Showing 6001 words to 9000 words out of 28317 words
Chapter 3 - Sai Na Auri Marubuci Nafseen Complete by Zulaihat.txt
hijabinta tai tasa Wanda ya rufe mata jiki har kasan kafafunta,ta fito falo ba Mammah hakan ya bata damar nufan kichin domin ta San in bata falo to tana kichin.
Jin alamun taku ya sa Mammah ta daga batare da Nafeesa ta isa gareta ba, Murmushi ta yi, "Ah Ammien Abhi ina zuwa da yamma haka? Ina shirin Sa Sabeer ya tasoki ki karba girkin ina son yin wani bincike."
Nafeesa ta shagwabe fuska, "Ayyah Mammah agidan su Maryam zani in karbo littafina an bamu assignment kuma ma ba zan Iya ni daya ba tare zamu yi."
Mammah ta ce, "To Allah ya kiyaye hanya,ki kula bana son shashanci kin sani ko? Ki kama kanki kamar yadda shigarki ta nuna kuma karki kai dare."
Murmushi Nafeesa ta yi, "To Mammah in sha Allah zan kiyaye sai na dawo,Sabeer byebye."
"Bye bye Anti ki siyomin chocolate." Cewar Sabeer ya na wasa
Nafeesa na fita ta nufa gidansu Maryam da sallama da shiga,Aunty ce zaune afalo tana kallo, ta amsa mata da fara'arta, "Ah Yau Nafeesa ce agidan namu? Lallai munyi babbar bakuwa."
Nafeesa na Murmushi ta durkusa, "Ina hini Anty?."
"Lafiya lau Nafeesa fatan kina lafiya,ya su Mammah kuma?"cewar Aunty
Nafeesa ta Amsa da, " Duk lafiya lau, Aunty Maryam fa."
Kan Aunty ta bada amsa Maryam ta fito da Sauri, "Oyoyo Habeebbty muryarki naji kamar amafarki Ashe da gaske ke din ce."
Aunty ta tashi tana, " kamar an shekara ba aga juna ba,ina jin dai miji daya zamu Baku."
Dariya kawai Maryam da Nafeesa sukai.
Nafeesa na ganin Aunty ta Shiga daki ta ce, "Habibbty littafi zaki rakani siyowa karya nawa Mammah nace assignment zan zo muyi, kin San in taji littafi zan siya zata hanani wai idona yanzu ma karatun aboye nake wallahi kuma ni ba zan Iya dainawa ba."
Maryam ta ce, "Allah Habibbty da gaskiyar Mammah so ki ke ki rasa idanun naki gabadayane? Haba Dan Allah yakamata ki rage karatunnan fa."
Rike hannun Maryam ta yi, "Dan Allah Habibbty kar Ku toshemin hanyar farincikina,karatun littafinnan kadai ke bani walwala da nishadi,Ina son karatun littafin Marubuci Nafseen kuma inda rai da rabo watarana sai na ganshi kuma na auresa muddin ina numfashi."
Magana take hawaye na gangarowa daga cikin idaniyanta.
Maryam ce tasa hannu tana goge mata ya yinda itama ta fara kwallan, "Ki daina Kuka Habibbty zaki gansa kuma zaki auresa in sha Allah,yanzu bara na fadama Aunty ta ba dreba motarta ya kai mu kasuwan ko?"
Nafeesa ta ce, "Eh jeki dawo akwai labari Nima na zama marubuciya fa."
Maryam ta fito tana dariya, "ai ke kam zaki Iya zama labarin ma da kansa ba mai rubutawan ba."
Da key din motar Aunty Maryam ta dawo ahannunta yawwa, "Habibbty muje."
Suna fita Maryam ta baiwa dreba key ita da Nafeesa suka shige baya tare da fadin ya kai su sabuwar kasuwa.
Dai,dai gun masu saida littafi inda Nafeesa ta saba siya Maryam ta ce dreba ya tsaya.
Aiko Nafeesa ta yi nasara zuwa domin sababbin littafan marubucinta har biyu sun fitofito,SO SHAMATAR ZUCI Da kuma YAN MAZA.
Nafeesa ta kasa Boye farincikinta hakan yasata sai was he Baki take awajen.
Sun gama siya ke nan Nafeesa ta hango shagon da ake saida Films, ta ce, "Habibbty zan siya film."
Maryam ta kalleta cike da Mamaki, "Habibbty ke da bakya kallo me za ki yi da film kuma?"
Harararta Nafeesa ta yi, "To na fara kallon daga yau,ni muje shagon cen mu siya."
Binta kawai Maryam ta yi domin bata da tacewa.
Da sallamarsu suka shiga shagon cikin fara'a kuwa mai shagon ya amsa.
Nafeesa ta ce, "Films muke so Amman Wanda marubuci Nafseen ya rubuta."
Murmushi mai shagon ya yi, "Ah madam an gama daman ko duk wa'inda ya rubutane Sabin fitowa Dan dazu da safe ma na karbo biyun nan,SIRRIN DA KE RAINA, NIDA KE MUN DACE, Da sauri Nafeesa ta karba tana mai yi masa godiya tare da mika masa kudin.
Suna komawa Mota Maryam ta ce, " Yawwa Habibbty kin ce min kin zama marubuciya tayaya?"
Dariya Nafeesa tai, "Ta inda kowa ke zama mana duk abin da zai hadani da Nafseen dina kusa gareni koma miye zan Iya ina tabbatar miki da hakan,na fara rubutu na zama marubuciya domin kasancewata da shi kawai."
Maryam ta gyara zama , "Kice min kun hadu ma."
"Umm haba dai ba ajima da sani ba,kuma kaf na duba cikin group din ba mai irin sunansa Abu daya na rike akullum jikina na bani cewa yana group din,ko da wannan aka barni ina jin dadi araina."
Murmushi kawai Maryam ta yi domin bata da tacewa, sai da su kai Nafeesa har gida sannan suka koma na su gidan.
***Tun da Nafeesa ta koma bayan ta yi sallah kallo kawai ta Sa tanayi.
Mammah ta ce, "ai da karatun littafancen gwanda miki kallonma wallahi."
Nafeesa ba ta ce komai ba sai murmushi.
Sai da Nafeesa ta gama kalle films din tsaf wajen 10 kan ta tafi daki ta kwanta, sha biyun Dare dai,dai ta fara mafarkin Nafseen na Online kamar da wasa ta farka,ji ta yi barcin ya bace a idonta gabadaya,wayarta ta dauko ta kunna,abun mamaki tare suka hau online awannan lokacin.
Sallama ya yi agroup din marubuta kasancewar komin dare ba a rasa yan surutu aciki.
Nafeesa.......
Urs Xayyeesherth
https://www.facebook.com/106494781436168/
_*SAI NA AURI MARUBUCI📝📝📝*_
_(Nafseen)_
*NOBLE WRITERS ASSOCIATION*
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
_Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu._
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
NA
XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH
✨6STARS INDEED
_*SAI NA AURI MARUBUCI...Kirkiraren labarine, mai dauke da nishadi na mussaman, al'ajabi tare da ban tausayi,tsantsar soyayya da kauna mai ban mamaki*_
PAGE 12
BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM
☹️KO KU TUNAMIN JIYA NAYI MISTAKE NAKARASA 11 MAIMAKON 12 DAN KUNGA GUNTUNE🤣TO SHI KE NAN ABARSA A KARASHEN 11 DIN KAWAI YAU GA 12
😂😂ANATA MAGANA KAN SIRRIN DA NAFEESA ZATA FADAWA MARYAM KAR KUJI KOMAI SIRRIN NA NAN TAFE🥰🥰
Wayarta ta mutu,wani irin tsaki tayi domin batama lura da cewa chajin wayar ya kusa karewa ba sai ganin mutuwarta da ta yi adai,dai lokacin da tafi bukatar wayar Amman ba dama,ba ta San lokacin da kwalla ya fara zubo mata ba gashi ba nefa alokacin ji take tamkar An rabata da muradin rantane baki daya,kuka tayi mai isanta har barci ya dauketa batare da ta sani ba.
Da Asuba kuwa Mammah na tashinta kan ta yo alwala sai da saka wayarta chaji, tsabar wayar ta kona mata rai bata kara bi ta kanta ba sai da ta gama shirin tafiya skul,ko kunnata ba tai ba, tasa acikin Jakarta kawai.
Tare da suka fito da Mammah ,Ita tai Skul Mammah kuma asibiti shi ko Sabeer tun karfe bakwai ya tafi skul.
Nafe daya suka shiga sai da aka sauke Nafeesa Kan Mammah ta huce asibiti.
Nafeesa na Sauri zata shige Skul kicibis tai da taron mazaje sun mamaye kofar gate din makaranta, Mutansir ne da abokansa.
Zagayeta sukayi suna wata irin dariya ta k'eta.
"Ke Kin Isa ko? Kin yi shaharar Da har ni zaki Mara cikin mutane? Ni zaki tozarta yar matsiyata,makauniya,ke wai atunaninki Dan me nake sonki ne ma? Kin taba tambayar kan ki hakan? A kyau dai inajin Fatima ta dama ki,bare kuma azo maganar arziki yau dinnan zaki San ni kika Mara kan wani marubuci Mara aikinyi Da bai San kina yi ba, yau zan nuna miki ni wanene agarinnan, zan yi abun da ba Wanda ya isa ya fito nema miki hakki ko ahukuntani, kinfi kowa Sanin waye mahaifina bare kuma azo maganar waye ni karan kai na ." Cewar Mutansir yana zagaye Nafeesa, maganar yake cikin izza yana mai nuna mata hannu
Kuka Nafeesa ta fara, "Dan Allah kayi hakuri kar Ku chutar dani, natuba Dan Allah kuyi hakuri ba zan kara ba,komai kace inyi zan yi Amman karka batamin rayuwata,ni Yarinyace ka jikaina da na iyayena karka cutar dani Dan Allah." Ta durkusa kasa tana mai bashi hakuri.
Daga Mutansir har Abokanansa wata irin dariyar mugunta suka fara awajen.
"Alokacin da ki ka mareni,kika ci min mutunci,kika tozartani kin tuna cewa ke yarinyace? Ai da Yarintartaki ki kai amfani ko? To ba shakka nima ayau da Yarintartaki zan yi amfani ta yadda ba wani namiji da zai so ki bare ya aureki, ko shi Wanda kike haukar akasan ina da tabbacin bare so ki ba,kin ga anyi biyu babu ko? Adalci daya zan miki, ki zaba tsakanin acide afuska da kuma umm ba sai na Fada ba ai kin gane, duk dai fuskar taki ma ba wani kyau gareta ba." Cewar Mutansir.
Daya daga cikin Abokan nasa ne yayi magana, "Oga ya za ka mana hakane? Karka manta fa ita ba zabi tabaka ba ga mari ga fitsari in kai bazaka Iya ba ka bamu dama kawai mu far mata in an gama sai mu koma ga acide din kaga ba hanyar moruwa to kowanni bangare ke nan."
Muntasir ya yi wata irin hamshakiyar muguwar dariya, "Mole walle ina kaunarka kwakwalwarka na matukar ja, tun kan ya Sa ido su bayyana Ku kai min ita hostel."
Kara durkusa gabansa Nafeesa ta yi, "Dan Allah kayi hakuri karku batamin rayuwata Dan Allah, nace Dan Allah." Maganar take cikin kuka har ta shide ta kasa fadin komai ma.
Daukanta sukai cikin hanzari tana ihu Amman ko kadan ba mai jinta domin sun toshe mata bakin, hostel din maza suka nufa dakin d Mutansir yake, ga dakin duhu baka ganin komai jefa Nafeesa sukai kan katifar tare da fita, Mutansir ya shigo yana wani banbankarewa.
Kayan jikinta ya fara kokarin rabata da su,tun tana motsi har ta yi shiru illa ajiyar zuciyar da take.....
Urs Xayyeesherth
https://www.facebook.com/106494781436168/
_*SAI NA AURI MARUBUCI📝📝📝*_
_(Nafseen)_
*NOBLE WRITERS ASSOCIATION*
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
_Gidan karamci, rubutu don cigaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu._
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
NA
XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH
✨6STARS INDEED
_*SAI NA AURI MARUBUCI...Kirkiraren labarine, mai dauke da nishadi na mussaman, al'ajabi tare da ban tausayi,tsantsar soyayya da kauna mai ban mamaki*_
PAGE 11
BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM
🤣🤣DAN ALLAH KAR KUYI KORAFIN GAJERANCIN FEJIN NAN
Ce ta amsa tare da fadin, "Wa'alaika salam."
Batare da ta lura da sunan ba.
Jameel (Nafseen) ya yo reply da , "Ah ya naga kamar bakuwa muka yi agidanne."
Nafeesa ta tura da alamar dariya, "Tab ai ko ni ba bakuwa bace nafi wata agidannan fa, ko kai na rigaka."
Kamar yadda tai dariya Shima hakan ya yi, "Kin San Bamai? To indai kin San Bamai shi kan shi na rigasa zuwa gidannan."
Xayyeesherth ce ta katse masu magana da, "Ah Ah Yaya Jamilu adai rage mana."
Maganar Xayyeesherth ne ya baiwa Nafeesa damar kallon sunan da kyau kamar yadda take tsammani Jameel Nafseen ta ga an rubuta,batare da ta Ankara ba wani irin farincikine ya mamaye zuciyarta, ihu ta fara tana tsalle da rawa ta ma rasa me za ta yi illa rungumar wayar da tai tana rawa da tsallenta.
Xayyeesher ya maidawo da Reply, "Ke Xayyishatu ina wasa da ke ne? Dare ya yi maza jekiyi barci manya na magana kina sako baki."
Dariya Xayyeesher ta yi, "Aradu ban kwanciya yau kam sai naga ka sauka tukunna nima."
"Iyee,ina fadi kina fadi to kinyi abakin chocolate din ki." Cewar Nafseen.
Alamar kuka ta tura, "Haba Yaya Jamilun ba ma haka,gudnyt walle na tahi sai da sahe."
Ya ce, "Yawwa Yar Albarka,Allah tashemu Lafiya."
"Byebye adai kula ban da...... Bata karasa ba ta Sa emojin gudu.
Dariya ya yi, " Allah ya shirya mana kai in ki ka Shiga hanuna zan baki mamaki."
Nan take Xayyeesher ta sauka tana Dariya, Nafeesa kuwa tunda taga sunansa ta ma kasa maido masa da reply kallon sunan take karayi da Mamaki shin daman da gaske zata yi Magana da Nafseen aduniyarnan har suyi wasa da dariya? Ga yadda tai tunani Sam ba haka yake ba, tunaninta zai kasance mai girmankai da jijji da kai amman ko Kadan hakan bai samu ba.
Mentioning Sunanta Yayi ganin cewa ta bace cikin gidan, "@Nafeesa ko dai kin bi sahun Yarinyarcen ne kinyi barcin?"
Wani irin bugu taji zuciyarta na yi ganin yadda ya ambaceta cikin bazata,tana kokarin yi masa reply kenan...
A yi hakuri👏bana da chajine Amman in sha Allah gobe zan yi typing awadace,Ku taba wannan Ku lashe😘😘Ina yinku masoyana son so fisabillillah🥰
Urs Xayyeesherth
https://www.facebook.com/106494781436168/
_*SAI NA AURI MARUBUCI📝📝📝*_
_(Nafseen)_
*NOBLE WRITERS ASSOCIATION*
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
_Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu._
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
NA
XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH
✨6STARS INDEED
_*SAI NA AURI MARUBUCI...Kirkiraren labarine, mai dauke da nishadi na mussaman, al'ajabi tare da ban tausayi,tsantsar soyayya da kauna mai ban mamaki*_
PAGE 13
BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM
🤦♀️🤦♀️ALLAH SARKI MASOYAN ASALI ATA HAKURI DANI RASHIN TYPING KAN LOKACI KUN SAN DALILI KE JAWO HAKAN😁NASAN ZAKU MIN UZURI KUMA HAKAN BA ZAI HANA NI GANIN RUWAN COMMENTS BA🥰
GAREKU MASOYAN NAFEESA FATAN BURINKI YA CIKA😁
A dai,dai lokacin da yake shirin yi mata mai gabadaya Nafeesa tai wata irin kara mai kama da na damusa,damkosa tai kawai ta fara jibga ba ji ba gani,jin ihunsa ya Sa sauran mazan da ke waje shigowa ko ajikinta kamar batai komai ba, dukansu ta farayi bilhakki da gaskiya,gabadaya sunyi Jina,jina ba kwari bare karfi,kan kace me har sun fara Jan jiki suna tserewa ahankali,gabadaya sun tsorata "anya kuwa Nafeesa ba namiji ba ce,in ko macece to ba tantama aljanace."abun da wani cikinsu ke ta fada kenan shi ko Mutansir da yafi kowa jibguwa nan take ya sume awajen.
Sai da ta gama jibgarsu kowa ya tsere illa Mutansir da ke kwance ta dawo hayyacinta kallon jikinta ta farayi awani irin yanayi daga ita sai kananun kayan ciki, ta bi dakin ko ina da kallo sai shegen duhu da kyar ta kura ido sannan ta fara hango kayanta gefe guda,cikin sauri ta karasa wajen tare da dauka tana sawa,har yanzu bata fahimci meya faru ba bare abun da ya kawota dakin hakan ya Sa taketa kara hanzari wajen ganin ta bar dakin, kicib da mutum akasanta kallon da zatayi ta ga Mutansir,nan take hawaye ya fara zubo mata, jakarta ta kara hangowa gefe guda ta dauka ficewa daga dakin tayi cikin kuka, abun mamaki duk abun nan da ya faru glass dinta bai bar idonta ba koda na second daya.
*****Tana fita ba inda ta nufa sai bakin titi, tsare mai Nafe tayi kawai ba inda ta nufa sai gida, Mommah bata nan Sabeer ma na Skul duk ba su dawo ba, dakinta ta huce ban da kuka ba abun da takeyi azuciyarta tana fadin, "Kaddarar rayuwata ke nan Wanda ke so na baya sona Dan Allah gangar jikina yake so,ni kuma Wanda na ke so bai San inayi ba,ban San ma ko zai soni ba, da yanzu Mutansir ya Lalata min rayuwata shi ke nan." Fashewa ta karayi da kuka can kuma ta tuna da yanayin da ta tsinci kan ta, atsorace ta tashi ta zauna tana mamakin shin to ma wai "meyasami Mutansir ne? Kar dai mutuwa ya yi? Waya hanasa ketamun haddi ina sauran Abokan nasa
Shin wai me ke faruwa dani ne? Kokarin fara tuna abun da ya faru a islamiya tayi nan take kanta yafara juyawa duhu ta fara gani bata gane komai nan take wani irin gawartaccen barci ya yi awon gaba da ita.
Sai karfe biyu Mammah da Sabeer suka dawo tare ba karamin Mamaki Mammah taji ba ganin Gidan abude suna Shiga kuwa ta nufi dakin Nafeesa kamar ta sani gata nan kwance "ga duk kan alamu tana wannan barcin ne data saba aduk lokacin da aka bata mata rai." Abun da Mammah ta Fada aranta ke nan tana kallon diyartata cike da tausayi.
Kamar wasa har dare Nafeesa ba alamar motsi atattare da ita, Mammah ta zo har ta gaji da dubata lamarin ya sha bambam da Wanda tasaba yi.
Addu'ah kawai Mammah ta shafa mata tare da janyo kofar ta fita.
*****Wa she Gari da Asuba Mammah na tashi ta nufi dakin Nafeesa,tana nan dai yadda aka barta, ba Dan tana numfashi ba kai kace mutuwa tayi,Abun har ya fara damun Mammah gashi Abhi yau zai dawo hakan ne ma ya Dan sanyaya mata zuciya tafi minti biyar tana kallon diyartata kan daga karshe ta fita.
Karfe uku na yamma dai,dai Abhi ya isa.
Da Murmushinsa Ya shigo gidan,da gudu Sabeer ya rungumesa, Mammah na fadin, "Barka da dawowa Oga." Maganar take cike da fara'ah.
Abhi ya dubi ko ina ba alamar gilmawa Nafeesa.
"Niko wai Ina Ammynane?naga kowa Amman ba ita." Cewar Abhi ya na kara waige-waige.
Mammah tai murmushi, "Ammynka ba Lafiya barci take,."
Abhi ya ce, "Ayyah shiyasa gidan ba dadi Sam gaskiya sai na tada gimbiyata muje."
Mammah batace komai ba kawai suka bi bayan Abhi ita da Sabeer, suna shiga Mammah ta fara kwalla.
"Tun Jiya take barcinnan bata farka ba." Cewar Mammah cikin yanayin damuwa.
Abhi ya ce, "Subhannallah, Shine baki fadamin ba? Kuma baki kai ta asibiti ba?"
Mammah ta ce, "Na dubata Amman ba abun da asibiti za su Iya mata addu'a dai itace asibitin da maganin, tanayin hakan mun sani Amman wannan yanayinsa dabanne sai dai muta addu'an kawai."
Sam Abhi bai ji dadin lamarin ya ma kasa magana kawai ficewa ya yi, azuciyarsa yana matukar tausayin diyarnan tasa domin tunda tazo duniya take fuskantar kalubali kala daban daban iri iri.
Addu'o'i da saukan Al'qur'ani kawai suka Sa agaba.
Kwannan Nafeesa shida kwance ba motsi.
****wani bangaren kuwa na Mediya cikin Group din Marubuta anata hira da ban dariya,Mussaman Nafseen da ya Sa yan Matannan d ya Sa su agaba da tsokana, kamar wasa yana kokarin tagging din gaurayen yan matan gidan, sunantane NAFEESA ya fara fitowa awayarsa batare da Sa komai aransa ba kuwa ya danna kan sunan.
A dai dai lokacin Nafeesa..........
Urs Xayyeesherth
https://www.facebook.com/106494781436168/
_*SAI NA AURI MARUBUCI📝📝📝*_
_(Nafseen)_
*NOBLE WRITERS ASSOCIATION*
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
_Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu._
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
NA
XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH
✨6STARS INDEED
_*SAI NA AURI MARUBUCI...Kirkiraren labarine, mai dauke da nishadi na mussaman, al'ajabi tare da ban tausayi,tsantsar soyayya da kauna mai ban mamaki*_
PAGE 14
BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM
*UMMU AFFAN* *MARUBUCIYAR YAFI DARE DUHU*
*INA GODIYA MATUKAR GASKE,ALLAH KARA BASIRA DA HAZAKA*❤️❤️
*SADAUKARWA GA MASOYAN ASALI BASA FUSHI DUK KWANAKIN DA ZAN DAUKA BNYI TYPING BA ZARAN SUN GANI ZASU SAMBADOMIN SHARHI INA YINKU WALLE*😘😘
Mrs Mubarak
Belar maxare(Maman tima)
Asma'u aji Ibrahim
Fatima Zahra
Fiddausi
Mrs Auwal Forever.
***
Ta farka , Hamdallah Mammaah ta fara. Cikin farinciki ta fita.
Maryam ta rike Nafeesa, "Sannu Habibbty kin tashi?"
Kan gadon ta fara bincikawa ta nemo glass dinta tare da kafawa a idonta ta gyara zaman.
Da Murmushi Nafeesa ta kalleta , "Na tashi Habibbty yaushe kikazo?"
Maryam ta ce, "Tun Safe kinata barcinki abunki."
Waige,waige ta fara, "Umm Habibbty ina wayata naji ana kirana,ki dubamin ita."
Maryam ta tashi tana, "Oh keda kike barci ina zakiji wani kiri ni