Showing 9001 words to 12000 words out of 28317 words

Chapter 4 - Sai Na Auri Marubuci Nafseen Complete by Zulaihat.txt

kaina banji Ba bara na duba jakar nan taki."


Cikin sa'a kuwa ta Ciro wayar tare da mik'a mata, "To Madam ga shi wayar ma da akashe take, ko ta ina ki ka ji kiran mu ba mu ji ba oho."






Murmushi kawai tayi tare da kunna wayar kamar yadda taji aranta cewa Jameel na nemanta hakan ya sa ba inda ta fara lekawa sai Group din Marubuta, Message ko na farko d ya fara zuwa mata shine wan da sahibinta ya yi tagging dinta.




Tsayawa kallon message din tayi kawai tana sakar murmushi ba tare da ta Ankara ba.




Shigowar Mammah da Abhi ne ya katse ta daga duniyar ta shige acikin kankanin lokaci.




Abhi ya karaso gareta tare da dafa mata kai, "Ammienah ya jikin dai, barcin nan na lafiyane kuwa?"






Kallon agogon wayarta ta fara yi sannan ta dago ta kallesa, "Lah Abhi Yaushe ka dawo yau date 30 fa."




Cikin fara'a yake fadin, "Eh mana nazo kinata sharban barcinki nace ko takwararaki ce tazo kuke hira taki karewa kun manta damu."




"Abhina ke nan, ai da naga Kaka ko ba zan dawo ba yasin sai dai inyo maku byebye." Cewar Nafeesa tana kokarin latsa wayarta






Abhi Yayi Murmushi, "Wato dai ba za a ajiye wayar nan ba ko? To maza a ajiye ayi wanka ai sallah sannan aci abinci."




Shagabewa ta yi, "Umm Abhi nemana ake bara ince masu ina zuwa tam."




Shafa kanta yayi yana, "Yawwa Yar Albarka Ammiena,bara mu barki da Maryam ta tayaki kintsawa Muna falo in kin gama kya fito ki karbi tsarabarki."




Girgiza kai tare da murmushi kawai Nafeesa tai.






Mammah,Abhi tare da Sabeer suka fita, sai Nafeesa da Maryam.


Reply tayowa Jameel da , "Tab Yasin ni ba gauruwace ba,Dan dai bana da lafiyane Amman da yanzu nayi jajjagen miyar Kuka da kai."






Message din na Isa Yayo murmushi , "ni ko zan jira har ki samu sauki domin inga yadda ake jajjage da mutane."






Dariya Nafeesa tai wadda sai da ta fito fili ta ce, "Bara inyi wanka in dawo yau zanyi caskale da wani agidannan."




Da fadin hakan ta rufe data Amman har yanzu murmushi ya kasa gushewa daga fuskarta hakwarannan kamar mai tallan makilin.




Mamaki ya sa Maryam yin shiru tare da tafiya dogon tunani,domin tun da take bata taba ganin Nafeesa Cikin farinciki kamar na yau ba,duk da kasancewar kullum cikin murmushi take Amman bata cika washele baki da sunan tana dariya ba.




Nafeesa ce ta dakawa Maryam duka abaya, "Dilla ni kin tafi wani tunani rikeni in tashi jikina ba kwari."






Cikin Ranzana Maryam tayi tsaki, "To ai ke dince naga kinata wani kyalkyala dariya tamkar sabuwar kamu wai miye Sirrinne?"






Dafa Maryam Nafeesa tai tare da kokarin tashi, "Sirrin na da tsawo Dana baki labari."




Maryam ta riketa ta karasa tasowa tana, "Ina binki fa bashin wani sirrin ga wani ma na yau ni gaskiya na zaku inji sirrukannan Dan kwanakinnan salon ya chanja gabadaya."




A kofar toilet din ta tsaya, "In Lokacin ki San Sirrin yayi zan sanar da ke batare da kin ankaraba Amman ba yanzu ba." Ta sake mata murmushi akarshen maganar tare d shigewa cikin bandakin.






Wanka tayo tare da dauro alwala sannan ta fito tayi sallah, gabadaya yau yanayin Nafeesa ya chanja ba Magana illa murmushi da ke bayyana afuskarta.




Cikin Shigarta ta Farar doguwar Riga tare da mayafinta ta fito hannu rike Dana Habibbtynta.




"Oyoyo Ammien Dady,kullum kara girma da kyau Babyna ke yi." Cewar Abhi.






Rufe fuska da hannu Nafeesa tayi tare da shagwabewa , "Uhum Abhina ni ka daina."




Abhi ya ce, "To, to na dain a Ammien Abhi Zo in baki abinci da kaina nasan Mammah ba wani kulamin da ke take ba."karasa maganar yayi tare da bude hannunsa alamar tazo.




Sabeer ya sa kuka, "Mammah kin gama Abhi ni baya ban abinci abaki Amman zai baiwa Aunty ko?"




Mammah ta ce, "Rabu da su Sabeer dina Dadinta ma kowa ya san kai ne Auta ita kuwa gardiyace."




Dariya Sabeer yayi yana kallon Nafeesa tare da yi mata gwalo.




Nafeesa ta kalli Abhi , "Abhi ka gan su ko?"




"Sharesu ke kadai zan ba tsaraba da Maryam,Amman Sabeer kam da Mammahsa sai kallo." Fadin Abhi.




Gwalo ita ma tai wa Sabeer kamar yadda yayi mata.




Gabadaya dariya suka sa afalon.




Abhi ya fara bawa Nafeesa Abinci,kamar magani take karba cikin shagwaba harda guntun kuka, can ta tuna da tacewa Sahabinta tana zuwa.




Azabure ta mike batare da ta ce komai ba ta shige dakinta aguje.




Tsayawa kallonta kawai sukai sai gashi ta dawo hannu dauke da waya.




Abhi ya ce, "Oh wannan waya dai, to zo ki karasa abincin ko?"




Cikin shagwaba take fadin, "Um umm ni na koshi Abhi inna kara amai zan yi fa."






Murmushi yayi, "Allah dai ya shiryamin Ammienna."






Itama Murmushin ta yo masa tare da bude wayarta ta shiga WhatsApp .


Kamar Yadda take tsammani Reply Din sa ta fara gani.


"Hhhhh Lallai yau ba samu gamona ni za ayi caskale dani,ni da nake da mutane yau za ayi Dani,Oh shiyasa nakejita jin tsammi maza kam aje ayi wanka." Cewar Nafseen.






Nafeesa ta gyara zama tare da fadin, "Hhh To ai dai gani nadawo ba kai ne zakayi Fada da jarumar mata ba? Muzuba mu gani,kuma ysin ni bani tsami sai dai wani." Ta kare maganar tare da murguda baki tamkar yana wajen.






Cikin sa'a kuwa yana Online ya maido mata, "Yo za mu gani dai Amman da kwai yan adawata agidannan sosai gwara muje PC kin ga ko kin kayar dani ni daya zanji kunya batare da wani yaji ba."




"Hhhhh To Ashe dai ana tsoro, Wanda ya Riga zuwa Pcn ma shine Jarumi." Reply din Nafeesa.


Jameel....










Urs Xayyeesherth
https://www.facebook.com/106494781436168/


https://www.facebook.com/106494781436168/




_*SAI NA AURI MARUBUCI📝📝📝*_
_(Nafseen)_






*NOBLE WRITERS ASSOCIATION*


°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
_Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu._
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
NA
XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH






✨6STARS INDEED


_*SAI NA AURI MARUBUCI...Kirkiraren labarine, mai dauke da nishadi na mussaman, al'ajabi tare da ban tausayi,tsantsar soyayya da kauna mai ban mamaki*_


PAGE 15


BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM






_*SADAUKARWA GA DUK MASOYAN JAMEEL (Nafseen) aduk in da suke🤗Hadda nima Yayana,Za mu yi yadda mukeso da Fejinnan❤️KAI ARADU MA HARDA MAKIYANKA😅KU KARANTA KYAUTA NA KU NE,SON SO FISABILLAH ZUCIYA DAYA❤️🙌🏻*_


Jameel ne yafara yi mata magana ta private , "Assalam Alaikum, tun yanzu gashi na fara cin nasara."






Bata Rai Nafeesa tai cike da yanayin shagwaba tamkar yana ganinta ta yo masa reply, "Umm umm Yasin ta katanga ka diro ni ko ta kofa na Shigo nice dai Jarumar."




Dariya yanayin maganarta ta tabashi domin yanayin shagwaba karara ya bayyana.


Murmushi Ya yi , "To! To!! Yanzu fadamin tsakanin ni da ke waye Jarumin?




Da sauri Nafeesa na wangale baki ta ce, " Nice."




"Iye Cuwacuwa kenan kin yi sonkai Amman shi ke nan ba komai aje zuwa." Cewar Nafseen.




Nafeesa ta ce, "Umm ni kam.




Nafseen yace "Umm ke kam me"? Tace "a'a bance komai ba" yace "faɗi gaskiya zan siya miki sweet" nan take tace "haba kamar wata yarinya" yasa Alamun dariya "to da wace in ba yarinya ba"? Jin yace hakan kawai sai ta sa Alamun tafiya kamar dai taji haushin kiran ta da yarinya da yayi, nan take ya shiga lallaɓa ta har yana cewa "haba jaruma ya kike haka ne kamar ba jaruma ba"! Ai kuwa nan da nan ta saki wani murmushi a zahiri saboda kiran ta da jarumar da yayi ya sosa mata inda ke mata ƙaiƙayi nan take tace "umm umm to ka yarda cewa ni jaruma ce yanzu"? Yace "ai ya zama dole na yarda tunda naga kin nuna jarumtar" cikin mgnr sa sai ya haɗa da alamun gwalo a nan sai ta ƙara cewa "umm wato wayo zaka min shine ka kira ni da jaruma saboda ka lallaba ni ko"? Yace haba dai wane mutum, ai da gaske ke jarumar ce" tace "to shikenan kaci sa'a da yau idan na tayar da rikici sai ka zo da ƙafar ka ka bani haƙuri zan haƙura" yayi murmushi zuciyar sa cike da mamaki ya fara zancen zuci yana cewa "shin wannan yarinyar me take nufi da cewa sai naje da ƙafa ta na bata haƙuri" nan zancen zuci ya fito fili yace "koda yake meye ma zan tsaya wani zancen zuci muje zuwa dai koma menene zamu gani idan muna raye"




Ganin shiru bai yo reply ba yasa Nafeesa fadin, "Ko dai kaji tsorone,Hhhh Gaskiya ni Jarumar gaskiyace."




Tana tura masa karaf Abhi ya kwace wayar batare da taga reply din Sa ba.




"Haba Ammie na tun tuni kina kan waya kamar wata mai aikin office? ga Maryam kin barta gaho ko? To na kwace wayar nan ba zan maido miki yanzu ba." Cewar Abhi.






Nafeesa ta zaro Ido kan Maganarsa ta karshe cewa ba zai dawo mata da wayarba,,nan take ta tuno Nafseen, lokaci guda kanta ya fara Sarawa ta fara gani bibbiyu, zata.....




Urs Xayyeesherth
https://www.facebook.com/106494781436168/




_*SAI NA AURI MARUBUCI📝📝📝*_
_(Nafseen)_






*NOBLE WRITERS ASSOCIATION*


°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
_Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu._
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
NA
XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH






✨6STARS INDEED


_*SAI NA AURI MARUBUCI...Kirkiraren labarine, mai dauke da nishadi na mussaman, al'ajabi tare da ban tausayi,tsantsar soyayya da kauna mai ban mamaki*_


PAGE 16


BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM




*SADAUKARWA GAREKI SISTER ZEEY YAR MUTAN ZAZZAU,ALLAH KARA BASIRA DA HAZAKA INA YINKI WALLE HAR CIKIN RAINA🥰*




*TUKWICI GAREKI MY MAREEYA😍CAN'T LOVE YOU LESS ADDU'AHTA A KULLUM BAI WUCE ALLAH YA BAKI LAFIYA MAI INGANCI BA*




🤔🤔 *SHIN NI KADAI NA FAHIMCE CEWA A LAMARIN NAFEESA SURUKANNA NA DA YAWA,NA DAYA BA SUMA TAKE BA,KUMA BA BARCI TAKE BA🤔SHIN ME TAKE??*




Zata fadi Maryam ne ta riketa Abhi ko yana amsan wayan tafiyarsa yayi bai ma tsaya ba, Maryam ne ta daga ta suka shiga daki sai kuka Maryam dinma take ta kan yi, aiko abin data sani shi ne ya faru Nafeesa faduwa tayi tamkar wata matacciya gefen Idonta sai hawaye ke fita ga shi bata numfashi,Maryam ko tasa niyyan bazata fada ma su Mammah ba sabida Ita a ganin ta yaushe suka Fita a damuwa kan Nafeesa kuma su kuma komawa gaskiya gara suyi farin ciki suma, ta dauka alkawarin bazata fada ma kowa ba in sha Allah har sai Allah yayi farkawan Nafeesa.














Maryam Wayan ta,ta dauka ta kira Umminta ta mata bayani sosai kuma ta fahimta itama anan ta ce mata zata kwana da Nafeesa Ummi ta amince Mata ta ce, " Zan fada ma Abban ki kinji." Maryam ta ce, "thank you Ummi na shiyasa nake kara sonki."


Ummmi dariya tayi ta ce, " yadda Kike a Zuciyata haka Nafeesa take kinga ko ba banbanci ko?" Maryam ta ce, " hakane kan Ummi ", Ummi ta ce to sai anjima ki kula da ita sosae kinji Maryam tace in sha Allah ummi." sallama sukayi ummi tadan wayan aranta ta ce, " bansan mesa Allah ya daura min son Nafeesa da tausayin ta ba ya Allah ka yaye ma wannan yarinyan ka cika mata burinta in dai shine mafi alkairi."






Tana cikin wannan tunanin Abba yadawo ya tadda ta ya ce, "Lafiya kuwa Ina ta magana shiru?" Ta ce , "hmm Wlh ban san ka dawo ba."




" haba uwar gida tunanin me Kike hakane Ina Maryam naji gidan shiru anan Ummi ke ba shi labarin abin da ke faruwa shima shiru ya yi ya ce, " wlh kin ga duk abin da zanwa Maryam Zanyi ma Nafisa,Allah zai cika mata burinta kuma zai yaye Mata." da Ameen ummi ta amsa suka wuce ciki .












Abangaren Maryam kuwa bayan ta ajiye wayan fitowa tayi falo Mammah ke tambayarta ina Nafeesa Maryam me hanaki tafiya har yanzu?
yanzuma fitowa nayi nace Maki yakamata ki koma Gida dare ya yi."
Maryam ta ce, "Mammah Zan kwana a tare da Nafeesa harna Kira Ummi na fada mata kinga bata da lafiya kuma Abhi yadawo yakamata a samu Mai zama kusa da ita shine na ce zan kwana a tare da Ita." Mamma bata San Erin dadin da taji ba koba komai Nafeesa tayi dace da kawa ta gari bata San da bakin da zata godema Maryam ba.


"Ngode sosai da Erin abin da Kike ma Nafeesa a lokacin da mutane da yawa suke kallon matsalanta kaman ba gaske ba amma ke kin tsaya akan Al,amarinta Maryam nagode sosai, Allah saka miki da alkairi ."tana yi tana zubda kwalla Maryam itama kukan ta Fara "Mammah Dan Allah ki daina Fadin haka ki daina kuka." hannu ta sa tana goge hawayen dake zuba a Idon Mammah,


"Mammah plzz you have to and rest, stop crying kinga Abhi yadawo zan kula da Nafeesa kar ya ga kina cikin damuwa."










Mammah ta ce, "to Maryam thanks so much god bless you let me letf but before I have to see Her." Maryam ta ce, "Ok Mamma amma bacci take a Haka suka shi ga dakin tare Mamma taje ta zauna a gefen Nfeesa addu'ah sosai ta Mata kan ta fita a dakin .




Maryam ta kara gyara. Mata kwanciya tana, " Nafeesa Allah baki lafiya in sha Allah burinki zai cika,kuma komai ma zai wuce."










.
Abangaren napseen kuwa, replied yayi da look at that baby girl nifa bana tsoro sai dai aji tsorona Dan kiji ." ya tura tare da emoji na gwalo amma shiru bega reply nata ba kuma ga hiran nasu yana sashi nishadi shirun daya ji ne yasa ya Kara tura "yeeee itane Ashe taji tsoron ma.. still shiru yace "aa lafiya kuwa ina ga she have a lot to do Bari nima na sauka ."nan ya sauka.












Abhi ko yana amsan wayan ya kashe shi baki daya yaje ya ajiye sai da dare yayi yadawo daga mosque shida sabeer yake cewa , "Ammyna lafiya kuwa bata fito ba ga lokacin dinner ma yayi." anan mamma ke gada masa ai bacci take ta yi ma Maryam ma zata kwana da ita nan da nan hankalin Abhi ya tashi meya faru da ita mamma ta ce. "aa ba komai kasan dai yau bata jin dadi ana bukatan ta huta ai karka damu ba komai."




amma Abhi dai hankalinsa bai kwanta ba ya ce , "to bari na dubo ta amma nan suka wuce dakin Nsfeesa suka ganta tamkar ba rai a jikinta amma tana numfashi Abhi ya ce, " Maryam Allah miki albarka ." da "Ameen" ta amsa Abhi ya ce, "to kin ga tana bukatan Hutu amma ta biye ma waya kinga ma gara Dana amsa ."Maryam kirjintane ya buga taji wani hawaye na bin face nata aranta tace "Allah sarki Ahi besan rashin wayan shine ya jepata a wannan yanayin ba amma in sha Allah zanyi kokarin ganin abhi yadawo Mata da wayan amma dole saita hakura da kanta dole zan bata hakuri ta danne duk abin da zataji tayi ma Abhi biyayya ."




Fita su kayi Mamma ta ce, "Maryam ta fito suyi dinner haks nan ta fito amma duk hnklnta bayi jikin ta .










Nafseen kuwa ta bude data tare da zumudin ganin Erin amsan da samu wajen Nafeesa amma me sai yaji shiru Kawai ji yayi ransa ya baci ma ko group din be shiga ba ya rupe datan sai kuma ya fara tunani shi kadai "to meye ma bashi na damuwa har haka yayi kokarin cire tunanin ta aransa amma hakan be samu ba Sabida Nfeesa Yarinya ce shagwababbiya Edan yana tuna Erin yadda take masa shagwaba sai yayi murmushi kuma sai yakara cewa meke damu na ne Haka to mema zaisa na damu haka, Abu daya yake tunawa salon yarinya yana matukar birgesa gata yarinya Amman in tai wani abun babbama ba zai ba, duk abunnan bai taba ganin hotonta ba kuma bai taba tambaya ba Amman yana sawa aransa cewa kyakkyawace ajin farko kamar yadda halinta da kalamanta suke.
















Maryam bayan tadawo addu,a ta karama ma Nafeesa ta kwanta aiko can cikin dare wajen 2:00 taji nafeesa na "Abhhi Dan Allah kayi hakuri kabani wayana na san Nafseeen ya min reply." Nan take ta fashe da kuka , Maryam ta riketa.


"Abhi ka taimaka min kaji Dan Allah Wallahi rabani da wayannan kaman Ana min baraxana da rayuwats ne Abhi plxxx ."




Maryam ta ce, "haba Nafeesa ki dawo hankalinki mana Wai yau ke ce Kika tashi ba addu',ah a bakinki keda Kike yima wasu fada akan addu'ah amma ace yau kene kika tashi ba ita?"


nan Nafeesa ta Fara share hawaye ta ce, " Astagfiirullah addu'a ta fara jerowa tana hawaye tana tuna abin da ya Faru Wai da gaske Abhi ya amshi wayana gaskiya bazan iya jure hakan ba.






tana wannan tunanin Maryam tace , "Mata babe oya a tashi a yi sallah ko nan ta Mike tayi alwala ta rama dukkan sallanta ta dear tana edarwa tasa kuka tace, " Maryam meya hanani tafiya kuma Wai da gaske ne Abhi ya kwace min wayana Maryam Idan ya baki ki bani ne Dan Allah kar kimin wasa kinsan yadda nakejikuwa?"
Maryam da hawaye suka cika mata Edo ta ce, ' nafeesa ki kwanta ki huta zamuyi maganagobe kinji."




kuka Nafeesa takara sautinsa "plss Maryam kibani amsa Dan Allah." Maryam ta ce ,"promise zan fada Miki gobe amma yanzu ki samu ki huta da kyar Maryam ta lallaba nafeesa ta hakura akan sae gobe.














Wa she gari






Ana kiran asuba Nafesa ta Fara tashin Maryam Sabida ita bacci ko na second daya be dauke ta ba hasalima hangowa take Erin amsan da Nafseen ya tura Mata gobe Maryam na bata wayan shi zata fara dubawa nan suka yi alwala sukayi sallah Nafeesa ta ce , "to ban wayan Habibbty."






Maryam ta ce, "baby girl ki saurari abin da zan fada Miki ."




Nafeesa ta ce , ,"to ban wayan sai muyi maganar."




Nafeesa Maryam ta fada cikin raunanniyar murya Mai dauke da damuwa nan da nan Nafeesa ta ba da attention dinta wa Maryam Sabida tasan abind a zata pada Mata yanada mahimmanci.




"inajinki baby girl da farin cikin ki Dana su Abhi wanne kika fi so ?"


Cewar Maryam.




Nafeesa ta ce, " Na su Sabida suma koda yaushe suna hana Kansu farin ciki domin suga nasamu."




Maryam ta ce to, " yanzu suma suna bukatan taemakonki da kuma kulawanki ."


Nafeesa ta ce , "akan me kenan ?"




Maryam ta matso

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login