Showing 1 words to 3000 words out of 28317 words

Chapter 1 - Sai Na Auri Marubuci Nafseen Complete by Zulaihat.txt

_*SAI NA AURI MARUBUCI📝📝📝*_
_(Nafseen)_








_GAJERAN LABARI📝_


NAH


AISHA MOHAMMAD SANI
(Xayyeesherthul-humaerath)




_*SAI NA AURI MARUBUCI...Kirkiraren labarine, mai dauke da nishadi na mussaman, al'ajabi tare da ban tausayi,tsantsar soyayya da kauna mai ban mamaki*_




_FREE NOVEL NE AMMAN RASHIN SHARHI ZAI IYA SAWA YA DAWO NA KUDI, YANAYIN YADDA KUKA DAUKA NIMA HAKAN ZAN DAUKA✌️JUST FOR MY FANS,LOVE YOU LODI,LODI🥰❤️💃_


MARUBUCIYAR👇
KUCHAKAR KISHIYA
BABU RUWAN SO
AZZAWAJUL-MUKADDAR
WASA DA SO
KWADAYI 2020
MATAR POLICE 200
JAMEEL 200


NA YANZU: SAI NA AURI MARUBUCI




PAGE 1/2


BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM.




_*FEJIN FARKO SADAUKARWANE GAREKU FAUZIYYA TARE DA JANNAT YAR BABA KUJI DADINKU🥰🥰🥰*_


........Wata Yar matashiyar yarinya na hango da bazata huce shekara goma sha bakwai ba aduniya, kwance take tana barci cikin nishadi da walwala domin da zaran an kalli yadda yanayin murmushi ke bayyana afuskarta wannan ka dai ya isa laburta cewa tana cikin yanayi na farinciki,ta kankame littafin Hausa akirji tamkar tana gundu a kwace mata, mafarkine Wanda ta sabayi kamar kullum Amman ko wanne da salonsa ko na yau din ya yake? Bara mu lekye cikin mafarkin Nafeesa.




"Nafeesa kin San cewa ba jin cewa akwai Wata 'ya Mace da zan so kamarki? Kina jin cewa zan iya furta Kalmar so ga Wata 'ya Mace bayan ke?, Hmm babu tantama cewa ke ce zabina sannan kuma kece burina,ina miki so fiye da yadda majnun ke son laila,ina kaunarki fiye da yadda kifi ke bukatar ruwa domin rayuwa." Cewar Nafseen da ke zaune gaban Nafeesa.








Gyara zama tai tare da kara kura mai kallo tai murmushi kan ta fara da, "Da ace ana Iya kidaye adadin soyayya a sikeli na tabbata cewa wadda nake yi maka bazata taba kidayuwa ba,kamar yadda Dan Adam ba zai Iya rayuwa batare da ruwa haka Nima nake jin cewa ba zan iya rayuwa batare da kai ba, ka zamemin jinin jikina,numfashina da walwalata, ada nakan ji cewa ka fi karfina ba zan taba samunka arayuwata Amman wai yau nice tare da kai har kake furtamin Kalmar so? Dan Allah Nafseen ka rayu da ni karka barni karkacemin wannan mafarkine nake yi."




Rik'o hannunta ya yi,yana kokarin yin magana.


Karaf Mama ta shigo tare da bugawa Nafeesa dundu abaya.


Sambatu take,"Ka kara cewa kana so na ko da sau dayane Dan Allah kar ka tafi."




Dukan da Mama ta kara kai mata ne ya sa ta saurin razana tare da dawowa hayyacinta, "Mama kin kuran min shi, Mama kice ya dawo yau ya fadamin cewa yana sona mama Dan Allah kice ya dawo."




Tsaki Mama tayi, "Ki bar min wannan shirmen tun kan na kai miki mari maza tashi kije kiyi sallah wawiya kawai."




Kara kallon dakin tai da kyau ta ga da alamar gaske dai daga itane sai Mama, kuka kawai ta fara tana, "Mama wallahi in ban gan shi na aure shi ba mutuwa zan yi, ni kan sai na AURI MARUBUCI." ta kara fashewa da kuka.




Wani irin bakin cikine ya kara tirnik'e mahaifiyarta ta, ta fice batare da tace komai ba illa azuciyarta da take fadin, "Ban San wannan wani irin bala'in so bane ga mutumin ba ba a taba gani ba, daga karatun littafi kawai, anya kuwa ba aljanune suka shiga jikin Nafeesa ba kuwa? Ya Zama dole in sanar da Abhee abin da ke faruwa adaren yau."


Ta shige daki.




Ita kuwa Nafeesa kara kyankyame littafin tai tana kuka sai da tai mai isanta kan ta dauro alwala tai sallah, tana idarwa ba abun da ta fara rok'a illa Allah ya nuna mata marubucinta Nafseen Sanan kuma Allah ya bata ikon auransa.


Bayan ta kammala addu'ar tashi tai ta fita waje da littafinta ahannu, zama tai afilin tsakar gidan na su tare da chok a hannunta Zane ta farayi tana waka Wanda da farkon zanen duk Wanda ya kalla zai dauka cewa shirme take zanawa,Amman ahankali kyahun zanen na fitowa,da mamaki duk da kasancewar Nafeesa ba ta San Nafseen ba Amman tsaf yanayinsa da kamaninsa take zanawa,ba musu duk Wanda ya San Nafseen kuma ya ga zanen Nafeesa zai dauka cewa ta San shi kuma kyakkyawan sani ma, azahirin gaskiya ko bata taba ganinsa ba bin abun da zuciyarta ke rada mata kawai take ya yin zanen tundaga farko har karshe.




Kallonsa ta tsayayi tana mai farinciki ji take tamkar na gasken ne agabanta, cikin littafan da ta fito da su ta dau daya mai suna YAR AUTA NA JAMEEL NAFSEEN, Karatu ta fara cikin nutsuwa da zakuwa akowanni feji ganin ta riski gaba, labari Indai na shi ne ko wani irin salo na tafiya da zuciyar Nafeesa.


Gabadaya hankalinta ya tafi ga karatun kaninta da ba zai huce shekara Takwas bane ya fito yana buga boll ta gabanta ya huce ba tare da sanin Sa ba har ya goge mata zanen Nafseen.




Ji tayi ajikinta hakan ya Sa ta saurin kallon kasanta gani tai tamkar na gasken ne ya yi hatsari hakan ya sa ta Jan dogon numfashi tare da suma awajen nan take.


✌️YAWAN SHARHI YAWAN TYPING


Urs Xayyeesherth
_*SAI NA AURI MARUBUCI📝📝📝*_
_(Nafseen)_
12/1/2021






_GAJERAN LABARI📝_


NAH


AISHA MOHAMMAD SANI
(Xayyeesherthul-humaerath)




_*SAI NA AURI MARUBUCI...Kirkiraren labarine, mai dauke da nishadi na mussaman, al'ajabi tare da ban tausayi,tsantsar soyayya da kauna mai ban mamaki*_










PAGE 3/4


BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM




*🥰🥰 WANNAN FEJIN SADAUKARWANE GAREKA YAYANA,ABUN ALFAHARINA,YAYA MUSADDAM😘YAYANAH YA FI NA KOWA💃ANGON MAI AWARA SON SO FISABILILLAH*




MY GROUP XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH FANS GROUP INA KAUNARKU HAR CIKIN RAINA MASOYAN ASALI😘😘




Sabeer bai San lokacin da kurma uban ihu ba, "Mammah kizo Anti Nafeesa ta mutu,Mammah."




A rikice Mammah ta fito tana, "Sabeer wai meyafaru ne ba yanzu ta fito karatu kalau ba?"




Sabeer na kuka ya ce, "Ban San tayi zane bane na goge mata tana kallo shine ta fadi."




Dafa kai Mammah tai tare da fadin, "Yah Allah!


Kokarin daga Nafeesa daga wajen tai domin maidata cikin gida, da yake Mammah malamar asibitice kokari tai domin dawo 'Yartata cikin haiyacinta a Dan kankanin lokaci.




Bude Idon da Nafeesa za tayi ta fara, " Mammah Nafseen dina Sabeer ya gogemin, sai ta kara fashewa da kuka."


Mammah bata da zabin da ya wuce ta rarrashi 'Yartata awannan lokacin hakan ya sa ta Jan Nafeesa jiki tana shafa mata baya, "Ki yi hakuri kinji Nafeesa bai sani bane, kuma ai zanene na San zaki Iya zana Wanda ya fi wannan kyau ko?"




Wani Dadi Nafeesa taji aranta nan take ta mik'e "Sabeer Bani Littafina zan tafi madarasa."




Mammah ta ce, "Madarasa da littafin Hausa? Haba Maman Abhi kibari in kika dawo kyayi karatun."




Nafeesa ta fara buga kafa, "Ni dai da abuna zan tafi wallahi."




Tashi Mammah tai kawai tana fadin, "Allah ya kyauta."


Nafeesa kuwa Hijabinta ta Sa har kasa tare da nikabinta ta yafa jakar makarantarta agefenta na hagu sannan littafin hausanta na marubucinta NAFSEEN a hannun dama wato Yar Auta.




Ko da ta isa makaranta anfara karatu Neman waje kawai tai ta zauna tare da bude littafinta domin cigaba da karatu.


Karatu ake yi masu Amman gabadaya hankalinta na kan littafin da take karanta, murmushi ne kawai ke bayyana afuskarta, kara gyara zama tai tare da Jan dogon numfashi ta cigaba da karatun, Malamin ne ya lura da yanayinta ganin cewa hankalinta baya tattare da shi duk da kasancewar bai hango me take kallo ba.


"Ke Nafeesa, ta shi ki karantomin hadisin farkon nan da na kawo."




Cikin Sauri ta ta shi arikice take maganar, "Mallam, ai Nafseen bai fadamin ba aciki."




Sake baki ya yi yana kallonta kawai cen ya daka mata tsawa, "Waye Nafseen? Karatu muke ko maganar wani anan, Iye ba tambayarki na ke ba?"




Sunkuyar da kai Nafeesa tai batare da ta kara kallon malamin ba.




Cikin tsawa ya kara fadin, "Nace waye Nafseen?"




Karaf wata yarinya ta ce, "Malam wani marubucin littafan hausane."




Kara fusata malamin ya yi, "Ah ya yi kyau aiko yau zakiga Nafseen a makarantar nan ganin idonki bani littafin."




Jiki asanyaye Nafeesa ta mik'a masa littafin .




Yana karba ya karema littafin kallo kamar yadda aka Fada sunan marubucin Nafseen,tsaki ya yi Sannan ya fara fata-fata da littafin yana yankawa.






Kuka Nafeesa ta fara yi bilhakki da gaskiya,tun tanayi ahankali har ta fara shidewa daga karshe ma ta k'ame awajen nan take.




Ganin yadda tai, abun ya matukar ba malam mamaki daga yaga littafi, tsaki ya yi yana fadin, "kar in ga kowa ya fita kuzo mu cigaba da karatun mu in iskancine nawa yafi nata.




Kwance take awajen cen kuma ta mik'e tare da wani irin gawartaccen kara,Malam ta nufa kawai tare da damkosa tana wani irin numfashi.




Ihu ya fara yana, " Dan Allah Ku kwaceni Nafeesa za ta kasheni,wayyo Allah na."




Dalibai kuwa sai dariya.




Nafeesa kuwa bata fasa jibgar malam ba.


Dalibanne suka kira sauran malaman dakyar aka karba Malam a hannun Nafeesa sai numfarfashi take tana kara kokarin cacumosa.


Malam na samun hanya ya fice adari yana, "Wallahi Yarinyarnan ba mutum bace Ku bincika." maganar yake cikin Sauri da hakki domin ji yake tamkar zata kara damkar shi.




Suko dalibai ba abin da suke ban da dariya yau Mallam yaji a jikinsa Dama ba baya ba wajen jibgar dalibai.






Ita ko Nafeesa ban da kuka ba abin da take Dan arayuwanta bata taba shiga tashin hankali irin wannan ba Wai Lttafin Nafseen din ta aka yaga a gabanta sai ma take ga kamar har shi din aka taba ba Iya Littafin ba D ji take Zata Iya fada da kowa a yau dai kam.




Wani Malamine yazo kusa da ita ya ce, "Nafeesa me ke damunki ne ?" aiko sai ta Kara sanya wani irin kuka cike da sauti ta ce, " Malam Nafseen dina ya yaga min ya taba min rayuwa ta yamin kacakaca da Nafseen dina Wallahi bazan bar shi ba dole sai ya ji abin da na ke ji ," kowa sai ya tsaya tsaro tsaro yana kallon Nafeesa yayin da wasu ke ganin ta haukace kuma ta hadu da bakak'e aljanu.








Da kyar akasamu Nafeesa tabar wajen,biyu daga cikin Malamamsu mata aka nada domin yi mata rakiya gida ganin cewa lamarin yafi karfinsu har suka bar makarantar bata dai na maganganu ba kaman wata sabuwar kamu ,"wallahi daka rabani da Nafseen gara ka yanki naman jikina wayyo Nafseen Dina sai hakuri ake bata amma bata San ma anayi ba sai kara bankarewa da take.










Da Haka har suka kai gida Mamma na daki taji sumbatu Irin na Nafeesa sai ko ta daura hannu aka tare da fadin, " innalillahi Wa'inna ilaihir rajiun me kuma yake faruwa da Nafeesa lafiya Fa muka rabu ."nan da nan hankalin Mamma ya ta shi abinka da uwa a gigice ta kara so garesu.


👍Gajeran labarine Dan haka gajerun fejis za Ku na samu,Amman yawan sharhi kan Sa in kara🥰






Urs Xayyeesherth
_*SAI NA AURI MARUBUCI📝📝📝*_
_(Nafseen)_


13/1/2021






_GAJERAN LABARI📝_


NAH


AISHA MOHAMMAD SANI
(Xayyeesherthul-humaerath)




_*SAI NA AURI MARUBUCI...Kirkiraren labarine, mai dauke da nishadi na mussaman, al'ajabi tare da ban tausayi,tsantsar soyayya da kauna mai ban mamaki*_










PAGE 5/6


BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM




*👌ANAYI INA JIN DADI ANA BARI INA JIN HAUSHI MARUBUTA YAN UWANA KUNA BIRGENI FA ARADU GULMA KWAI DADI😂*






_*Wannan shafin na ku ne my group members, Momin shuraim,Mrs Mubarak,Mariyata,Aisha shu'aib,Meenat,Aishatul-humaerah,kuji dadinku sharhinku na bani nishadi walle😘😘*




Karasowar Da Mammah za tai nan take Nafeesa ta Fada kasa sumammiya.




Ba karamin tashi hankalin Mammah da na sauran malaman ya yi ba, kokarin daukatar suke domin kai ta cikin gida.


Dakinta sukaje sannan aka shimfideta kan gadonta.


Cike da Mamaki Mammah ke kallon 'Yar ta ta gata nan dai domin ba suma tai ba alamu sun nuna cewa barcine ya kwasheta lokaci guda.




Mammah ta ce, "Ikon Allah daga isowa gida sai wani kalan barci mai ban mamaki."


Ta kalli Malaman tare da fadin, "Mun gode Allah ya saka da alkairi."




Da "Ameen." suka amsa sannan sukai mata sallama.




Kara gyara mata kwanciyar tai sannan ta fice daga dakin.




Kamar wasa karfe biyar tayi ko alamar tashi Nafeesa ba tai ba, Mammah ta dubata gata dai lafiya Amman bata tashi ba.




Ko da Abhi ya kira waya abaiwa Nafeesa, kawai
Mammah cewa tai tana barci domin ta San da zaran ta Fada mai hankalinsa tashi zai mussaman yadda yake matukar kaunar 'yartasa.






WACECE NAFEESA? SANNAN WANENE NAFSEEN? NA SAN MA SU KARUTU DA DAMA SUN ZAKU DA SU SAN ASALIN NAFEESA DA NAFSEEN TO GA BAYANANNE NA NAN TAFE.




WACECE NAFEESA?


Nafeesa 'Yace ga Malam Aminu Direba (Abhi) tare da Mahaifiyarta Dr Salima wadda suke kira da Mammah,itace yar SU ta fari sannan kaninta Sabeer mai shekara goma su biyu kadai Allah ya baiwa Iyayensu,baza asa su sahun masu arziki ba sai dai ace masu rufin asiri,domin kuwa Abhi Direba ne dake tuki gari gari wani lokacin ma sai ya yi sati baya gida,Mammah kuwa malamar asibitice da yake tayi karatu da haka suke rayuwarsu cikin farinciki da annashuwa ba tare da sun Sa son duniya aransu ba,gidan su Dan karamine iyaka arzikinsu daki biyar biyu na Mammah daya na Abhi sauram kuwa na Nafeesa da Sabeer.








Daga ita har iyayenta acikin garin Yola suke da zama.




NAFEESA Yarinyace mai ilimin addini da na boko tana da hankali matukar gaske ba za ace da ita kyakkayawa sannan bata sahun munana daidai gwargwado take,tun Nafeesa na da shekara goma aduniya ta fara karatun Hausa Novel kamar wasa malamin hausansu na Boko ya fara karanta musu littafin *YAR AUTA* na Jameel Nafseen tun daga lokacin Nafeesa ta fara karatu domin gabadaya ji take marubucin na birgeta, alokacin bata San miye so ba Amman ta San cewa tana son littafansa kuma a kullum bata da burin da ya wuce karantasu, YA kasance a kullum Nafeesa ta kwanta barci bata da aikinyi sai mafarkin Nafseen aduk ranar da ba tai mafarkinsa ba to ba zaman lafiya domin ba mai gane kanta in ko tayi tana tashi zata fara sabga uban kuka sai tayi mai isarta kan ta bari,har ta San menene so kuma ta fahimci cewa son Sa take tare da kudurin cewa sai ta AURI MARUBUCI, duk da Iyayenta sun sani Amman ba Yarda suka Iya domin gani suke basu da arzikin nemawa Yar su shi bare ya aura, tsantsar so mai ban mamaki bata taba ganinsa ba Amman tana Iya zana kamanninsa sak kuma akan Sa ta fara Zane sannan bata taba Zane Indai ba shi za ta zana ba,bangon dakinta ko ina ban da zanen Nafseen ba komai har zanawa tai aka maida mata shi tamkar photo, ta Sa agefen gadonta.




Ko da wasa Ba ta son jin an zagi wani mai suna Jameel bare kuma Nafseen dinta kacokan ta kan iya komai kan hakan domin ficewa take ahankalinta nan take.


Shin me kuke tunani zai faru ranar da Nafeesa ta ga Nafseen kuma sak ga kalan zanen da ta saba??




Wannan ke nan kadan daga tarihin Nafeesa.






WANENE NAFSEEN?


Wani Hamshakin Matashin marubucine,kuma mawaki sannan director,kuma producer, waanda ke zaune cikin garin Kaduna, Ya rubuta littafai da dama na Hausa da kuma wakoki kuma ya jogaranci fina finai daban daban, yana da matukar basirar rubutu mussaman na Hausa, salon Sa na matukar tafiya da mai karatu hakan ya Sa a kullum masoyansa daduwa suke duk da kasancewar yana da mata ko kadan hakan baya damun al'umma, kowacce burinta kawai ta samu Shiga azuciyar matashin saurayin nan mai tashe da zamani,baya da wulakanci ko kadan kullum kokarinsa bai huce yaga ya faranta ran masoyansa ba,hakan ke kara masa kima da daraja a idanun mutane da dama.




Wannan ke nan.


Cigaban labarin.....


******Afirgice ta farka abarcin ganin cewa ba kowa dakin,leka falon ma tai ba kowa hakan ya bata damar fita agidan.




Tafiya kawai take batare da tasan inda take nufa ba,wani haskene ya bayyana agabanta tsintar kan ta da bin wannan hasken tai, tafiya take adaji babu ko alamar mutane bare mutum illa ita daya, ta na cikin tafiya wannan hasken ya tsaya cak,tare da fara komawa wani irin launi, me za ta gani???




Nafseen ne ke bayyana gareta....








Urs Xayyeesherth
_*SAI NA AURI MARUBUCI📝📝📝*_
_(Nafseen)_




14/1/2021




_GAJERAN LABARI📝_


NAH


AISHA MOHAMMAD SANI
(Xayyeesherthul-humaerath)




_*SAI NA AURI MARUBUCI...Kirkiraren labarine, mai dauke da nishadi na mussaman, al'ajabi tare da ban tausayi,tsantsar soyayya da kauna mai ban mamaki*_










PAGE 7


BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM




💋💋💋 *MY GROUP MEMBERS WALLE KUNA KAHE INDO DA COMMENTS FA,INA YIN KU IRIN SOSAI DINNAN❤️❤️*






Karasawa tai aguje domin riskarsa.




Mik'a hannunta tai domin rungumarsa anan ta Kara wata zazzafar firgita nan take ta bude idonta kwance take adakinta Wanda tun jiya da aka dawo da ita daga makaranta bata farka ba.




Sautin Kukanta shi ya fahimtar da Mammah cewa ta farka,cikin sauri ta karaso gareta tare da fadin, "Nafeesa Lafiyanki kalau ko? Ki dai na kuka kinji? Ina kina son Nafseen?"




Ta girgiza kai.




Mammah ta kara da , "To kina so in miki addu'ah tare da tayaki nemansa ko?"




Nafeesa ta ce, "Eh, Mammah ina glass dina bana gani sosai."




Cike da tausayin 'Yartata ta mika mata glass din tare da taimakonta wajen sawa.




Tsabar karatun littafin Jameel da kukan rashin ganinsa yasa Nafeesa bata gani sosai sai da glass, ko da ta karanta littafinsa sau dari hakan ba zai hanata kara karantawa anjima ba,har ta kai ga takusa daina gani,da kyar aka samu damar ceton idonta tare da bata glass kuma hakan bai sa ta daina karatun ba.






Bayan ta sa glass din ta tashi, "Mammah zan yi sallah."




Mammah ta ce, "OK to muje in raka ki toilet din ko."




Murmushi Nafeesa tai, "Tab ni dai bazaki lek'ani ba, zan Iya fa."




Murmushi ita ma tai , "Shi ke nan Ummana Jekiyi ba zan lek'aki ba." Cewar Mammah.




Sai da tayi wanka sannan ta dauro alwala sallarta tai cikin nutsuwa har ta idar.


Kayanta tasa tare da dauko Jakarta domin tafiya makaranta.


Mammah da ke shirin tafiya office ta kalleta, "Nafeesa ko karya baki ba miye na saurin haka,kuma naga ma ba lafiya gareki ba?"




Ta ce, "Mammah yau fa munada lectures da safene kuma inna bari malamin ya zo ba zai bari in Shiga ba, ni jikina bana jin komai."




Mammah ta mika Mata Dari biyar tare da fadin, "Ga shi nan ki sai wani abun kice sauran ki yi kudin mashin Dan kinga Abhi baya gari kudin hannuna ya kare gashi ba albashi."






Murmushi Nafeesa tai, "Allah amfana Mammah."




Tana fita ta samu Nafe nan kuwa ta Dane cikin sauri domin ta zaku ta shiga Skul, cikin sa'a kuwa tana isa ta fara hango yan Department dinsu da alama ba ashiga aji ba, Hamdallah tai azuciyarta, ta cigaba da tafiya.




Wata Yar budurwa da bata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login