Showing 6001 words to 9000 words out of 21599 words

Chapter 3 - SULTANAAH Book 1 by Ashanty love.txt

27 Nov 2024

1661

yake ba fita nake bane shi yasa babu lallai nasan dashi."


Ido waje naga tana kallona kafin ta kama hannu na da sauri taja ni gabanta.


"Me naji kina cewa Nadine?,kinsan inda ki ka tsinci kan ki kuwa?, wa ki ka gani a gurin ?,kin had'u da wani"


Kai na girgiza ina kallon fuskarta dake d'auke da tashi hankali k'arara.


"Babu wanda na haɗu dashi Mama Azeema amma me yasa naga kin shiga damuwa"


"Saboda wannan gurin b'angaren Sarakai ne . King Azrah yasa aka gina shi bayan nad'in sa. Babu wani bawa daya isa ya shiga gurin har saida iznin sa. Ko da ace ka shiga gurin ne cikin rashin sani sai ka karb'i hukunci. Akwai bayi da dama da suka samu b'atan hanya irin ki har yau babu wanda ya k'ara jin labarin su"


Shiru tayi tana maida numfashi na zuba mata ido ina tunanin mutumin dana had'u dashi cikin garden d'in. Suturar jikinsa na tuna da bata da banbanci da kayanmu na bayi. Mu mata muna sanye ne da doguwar riga mai d'an fad'i daga kasa wajen kugu an dan tattare ta kad'an ya zama kaman sket, sai saman rigar wajen k'irji da mad'aurai gudu uku. Rigar mai three quarter d'in hannu ce. Su kuma maza suna sanye ne da riga da wando ruwan toka mu kuma farare. Rigar kaman Y'ar Pakistan ce da wandon ta. Sai hula ko dan hankici da zamu daura a ka ga duk mai so.


Ance ko wane b'angare da irin kalan kayan su. Mu namu b'angaren kalan namu kenan. Ba'a chanzawa sai in ana cikin d'aki ko kuma ranan da babu aiki. Nikam ina dasu wajen kala goma da Mama Maria ke sawa ana d'inka min duk lokacin da aka samu yadi mai kyau.


Tunanina ne ya tsaya kan cewa shima bawan ne amma ba b'angaren mu ba. Yanzu haka ko shike kula da garden d'in shi yasa kayan sa suke farare kal . Gum nayi da baki na ban k'ara cewa komai ba na wuce na kamata aikin ina na taimaka mata da yanka kayan lambun dana kwaso. Har muka gama tunani na na kan wannan mutumin Mai Kyau. Sunan dana rad'a masa kenan. Saboda rashin Mama Maria nina fita da abincin da taimakon Mama Azeema da sauran mutane da muke abinci tare muka kai can inda ake ajiyewa. Shi kanshi gurin d'aukan abinci idan kaje kaman karka fita saboda kyau. Komai Allah ya wadata su dashi dole kuwa suyi abunda suka ga dama. Allah ya kyauta.




✿︎✿︎✿︎✿︎




Tsawon kwana biyu kenan da haɗuwa ta da wannan bawan Allah har yau kuma ban k'ara sashi cikin ido naba. Sai naji duk babu dad'i na saddakar cewa bazan k'ara ganin saba. Duk irin kashedi da Mama Azeema tayi min akan garden d'in nan ban fasa satar hanya ba nabi ko Allah zaisa na ganshi ta wajen don tunani na yafi k'arfafa ne a nan yake nashi aikin, amma sai naje na gama zagaye ne ban ga ko inuwar sa ba.




✿︎✿︎✿︎✿︎




Qur'anin dake hannuna na ina bitar karatun da muka yi da Mama Maria na rufe sakamakon bugun k'ofar da naji ana yiwa k'ofarmu. Agogon dake mak'ale jikin bango na kalla. Karfe shida da rabi ya nuna. To waye haka yanzu da sassafen nan?. Ko aiki bama farawa sai bakwai dan su kansu wanda muke yiwa bautar basa tashi sai wajen d'aya na rana sannan za'a kwashi abincin su nasafe a kai musu lokacin mun kusa sauke na rana. Kunga abunda yasa bama zama da yunwa.


Qur'anin na ajiye da sauri na tashi na ajiye gefe saboda bugun k'ofar ya yi yawa. K'ofar na nufa a hanzarce ina cewa gani nan. Da rawar jiki na buɗe k'ofar dan ganin masu wannan bugun. Matsanancin bugawa k'irjina ya yi ganin Royal Gaurd(dakarun Sarki na musamman) ba'a ganin su sai in mutum ya yi laifi. Laifin ma mai girma da zaisa King Azrah ya turosu da kanshi suzo su tafi da mutum. Ganin su babbar musifa ce. Innalilllahi wa Inna'ilaihi raji'un. Me ya kawo su k'ofar mu? Me nayi?. Ko an gano ina zuwa Garden d'in ne a b'oye? bugun K'ofar da suke ya fito da Mama Azeema da sauran mutanen dake nan b'angaren namu. Ina kallon yanda tashin hankali ya bayyana k'arara kan fuskar Mama Azeema da sauran Mutane gashi basu isa su tunkaro inda suke ba ko saji ba'a sin zuwan su nan.


Tashin hankalin dasu Mama Azeema suka shiga ba komai bane kan wanda nake ciki. Kad'an ya rage ban saki fitsari ba har wani gumi ke kyetomin tsabar firgici. Kallon su nake jiki na, na rawa na fara k'ok'arin buɗe baki nayi magana suka rigani da firgitacciyar murya d'aya daga cikin su ya yi magana.


"Anty NADINE ?" (kece Nadine?)


Jikina na rawa na d'aga kai dan bazan iya basu amsa ba ji nake kaman na fashe da kuka. Kallon juna suka yi suka k'ara kallo na kafin d'ayan ya cigaba da cewa


"Ana buƙatar ki cikin masarauta yanzu-yanzu"


Wani irin kullewa cikina ya yi naji kamn zan kifa saboda firgici. Nashiga Uka ni NADINE. Mama Maria kizo ki cece ni. Me nayi yau ake nemana cikin masarauta? Tsawon shekara goma sha takwas ban taɓa takawa cikin taba ko wani guri makamancin ta bare nayi laifin da za'a nemi cikin ta. Idan ka cire garden d'in nan. Shima kuma bana shiga saidai na kewaya shi tunda tunda katangar sa da wani irin glass aka yi shi. Kai ko King SAIFULMULK da QUEEN AIRA basu san da zamana gurin Mama Maria ba. Inma sun sani to sun manta dani dan ina bin duk wasu dokoki saboda gujewa wannan rana. Maganan su ta katsemun tunani


"Ki hanzarta kina tsaye. Umarni ne daga EMPEROR AZRAH "


Wai ai tuni naji fitsarin da nake riƙewa yana k'ok'arin kufcewa a guje na juya na koma d'aki. Tsawar su naji bayana sunyi tunanin ko guduwa zanyi. To in gudu inje ina?. Da gudu na fad'a d'an banɗakin mu dake cikin d'akin da muka kewaye shi da labule. Ina jin sawun tafiyar su bayana suna ganin na shige suka ja tunga bakin k'ofa suka tsaya suna jirana. Saida na rage marata na fito jiki a salube ina kallon su kaina. Wasu d'irka-d'irka dasu jiki duk a murmurd'e. Ga wasu kaya da suka sa na yak'i dake k'ara firgita mutane.


Gaba nayi suka rufamin baya. Ina fitowa na iske su Mama Azeema da sauran mutane tsaye k'ofar d'akin namu. Tana ganin na fito ta tawo da sauri ta rungume ni tana kuka.


"Me ki ka yi Nadine? Me ki ka yi da har King Azrah ya turo a tafi dake?"


Murya ta na rawa nace "nima ban sani ba Mama Azeema. Ke shedace babu inda nake zuwa cikin masarautar nan"


Kai kawai ta d'aga hawaye na bin fuskarta. Tsawa suka daka min


"Wuce muje mana kina b'ata mana lokaci "


A sanyaye Mama Azeema ta sake ni na wuce ina sharar hawaye kasan zuciya ta ina kiran Mama Maria. Da ace tana nan nasan sai inda k'arfi ta ya k'are wajen ganin ta hana sun tafi dani. Inma bata hana sun tafi da niba to tabbas babu makawa tare zamu tafi da ita.


Kome zan tarar kuma cikin masarautar da ban taɓa taka k'afata cikin taba??








♔︎ ♔︎
𝕊𝕌𝕃𝕋𝔸ℕ𝔸𝔸ℍ
𝒕𝒉𝒆 𝒖𝒏𝒌𝒏𝒐𝒘𝒏 𝒑𝒓𝒊𝒏𝒄𝒆𝒔𝒔








ASHANTY LOVE.













☆𝐈'𝐌 𝐀 𝐒𝐓☆𝐑☆








Chapter
16/20.












Tafiya nake ina sharar hawaye suna biya dani. Tunanin mak'omata cikin wannan masarautar nake. Tsawon minti hud'u muka dauƙa muna tafiya kafin na fara hango tangamemen ginin daya raba mu da cikin masarautar. Dakarune kewaye da ita ta ko ina tun daga farkon ta har k'arshen katangar da baka ganin sa. Ajiyar zuciya na sauke mai k'arfi zuciya ta fal tsoron abunda zan tarar. Da sauri naga sun wuce ni zuwa bakin k'ofar suna wa katon Gaurd dake gadinta magana. Shi kaɗai ma ya isa yasa ka juya da gudu tun kafin ka k'arasa.


Katon gate d'in suka buɗe da aka yi da zallar Crystal stones. Baki na hangame na tsaya chak ina kallon wannan masarauta kaman aljanna duniya. Hak'ika babu abun yabo da bauta sai Allah. Shike bayarwa kuma shike hanawa ga wanda yaso.Gaskiya dole su shagala da duniyar da Allah ya basu su manta cewa zasu koma gareshi.

Ji nayi kawai sun tankad'ani nayi taga-taga kaman zan fad'i Allah ya taimake ni na tsaya da k'afafuna. Tsawa suka daka min


"Wuce mana kinja kin tsaya. Ko kinsan illar barin KING AZRAH zaman jira?"


Bance komai ba na cigaba da tafiya bansan inda zanyi ba don yaune karo na na farko dana shigo cikin wannan Palace. Lura da hakan da suka yi suka k'ara wuce ni na cigaba da binsu a baya. Katon gini muka shiga mai masifar kyan gaske da doguwar hanya kaman corrido. Shima saida muka yi y'ar tafiya sannan muka bulle wani irin Garden mai tsananin kyau dayafi na b'angaren mu. Ta cikin sa muka shiga sai gamu mun bullo Royal Palace.


Ido waje nake kallon ginin. Kunne nayi baki nayi. Sosai na zama y'ar kyaune na hangame baki ina kallo. Tankamemen falo muka shiga da ke dauke da kujerun gold da garden cikinsa kai harma da kwani na ruwa a tsakiyar sa ga wasu tattaburu farare dake shawagi kansa. MashaAllah hak'ika Allah ya basu duniya saura lahirar su kuma.


Glass staircase dake can k'arshen falon ya kewaye shi ta ko ina suna nufa na rufa musu baya. Kaman dai yanda ko ina yake zagaye da dakaru haka shima falon yake tun. Saboda yawan benen saida na gaji na d'an yunƙura zan hutu suka k'ara dakamin tsawa na miƙe da sauri na cigaba da binsu. Ajiyar zuciya naja mai k'arfi na dafe gefen cikina ganin mun kawo k'arshen benen. Kai wannan wahala da yawa take. Mutum in mai k'iba ne ai cikin kwana biyu zai ya zazzage gaba d'ayan sa. Hanya muka bi doguwa nan ma kaman corrido mai d'auke da kofofi wajen shida ko wacce a gark'ame da matakan tsaron a bakin ta. K'ofar dake tsakiya warda tafi ko wace girma da kyau tana fuskantar mu ,mu ka tsaya.


Kai na d'aga ina kallon jibgegiyar k'ofar da aka yi kaman da gold sai shek'i take saman ta an rubuta EMPEROR EZKE'IL CHAMBER da stone's na crystals abun sai ya k'ara armashi sosai. Dakurun dake zube gaban k'ofar na maida hankali kai ina kallo cikina na bada sauti saboda matsanancin tsoro. Sai yanzu nake jin irin bugun da zuciyata take da mugun gudu kaman zata tsaga kirjina ta fito. Gyaran murya d'aya daga cikin dakarun da suka titsiyoni nan ya yi nayi saurin maida hankali ina kallon su. Kai ya jinjina ganin na maida hankali ina sauraran shi ya fara magana.


"Idan an buɗe kin shiga kar ki kuskura ki d'aga kan ki har sai ya baki umarnin hakan. Ki kiyaye kallon sa ba tare da izni ba kinji ko"


Sakato na tsaya ina kallon Gaurd d'in. Wane irin abu ne kuma haka? Tsawa ya dakamin


"Kinji abunda nace?"


Da sauri na d'aga kai cikin firgici. Kai ya d'aga ya juya. Ina kallo yaja numfashi mai k'arfi kafin ya d'aga hannu ya buga k'ofa sau biyu ya koma baya ya wani k'ame ko motsin kirki baya yi kaman an zare masa laka bashi kad'ai ba gaba d'aya dakurun sun k'ara k'amewa kaman basu numfashi. Tun daga nan na fara hango makomata. Tsawon minti goma muna tsaye babu alamun za'a amsa bugun k'ofa bare a buɗe. Kafafuwan har sun fara gazawa na fara k'ok'arin sunkuyawa sai kawai naji wata irin murya mai shegen gard'i da sanyi gata so, so Deep tayi magana daga cikin d'akin a kasalance kaman wanda maganan kewa wuya.


"Minnnn ?" (Waye?)


Ai tuni hanjin cikina suka k'ara kad'awa na gyara tsayuwata da sauri kaman yanda naga dakarun sunyi. Jiki na rawa ya bashi amsa.


"Mune KING AZRAH. sakon da kace a kawo maka gashi mun tawo dashi"


Sak'o? Ban ma isa a kirani da mutum ba kenan?. Nan ma dai sai da ya d'auki sama da wajen minti goma kafin ya bada amsa. Wannan wace irin rayuwa ce?. Wace irin isa ce wannan?wai shin da mai kuɗi da mulki, arziƙi ,talaka duk ba d'aya suke ba gurin Allah?. Me yasa wasu mutanen idan sunga Allah ya basu duniya sai su dinga ganin kaman sunfi kowane?. Bafa dabara ko iyawa tasa Allah ya basu wannan matsayin ba. Duk wani abu da zai samu bawa a wannan duniyar jarabawa ce a gareshi. Wani zata kaishi wuta wani ta kaishi Aljanna. Ga wad'an da suka fifita duniyar su kenan a kan laharir su. Sun manta cewa duniyar nan ba komai bace.


Maganan gaskiya iya fusata nayi. Wannan wulaƙanci ya yi yawa. Yasa an kawoni ba tare da nasan abunda nayi ba. Nazo kuma sai iko yake mana. Anya kuwa zan iya jure wannan isar?


A kasalance naji ya yi maganan da saida na kasa kunne sosai naji. Cikin harshen nasara yanzu yace


"Let her in"


Kallo na gaurd d'in ya yi ya matsa k'ofar da sauri don ya buɗe yana cewa


"Kar ki manta gargad'in da nayi miki. Kar ki d'aga kai har sai ya baki umarni"


Ban bashi amsa ba na d'auke numfashi bayan buɗe k'ofar da ya yi duhun d'akin ya yi min sallama da wani irin kamshi da sanyi mai ratsa bargo da kashin mutum. Da kyar na d'aga kafata da suka yi nauyi na tura kai cikin d'akin bakina d'auke da siririyar sallama. Bana iya ganin komai saboda duhu sai y'ar fitilar dake can kan wata tebir katon gaske mara haske. Ido na buɗe sosai ina kallon kaman mutum ne zaune gaban tebir din ya d'an jingina dashi. Cikin duhun na fara bin kafafunsa da fitilar ta d'an haska min da kallo. Kaman wando ne na suit a jikin sa daya dan kama shi sai farar riga mai botira da kusan gaba d'ayan su a balle suke hannuwansa harde a kirji ya tattare hannun rigar zuwa gwiwar hannun nasa. Cigaba nayi da kallon nasa na d'aga ido na zuwa wuyan sa dake sanye da wata irin sarkar data kwanta kan faffaɗan kirjin sa dake a murd'e sai shining yake ga gashin kansa dake zube wajen kafad'unsa wasu sun zubo kan kirjin nasa sun kwanta.


Ido na k'ara d'agawa zuwa dogon wuyan sa wajen Adam Apple nashi (makwalato) na cigaba wajen fuskar sa sai diff wutar ta d'auke gaba d'aya. Tuni na dawo cikin hayyaci na na tuna da gargad'in da aka yimin. Innalilllahi meke damuna na ne? Nashiga uku ni Nadine. Rarraba ido nake saboda matsanancin duhun d'akin baka ganin komai. A mugun hankali naji kaman takun tafiya na kasa kunne inda nake jin takun da baya fita kaman wanda ke sand'a sai kuma naji diff shima ya d'auke. Yanzu nake jin ciwon rashin ganina cikin duhun da banayi. Da Sam ban damu ba amma yanzu saboda wannan mugun naji ina ma ya dawo ko na samu naga abunda yake kar naje ya kashe ni a banza.


A hanzarce na kai hannu na kare ido na saboda wani irin haske dal da dakin ya dauka lokaci d'aya. Murmushi (chuckling) naji anyi mai birkita lissafin mutum nayi saurin juyawa inda naji sautin. Sai da na kusa zubewa a k'asa lokacin da kwayar idon mu suka had'u jikina ya hau kyarma bansan sanda na d'aga hannuna na nuna saba. Yana zaune yanzu kan kujerar katon glass tebir irin ya dogara duka gwiwar hannun sa kanshi ya talleb'e hab'ar sa da yatsun sa daya had'a su guri d'aya.


Innalilllahi wa Inna'ilaihi raji'un. Baza kuso kuga irin matsanancin tashin hankalin dana shiga ba wannan lokacin babu abunda ke yawo a kwanyar kaina sai kalmomin dana furta ranan kaman


" 𝒎𝒖𝒈𝒖𝒏 𝒎𝒖𝒕𝒖𝒎 𝒏𝒆 𝒎𝒂𝒊 𝒌𝒂𝒏 𝒂𝒈𝒘𝒂𝒈𝒘𝒂 , 𝒎𝒖𝒎𝒎𝒖𝒏𝒂 𝒎𝒂𝒊 𝒌𝒂𝒕𝒐𝒏 𝒄𝒊𝒌𝒊, 𝒂𝒛𝒛𝒂𝒍𝒖𝒎𝒊 𝒎𝒂𝒓𝒂 𝒊𝒎𝒂𝒏𝒊"


Innalilllahi wa Inna'ilaihi raji'un shi ne King AZRAH. Shine na gama zagin sa kan idonsa cikin rashin sani duk da cewa wasu kalmomin da hausa na fad'e su. Na shiga Uku, Na shiga Uku.


Da kyar na d'aga ido na na kalle shi har yanzu yananan yanda yake fuskarsa babu wani expression a kanta. Kwayar idansa da ke da girma gata baka sid'ik kaman midnight dake bada wani calm expression ya zubamin kaman mai ganin hanjin cikina. D'aga gira ya yi gefen bak'in sa shima ya d'aga (smirk) da alama tsoron sa da ya gani kwance kan fuskata ya bashi enjoyment. Magana ya yi a kasalance muryar sa a kausasashe


"Masmik?"


Saboda firgici na kasa bashi amsa sai kai kawai da nad'aga. Gira ya k'ara d'agawa da alama kaman yin hakan nature nashi ne. Da sauri yanzu nace murya na rawa


"NADINE"


A d'ai-da'i ce ya kira sunan nawa "NA-DI-NE.. hmm"


Sunayen Allah kawai nake kira cikin raina da duk wata Addu'a data zo baki na. Murmushi ya k'arayi na lura da double dimples nashi a ko wane kunci. Tun daga sama har k'asa ya kalle ni sai kuma ya tashi daga zaunen da yake ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login