zataci. Anyi adalci kenan? Ko so ki ke ya yi mata wata illar?"


"Au to ni zaku tsaya kunawa kumfar baki?too ni ina ruwana?, nima umarni ne aka bani kuma nake bi don haka itama dole tabi umarni"


Cece-kucen nasu ya yi min nisa don nayi zurfi cikin tunanin maganganun sa. Bansan cewa rashin Imanin nasa ya kai haka ba. Gwanda kawai na mutu nima ko na huta da wannan ukubar da nake ciki. A zafafe na juya na warce kwanon daga hannun ta taja mugun tsaki. Ban saurareta ba na wuce Mamee da Layher biye dani suna magana kar naci abincin nan. Duk wanda yace naci abincin nan to bashi da imani mugun mak'iyi nane. Wai danma basuji waye ba don nikam nasan bani da mak'iyi kaman shi.


Guri na samu na zauna na tankwashe k'afa. Mamee tayi saurin sunkuyawa zata d'auke kwanon na riƙe da k'arfi na hanata d'auka dole ta hak'ura ta kyale ni amma sai magana sukemin ita da Layher nayiwa Allah kar naci abincin nan. Toshe kunnuwana nayi na rufe ido ina tunani. Badai burinsa yaga ya bak'anta min ba. To zanci abincin kowa ya huta dama kuma bani da kowa da zaiyi rashina sai Mama Maria. Numfashi naja mai k'arfi dan hana kwallan da naji ta cika min ido fitowa. Ido na buɗe na d'ora kan abincin kafin na mik'a hannu da sauri na deb'o abincin.


Wani Numfashin na k'ara ja mai k'arfi kafin na d'auke numfashi saboda warin abincin daya dake ni. Da sauri na kai hannu baki bayan na k'ara runtse ido. Sakan d'aya ina k'ok'arin kai abincin baki cikin sakan d'ayan kuma naji wuff an warce abincin kaman iska sai kuma k'arar kwanon nawa da naji kaman anyi jifa dashi gurin gaba d'aya ya amsa. Kafin na kaiga buɗe idon nawa naji muryar sa cikin wani irin b'acin rai da k'araji


"Wanene ya bata wannan abincin taci?,kare ce ita ?"


Gurin ya d'auki wani irin shiru da azama na buɗe ido na don na tabbatar da abunda naji. Ban sauke idona a ko ina ba sai bayansa daya juyamin. Sanye yake cikin kananan kaya farare ya d'ora wata doguwar rigar sarauta bak'a da aka yiwa ado da gwal ba. K'afar sa sanye cikin wani flat takarmi mai rufe . Ya saki gashin kansa daya zubo har gadon bayan sa sai shek'i yake gashi bak'i sid'ik dashi.


Mafarki nake ne?. Na kasa gane inda ya dosa. Tsawa ya k'ara dakawa gurin ya amsa saboda yanda gurin ya yi tsit kaman babu mahaluki a gurin.


"Nace waye ya bata wannan abincin?"


Jikin wannan mai kula da abincin na rawa ta matso gaban sa daga can nesa ta durkushe a k'asa. Cikin tsananin tashin hankali ta fara bada hak'uri tana neman gafara hawaye na ambaliya kan fuskarta. Wani irin kallo ya watsa mata kafin naji yace


"Is she a dog?"


Wani irin jijjiga kai tayi kaman zata karya wuya don kukan da take ya hanata magana.


"To why zaki bata rotten food taci?"


Shiru bata bashi amsa ba sai sheshshek'ar kukan ta dake tashi cikin gurin. Wani irin takawa ya yi gabanta zo kaga yanda ake ja baya a guje. Gabanta ya wani irin durkushe k'afa d'aya a gaba d'aya a baya ya dan gicciya.


"D'auko abincin kici ina kallon ki"


A guje ta rarrafa tabi abincin tana ci. Loma d'aya tayi kuwa ta fara sharara amai kaman zata amayo hanjin cikin ta. Nayi tunanin aman da tayi zai kyale ta sai naga sab'anin haka. Kallo naga ya watsawa Gaurds nashi dake biye dashi. Cikin azama mutum biyu suka matso suka rirrik'eta d'aya ya tsaya a gabanta suka hau d'ura mata abinci babu imani. Ko numfashi basu bari tana shak'a. Da sun dura mata sunga ta fara yunƙurin amai zasu toshe bakin da hancin sai ta had'iye su k'ara d'ura mata wani.


Saida ta cinye abincin nan tass ta suka watsar da ita gefe ko numfashi bata iya ja mai k'arfi. Wannan abunda naga ya yi ya k'ara samin matsanancin tsoron sa. Bama ni kaɗai ba duk wanda yake gurin a mugun tsorace yake ko motsi mai kyau basa iyayi kan kowa na k'asa sai ni kaɗai dana kasa d'auke kaina daga kansa. Miƙewa ya yi daga durkushen da ya yi ya wani juyo inda nake zaune firgici yasa na k'asa motsawa dan ganin komai nake kaman a mafarki. Ido muka had'a na sakan biyu kafin ya juya ya wuce matakansa suka rufa masa baya.


What just happened?. A me ya kamata ma d'auki abunda ya yi? Kula?,damuwa? Kai A'a. Dole akwai wani abu dana kasa ganowa a tattare dashi. Idan bashi ne yasa aka bani wannan abincin ba to waye?. Anita, zuciyata ta bani amsa kaman ance na d'aga kaina kuwa na hango ta can baya tsakanin gini babu wanda ya lura da ita saini. Kallon da takemin ya tsorata ni matuƙa nayi saurin kawar da kaina daga kallon ta dan sai nake ji kaman tana ganin hanjin cikina.


Ihun Layher ne ya katse shirun da gurin ya d'auka ta fad'o kaina cikin matsanancin farin ciki tana tsalle kaman wadda aka yiwa albishir da aljanna.


"Wayyo Allah yau naga King Azrah ido da ido kuma kece sanadin hakan. Ai kuwa babu wani..."


Maganan ta ta ta mak'ale sakamakon kwadeta da Mamee tayi


"Shashasha kawai sake da Allah taji da abunda ke damunta. Kin fara wannan tunanin naki na gaibu "


Baki ta turo ta tashi tana sosa k'eya. Murmushi nayi na mik'e da sauri dan na bar gurin saboda idon Anita da nakeji a kaina kaman kaifin wuk'a. A hanzarce na bar gurin mutane sai bina suke da kallo kaman sunga sabon halitta. A guje na k'arasa shigewa d'akina na banko k'ofar. Jingina nayi jikinta ina maida numfashi.


Ganin tunanin bazai fissheni ba na d'auro alwala na tada sallan azahar bayan na idar na zauna ina tulawar karatuna nutsuwa na ratsani ta ko ina. Duk wata damuwar da nake ciki ta ya ye a wannan lokacin babu kowa cikin raina sai anbaton Allah da Manzon sa sai kuma iyayena da Mama Maria. Ban tashi ba saida nayi sallan la'asar sannan na samu guri na kwanta tunda babu abunda zanyi.


Har barci ya fara d'auka ta naji bugun k'ofa ta sama-sama ana kuma kiran sunana. Da sauri na tashi jin muryar Layher. Ina buɗe k'ofar ta kutso kai cikin farin ciki d'auke da kaya da muka wanke d'azu.


"Can you imagine yau zamu shiga masarauta da kanmu?. Mamee tace muje mu kai kaya aiki ya yi mata yawa. Sauri muje na kagu na taka k'afata cikin ta. "


Bata bani damar cewa A'a ba ta jani da sauri muka yi waje. Badan naso ba na bita muka nufi k'ofar shiga Palace sai zuba take tana tsalle kace yarince k'arama da aka bata alawa. Abun nata sai ya bani dariya duk damuwar da jimamin shigar da nake saida na dara. Muna zuwa bakin k'ofar babu wani musu suka buɗe mana muka shiga kodan sun ganmu da kaya ne niki-niki. Wani corrido mukabi mai shegen kyau dake cike da dakaru sai ga wata babbar mace ta bullo daga wata k'ofa . Tana ganinmu ta k'araso da sauri


"Yauwa kun kawo kayan ko wanne da inda zaku sashi"


Layher ta nuna tana d'aga kayan dake hannun ta ta nuna mata wata k'ofa


"Ke nan zaki shiga ki shimfiɗa zanin gadon ke kuma"


Ta juyo kaina " muje na nuna miki d'akin da zaki shimfiɗa na hannun ki"


Da sauri ta wuce na bita da kallo Layher kuwa a hanzarce ta fad'a d'akin da aka nuna mata. Murmushi nayi na girgiza kai nabi matar da sauri ganin tasha kwana. Bakin wata k'ofa mai kyau na sameta tayi saurin d'agamin hannu nayi sauri.


"Yauws ki shiga nan ki shimfiɗa kiyi ki fito"


Ko amsa bata jira na bata ba ta wuce ta da sauri kaman walk'iya. Kai na girgiza na tura k'ofar a hankali bakina d'auke da y'ar sallama. Ya illlahi ,rabbil Alamin. Tsananin kyawun d'akin yasa na saki baki da hanci ina kallo. MashaAllah Allahumma arzukuni wanda yafi wannan a Aljanna. Duk irin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login