Showing 12001 words to 15000 words out of 21599 words
ruwan wankan ne ashe. Da wanda za'a zuba ruwan ya yi kala, da wanda zaiyi kamshi, da wanda zaisa ruwan ya dinga fidda hayak'i mai dad'in kamshi. Gasunan kala-kala na riฦe su a kaina saboda gudun aikata ba dai-dai. Tana gama yimin bayani ta juya ta fice tana cewa
"Ki hanzarta kiyi ki fito ina jiran ki a waje. Ruwan dake cikin kwamin sai kin zubar dashi duka kin tara wani sannan ki kunna fanfon dake ciki ki tara wani kafin ki fara zuba kayan dana lissafa miki"
Sakato na tsaya ina kallon k'ofar data fice kafin na tattaro ragowar k'arfin daya ragemin na k'arasa bakin kwamin. Yanzu ta ina zan fara zubarda ruwan nan fisabillahi banga wata hanya da take nuna da inda za'a buษe ba ruwan ya fita. Rigata na tattare na dora k'afa kan kwamin na zauna kan abin. K'afata d'aya a waje daya cikin ruwan . Sosai na sunkuya ina laluben inda zan buษe ruwan ya fita kaman wadda aka ja naji na kifa cikin ruwan wankan gaba d'aya.
Y'ar k'ara na saki kafin na jini cikin ruwan gaba d'aya. Ashe zurfine dashi gashi ban iya ruwa ba. Babu shiri na fara kici-kicin ceton raina. Hannu kawai na gani mai shegen kyau dake dauke da zararan yatsu dogaye gwanin sha'awa . Ban tsaya duba wanda ya kawomin d'aukin ba na kama hannu da sauri ya jani kyee na fito daga cikin ruwan. Ba'a sake ni ba saida aka tabbatar na tsaya da k'afafuna sannan naji koma waye ya sakemin hannu. Ga hannu da shegen laushi kaman audiga kaman ba hannun mutum ba.
Gashin kaina daya rufe mun fuska na fara k'ok'arin tattare shi na sak'ale bayan kunne na. Da farar riga da wando naci karo na wanka doguwa mai madauri ya kwance rigar gaba d'aya. K'irjina ya fara harbawa na fara d'aga kaina a mugun hankali kaman slow motion har zuwa kugun sa inda wandon ya tsaya. Yawu na had'iye kut na daga ido zuwa vline nashi da yabi cikin wanda sa mai tazuge zuwa shafefen cikin sa dake dauke da well difine 8 pack abs (muna ce musu guraye).
Chak na tsaya da idona kan murdadden faffaษan k'irjin sa dake uban shining. Wani irin yawu na k'ara had'iye da mugun k'arfi da ya yi sanadin daya saki murmushi(chuckling) . Da azama na k'arasa d'aga kaina muka had'a ido dashi da d'agaggiyar girar sa guda daya gashin kansa tufke tsakiyar kansa sai gefen fuskarsa da wasu suka kwanta har k'irjin sa.
Wani irin komawa baya nayi zan kara fad'uwo nayi sauri dafe kwamin. Tashin hankalin dana ke ciki yasa zazzab'in da nake ma na nemeshi na rasa. Gira ya k'ara dagawa ganin yanda na kafeshi da ido. Muka zubawa juna ido na y'ar tsakanni kafin naji Deep voice nashi yana magana cike da kasala
"Pervert"( y'ar iska kenan ko a hausan ce?๐
)
"For the 3rd time kin k'ara karya min doka?. Kina a matsayin baiwa amma kinga abunda bai kamata ki gani ba. So what kind of punishment ya kamace ki?"
Wani irin matsowa ya yi naja baya cikin ruwan da sauri . Sunkuyawa ya yi ya d'ora hannuwansa kan kwamin ya d'an rankwafa yana kallo na tun daga sam har k'asa fuskarsa babu wani expression. Wajen minti biyu muka yi a tsaye a haka yana k'aramin kallo nayi duk iya bakin k'ok'ari na kar na kara kallon shi.
"So tell me wane irin punishment ya kamace ki?, "
Murya ta na rawa nace
"Don Allah kayi hak'uri wlh ban sani ba"
"Hmm. No you must be punish. You have seen me naked. So kema zaki cire naki kayan"
A rude na dago kaina ido waje ina kallon fuskar sa da babu alamun wasa. Innalilllahi wa Inna'ilaihi raji'un. Komawa baya yi lazily ya zauna kan kujera ya wani bararraje. Gira ya d'aga da dakakkiyar murya yace
"Don't keep me waiting. Strip" ( kar ki barni zaman jira. Cire kayan ki)
Ya hayyu ya kayyum. Allah kaga halin da nake ciki wannan wace irin rayuwa ce?. Wai hala ko ya manta haramcin hakan ne? Me yasa yake abu kaman ba musulmi ba?.
Wata irin tsawa ya dakamin.
"You dare to disobey me?. Nace ki cire kayan ki"
A yanzu kam matsanancin kuka na rushe dashi na durkushe cikin ruwan ina k'ara k'ank'ame jiki. Wlh bazan taba cire kayana ba sai dai ya yi duk abunda zaiyi. Mugu azzalumi mara imani. Fasikin banza da wofi.
๐ k'ak'a -k'ak'ara-k'ak'a. Bari na baku suspense ko๐คฃ๐คฃ๐คฃ??.
โ๏ธ โ๏ธ
๐๐๐๐๐ธโ๐ธ๐ธโ
๐๐๐ ๐๐๐๐๐๐๐ ๐๐๐๐๐๐๐๐
Ashanty love.
โ
โ๐'๐ ๐ ๐๐โ๐โ
Announcement.
READ PLS๐.
Littafin SULTANAAH PAID BOOK NE. 500 kacal๐ค. Book 1 is free wanda shi muke yanzu. Idan mun kusa gama free pg zan bada ACCOUNT da number da zaku turo shedar biya. Wannan ne kad'ai Announcing da zaku samu so pls read. Bana so sai na gama free page a dinga tambaya dama paid book ne?.
Nevertheless enjoy ๐
Chapter
31/35.
A fusace naji ya taso na k'ara k'ank'ame jiki na d'ago dan inga abunda zaiyi. Da wani irin fushi ya miฦo hannu zai kamani sai ga Anita ta fad'o cikin banษakin kama wadda aka wullo. A karo na farko da ta ceci rayuwata. Duk duniya a yanzu naji babu mace da nake gani da kima sai ita. Chak ya tsaya da abunda yake shirin yi bai juya ya kalleta bai kuma mayar da hannun saba. Nida ke kallon ta na samu ganin matsanancin b'acin ran dake kwance kan fuskarta. Mugun kallon da take jefana dashi bai hanani jin abunda nake jiba na ceton rayuwata da tayi. Da kyar ta iya buษe baki tayi magana
"I'm sorry King Azrah. Queen Aira ke buฦatar ka cikin gaggawa "
Sai a lokacin ya ajiye hannun sa ya juya ya watsa mata kallo tayi saurin sunkuyar da kai. Ashe isa da takamar da take a bayan idonsa ne kawai?. Y'ar firgita nayi na k'ara ja baya cikin ruwan ganin ya maida hankalin sa kaina. Wani kallo ya watsomin da bazan iya tantance abunda ya kunsa ba. Rigar sa ya tattare ya kama mad'auran ya d'aure ta kafin ya k'ara jefana da wani last kallo ya juya cikin tafiyar izza yabi ta wata k'ofar ya fice.
Ajiyar zuciya na sauke mai k'arfi bayan ficewar sa. K'ok'arin miฦewa na farayi cikin kwamin naji anyi min wata mahaukaciyar fisga an janyo ni da k'arfi an watso ni wajen kwamin. Ban gama jin zafin ba ta kama gashin kaina da iya k'arfin ta ta d'ago fuskarta na saki kara dan rik'o ne tayi min bana wasa ba. Tuni hawaye suka fara gudu kan fuskata.
"Don ubanki me ki ke cikin kwamin wankan sa?, me yake shirin faruwa tsakanin ku?"
Bata bari na bata amsa ba ta d'auke ni da mari. Saida ta jeramin uku masu zafi ta jani kee ta gashi kaman kayan wanki tayi waje dani ta jefar. Wajen kaina ta k'ara durkusawa ta kara fincikar kaina na d'ago ina kallon ta da fuskata da tayi jege-jege da ruwan hawaye.
"Me nace miki?, ke mai taurin kai ko? Banga alama kina son rayuwar kiba .kin d'auka wasa nake ko?, za kici ubanki na k'ara ganin wani abu ya shiga tsakanin ki da Azrah sai kin kwammace mutuwar ki."
A zafafe ta saki kan nawa goshi na ya bugu a k'asa. Tsaki naji taja mai k'arfi ta tsartar da yawu gefe ta wuce a fusace wasu daga cikin masu tsaron suka bita. Komawa nayi k'asan na kwanta dan sai naji kaman an d'auko katon dutse an d'oramin zazzab'i da nake ji dazu ya dawo ya rufeni ruf. Motsin Mamee naji da Layher suna k'ok'arin d'aga ni sai sannu sukemin. Had'uwa suka yi suka kamani suka kaini d'aki suka kwantar. Ina Mamee na k'ok'arin d'oramin dan hankici data cika a goshi daga nan kuma wani irin barcin wahala ya kwashe ni ban k'ara sanin abunda ya faru ba.
โฟ๏ธโฟ๏ธโฟ๏ธโฟ๏ธ
WANI YANKI DAKE CIKIN EGYPT
A firgice ta farka daga barcin da take tana salati. Jalila dake kwance kusa da ita ta tashi da saurin tana tambaya
"Mama menene?, yauma kin k'ara yin mafarkin ne?"
Ajiyar zuciya Maria taja mai k'arfi tana girgiza kai bata bata amsa ba saida ta k'arasa Addu'ar da take. Huzaifa da Baban sa Abu Khamis suka shigo d'akin jin muryar Jalilan. Da kallo Maria ta bisu kafin ta fara magana tana k'ok'arin miฦewa tsaye.
"Jikina yana bani Nadine na cikin wani hali tana buฦata ta a kusa da ita."
"Mama Don Allah kiyi hak'uri keda baki da lfy. Kinaji d'azu abunda Doc yace ana buฦatar ki samu hutu har tsawon wata biyu kafin ki koma bakin aiki. Abu ya riga da yaje ya sanar da King SAIFULMULK da QUEEN AIRA kuma suma sun amince da neman lafiyar taki. Nadine ba yarinya bace zata kula da kanta inshaAllahu babu abunda zai same ta nida Jalila zamu dinga zuwa a kai a kai muna dubu miki ita"
Kai ta girgiza tana kallon Huzaifa "A'a Huzaifa yarinya nan marainiyar Allah tana buฦata ta a kusa da ita. Bata da kowa saini gashi nima nayi nesa da ita. Don Allah ku bari na koma Nadine zata kula dani kuma kunsa hakan"
Cikin fushi Abu Khamis ya fara magana
"Me yasa ne kinfi fifita yarinya nan sama da yaran ki. Su basu buฦatar ki sai ita kaษai? Su wad'annan basu ne ki ka haifa a cikin ba. Mu bama buฦatar ki? Mu baki damu da halin da zamu shiga ba sai ita.?"
Ajiyar zuciya Maria taja saiga hawaye shar sun biyu kuncin ta. Tunda Khamis ya yi mata magana haka tasan ransa ne a b'ace amma Khamis baya taba banbanta Nadine da yaransu. Shima yana d'aukan te kaman Y'ar da suka haifa a cikin su. Hannu sa ta kamo cikin muryar lallashi ta maijinya tace
"Kayi hak'uri Abu Huzaifa. Kar ranka ya b'aci. Bacin ranka babban tashin hankali ne a gareni. Kayi hak'uri zan zauna daku har na samu lfy. A duniya babu wanda nake buฦata sama daku a duniya. Ana Uhibbak ya zauji"
Numfashi yaja mai k'arfi ya had'asi gaba d'aya ya rungume ya kuma bi goshin su gaba d'aya ya sumbata.
โฟ๏ธโฟ๏ธโฟ๏ธโฟ๏ธ
Bani na farka ba sai wajen asuba shima Mamee ce ta tasheni nasha maganin na gargajiya data jik'a ta kawomim. Da kyar na iya kurban maganin dake da mugun d'aci ga bauri amma kuma ina sha cikin ikon Allah ko minti goma banyi ba cikakke na fara had'a zuba. Miฦewa nayi da taimakon ta naje na kuskure baki na d'auro alwala. A daddafe na jero sallolin dake kaina ina cikin sallan Layher ta dawo dauke da faranti na abinci. Na dauka zanga irin cimar su sai naga abinci ne mai rai da lafiya harda kaji da y'ay'an itatuwa.
Zagewa nayi naci na koshi kamin na ture na samu guri na kwanta sai barci.
Nayi mamaki da naga tun ranan Anita bata k'ara lekowa inda nake ba. Ban sani ba ko taji bani da lafiya ne ta sarara min na warke ta cigaba daga inda ta tsaya?. To amma shifa wancan azzalumin? Shima bai k'ara aikowa nazo ba duk ina ta jiran fuskantar hukuncin sa dan bazan manta kallon da ya yimin dake nuni da akwai unfinished business tsakanin mu.
Alhamdulillahi yau naji kwari sosai dan har na dan fito na kamawa Mamee da Layher wani abu bayan na gama ne na d'an zagaya dan tunda na shigo ban taษa fita ba.
Wani d'an k'aramin Garden na bulle dake can baya . Da alama dai kaman ba'a cika amfani dashi ba duba da yanda komai ya bushe baya samun ruwa fulawoyin duk sun zube. Wani d'an k'aramin d'aki na hango kaman mab'oya ta tsuntsaye. D'akin na shiga duk da rashin kula da yake samu amma guri da aka kashe masa dukiya.
Gaban windon d'akin na zauna kan kujera dake gefen sa ina kallon wajen sa. Wati irin iska mai dad'i dake saka nutsuwa ta fara kad'awa a hankali na ciro sark'a ta dake boye a wuyana na sumbace ta ina murmushi kafin na mayar da ita. Haka kawai nake jin nishaษi da ni kaina bansan me yasa ba. Sannu a hankali na fara rera wak'a da larabci ina d'an jijjga kai gashin kaina dana tufke da hankici iska nata kad'ashi sai ga wata tsuntsuwa mai shegen kyau fara tas da ita ta sauka kan gwiwar k'afata . Murmushi nayi na mik'a hannu a hankali zan tab'a ta komai ya tsayamin chak.
Tsuntsuwar data sauka kan k'afata ta tashi da sauri ta koma inda ta fito. Baiyi motsi ba baiyi sallama ba amma naji a jikina. Aura d'in sa daban take a ko ina duk inda yake ya fita daban cikin mutane. K'irjina ya harba da k'arfi na ja doguwar ajiyar zuciya na miฦe tsaye kafin na juyo a hankali na fuskance sa.
โ๏ธ โ๏ธ
๐๐๐๐๐ธโ๐ธ๐ธโ
๐๐๐ ๐๐๐๐๐๐๐ ๐๐๐๐๐๐๐๐
Ashanty love.
โ
โ๐'๐ ๐ ๐๐โ๐โ
Chapter
36/40.
Tsuntsuwar data sauka kan k'afata ta tashi da sauri ta koma inda ta fito. Baiyi motsi ba baiyi sallama ba amma naji a jikina. Aura d'in sa daban take duk inda yake ya fita daban cikin mutane. K'irjina ya harba da k'arfi na ja doguwar ajiyar zuciya kafin na juyo a hankali na fuskance sa.
Wane irin mutum ne shi bakajin motsin sa bare takun sa mutum ne kaman aljanni. Duk da kasancewar nan guri ne dake public amma boyeyyen gurine da zaka iya kad'aicewa cikin sirri yanzu inda yazo ya sameni ina yin wani abu da bai kamata ace ya gani ba fa?. Da kwarin gwiwar dani kaina bansan ina da irin taba na fara magana a zafafe
"Can you please not do that? Appear out of no where.? mutum sai dai ya ganka tsaye babu sallama babu komai inda ina chanza kaya ,ko ina yin kashi ko fitsari fa,ko wani abu makamancin hakan fa? "
Saida na gama maganan ina maida numfashi na tuna irin muguwar katob'arar dana aikata k'irji na ya cigaba da bugawa kaman zuciya ta zata fito fili. Innalilllahi mena aikata haka?. Shida yake nesa dani ma nasan yana jin bugun zuciyata bare ni da take cikin jikina. Har zuwa lokacin yana tsaye tsakiyar d'akin sanye cikin kananan kaya. Dogon wando Jean's baki da farar riga daya balle mab'ellenta wajen guda hudu , hannun rigar ma ya tattare shi zuwa gwiwar hannun sa sai katuwar bak'ar jacket dake hannun sa mai hular gashi.
Tsawon sakanni na cigaba da kallon sa ina jira ya aikata wani abu, dan nasan dole zai aikata. dole zai hukunta ni kaman yanda ya saba hukunta duk wani wanda ya karya doka. Fuskarsa dake very cold babu wani emotion ta firgita duk mai kallon ta. Kwayar idansa kad'ai ta isa tasa mutum sakin fitsari a wando yabi umarni cikin gaggawa. Kirjina ya cigaba dabugawa na had'a hannuwana guri d'aya dan hana kaina rawar jikin da naji kafafuna suna k'ok'arin yi.
Gefe na na kalla ina neman hanyar da zan tseratar da rayuwata. Cikin azama na juyo da kallo na kansa. Saidai me inda yake tsaye babu shi yanzu banma k'arasa juyowar ba da kyau naji wuff anyi sama dani kaman iska kafin a had'ani da bango da mugun k'arfi saida bayana ya amsa. Kakari na fara saboda hannun sa daya sa ya shakemin wuya dashi ina kallon sa ya d'aga ni da hannu d'aya har saitin idan sa. Da karfin hali na fara k'ok'arin cirewa hannun sa dake shak'e da wuyana
"I'm your king. You dare to speak to me like that?. Wacece ke da zaki gayamin what or what's not to do?, this is my kingdom. Ina da ikon da zanyi duk abunda naga dama dake. You dare to question me?, how dare you?. Who are you?"
Sauran maganganun nasa suka yimin nisa saboda numfashi na da naji ya fara barazanar d'aukewa. Tuni idanuwa suka juya bayan kai na. Babu abunda yazo min a rai wannan lokacin sai Mama Maria. Ita kaษai ce ta ragemin a duniya kaman yanda nima na rage mata. Bak'in ciki zan tafi na barta. Allah kad'ai yasan irin kuncin rayuwar dazata shiga idan na mutu a hannun wannan azzalumin. Kalman shahada na fara yi cikin raina dan na saddakar mutum zanyi.
Babu zato ya sake ni na zube kasa ina mugun tari da Jan numfashi mai k'arfi kaman mai Asmah hannu na riฦe da wuya na. Duk da haka na ki bashi damar da yake ganin ya samu nasara a kaina. Da karaji