Showing 27001 words to 28317 words out of 28317 words

Chapter 10 - Sai Na Auri Marubuci Nafseen Complete by Zulaihat.txt

Maryam tana cikin yanayi na damuwa azuciyarsa yake fadin hakan wanda a zahiri kuma ya ce, "Daman naje gidane Mama ta sanar dani cewa kina nan Nafeesa ba lafiya, Fatan yanzu jikin dai da sauki?"






Sabeer ne ya katse Maryam wajen yin maganar tare da cewa , "Anty Wai inji Mammah bakon ya shigo cikin falo."




Maryam ta ce, "Bismillah mu shiga ciki."




Sun shiga sun tarar da Mammah na waya da Abhi yana sanar da ita yadda suka kaya da Alhajin Mutansir, Mammah ta numfasa, "Lallai ma Mutuminnan wato da kudi yake son siyanmu da ma 'yar tamu shiyasa ko biyar ban taba ba akudin da ya bada.".




Abangaren Abhi ya ce, "Yawwa Matar kirki kinga hakan yafi kuma in sha Allah da zaran na shigo gari zan zo na maida masa kayansa,tsaya wai ina Ammiena ne? kwana biyu fa ko waya bama yi kodai karatunne?"




Cikin Sauri Mammah ta ce, "Eh,eh dazuma suka fita da Maryam,maganar take hawaye na zuba a idanunta."




Jikin Abhi ya yi sanyi yi yana kokarin fahimtar cewa da kwai lamarin da ake boye masa ya ce, "Madam ki fadamun gaskiya,Ammiena tana lafiya ko ya?"




Goge hawayen tai cikin dauriya ta sake murmushi wanda sai da sautinsa ya fito ta ce, "Ammien Abhi na lafiya Kasanta da nacin karatu inta dawo in sha Allah zan sa ta kiraka."




Shima sakar Murmushin Yayi to, "Ma sha Allah."


Daga nan sukayi sallama.




Mammah ta dawo da dubanta ga Kabeer da Maryam.


"Ah Maryam kin bar bako ba ko ruwan sanyi? maza jeki dibo masa ruwa."Cewar Mammah.




Kabeer ya sauka akujerar ya gaida Mammah cikin girmama kan ya zauna tare da fadin, "Mama Ina Nafeesa fatan dai jikin da sauki."


Mammah ta ce, "To Alhamdulillah da saukin dai zamuce amman Nafeesa kam gata nan a mutun amman kamar gawa."




"Subhnallahi! Mama ko zan iya ganinta."


Mammah ta tashi , "bismillah."


Kabeer ya jima yana kallon yanayin Nafeesa kan ya duba Mammah tare da fadin, "Wanene wannan da Nafeesa ke mutuwar so?"




Sai da Mammah taji wani ras tare da zubawa Kabeer ido.


Murmushi Yayi , "Mammah karki damu ban san gaibu ba,amman Allah ya mun baiwar fahimtar matsaloli mussaman wadda ta shafi irinta Nafeesa,kuma in sha Allah Nayi alkawarin nema ma Nafeesa mafita,In ba matsala muje falo mu tattauna."








Mammah ta ce, "Ok ba komai muje."


Ko da sukaje falo Mammah ta bukaci Maryam da tayiwa Kabeer bayanin komai domin ita ce tafi kowa kusanci da Nafeesa dan haka tafi kowa sanin komai.


Maryam ta masa bayanin komai, akarshe ta kara da, "A kullum inna bukaci Nafeesa da ta fadsmun wani abu game da Nafseen ta kan cemun Sirrine bata taba fadamun, kuma aduk lokacin da wani mummunan abu ke shirin faruwa da ita yanayinta na chanjawa ko da batai komai ba alokacin wanda ya mata abun ko ya bata mata rai sai wani abu ya sameshi nan take, akwai lokacin da nazo na kwana Mammah batasan daliliba wannan barcin Nafeesa tayi bata farka ba har sai da na yarda zanenta akuskure zanen da tasabayi akullum tana fadin cewa shine NAFSEEN dinta.


Kabeer ya gyara zama tare da fadin , "inba matsala ko zan iya ganin zanen?"




Mammah ta ce, "Me zai hana? Maryam tashi ki dauko."




Haka kuma akayi Maryam ta dauko zanen tare da mikawa Kabeer.


Sai da Kabeer yayi suman zaune na wasu sa'anni "Abun Mamaki baya karewa tabbas wanda ke jikin zanen sunanshine Jameel Nafseen kamar yadda Nafeesa ta saba fada maku kuma abokinane mazaunin garin kaduna,zanen ba inda ya banbanta da Nafseen tambayata anan duk da nasan bakwa da amsarta shin Nafeesa ta taba ganin Nafseen ne? abun da matukar mamaki wannan wace irin sarkakiyace mai cike da boyayyen sirri."




Mammah ta ce, "Kwarai a kullum mai maganinta kan fada mana cewa akwai boyayyen sirri kuma itama hakan take fadi,Amman yanzu wani taimako zaka iya mana tunda abokinkane, ba damuwata ace ta auren shi ba Aa ya bayyana ko ma huta da wannan lamarun."




Murmushi Kabeer yayi, ga duk alamu tunani yake ya diba dan lokaci kan ya ce" In sha Allah komai ya zo karshe yanzu bara in gwada wani abu Ko Allah zai sa adace,Mintuna kadan zan dawo."




Har yaje kofar fita ya dawo yana, "Watakil ba arasa ba,kuna da daya daga cikin wa innan turarukan Tempot smart,Blackberry,koMemory?"




Da sauri Maryam ta amsa da , "Eh wa innan sune turaren Da Nafeesa ke amfani da su ai kuma duk da kwai adakinta."




Alamun Mamaki ya bayyana fal azuciyar Kabeer yana son yi magana sai kuma ya tuna abun da ke gabansa na farfadowar Nafeesa Kallon Maryam ya yi kan ya ce, "Muje ki bani?"


Abun mamakin anan shine dukka turarukannan da Kabeer ya jero sune wa inda Nafseen ke amfani da su kuma ga Nafeesa ma da su,shin wannan wace irin soyayyace? kada ku manta Nafseen bai ma san Nafeesa ba bare ya san wacece ita.




Suna shiga kuwa gasunan duka ukun ajere kan dress mirrow dinta,Maryam ce ta karasa tare da dibo masa ,tempot smart ya karba tare da budewa kan ya yi kokarin fesawa Nafeesa ta bude ido,wani irin numfashi take tare da shekar kamshin.


Dan Mamaki kowa ya rasa tacewa.


Kokarin motsi take amman ba dama jikinta kamar adaddaure,Bude bakima tai magana ta kasa harshenta ya rike.


Duk abun nan da take ba mai gani, illa hawaye da ya fara kwarara daga idanunta,Subhannallah cewar Kabeer, Maryam da Sabeer kuwa sai Kuka, Mammah ko ta rasa abun yi.




Ruwa Kabeer ya bukata Mammah ta kawo yayima Nafeesa addu'o'i tare da shafa mata ihu ta fara tana, "Wallahi sai mun kasheta bazata taba auren shi b mu zamu auresa."




Kabeer ne ya masu tsawa tare da fadin, "Shi wa?"




"Shi,shi din." cewar su


Tsawa tare da ruwan addu'ar ya kara yarfa masu, "Na ce ku fadsmin shi wa?" ya karasa maganar yana feshe masu turaren hannunsa


"Shi MUTANSIR din."


Kabeer ya ce, "Waye kuma MUTANSIR?




nunu Maryam suke suna, "ita ta san shi kuma tasan komai."




Nan da nan jikin Maryam ya fara rawa ta kasa magana sai Mammah ce ta ma Kabeer bayani atakaice tun da itama ba ta gama sanin komai ba.


Dawowa yayi ga shedanun ya na , "Waya turo ku? ku fada mun ko kuma in cigaba da azabtar da turaren nan."




Kukan Wahala suke suna fadin, "Amina,Amina budurwar Mutansir ta turomu mu kasheta,mun zo tana barci ba dama muyi abun da mukaso aikatawa masu tsaronta sun fi karfinmu hakan yasa mukai nisa da barcin nata ya zarce wanda ta saba, sun hanamu mata komai mu kuma bazamu barta ba har sai ta rabu da Mutansir."




Kabeer ya yi ajiyar zuciya, "Wai shin ku wasu irin Shedanune? me ta tare maku? na ga shi Mutansir din ke son ta ba ita ke son shi ba,ina mai tabbatar maku da cewa ku fita ku bar ta ko in cigaba da azbtar da ku."






Haka dai Kabeer yata fama da azzalumai da kyar suka tafi,suna tafiya kuwa Nafeesa ta samu barci.


Cikin damuwa Mammah ke fadin, "Fatan dai ba komawa tai ba?"


Kabeer ya ce, "Aa ba matsala wannan normal barcine nan da anjima ko cikin dare zata farka."


Mammah,Sabeer da Maryam suke hamdala


Godiya sosai Mammah tayi Kabeer tare da sa albarka,Maryam kuwa sai da ta rakashi har wajen motarshi.




Godiyar ita ma ta fara mai,cikin fara'a yake fadin, "Ki dai na godiyarnnan ban so,an kusa kiran Sallah ki koma gida,sannan in da hali kima NAFEESA alwala kan ta farka,In sha Allah gobe na tashi daga aiki zan zo mu karasa yadda za a abullowa lamarin."




nan sukayi sallama.








***********Misalin karfe shabiyu na dare Nafeesa ta fara kiran sunan Nafseen," Uncle Dan Allah karka mutu, in ka mutu nima ba zan..........










*HAR YANZU DAI MUNA CIKIN GASAR NAN😉LAMARIN NA MUSSAMANNE AKWAI WANI ABU DA BAN BAYYANAR DA SHI BA CIKIN FEJINNEN KO WACECE ZATA IYA FADAMUN? NAFEESA TA FARFADO LOKACIN DA TAJI KAMSHIN TURAREN SAHIBINTA,KAN DAGA BISANI SHEDANU SUKA BIYO BAYA🤔KU TUNA LOKACIN DA NAFEESA TAI WANNAN BARCIN MEYA FARU ALOKACIN? SANNAN BAYAN WANNAN ABUN YA FARU ME YA KARA FARUWA DA YASA BARCINTA NISA😉A BAYYANE ABUN YAKE AMMAN BA KOWA ZAI FAHIMTA BA😉FATAN ALKAIRI MASOYANA🥰*




DOMIN TURO SHARHI KO AMSA


08103080717




Urs Xayyeesherth


✍️ Xayyeesherthul-humaerath

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login