Showing 18001 words to 21000 words out of 23100 words

Chapter 7 - HABIBI DAIMAN Compelet Hausa Novels BY AUFANA.doc

kota k'arfin tsiya ne".

Woni irin murmushin jin dadi momy tai tace "kai shys nake k'ara kaunarka Abba na, sbd dik lokacinda nazomaka da kukana, acikin lokaci k'ankanen kake shareman hawayena, Allah yabarman kai Abba na" dariya yai yace,

"To idan banmakuba saudatu wazan yiwa, kune farincikina fa" murmushi tai sannan tace "to gobe zankoma gida, da harnace zanyi sati d'aya sbd gaba d'aya rayuwota abace take banajin dadinta amma yanzu dik yafita raina yayi fari tas" shima murmushi yai yace "to shkn, ki kwontarda hankalinki matuk'ar ina raye baku ba bak'in ciki, bazaku tab'a zubda kwallah ba sbd bak'in ciki".

Tashi tai zuciyarta fara tas sai murmushi take tanajin woni farinciki da dadi suna ratsa Zuciyarta da gangar jikinta gaba d'aya.

_____________________

Cikin nasara da ikon ubangiji likitoci suka samu nasara inda numfashin HUDAYYA yadawo, ganin numfashinta yadawone yasa suka fara kokarin tsayarda jininda ke zuba ta hancinta da bakinta.

Dakyar da sud'an goshi aka samu jinin yatsaya sannan aka fara treatment d'in ciwuwwuka da raunikan dake fuskarta da goshinta da hanunta,

Bandage suka saka suka nad'e goshinta da gefen fuskarta sannan suka saka wosu k'arafa a bakinta sbd hak'oranda yafita wojen yai kaba sosai ya kumbura fuskarta kamar baita bace sbd dikta sauya, a hanunta kuma tasami targad'e Allah yakyauta ba kariya bace danhaka bandage kawai suka saka suka daure hanun.

Komai dai Alhmdllh dan ba woni babban rauni ssi saidai tinda ta farka har yanzu kuka take tana kiran sunayen y'an uwonta humaida da hunayya, dakuma Ammin su.

Ganin haka yasa sukamata injection na bacci sannan suka doramata jini wonda aka diba agun Ammar a hanu d'aya, d'ayan kuma shine wonda tai targad'e dashi shikuma sun dauresa,

Baccine mai nauyi yai awon gaba da'ita sbd tasami saikin zafi da radadin ciwon sannan tadaina sambatu.

Bayan komai yalafa har tai bacci sannan likitocin suka fito lokacin dai dai dadyn su HINASH ya'iso.

Y'an bayanai sukai masu akan raunikanda tasamu sannan sukamasu jaje dakuma yimasu albishir d'in insha Allah nanda anjima ko zowa gobe zata farka tadawo normal, hak'oranta d'aya yacire idan akwoi yanda zaayi ana siyarda na roba sai a siya asaka mata,

Anan take cikin sauri HINASH yace zaisiya matuk'ar hakan bazai kawo wota matsala ga lafiyarta ba, nantake docton yai na'am da bawota matsala matuk'ar akasaka mata shi zataji kamar yanda take a da..

#/Vote
#/Share
#/Comment
#/AUFANA for life
_*HABIBI DA'IMAN*_
_*BY~AUFANA*_
_wattpad@Aufana8183_

_*Intelligent writer's association*_

_*Page 21~22*_

_*Bismillahir rahmanir rahim*_

Cikin sauri HINASH yaje yabiya kud'in komai sannan yadawo gunsu mami.

Koda yadawo saiya tadda mami da dady suna magana,mami namagana cikin b'acin rai tana fad'in "Likita" kamar yanda take kiran abbansu HINASH kenan "nariga dana fad'amaka gobe goben nan nakeso a daura auren yarannan, so nake nanunawa saudatu nafi k'arfinta, so nake nanunamata ba'aja da ikon ubangiji, so nake nanunamata dik abonda take tak'ama da tink'aho dashi nafita shi, a gobe nakeso a d'aura aurensu".

"HISHAM" takira sunansa yad'ago yakalleta cikin sanyin jiki saitacigaba da magana,

"Kaje kasanarda gidajen radio da talabijin da dik wota kafa ta yad'a labarai, suyi sanarwar daurin auren HINASH UTHMAN BAFFA da HUDAYYA ALIYU MO'ALLAYID'I ranar gobe asabar damisalin 12pm, za'a daura auren aharabar gidan ALHJ. MODIBBO MOHAMMAD MOALLAYID'I" to kawai yaiyacewa.

Dady ne dasauri yariko hanunta cikin tattausar murya yace "haba Nana Aysha ta, bansanki da saurin fushiba, fushi da d'aukan zafi akan abu baya dagacikin halayyarki, hak'uri, tausayi dakuma juriya sune mafi girman halayyarki, meyasa zaki bari was shaid'an yai galaba akanki haryakaiga zuciyarki tafarfasa,


Kiyi hak'uri Aysha ki kwontarda hankalinki, wonnan hukuncin da kika yanke sam baiyiba bai daceba auren gaugawa, dikda nasan bak'aramin abu bane yasa kika yanke wonnan hukuncin amma kiyi hak'uri dan Allah har izuwa yarinyar tasamu lafiya kinga zowa lokacin kowa da kowa sai asanardashi kowa koma saiya shirya harda dangin mahaifiyarta".

Cikin sauri tace "Likita bawoni shiri dazaayi, koma mezaayi dai nidai inaso a d'aura aurensu a gobe" dasauri su Affan da hanash da yaya hisham sukace,

"Dan Allah mami kiyi hak'uri abar auren nan har HUDAYYA ta worke, kinga suma su Amira ansaka ranar bikinsu kinga sai ahad'e atare, dan Allah kinji mamin mu" haka suma su Amiran rokonta suka dingayi damata magiya, zuciyarta ne tai sanyi ganin yanda yaran da girmansu zakwa zakwa manyan samari amma sun langwab'arda kai tamkar marayu suna rokonta, nannauyan numfashi tasauke "Hmm......!!!" sannan tace,

"Shikenan nahak'ura har izuwa lokacin bikinsu Amira ayi atare, amma wlh nayi hakan ne dan ku badan hakaba a gobe goben nan za'a daurasa yaso sainaga abonda zatayi" murmushi sukai sukamata godiya dady yace.

"Shiyasa nake k'ara k'aunarki matata, bakyada saurin fushi kuma idanma kinyi fushin cikin saurin kike sauka, Allah yakara maki albarka ya rayamana zuriyarmu" cikin dariya suka amsa da ameen.

_____________________

Har kusan 12am HUDAYYA bata farkaba tana bacci har goran jininda aka doramata ya kare aka sake doramata drip,

Ganin dare yayi yasa mami tace su abbu da dady dasu HINASH sutafi gida ita zata kwana anan ita da humaida su hunayya ma sukoma gida,

Haka kuwa akayi saidai dakyar hunayya ta yarda takoma gida sbd ji take kamar y'ar uworta mutuwane zatayi bazata iya tafiya tabarta ba.

Koda suka isa gida kuwa fafur hunayya taki amincewa takoma side d'insu sbd gani take kamar momy zatamata irin abonda tayiwa y'ar uworta, saida su mama sukace ai batanan sannanfa ta amince tashiga.

******

Washe gari tin bayanda HINASH yai sallar asuba baisake kwonciya ba, wonka yai yasauya kaya daga kayan bacci izuwa tsadajjiyar shaddah galila milk color d'inkin riga gajeruwa iya guiwa mai gajeren hanu da wondo.

Sai hula milk, lemon green and black color da takalma black color masu gidan yatsa irin na mutan turkey,

Hanonsa sanye da agogo silver color mai shegen kyau da tsada, woni ni'imtaccen k'amshi ke tashi ajikinsa mai sanyin k'amshi,


Bayan yagama shirinsa tsab sannan yad'auki Key's d'insa yafita, koda yafito dady nakan dining table yana karin komallo ma'aikata kuma kowa yana aikinsa.

Cikin ladabi yaje yagaida mahaifin nasa ya amsa sannan dady yace "ina zakaje tinda safiyan nan ko breakfast bakaiba" d'an sosa bayan kansa yai kamar makaryaci sannan yace,

"Am dady inaso naje naga yanda su mami suka kwana da yarinyar nan, wlh gaba d'aya jiya kasa bacci nai sbd yanayinda nabar yarinyar, shys nakeso naje naga halinda take ciki".

D'an murmushi dady yai sannan yace "ehhh gsky kam yakamata kaje nima idan nadawo daga gidan barrister ( y'ayansa kenan shi dady kamar yanda yake kiransa) zanzo naduba jikin nata, may be ma muzo atare da barrister".

OK....yace sannan yajuya yana fad'in "zan woce dady saikunshigo d'in" dady yace Ok.

Yazo dai dai k'ofar fita saiga hanash yashigo sanye da jallabiya bak'a, kallo d'aya yamasa yace "bros...ina zakaje yanzu tinda sassafennan" batareda yatsaya ba yana tafiya yace,

"Hospital zanje gunsu mami".

Ok....to nima zanzo amma sai zuwa anjima gsky, akwoi aikinda zanyi yanzu" baiko jira yaji mezaiceba kawoi yashige motarsa gateman yabude masa gate yafice.


Kai tsaye katafariyar hospital d'in yafice yawoce, kan hanya yatsaya yamasu siyayyar naman kaza gasasshe da fruit's,

Bayan ya'isa yai parking sannan yadibo kayan yaiwa motar key sannan yawoce izuwa ciki.

Room No,56 shine dakinga HUDAYYA take aciki, ahankali yabude k'ofar cikin sallama yashiga ciki, cikin disasshiyar murya humaida dake a zaune kusa da HUDAYYA ta amsa masa kasancewar mami lamizi take.

K'arisowa yai ya'ajiye kayanda yashigo dasu sannan yatako yazo kusa dasu yai tsaye, gaidashi humaida tai cikin disasshiyar murya ya amsa sannan yace,


"Humaida, woi haryanzu bata farka bane?" ahankali tace masa "ta farka amma bazata iya woni dogon motsiba kagama ko abinci ta hanci suke turamatashi acikin wonnan robar" tanuna masa "amma dai yanzu bacci takeyi, sunce anjima zasu d'auketa aje asaka hak'oran daya fita".

OK...

Kawai yaiya cewa sannan yaje ya zauna akan 2seater d'inda ke cikin d'akin.

Bayan mami tagama sannan suka gaisa yatambayeta jikin HUDAYYA tace taji sauki Alhmdllh tinda ta farka,.

Shuru yaratsa d'akin bamaicewa uffan kowa da abonda kecin zuciyarsa na bak'in ciki da damowa da takaici,

Knocking d'inda sukaji anayine yasa dika hankalinsu yadawo gun k'ofar, HINASH ne yatashi yaje yabude k'ofar, humaida naganin wocca keyin knocking d'in ai dagudu taje ta rungumeta tareda fashewa da woni irin kuka mai ban tausayi,

Itama d'in rungumeta tai tana bubbuga bayanta alamar rarrashi sannan tarik'ota suka shigo ciki, cikin ladabi suka gaisa da mami HINASH ma yagaidata cikin ladabi ta amsa mami tace,

"A,A fatima yaushe kukashigo garin ne?" momy fati tace "Wlh jiya muka shigo kwatsam kuma sainaji mummunan labari akan y'ayana" d'an murmushi mami tai sannan tace,


"Hmm....ai bari kawoi fati saudatu so tai takashe yarinyarnan Allah ne dai kawai baibata nasaraba da saidai muji mummunan labari" cikin b'acin rai momy fati tace "aikuwa wlh da itama saitaje inda ta aikata, dan wlh bazamu dauki asaraba koda bankashetaba wlh saitaje gidan kaso, dama bata k'aunar yaran nan, tinda mahaifiyarsu takwonta ciwo take ganamasu azaba take azabtardasu tamkar bayinta, to wlh ta Allah ba tataba dik bakincikinta saitagansu a duniya kuma acikin gidannan amatsayin y'ayan mijinta, muguwa, azzalima".

D'ago da fuskar humaida tai tasharemata kwallah tace "kidaina kuka yata insha Allah kunkusa fita daga cikin wonnan k'angin bautar" mami kam rasa mezatace tai HINASH kuwa tsaye yai yana sauraronsu batareda yace uffan ba.

Gun HUDAYYA taje tai tsaye tana kallon yanda momy saudat tasauya mata kamanni taso ta illatata kokuma tarabata da duniya gaba d'aya,

Sallama sukaji saisuka waigo momy fati tace "ah huzaifa am sorry nabarka woje kaikad'ai" murmushi d'an samarin yai yace "ah no bakomai momy ihsan ce tafara kuka" yarinyarda take goyo yanzu kenan.

Gaida mami yaron yai cikin tsintsar ladabi da fara'a ta amsa sannan ya tambayeta jikin HUDAYYA tace Alhmdllh, hanu yabama HINASH sukai musabaha suka gaisa shima yatambayeshi jikin HUDAYYA yace taji sauki,

Momy fati ce tace "am sunansa huzaifa, shi d'anane d'an mijina mahaifiyarsa ta rasu tin yanada shekara d'aya, bayan yagama karatinsa na secondary ne yatafi k'asar Cyprus inda yai degree d'insa na farko dana biyu akan mass com, yanzu kuma yafara aiki a CCTV dake abuja".


Masha Allah su mami suka fad'a mami tace "Allah yasanya albarka" sukace ameen HINASH ma yamasa congrat ya amsa cikin farinciki,


Momy fati tacigaba da fad'in "yanzu kuma inaso idan badamowa hajiya Ayaha dan Allah kibama yarona huzaifa auren yarki humaida dama tinda dadewa nace insha Allah ita nakeso ya aura" murmushi mami tai sannan tace,

"To inbanda abunki hajiya fatima ai kinada damarda zaki zab'awa humaida miji saidai mu muduba muyi bincike idan yadace da'ita ta auresa, huzaifa ai namune tinda d'ankine,

Ni dai na amince, saidai kinsan komai yanason ayisa cikin kwonciyar hankali sbd haka kijira harzuwa yarinyar nan tasamu lfy ni dakaina zansami iyayenta maza namasu maganar dik yanda takasance zankiraki".

Murmushin farinciki momy fati tai sannan tace "to Alhmdllh naji dadi ssi wlh, Allah yatabbatar mana da alkhairi" suka amsa da ameen.

HINASH ne yace "wato tuwona mai na zaayi kenan" huzaifa yai dariya suma su mami sukayi mami tace "shima wonnan shine akai baikon HUDAYYA dashi da sadaki naira dubu tamanin".

Momy tace "Ah kai masha Allah, amma gsky baku kyautaba, muma ai yakamata asanardamu zaayi tambayar HUDAYYA, dikda mu gefen uwa muke amma dai ana fitarda hakkinmu" d'an murmushi mami tai sannan tace,


"Eyyah, amana afuwa wlh abonne yazo cikin gaugawa shsy" momy tace "to shikenan Allah yanunamana lokaci da rai da lfy" suka amsa da ameen.

Momy fati bata woni jima da zowa ba saigasu hunayya dasu Amira dasu mama harda hajiya sunzo, hunayya naganin momy fati taje dagudu tafad'a jikinta, bayan sungaisa dasu mama da hajiya sannan su Amira suka kawomasu abincinda sukazo dashi,

Su mama kam basu woni jimaba sukamasu sallama su yaya Affan suka maidasu gida, fitarsu dakamar 30mnts saigasu aunty billy da yaya hisham dasu baby aami,

Itama dai aunty billy girki tayomasu namusamman tazo masu dashi acikin zunduma zunduman food flak's, anan suka wuni su hinash na'awoje kokuma masjid idan sunje sallah kokuma sunaso su kwonta, su mami kuma suna aciki,


Around 6pm nurse's sukazo suka d'auki HUDAYYA suka tafi da'ita gunda za'a sakamata hak'oran roba domin amaye gurbin wonda yafita.

Saida suka kwashe kusan 1hr sannan suka mayarda ita.

Aunty billy da hanash bayan anyi sallar magrib suka woce gida, su hunayya kuwa sai kusan 11pm sannan Ammar yazo yamaidasu gida, HINASH kuwa sai kusan 12am sannan yatafi shima dan mami tamatsamasa ne dak'ilama anan zai kwana,

Momy fati kuwa huzaifa takira yad'ibo mata kayanta na amfani sbd anan zata kwana.

*******

Haka suka cigaba da jinyar HUDAYYA dabata cikekkiyar kulawa daga bangarensu dakuma bangaren likitoci,

Sannu ahankali kuwa lafiya tafara samowa dan yanzu dakanta tana tashi kuma tana iyacin abinci sbd bakinta yahuce da kumburinda yai kuma yadaina mata ciwo, hakama sauran ciwuwwuka dataji dik sunfara workewa sbd tanada kyan jiki.

Yanzukam Alhmdllh har fira akeyi da'ita, aikuwa karkuso kuga su humaida kamar su goyeta haka sukeji, su hunayya dasun dawo daga school anan suke wuni sai dare sannan Ammar ko Affan yamaidasu idan sunzo kawo abinci,

Haka itama HUDAYYA har dariyansu takeyi, mami tini takoma gida tabar momy fati da humaida, HINASH kuwa kiran gaugawa yasamu daga office d'insu, badan yasoba dole yabar HUDAYYA acikin wonnan halin yatafi, yanzu kuwa tinda taji sauki tafara magana saiya kira ta woyar Amira idan tazo sugaisa yakuma tambayi jikinta.

*****

Momy saudat kuwa tinda tadawo daga lego's batasake cewa kowa uffan ba, idan tatashi fitarta driver dinta ke kaita hattasu hajiya yanzu baruwonta dasu ko gaidasu batayi,

Tini tasake siyan wota galleliyar mota mai shegen kyau da tsada yanzu kuma business takeyi, container container take dakkowa ita da wosu k'awayenta daga Saudi Arabia zowa Nigeria, haka kuma sukan tafi Dubai su dakko kaya, takanyi kwana biyar hud'u har shida bata gida, abun yadami hamida tarasa yanda zatayi,

Woni lokacin har tambayar kanta take, shin momy zaman aure take kokuwa zaman kanta? sbd da'ita da mai zaman kanta batada woni bambamci, fitarta takeyi lokacinda taga dama koda dasanin abba koma ba saninsa.

*****

Yau kimanin satin HUDAYYA hud'u cif a hospital kuma Alhmdllh tasamu lfy sosai wlh, suna a zaune mami tazo HUDAYYA na a kwonce tadora kanta akan cinyar humaida saiga babie yashigo,

Bayan sungaisane yacemasu "am likita yashigo?" humaida tace "Eh yashigo yadubata yace bawota matsala danhaka yasallamemu, amma yarubuta wosu magunguna yace tacigaba da sha".

"Ok....to Alhmdllh, dama daga gunsa nake nakarbo takardan sallaman" mami tace "Ah to Alhmdllh, HUDAYYA lafiya tasamu kenan" HUDAYYA tai dariya.

Nan dai suka tashi akai shirye shiryen tafiya, saida Affan da Ammar sukazo da motoci sannan aka saka kaya sauransu suka shiga motar ya Affan sauran kuma suka shiga motar babie sannan suka woce,

Olready tinkan su kariso ansanar gida gasunan zowa, aikuwa suna isowa su humaira dasu humair sukazo dagudu suna oyoyo oyoyo yaya HUDAYYA.

Itama cikin farinciki da kewar y'an kannen nata tarungumesu sannan suka shiga cikin gida, a side din hajiya aka woce da'ita dan tace itada side d'insu sai lahira kokuma idan Ammin su ta worke tadawo,

Haka kowa akayi ba'a takurataba saidai suma y'an uwon nata sun tattaro nasu i nasu sunbiyo bayanta yanzu komai nasu na amfani babu acikin bedroom d'insu sai hamida kawai suka bari acan, aikuwa taita kuka tana rokonsu dan Allah sukoma sucigaba da zamansu atare har ranar rabuwa tazo.

Saidai fafur sukak'i sukabata hak'uri kawai..

******

Kimanin satin HUDAYYA d'aya da dawowa takoma school tacigaba da karatinta.

Yauma kamar kullum bayan antadasu daga school suka fito ida dasu Amira, koda sukazo harsu humaira sunshige mota danhaka suma suka shiga driver yatada motar sukabar school d'in,

Suna isowa gida bayan driver yagama packing suka fito, food flak's dinta tadakko dana humair da school bag dinta sannan tafito,

Kai tsaye side d'in mama tafice takai food flaks d'inta dana humair sannan tawoce side d'in???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~? hajiya.

Tin a k'ofar shiga parlon hajiya tafara jiyo daddad'an sassanyar k'amshin tirarensa, k'amshinda ko amafarki tajisa tasan mamallakinsa sbd agunsa kad'ai ta tab'a jinsa kuma takejinsa,

Ahankali tashiga cikin parlon cikin sallama, zaune tahangosa yanacin abinci hularsa na hanun hunayya tana juyata humaida nakan kujera 2seater a kwonce,
hajiya kuma na'a gefensa tanajan carbi,

Su hunayya ne suka amsa sallamar, shikuwa binta yai da kallo kamar yanzu yafara ganinta, dariya ce takufcemata ganin yanda yasaki baki da hanci da ido yana kallonta kamar yaune yafara ganinta, dasauri tatoshe bakinta kar hajiya taji tafara jeromata tambayoyi sannan tak'ariso ciki.

Cikin fara'a da murmushi tacemasa "inawuni ya HINASH" sai alokacin yadawo hayyacinsa yace "um...am....lafiya, andawo" tace eh...sannan tashige ciki tana fad'in "hajiya on pinijam, noi chomri" hajiya kwa jan carbi take shys bata kulataba kawai tarakata da harara...

#/Vote
#/Share
#/Comment
#/AUFANA for life

_*HABIBI DA'IMAN*_
_*BY~AUFANA*_
_wattpad@Aufana8183_
_*Intelligent writer's association*_
_*Page 23~24*_
_*Bismillahir rahmanir rahim*_
*HAPPY SALLAH TO ALL MUSLIM'S UMMAH*
Bedroom d'in hajiya tashige tacire uniform tad'aura towel tashige toilet,

Wonka tai tareda d'auro alwola sannan tafito, bayan tafito sannan tashafa mai tasaka wota y'ar riga gown girmanta iya guiwa.

K'aton hijab tasaka sannan tashimfid'a prayer mat sannan takabbara sallar azahar.

Tana cikin yin sallah saigashi yashigo batareda saninta ba.

Zama yai yana kallon yanda takeyin sallar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login