Showing 9001 words to 12000 words out of 21599 words
zagayo gaban tebir d'in ya zauna kaman yanda ya yi d'azu dana shigo.
Kuttt na had'iye yawu ina kallon sa na matse kafafuwana dake rawa guri d'aya. A take yanayin fuskarsa ya chanza zuwa wani deadly calm expression. Magana ya fara da calm voice cikin harshen turanci
" what is that you say?"
Kuttt na k'ara had'iye wani yawun, naji kaman na juya a guje na fice. Ga mamakina sai naji yana maimaita abunda nace harda hausar da nayi.
" Kayi hankali cikin masarautar nan idan kai sabo ne. Tunda har ka shigo masarautar nan nasan kasan wane KING AZRAH. Ba sai na tsaya ina maka dogon bayanin rashin mutuncin sa da rashin Imanin saba,amma dai kayi hankali da takun ka "
Yana dasa aya na kusa zubewa k'asan gurin. Duk irin matsanancin sanyin na d'akin wanda tsab mutum zai daskare cikin sa zufa na had'a kaman wadda aka zubawa ruwa. Gashin kaina dana tufke shi a tsakiyar kai na d'ora hula a kan nawa ina jin yanda gumi ke biyowa ta cikin gashin yana bin wuyana da goshina. Shi kanshi gashin ya jike jagab. Ban gama shiga tashin hankali ba sai da naji ya k'ara magana yanzu da Hausa.
"Ko kinsan tsawon lokacin dana d'auka ina koyan wannan yaren naki saboda na gane ma'anar kalman MAI KAN AGWAGWA DA KATON CIKI?"
"You dare to insult me like that?, mene ma ki ka ce .Bani da Mutunci da Imani?, why not na nuna miki rashin Imanin nawa zahiri yanda zaki ji dad'in bada labari da kyau?, . You disrespect me in the worst way possible. I know you have being told not to look at me, amma gaki kina kallo na ido cikin ido?"
Da azama na sauke ido na k'asa jikina na rawa kaman mazari. Wani murmushi naji ya k'ara yi da nasan babu alkhairi cikin sa.
"So Nadine. Daga yau zaki zauna a nan don ki sheda rashin imani na da rashin mutunci na. Aikin ki ya dawo cikin masarauta daga yau. Know Dismiss.."
Baima k'asara ba na juya a sukkuwanne na fice da mugun gudu daga d'akin.
βοΈ βοΈ
πππππΈβπΈπΈβ
πππ πππππππ ππππππππ
Ashanty love.
β
βπ'π π ππβπβ
Chapter
21/25.
Bansan inda nake sa gaba ba saboda firgici saida na sadu da k'ofar da zata fitar dani daga cikin masarautar. Ajiyar zuciya naja mai k'arfi bayan na tsaya bak'in k'ofar na sunkuya rik'e da ciki ina maida numfashi. D'agowa nayi saboda idon da naji a kaina. Gaba d'aya hankalin dakarun yana kaina babu kuma wata alama da take nuna zasu buΙe min k'ofar na fita. Banyi k'asa a gwiwa ba na k'arasa ina kallon jibgegen Gaurd d'in dake tsaron k'ofar kaman yanda shima yake kallo na. Jarumta na aro na saita nutsuwa ta kafin nayi magana.
"Uhmmm ka buΙe min k'ofar zan koma b'angaren mu"
Kallo ya watsa min irin don't mess with me d'innan ya kauda kai gefe kaman da iska nake magana. Ai kuwa na k'ara tunzura a fusace na k'ara buΙe baki zanyi magana muryar mace ta katse numfashi na. A hanzarce na juya inda naji muryar. Kyakkyawar yarinyar ce da a kalla baza ta gaza haura shekaruna ba ashirin da hud'u ko biyar ba sanye da suit riga da wando da Air Bluetooth sakale a kunnen ta. Fuskarta dake d'auke da katon glass daya cinye rabin y'ar fuskar ta ta da babu wani annuri ko kaΙan a tare da ita. Bayanta wad'annan Gaurds d'inne yanayin ta ya nuna ita ce gaba dasu.
Tsawa ta daka musu da kausassar murya tace
"Me ki ke tunanin ki ke shirin yi?. You damn idiot gets her"
A hanzarce suka yo kaina dan cika umarni nayi saurin d'aga musu hannu.
"Kar wanda ya kuskura ya tab'a ni, zan tafi da kaina"
Na fad'a cikin tsawa. Saurin gimtse baki nayi. Ni kaina bansan inda na samu wannan kwarin gwiwar ba har na iya yin magana cikin tsawa haka. Shiru gurin ya d'auka kaman anyi ruwa an d'auke. Kallon da naga dakarun nayi min na k'ara shiga damuwa matuΖa. Da alama babu wani mahaluki daya tab'a tsayawa ya yi ja-in-ja da ita a matsayin ta na mace. Ga dukkanin alamu kuma tana da matsayi mai girma wajen King Azrah da sahalewar sa take duk abunda taga dama.
Da wani irin izza ta tako inda nake tsaye . Glass d'in dake fuskarta ta cire ta watsamin manyan blue eyes d'inta da suka k'ara fito da asalin kyanta. Da wani irin sinister voice ta fara magana
"Kar kiyi tunani ko na sakan d'aya saboda Kin dawo aiki k'ark'ashin Azrah kiyi tunanin matsayi ki ka samu. Ke d'in baiwa ce kaman sauran bayi babu wani chanji ko mahaluki da zai chanza hakan matsawar kina numfashi cikin masarautar nan. Dan haka ki kiyaye harshen ki in har kina son ki cigaba da rayuwa dashi a doron k'asa. Your nothing but a slave so stay within your limit"
Ta k'arasa maganan tana jifana da wani k'ask'antaccen kallo kafin ta mayar da glass d'in ta kan fuskar ta ,ta wuce da tafiyar izza wasu daga cikin masu tsaron suka rufa mata baya wasu suka tsaya don tafiya dani. Duk cikin kalamanta babu abunda nake juyawa cikin kwanyar kai na sai sunan King Azrah data kira gatsau babu sakayawa. Tun daga nan na tabbatar da lallai ita d'in macece mai babban matsayi a nan tunda har ta iya kiran sunan sa haka babu shakka babu komai. Tabbas ita d'in na daga cikin list d'ina da zan gujewa in har ina son zama cikin salama.
'Ya Allah babu abun bautawa da gaskiya sai kai, baka d'orawa bawan ka abunda bazai iya d'auka ba, ina rokon ka, ka bani ikon cinye wannan jarabawar.'
Addu'ar dana tsinci kaina ina yi kenan k'asan zuciyata data sama min nutsuwa. Numfashi naja mai k'arfi cike da kwarin gwiwar daya ragemin na fara takawa a hankali ina kiran sunan Allah nutsuwa na ratsa dukkan gabban jikina.
Sab'anin d'azu yanzu wata hanya muka bi y'ar siririya sai gamu mun bulle wajen bayi dake aiki cikin masarautar. Babu wani banbanci tsakanin b'angaren su da damu sai dai girma kawai. Guri ne har guri gari gudu ma'aikata nata kai kawo kace kasuwa ce.
Bakin wata matacciyar k'ofa na hango budurwan nan tsaye da wasu mata sanye da kayan bayi. Muna k'arasawa ta fara magana cikin izza
"Nan ne d'akin ki daga yau. Wad'annan zasu nuna miki aikin ki da kuma dokoki da zaki dinga bi. Dan haka ki kiyaye "
Bata jira amsa ta ba ta wuce bayan ta flipping gashin ta baya. Ban d'auke ido na daga kanta ba harta b'acewa ido na. Saida ta b'ace sannan naji matan sun sauke wani gauran numfashi na maida hankali kansu. Babbar cikin su wadda nake tunanin za tayi Mama Maria ta matso kusa dani da murmushi d'auke kan fuskarta.
" zo muje ya'ta. "
D'akin ta buΙe muka shiga. Wani irin wari da k'ari ya yi min sallama. Da alama an dade ba'a yi amfani da d'akin ba ga wata uwar yana da kura a kursurwoyin d'akin. K'aramin dakine dake dauke da wani tsohon gadon karfe duk ya mutu gefe masai ne ya yi bakikkirin ga wasu uban kyenkyesai suna yawa. Duk rashin wadatar b'angaren mu yafi nan sau dubu. A take naji amai na taso mun. Tabbas na yarda koma wace wannan yarinyar bata kauna ta.
Aiko mak'iyin ka baza kaso ya zauna cikin wannan a kurkin d'akin dake d'auke da abun cutar wa haka ba. Muryar matar naji tana magana da tsantsan tausayi cikin ta
"Ke kuwa y'ar nan meya hadak'i Anita? Babu wanda yake so yaga ya shiga cikin bakin littafin ta don bata da mutunci. Tana da karfin iko cikin masarautar nan saboda alak'ar ta da King Azrah . Gashi naji ance ke sabuwa ce kuma King Azrah ya zabe ki da kanshi. Tabbas sai kin jure don Anita babu abunda baza tayi ba kan EMPEROR EZKE'IL . "
Idan na fuskanci maganan ta Anita nasan King Azrah shima kuma yasan da hakan shi yasa take abunda taga dama?. To ni meya shafeni da hakan?. Kasa jure warin d'akin nayi na fito da sauri ina kakarin amai. Biyoni tayi tana d'an buga bayana ta cigaba da cewa
" wannan d'akin babu wanda ke amfani dashi saboda kazantar sa. Ni kaina nayi mamaki danaga ta ce nan ne d'akin ki. Sai kinyi hak'uri zamu taya ki gyarawa muje na nuna miki wajen karb'an abinci da sauran b'angarori. Layher ku da'n fara gyara mata d'akin kafin mu dawo"
Hannuna ta kama muka hau zagayawa tana nuna min b'angarori dake cikin gurin kafin daga karshe mu yada zango wajen cin abinci. Faranti ta dauka nima ta bani muka k'arasa gaban kanta da aka d'ora abinci . Wani irin fatan wake ne kaman gudawa sai wani ganye da farar shinkafa a gefe.
Yatsina fuska nayi ina bin abincin da kallo. Tabbas indai wannan ne cimar da zan dinga ci kullum na hak'ura da cin abinci. Wannan ai in kanaci kullum sai ka mutu a banza. Kallon yanda matar ke deban abinci take babu wani damuwa a tattare da ita alamun sabo da cimar. A take naji ashe mu kan a aljanna muke dan gaskiya mun fisu wadata suda ma suke cikin masarautar kenan fa.
Karb'an kwanon nawa tayi ta zubamin ganin na tsaya na kasa tab'uka komai. Ita ta d'auko mana abinci muka dawo k'ofar d'aki muka tarar da Layher har sun gama aikin.
Shiga d'akin nayi da ya yi kal yanzu sai warin aizil yake har zanin gado suka dan shimfiΙa kan a kurkin gadon.
"Kinga ya yi kyau ko?"
Kai kawai na d'aga dan gaba d'aya bakina ya mutu tunanin Mama Maria da mak'omata kawai nake. Ko wane irin aiki ne zanyi tunda ba'a sanar dani ba har yanzu.? Matar da na san sunan ta a yanzu da Layher ke kira da Mamee suka yi min sallama suka fice nayi musu godiya. Numfashi naja mai k'arfi na zauna bakin gadon ina bin a kurkin d'akin da kallo.
Hannuna na kai na ciro sark'a ta dake wuya na. Tun sanda Mama Maria ta cire min sark'ar ban k'ara sawaba sai bayan tafiyar ta. Shima kad'aici ne ya dameni na saka ta na tura kasan rigata. Sai nake ji kaman Abbu da Innati na tare dani a koda yaushe hakan yake d'an ya ye min damuwa. Kiran salla azahar da naji anayi na miΖe na fito dan neman fanfo nayi alwala.
Karo mukaci da Layher tana k'ok'arin shigowa tayi saurin ja da baya.
"Yauwa dama Mamee tace nazo na nuna miki inda fanfo yake sai ki samu bokiti da zaki dinga zuba ruwa kina kaiwa d'akin ki"
Kai na d'aga mata na bita ina tunanin wannan wace irin rayuwa ce?. Wajen fanfo ta nunamin nayi alwala ta bani bokiti na d'ibi ruwa na wuce dashi d'aki. Saida nayi salla na d'auko flat d'in abinci na zuba masa ido kafin na runtse ido na tura shi da kyar. In badan ina jin yunwa ba babu abunda zaisa ni cin wannan abinci.
To ranan dai haka na wuni cikin wannan a kurkin d'akin da tunani kala-kala da suka yimin kawanya. Har dare ina zuba ido ko za'a kirani naji matsayin aiki na ,amma shiru har nayi salla isha na takure kan gado bayan nayi Addu'a. Bazan iya cewa k'arfe nawa ba don babu agogo cikin d'akin amma nasan na dade banyi barci ba. Saida na daina jin motsin kowa da komai duk girman gurin ya yi tsit baza kace akwai dubban jama'a a gurin ba.
βοΈ βοΈ
πππππΈβπΈπΈβ
πππ πππππππ ππππππππ
Ashanty love.
β
βπ'π π ππβπβ
Chapter
26/30.
Bansan sanda barci ya d'auke niba ,haka ban dade da fara barcin ba na farka a firgice kaman zan shid'e sakamakon ruwan k'ank'ara da naji an zubamin shi a ka. A firgice na farka ina maida numfashi jikina ya fara rawa a take wani irin sanyi mai ratsa bargon jiki ya yimin salla. Nasan babu makawa sai na kwanta ciwo dan sam bana shiri da sanyi.
Maganan Anita naji a kaina
" barci ki ke?,bakiga ta barci ba. Ki tashi maza ki fito ki same ni a waje. Azrah na neman "
Bata jira abunda zance ba juya ta fice daga d'akin. Da ido na bita zuciya ta na suya. Wane irin wulaΖanci ne wannan kana barci a zuba maka ruwan k'ank'ara a jiki?. Da kyar na miΖe ina rawar dari saboda zazzabi daya rufeni lokaci guda hak'orana har kakkarwa suke. Da kyar na iya cire kayan jikina na tsaya ina tunanin to kayan da zansa fa tunda basu bari naje na deb'o ba. Kaman kuwa taji abunda nake cewa cikin zuci sai gata ta dawo riΖe da y'ar bakko na da nake ninke kayana a ciki.
Tsayawa tayi tsakar d'akin tana k'aramin kallo. Tun daga kan jikakken gashin kaina daya bazu har zuwa gwiwar kafata ya zubo gaba d'aya ya rufe ni. Har zuwa k'afafuwana dana rufe da doguwar rigata dana kare k'irjina da ita. Allah kad'ai yasan abunda ke cikin ranta dan jefo min jakar tayi ta juya ta fice daga d'aki a fusace. Ajiyar zuciya naja mai k'arfi na sunkuya da kyar na buΙe jakar ina rawar d'ari na d'auko doguwar rigata na saka kan jikakkiyar shimita da underwear d'ina da suke a jik'e.
Sosai nake jin zazzabi amma saboda gudun tashin hankali haka na daure na fito da kyar. Karo naci da ita bakin k'ofar sai cika take tana batsewa. Wani banzan kallo ta jefamin tana cire glass dake fuskarta.
"Na d'auka ai zaki shekara ne a ciki baki fito ba?"
Nidai ban bata amsa na sunkuyar da kai. Gashin kaina kuwa ya tawo yarr ya rufe min fuska saboda ban kama shi ba ina so ya bushe. A fusace naji ta k'ara magana
"Shi kuma gashin iyayi ne yasa baza ki tufke shi ba kaman yanda ki ka saba? Ko din kinji nace Azrah na neman ki?. Oh kina so ne idan kinje ki ja hankalin sa da wannan shegen gashin naki mai kama dana Aljanu?"
D'agowa nayi na zuba mata manyan ido na jin irin kazafin da takemin. Wannan aicin fuska ne ita bata ga yawan nata gashin ba sai nawa?. Allah na tuba me zanyi dashi?. Ita dai data d'orawa kanta wahala sai tayi ta yi ai. Shashasha kawai. Tsaki taja mai k'arfi ta wullo min wani hankici
"Ki kama gashin ki. Y'ar neman suna kawai banza mai ido kaman na mujiya. Wlh ina dai naga miki kar ki kuskura ki kara yin wani abu gaban Azrah da har zai bada intereste a kan ki inba haka duk abunda ya same ki kiyi kuka da kan ki"
Numfashi taja ta taune harshe kaman mai tunani kafin ta cigaba da cewa.
"Za kije Chambers nashi ki had'a masa ruwan wanka cikin kwami. Akwai kayan had'awa komai cikin banΙaki. Da zarar kin gama ki fito kar ki kuskura ya ganki. Ni bansan ma dalilin da yasa yace dole sai ke zaki had'a masa bayan akwai mai yi"
Ta k'arasa maganan tana jefana da muguwara harara. Hak'ika nayi Imanin da da wuk'a a kusa tsab zata dab'amin saboda kishi. Ita kuwa wannan wane irin so ne take masa haka?. Ta gamu da aiki kuwa babba. Da kanta ta kaini har b'angaren King Azrah ta zagaya dani ta bayan wata k'ofa sai gamu cikin wani dan garden da aka kewaye da glass tun daga sama har k'asan shi. Tsuntsaye nata shawagi a ciki daga k'arshen sa wata kifa ce katuwa mai girma ta silver.
Wasu madannai ta danna jikin k'ofar ta buΙe kanta kafin ta kutsa kai ciki nima na bita. BanΙaki ne katon gaske tsakiyar sa kwami ne na wanka kaman swimming pool sai turi ruwan ciki yake yana fidda wani irin hayaki mai shegen kamshi. Zagaye da ruwan kuma wasu kujerune na crystals da d'an tebir d'insa mai shegen kyau an k'awata shi da furanni. Gaban wata drawer dake can jikin bango ta tsaya ta fito da wasu kwala masu kyan gaske da kaloli a cikin su. Kan tebir d'in ta ajiye ta juyo tana kallo. Da fad'a ta ce
"Ni ki ke jira ne na kawo miki kayan?"
Da sauri na matsa gaban tebir d'in ina k'ank'ame jiki saboda zazzab'i. Tsaki taja mai k'arfi ta fara nunamin kwalaben. Duk kayan had'a