Showing 3001 words to 6000 words out of 28317 words

Chapter 2 - Sai Na Auri Marubuci Nafseen Complete by Zulaihat.txt

wuce sa'arta ba ne ta tawo da sauri, "Oyoyo Habibbty har na cire ran zuwanki wallahi."




Nafeesa ta galla mata harara "mai zai hanani zuwa makaranta da lafiyata."


Karaf wani saurayi ya cafe da , "Ai ko da baki zo ba ma ni zan zo gidan da kai na in daukoki."




Tsaki Nafeesa tai tana, "Kin ga Habibbty zo mu tafi."




Har sun fara tafiya ya ja gabansu tare da fadin, "Wai ke me na miki ne ki ka tsaneni? Dan kawai nace ina sonki? In ban da Soyayya ma da kwashe kwashe me zanyi da Makauniya wadda bata gani sai da glass, ko da yake naji labarin cewa wai wani banza da bai ma San kina nan ba kike so."




Nafeesa ta dago tare da fadin, "Mutansir kar ka kara ce masa banza kuma maganar makauniya da ka ke dadinta ba ni nai kai na ba ko? Kuma bance ka soni dole ba,Dan Allah ka kyalleni."






"Ke dakata, ki tsaya wai akan Banza mara aikinyi Wanda ya rasa sana'a sai ta rubutu ki ke Neman min rashin kunya? To na Fada banza."cewar Mutansir yana wuce kamar an saukewa jaki kaya.






Jin Zuciyata tai na bugawa zafin hakan take ji har cikin ranta yanayinta ya fara chanjawa.




Maryam da ta fahimci hakan ta fara Jan ta da niyar su tafi.




Har sun fara Tafiya Kawai Nafeesa ta juyo tare da bin bayan Mutansir ta sha mai gaba alokaci guda ta kai mai wasu zazzafan marika biyu afuskarta, shi ta mari Amman ita take kwalla domin jin zafin abun da ya fada kan Nafseen dinta.




Kamewa Mutansir yayi awajen ya kasa motsi domin tunda yake bai tabajin mari mai dauke da radadi irin na yau ba, zufa ya farayi ta ko ina, ga fitsari na zuba, sauran abokansane suka taso suna dariya.




Ita kuwa Nafeesa ko ajikinta ta cigaba da tafiya batare da ta kara waiwayo garesa ba.






Sai da Mutansir ya dauki minti goma kan ya dawo haiyyacinsa, "Wallahi,wallahi kunji na rantse sai na illata yarinyarnan,illar da har ta mutu ba zata manta ba."cewar Mutansir.




Sauran abokansa kuwa yan Neman ayi da suka gama shan dariyar kara zugasa sukai.




Urs Xayyeesherth
_*SAI NA AURI MARUBUCI📝📝📝*_
_(Nafseen)_




16/1/2021






_GAJERAN LABARI📝_


NAH


AISHA MOHAMMAD SANI
(Xayyeesherthul-humaerath)




_*SAI NA AURI MARUBUCI...Kirkiraren labarine, mai dauke da nishadi na mussaman, al'ajabi tare da ban tausayi,tsantsar soyayya da kauna mai ban mamaki*_








PAGE 8


BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM




*Wannan fejin Sadaukarwane Gareka Yaya Jamilu (Nafseen) tare da Antyna Iklima❤️Ina mai yi maku fatan alkairi tare da cigaba da rayuwar aurenku cikin farinciki,amana da Yarda,Allah Sa Anty Sa sambado mana an biyu🤣amin takwara*






Karatun tai hankali kwance sunfito ke nan dai,dai gate din makaranta zasu fita wata Yarinya da zata kai shekara ashirinne ta dumfarota da sauri, bangaje Nafeesa tai har sai da glass dinta ya fadi kasa, "Maga tayi ai,ke har kin isa ki tabamin Mutansir a makarantarnan,yar matsiyata, ko me kika masa ma ya nace miki oho, da alama dai ba a barsa haka ba, anga 'Ya'yan masu dukiya ana Neman hanyar shige masu Amman tsoro ya hana,to wallahi ahir dinki, ko da gaske ko da wasa naji cewa kina son Mutansir kin Riga kin kade yarinya ba ma ke kadai ba hatta Shi wannan driban da wannan ma'aikaciyar asibitin,makauniyar banza da wofi,wata yar shila da ke ,ko inama abun so ajikinnan ? Mtsww." Cewar Fatima tare da cigaba da yiwa Nafeesa wani mummunan kallo.




Tunda Nafeesa ta durkusar da kanta bata dago ba,ban da hawaye ba abunda ke zuba daga idanunta, Magana ta farayi cikin ruwan Sanyi, "Habibbty Bani Glass din nasaka bana gani."




Ita kan ta Maryam sai da hawaye ya fara bayyana daga fuskarta tsabar tausayin Nafeesa da take.


Karfan Glass din Nafeesa tai tare da sawa a idonta ta rik'e hannun Maryam suka cigaba da tafiya.




Tsaki Fatima tai domin bata so hakan ba Sam ta lura kamar Nafeesa bataji zafi sosai ba,hakan yasata kara tunkararta cikin sauri tare da shan gabanta, Glass din fuskar Nafeesa ta kwace tare da cigaba da tafiya batare da tace komai ba.




Maryam ba kokarin yin Magana Nafeesa ta rik'e mata baki, "Habbibty kar kice komai, wannan kaddaratace, kisa anafe kawai kar drebanku ya gaji da jiranki."










Kallon kawartata tai cike da tausayi, "A hakan zan Sa ki Anafe bayan nasan ba gani kike sosai ba, ki bari in karbo glass din wajenta sai dreban ya kai mu duka, wani iskancin ma Dan sunga ana barinsune."




Nafeesa ta kank'ame hannun Maryam , "Dan Allah ka da ki tada rikice akaina ni ba yar kowa bace kamar yadda ta Fada Amman na San cewa watarana zatayi nadamar abun da tamin,ni kawai akai ni Asibiti Gun Mammah ta nemamin wani glass din,Idon ciwo yake min habibbty wallahi ciwo ya faramin."




Cikin sauri Maryam ta laluba Jakarta tare da Ciro wani karamin glass , "Sorry Habibbty barin Sa miki wannan kan muje asibitin to."






Bayan ta sa mata glass din haka Maryam ta rik'e Nafeesa suka Shiga mota.




Suna shiga Mota Nafeesa ta Sa hannu ajakarta tare da lalubo wani littafi mai suna
*Ajaliin mace* Fasihin marubucin nan nata ne dai ya rubuta, kallon littafin tayi tare da rugumarsa tamkar mutum, wani kayataccen murmushi ta sake,domin ji take duk damuwar da ke ranta ta kau,indai tana tare da littafin da Farincikin ranta ya wallafa,rubutunsa tamkar muryasa gareta,sunansa tamkar hotonsa ne garesa, bangon littafin kuwa ji take tamkar bugun zuciyartane, ji take gabadaya ta nemi damuwar da ke ranta ta rasa,cikin murmushi ta ce, "Habibbty Dan Karantamin kinga bana gani da kyau Dan Allah, kan mu isa."




Murmushi Maryam ma tayi ganin cewa damuwa ta fice daga fuska har zuciyar Kawartata,karban littafin tayi tare da fara karanto mata.




Da mamaki Nafeesa ta haddace littafin tsaf a kwakwalwarta domin kan Maryam ta kai Aya Ita ta karasa mata, Maryam na kuskure wajen furuci zata gyara mata.




"Kai Habibbty ai kin gama haddace littafinnan to miye kuma na sai na karanta miki?"




Murmushu Nafeesa tayi, "Na haddace littafin nan tamkar yadda na haddace Al'Qur'ani mai girma,ko ina kika tabomin zan Iya karasa miki batare da na kalla ba,Amman kin San me? A kullum ina so akarantamin ko ni na karanta,domin aduk lokacin da nake sauraren kalaman banajin muryar kowa akunnena sai na Marubucina,sautin Muryarsa kadai ke sauka acikin kunnuwana, Habibbty mutane da yawa na fadin cewa karyane dan wani ya ce zai iya rasa ransa in ya rasa masoyinsa ko? To ni nasa araina cewa duk ranar da na tabbatar da cewa bazan Taba samun Yaya Nafseen ba, ba makawa zan Iya mutuwa nan take, Ina yi masa so fiye da yadda kowa ke tsammani,in ana maganar soyayya sai kije ana Sa Majnoon da Laiyla to ni ko Kadan basa gabana domin ji nake na ninnkasu natakasu a soyayyata,ko da ace Nafseen ba zai soni ba,akwai wani sirri tsakanina da shi, kuma inada tabbacin ya sani a ko ina yake ma duk da cewa ba mu San juna ba, kin san menene Habibbty?"




Maryam na gyara zama domin jin me Aminiyarta ta zatace dai,dai da lokacin da dreba ya tsaya domin sun iso asibitin batare da ma sun sani ba.






Nafeesa ta ce, "Yawwa Mun Iso."


Suna fita Maryam ta kalli Aminiyarta ta, "Habibbty fadamin sirrin."




Murmushi Nafeesa tai, "Sirrin,kina son jin Sirrin Habibbty?"




Maryam ta ce, "Sosai ma ."




Nafeesa ta ce, "




✌️😁 MY GROUP MEMBERS ANA TARE AYAU MA KUWA?
RUWAN COMMENTS YADDA AKA SABA MUTANEN KWARAI😘😘




Urs Xayyeesherth
_*SAI NA AURI MARUBUCI📝📝📝*_
_(Nafseen)_








NA
XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH


6STARS INDEED✨


_*SAI NA AURI MARUBUCI...Kirkiraren labarine, mai dauke da nishadi na mussaman, al'ajabi tare da ban tausayi,tsantsar soyayya da kauna mai ban mamaki*_


PAGE 9


BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM




"Zan Fada miki sirrin Amman sai lokaci ya yi."


Cike da Murmushi Maryam ta ce, "Allah ya kaimu zan so ko jin wannan sirri domin na San na mussamanne tamkar yadda Habibbtyna ta kasance ta mussaman."


"Umm ni kam kai ni gun Mammahna." Cewar Nafeesa.




Rik'e mata hannu Maryam tayi har suka shiga cikin asibitin, Mammah na ganin Nafeesa gabanta ya fadi tare da karasawa garesu cikin sauri.




"Nafeesa meya sameki? Ina glass din na ganki da wani kuma? Ya naga idonki ya yi wani iri ma lafiya kuwa." Cewar Mammah.




Rike hannun Mammah Nafeesa tayi , "Aa fa Mammah fad'uwa Glass din ya yi kuma ya fashe,shi ne iska ta tabamin ido ya fara hawaye."




Mammah ta kalla Maryam, "Anya kuwa Ku dai fadamin gaskiya."






Maryam ta ce, "Hakane Mammah da naga ta fara hawayenne yasa na bata nawa glass din ko iskanne ya tare mata."




"OK To Bara in dauko dayan,Allah ma yataimaka biyu na karban mata daman."
Fadin Mammah.




Maryam ta ce, "Habbity kar dreba ya gaji da jira Bara in tafi sai mun hadu goben."




"OK bye bye Na gode habibbtkuri
aida Anty." Cewar Nafeesa tana dagawa Maryam hannu.




Bai fi minti Biyar ba da tafiyar Maryam, Mammah da Nafeesa ma suka tafi gida,kasancewar dutyn rana Mammah ke da shi.




Nafeesa zaune tana ta karatun littafi kamar yadda ta saba, ta kai karshe tai karo Da number Jameel Nafseen, a kullum tana ganin number nan kuma tana Sa rai da kokarin kira Amman tsoro da kwarjini ya hanata ko Da ta dau number Da niyar kira kan ya shiga zata katse,ayau kam ta cire tsoro tare da kudiri niyar kiransa, daukan number ta ta danna kira zuciyarta ce ta fara bugawa cikin sauri da mamaki maimakon numberta fara ringing sai taji cewa akashe,tun daga ranar kullum sai ta gwada kira Amman wayar nan dai akashe hakan kuma bai Sa ta fasa ba.






****Safiyar lahadi ba Boko ba islamiya hakan ya Sa ta dauko wayarta tare da bude data chatting ta fara tare da lekya group din su na mata zallah ta ji ana maganar wani film mai suna Abu Hassan, bata wani tsaya ta saurari chat din ba karaf sai taji ana fadin cewa ai Jameel Nafseen ne ya tsara labarin, tsayawa tayi da chat din tana tunani shin dama sahibin nata har Films ya ke rubutawa? .


A zuciyarta take fadin, "Ya zamemin dole in nemi fina,finan da ya rubuta sannan akan su zan fara kallo."


Bata gama sak'e,sak'en ba karaf sai taji wata ta turo message , "Ai yawancin Marubuta yanzu sun dawo online, Dan natabajin Yayata da kawarta na fadin cewa akwai group na Marubuta anan whatsApp kuma duk marubutannan na ciki daga manyan har yaran."






Da sauri Nafeesa ta bi wannan yarinyar private, sallama tayi mata tare da fadin , "Dan Allah zaki iya min hanya in shiga group din marubutannan?."




Tayo mata reply da , "Eh to nima kawar Yayatace ke rubutu tana ciki, Amman ance zallan Marubuta ake sawa ciki."




Tunani Nafeesa ta tafi kan ta bata amsa, "A yau zan zama marubuciya kuma zan rubuta labari indai zai iskeni ga Nafseen,."




Bayan ta gama tunanin da Sauri tayo mata reply , "Ok nima ina rubutun ai ko zaki Iya hadani da kawar Yayar ta kin?"






Batare da tace komai ba, ta turo mata da number mai dauke da suna Nusaiba.




Saving din number Nafeesa ta fara yi sannan ta shiga wajen kira ta kira ta.




Ringing wayar ta fara har ta kusa katsewa kan Nusaiba ta dauka.




Sallama Nafeesa ta fara yi mata tare da gaisuwa,sannan ta ce, "Dan Allah Anty Nusaiba so nake asani cikin group din marubuta nafara rubuta littafi Amman ina bukatar ma su min gyara."






Washe baki Nusaiba tai domin irin sune yan karyan nan ma su so ace sune suka San kaza ko suka yi hanyar kaza, sai da ta gama washe bakin ta kan ta ce, "Ok karki damu da nayi rubutu Amman yanzu na daina, akwai Matar Yayana da ke yi dai kuma tana cikin group din zan bada numberki ta saki."




Hamdala Nafeesa tai har cikin ranta tana mai farincikin hakan.








Nusaiba ta ce, "Ko kuma ma dai kiyi min magana WhatsApp yanzu sai in Sa asakin."




Nafeesa ta ce , "To na gode Anty Allah saka da alkairi."




Nusaiba ta amsa da Ameen kan ta katse wayar da sauri ta fita adakin tare da nufan wani bangare, tana shiga ta ce, "Aunty Farida kizo kar inji kunya yau ta guna aka biyo Neman alfarmar shiga Group din nan na ku da kikace min akwai su Fauziya D Sulaiman da ma sauran marubuta da mawaka?"


Farida ta ce, "Eh fa ya akayi to."




Nusaiba ta ce , "Watace ta kirani wallahi wai tana son shiga ko tayama akayi ta sami numberta oho ni dai ki taimaka asata zan baki number ta WhatsApp."




Murmushi Farida tai, "Hmm Hajiya Nusaiba ke nan bakomai ki turo za asata Allah Sa group din ma da waje Dan cike muke fam."




Nusaiba ta ce, "Ni dai ataimaka kar ta rainani."




Dariya kawai Farida tai kasancewar tasan halin Nusaiba da shegiyar karya da kuri








Intaso karyartama cewa take ita ke rubutun ba Antynta ba.




Nafeesa kuwa tuni tayiwa Nafeesa magana WhatsApp kamar yadda ta bukata.




Ko reply Nusaiba ba tai mata ba kawai ta turawa da Farida Number.




PC Farida ta bi Bamai Dabuwa tare da fadin, "Dan Allah asa min wannan writern sabuwace."




Ya yi mata reply da , "OK bara dai in duba Allah Sa da kwai waje."








Urs Xayyeesherth
_*SAI NA AURI MARUBUCI📝📝📝*_
_(Nafseen)_


NA
XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH






✨6STARS INDEED


_*SAI NA AURI MARUBUCI...Kirkiraren labarine, mai dauke da nishadi na mussaman, al'ajabi tare da ban tausayi,tsantsar soyayya da kauna mai ban mamaki*_


PAGE 10


BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM




*WANNAN FEJIN NA KUNE KUJI DADINKU MASOYAN ASALI Deeymusah,Mr Mubarak,Momim shuraim,Fatima zahra,son so fisabillah😘Allah bar min Ku*




Dubawan da zai yi kuwa ya tarar group din cike yake ba damar Kara wani in ba wai wani ko wata sun fita ba.




Komawa Private ya yi tare da fadin, "Ba waje fa, group din acike yake sai dai ki bata hakuri ta jira ko wasu zasu fita."






Har cikin ran Farida bataji ba dadi ba Sam kawai sai ta ce, "To ni dai in an samu hali asata Dan tana da bukatar kasancewa agidan matukar gaske."


Wa she gari


Shiru shiru Nafeesa ta ga ba asata A group ba hakan ya sata Kiran Nusaiba,Nusaiba na ganin kiran Nafeesa ta kau da kai tare da yin tsaki, aranta take mita, "Kai wallahi Aunty bata kyautamin ba zata ja min raini." Ficewa tai fuu sai bangaren Anty Farida, tana shiga ta fara, "Haba Aunty Dan Allah, kina so yarinya ta rainani ne wai? Tun jiya kisa asata a group kin ki."






Farida ta ce, "Oh ni kam dai, na bada number ta daman na Fada miki group din acike yake,dole sai wani ko wata ya fita kan asata Amman har na bada numberta."






Nusaiba ta ce, "Ok shi ke nan Amman wallahi ko ta kira ma ba zan kara daukaba sai dai kawai ta gannta a group ta Kara ganin girmana ma,ba na son raini."






Dariya Farida ta yi, "Allah dai ya shirya mana kai."




Da Ameen Nafeesa ta amsa kan ta fice fuu kamar yadda ta shigo.




********Kwanaki nata tafiya har sati Amman ba asa Nafeesa a group ba, hakan ya Sa ta tsintar kan ta da fara rubuta wani littafi Wanda ta mai lakabi da SHI NAKE SO, kamar wasa ta Sa A group din su nan take taga an fara rububi tare da fadin cewa tayi ma su cigaba Dan Allah, har da ma su binta private suna hadata da Allah kan cewa labarin ya yi dadi ta cigaba.




Mamaki Nafeesa take har cikin ranta shin itace take rubutu kamar yadda Nafseen ke yi? Shin itace ake ta rububi kan karanta labarinta,ji take tamkar amafarki domin salo da tsarin rubutun sak irin ba shi ta bi,tamkar shi ke tsara mata labarin, ba mai tunanin cewa sabuwar marubuciyace.




Misalin karfe biyar na Ranar ba yan ta gama tura littafin rububin sharhi ya ragu tana kokarin kashe data da mamakinta kawai sai ganinta tayi tsimdin acikin wani group mai taken MARUBUTA.




Nafeesa ba ta San lokacin da ta tashi tana murna da ihu ba tare da washe baki,kara kallon wayar tai tare da rungumarta, "Alhamdulillah, Allah na gode maka."




Gyara zama tayi tare da wata nutsuwa ta mussaman ta shiga cikin group din, hira ake ba ji ba gani raha da wasa, wannan ya tsokani wannan wancen ya tsokani wancen abun gwanin sha'awa bin hirar ta fara yi ba tare da tace uffan agidan ba, sai dai ga Mamaki har yanzu bata ga alamar gilmawar Nafseen ba,Wanda ko wani suna ta gani sai ta kura ido Amman har yanzu bataci karo da shi ba.




Ganin cewa da alamar duk yan gidan na da saukin kai ya bata damar yin sallama.




Nafeesa "Assalam alaikum"


Wani ba da ba a tantance mace ne ko na miji ba kasancewar ba suna ya ko ta ne amsa da "Wa'alaiki sallam Yan mata."




Nafeesa ta yo reply da , "Ina Hini Yaya zan ce ko Aunty."




Da alamar murmushi aka maido mata da amsa, "duk Wanda kika zaba kina ganin ya yi miki to ba tantama."






Tsintar kan ta murmushin da ya bayyana har a zahiri tayi tare da fadin, "To ina ganin dai Yayane."




"To, aiko kin canka na Yarda ke din fasihiyar marubuciyace." Ya maido mata da reply.




Kan Nafeesa tai Reply
Karaf......






Urs Xayyeesherth
_*SAI NA AURI MARUBUCI📝📝📝*_
_(Nafseen)_


NA
XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH






✨6STARS INDEED


_*SAI NA AURI MARUBUCI...Kirkiraren labarine, mai dauke da nishadi na mussaman, al'ajabi tare da ban tausayi,tsantsar soyayya da kauna mai ban mamaki*_


PAGE 11


BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM




Wani ya yi sallama agidan.




Alamar murmushi "Umm." Kawai Nafeesa ta tura sannan ta amsa sallamar da Mai suna Dan gidan Imam ya yi.




Wancen ko ga duk alamu ya sauko domin bai kara fadin komai ba.




Sauran Mutanen Gidan Mata da Maza duk sun fito sai hira ake, Nafeesa da surutu kamar wasa arana guda har ta fara sabawa da Mutanen cikin Group din Marubuta Amman gabadaya hankalinta na waje gudu damuwarta ta ga gilmawar Masoyin nata Amman shiru har ta fara fidda rai.




Rufe data kawai tai domin lokacin sallar La'asar ya yi kamar yadda ta ga duk sauran yan group din na fadin lokacin sallah ya yi atashi ayi,har cikin ranta tsari da yanayin group din ya burgeta yau daya.




Alwala ta dauro sannan tai sallah ta jima tana addu'o'i tana idarwa ta gyara zaman glass din ta afuska, sannan ta duba wajen littafanta gani tai kaf ta karance su duk da ta saba maimaici daman Amman taji aranta cewa tana da bukatar Sabi,hakan ya sa ta duba jakar makarantarta Kudin da Mammah ke bata na kashewa bata kashe take Tarawa daukowa tai taga dubu daya ne da ita a yanzu, tsaki ta yi, "Ni kam ma ko za su isheni in siyo oho."




Janyo

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login