Showing 9001 words to 12000 words out of 23100 words

Chapter 4 - HABIBI DAIMAN Compelet Hausa Novels BY AUFANA.doc

tamasu zarra a kyau,

HUDAYYA wani sihirtaccen kyaune da'ita shsy momy saudat dik tafi tsanarta take kiranta da y'ar tsana,

Su HUDAYYA sunfi y'ayan saudat kyau sau million sbd su hamida mahaifiyarsu suka biyo shys sukafi kama da kad'o bama zakace jinin fulani bane saidai idan sun fad'a kokuma kaji suna yaren fulatanci,.

HUDAYYA kyakkyawa ce ajin farko, bazance maku fara bace bakuma zance maku bak'a bace zandai iya cemaku chocolate color ce wato kala mai tsadar gaske maikuma wohalar samu.

Ita ba mai tsayi bace kuma ba gajeruya bace, batada jiki sosai amma tanada hips waenda suka b'oye girman matasan zamanta, tanada cikar k'irji kamar sauran y'an uwanta,

Fuskarta bamai tsayi bace kuma bamai fadi bace sosai matsakaiciya ce wacca take d'auke da dara daran idanuwa farare tas tamkar auduga, dogon hanci mai tsayi kamar ink,.

Eye lashes nata masu d'an tsayine da sumar girarta wacca idan kaganta zaka dauka zanata akayi, bakinta bamai girma bane kuma bak'arami bane sosai dai dai fuskarta yake.

Yatsunta dogaye ne masu tsayi marasa kauri sosai, sumarta wacca momy ta gutsure tasake ciccikowa harma tafi ta da d'in sentsi dakuma tsayi gata bak'a wulik.

Atak'aice dai mai kyauce sosai,.

Zaune suke acikin katafaren parlon Ummi rukayya kusan rabin yammatan gidan waenda suke sa'annin su humaida hunayya da HUDAYYA,

Kayan engagement d'in Amira da mas'uda ne suke kallo an babbajesu acikin parlon,

Hunayya ce tace "um su Amira amaren gobe, yau zamusha alawa cwingom" dariya sukai suduka cikin fara'a da farinciki.

HUDAYYA ce ke dudduba kayan suna kara ganin abinda basu ganiba lokacinda aka kawo sbd yawan mutane masu zowa Allah shi kyauta yasanya alkhairi,

Tana cikin dubawa saiga momy da wasu k'awayenta biyu sunshigo ganin kayan, dasauri suka gaidasu amma k'awayenta ne kawai suka amsa dan ita ko kallo basu isheta ba,.

Komawa HUDAYYA tai kan kujera ta zauna itakuma tashiga nunawa k'awayen nata kayan.

Bayan sungama saita juyo ta kallesu tace "Amira Allah i sanya alkhairi Wlh kukam kun huta kunada farin jininku bakamar wasuba dasukeda bak'in jini kamar mujiya, ko mashinshina ba'ataba samuba bare har wani d'an arziki yakawo kansa".

Tinda tafara maganar suka fahimci inda zancenta yadosa sbd haka bawanda yacemata uffan harta gama tafice tareda k'awayen nata.

Bayan tafita ne HUDAYYA tace "mu bamuda bak'in jini wollahi natabbata da muma muna fita woje kamar yanda kuke fita da tini mun dade dasamun mazajen aure".

Hunayya tace cikin b'acin rai "Wlh daace muna fita da samari sai waenda mukaga damar kulawa".

Munawara ce tace "dan Allah kuyi hak'uri kudaina damuwa da abunda momy take maku sbd idan da sabo kunsaba da halayyarta sbdhaka baikamata kudinga damarda kanku ba, saurayi datake magana akai ai dik inda mace take mijinta har gida yake taddata",

Nannauyan numfashi humaida ta sauke sannan tace "ai nafada masu kullum kuma ina jara fad'a masu sudaina damuwa da halayyar momy".

Shuru yaratsa parlon kamin daga bisani Amira taje kitchen tazubo masu abinci a faranti suka baje suna kwasan girkin Ummi mai dadi.

****** *****

Yau kimanin wata biyar kenan da dawowarsu gida tini kowannensu yafara aikin government kuma Alhmdllh kowannensu albashinsa mai tsoka ne ssi,

Around 8pm bayan sundawo daga gun aiki suna gida, HINASH na zaune yana sarrafa system hanash kuma yana gefensa akasa yana sallah.

AAmi ce tashigo dauke da teddy dinta tana sanye da riga iya guiwa, yarinyar kyakkyawace ssi sannan tanada baki ssi akwota da shegen surutu shys suke batawa da HINASH sbd shi bayason damuwa ssi,.

Aikuwa yana ganinta yadafe kansa sbd yasan damunsa zataitayi.

Kan gadon tahayo tazo kusa dashi ta zauna tace "baby ashe kai mai kalya ne, dady napa yace mai kalya wuta ake sakashi" ba HINASH kadaiba hatta hanash dake jan carbi saida yai mamakin yarinyar,

A shekarunta bazakai tinanin tasan abunda k'arya ke nufiba,.

Murmushi yai sannan yace "my aami wace k'arya namaki" turo baki tai sannan tace "kace yau zaka kaini park nahau shillo amma baka dawoba".

Dariya yai sannan yadakko wata jaka dake kusa dashi yana fad'in "kai my aami badai rigima ba, to karba ga sweet da chocolate nasiyo maki".

Karba tai tana dariyar murna tasake cewa "to ina na yaya abdul" sake miko mata wasu yai sannan tasauka tad'auki teddy dinta tawoce tana murna,

Tana fita saiga hanifa tashigo, gaidasu tai sannan tace "brother's dady yace kuzo yana nemanku yana a parlon sama".

Amsa mata sukai sannan tafice abunta, tana fita HINASH yakashe system dinsa sannan suka tashi suka fita,.

Kai tsaye parlon suka nufa, cikin sallama suka shiga yana zaune mami nadaga gefensa tana yanka masa fruit's yanaci,

Amsa masu sallamar sukai sannan suka kariso suka zauna suma suka fara daukan fruit's d'in sunasha.

Dasauri mami tace "a,a malamai menene haka kuma? zakuzo kawai ku tsomawa mutane hanunku bako neman izini, nifa dan mijina nayanka sbd haka kuje ku dakko naku",

Baki suka bude suna kallon juna cike da mamaki, ganin haka yasa tacigaba da fad'in "Eh idan kunji haushi kuje kunemo mata kuyi aure sbd mungaji da cidaku, ehi idanma baku saniba yanzu kunsani to, dama dadyn ku yanata neman yanda zai fadamaku yakasa".

Juyawa sukai ga dadyn nasu atare sukace "wai hakane dady?" sukai maganar tareda kafesa da idanuwansu.

Dagowa yai fuskarsa ba alamun wasa yahad'iye kankanarda ya guntsa sannan yace,

"Eh tabbas hakane kunemo mata namaku aure shine kadai abunda yarage wanda yake nauyinku daya rataya a wuyana, nabaku ilimi na arabi da boko har kunkai matakinda zaku iya rike kanku, yanzu aurardaku kadai yarageman".

Sadda kansu sukai cikin tsintsar ladabi da kunya, HINASH ne yace "to ai dady dika dika bamufi wata biyar da dawowa k'asar bama bare har muhad'u da mata muga wacca mukeso, amana uzuri abamu lkc insha Allah zamu nemo mukawo",

Mami ce tace "Allah isa hakan dai shine yafiye maku tinkan nafara korar mutum daga gidana" shagwabe fuska sukai HINASH yace.

"kai mamin mu yanzu zaki iya korarmu kenan" hararansa tai tace "sosai makuwa, matuk'ar bakuyi aureba nanda 2 to 3 month's hmm zakusha mamaki yara" tak'arisa maganar taredayin kwafa.

Dariya suka kyalkyale da'ita cikin nishad'i, itama d'in d'an murmushi tai hakama dadyn su,

Sake dubansu tai sannan tace "Am dama abunda yasa mukace a kiraku shine, jiya saudat matar d'an uwana takirani a waya, bayan mungaisa tamaku barka da dawowa lfy,

To bayan dai mungama gaisawa ne take fad'aman abunda yake zuciyarta, tanaso d'aya daga cikinku ahad'asa aure da y'ar d'an uwana hamida,

Nai matuk'ar farinciki dajin wannan maganar sbd koba komai zumuncinmu zai kara d'aukaka, to bayan da muka gama maganane nasami mahaifinku nafad'a masa sbd kunsan komai banayi batareda shawararsa ba,

Alhmdllh shima yanuna farincikinsa ssi anan take muka yanke hukunci kai HINASH kaje kaga yarinyar kusasanta kanku tinda kaine babba shikuma hanash yanemo wacca yakeso nanda wata biyu zuwa uku mukeso ayi aurenku".

Zufanda ke ketowa HINASH ne yasanya hanu yana gogewa dikda kuwa sanyin A.C d'inda ke ratsa parlon,
???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?
Dakyar ya'iya cewa "tot..to mami badamuwa" yai maganar yana mikewa tsaye mami tace "kafa shirya jibi zamu wuce kebbi" to kawai yace yabar parlon.

Tini hanash yagano inda d'an uwansa yadosa, idan ransa yabaci baya juriyar zama acikin mutane shys yai saurin barin parlon,

Shikam yajima a parlon sunashan fruit's da dady suna firar gun aikinsu...
#/Vote
#/Share
#/Comment
#/AUFANA for life
_*HABIBI DA'IMAN*_
_*BY~AUFANA*_
_wattpad@Aufana8183_

_*Intelligent writer's association*_

_*Page 13~14*_

_*Bismillahir rahmanir rahim*_

Kamar kullum yauma bayan sun kammala aikace aikacensu sukai wonka suka sauya kaya sannan sukai breakfast.

Suna zaune acikin parlor kamar kullum tinda bainda suke zuwa dan momy bata barinsu sufita koina daga gida sai cikin gida sashensu momy ko hajiyar su Abba,

Hamida ce kecin gyada HUDAYYA kuma tana yiwa hunayya tsefa yayinda humaida ke kwonce, kallon TV suke wata Chanel zeeworld.

Momy ce tashigo hakan yasa sukai saurin nutsuwa suka mayarda hankalinsu gunta domin jin abunda zata basu umurni su mata,

Wani watsattsen kallo tamasu tareda fad'in "woi lfy kuka wani turoman idanuwana kuna kallona kamar jikokin zuri'ar mayu, zaku daina kallona ne kosaina tsole idon".

Dasauri kowacce tasha jinin jikinta tinkan ido yaraina fata, mtsss.....taja dogon tsaki sannan takalli hamida data b'ata fuska kamar zatai kuka sbd abunda mahaifiyar tata keyi tace,

"Am hamida kifara shiri tin yanzu sbd gobe around 4pm dot zakiyi babban bak'o" tak'arisa maganar tana murmushi".

"Bak'o kuma momy?"

Tajefa mata tambayar "Eh babban bak'o kuwa, yayanki ne HINASH wonda suka dawo daga k'asar Italy karatu, zaizo gunki domin kufahimci juna sbd insha Allah nanda 2months zaku zama ma'auratan juna",.

Narke fuska tai kamar zatai kuka tace "haba momy meyasa kike hakane dan Allah, meyasa bazaki bari shi yaganni dakansa yace yanaso na ba harsaikin tallata masa ni dakanki, wlh koda d'an uwanane wota rana saiyaman gori yace ai bashine yaganni yace yanasona ba bashi ni akayi".

Tak'arisa maganar kamar zata zubda kwallah.

Zari idanuwana momy tai tareda dafe bakinta da d'ayan hanu irin yanayin mamakin nan sannan tace "kajiman shegiyar yarinya arziki yana binki kekuma kina kaucewa, yo kodama manna masa ke nai miye damuwarki, yaro saurayi kyakkyawa jinin naira, gaba d'aya rayuwarsa baisan miye talauci ba, kici arziki kibar arziki, wlh tin wuri gwandama kisaki jikinki yarinya dan bazan taba yarda wonnan arzikin ya kufceman daga hanu ba bayan nariga dana damkesa hanu biyu,

Zan shiga ciki kizo ki karbi kud'i kije kasuwa kisiyo sauran kayanda babu a store dan girki kala uku zaki masa, sannan zakije gun gyaran jiki gobe da make-up" tana gama maganar tafice daga parlon,.

Wani k'ololon takaici ne yatokarewa hamida zuciya tajuya kawai batareda tace komaiba,

HUDAYYA ce tace "hamida kidaina musu da mahaifiyarki, uwa fa uwa ce koda tafi komai lalacewa, kuma itace wacca tafi kowa son ganin farincikinki da jin dadin ki, sbd haka kimata biyayya kawai koda kuwa abunda takeso ke bakya sonsa".

Kallon HUDAYYA tai tace "hakane sis...amma ni tawa uwar dik biyayyarka dole wota rana kasab'a mata".

Humaida ce tace "hakane amma dai kicigaba da hkr kuma kicigaba da mata biyayya wota rana sai lbr, lokaci kankane yarage kurabu kije gidan aurenki, kinga mu gashi ko irin taki uwar bamuda mukadai muke rayuwa".

Sadda kanta tai k'asa cikin jimamin abunda humaida tafad'a,

Shiru ne yaratsa parlon kamin daga bisani hamida ta tashi tafice izuwa gun momy.

***** *****

12pm dot jirginsu yasauka k'asar kebbi daga garin Abuja city a katafaren filin jirginnan na ahmadu bello International airport dake garin birnin kebbi l/gvmnt,

Barrister kabir kanen mahaifinsu shine yazo tareda iyalinsa suka taryesu, daganan suka shiga motocinsu suka wuce izuwa katafaren gidan dadyn HINASH dake unguwar ghesse phess 1,.

Almost 35mnts suka dauka kafin su iso a katafaren gidan, bayan anyi horn gate man yazo yawangare gate aka shiga daga ciki,

Ma'aikatan gidan ne sukazo sunamasu sannu da zuwa tareda kwashe kayanda sukazo dasu suka shiga dasu ciki sannan sukuma daga bisani suka shiga,

Kowa bedroom dinsa yawuce inda yaya hisham da iyalinsa suka wuce nasu side d'in, HINASH da hanash kuma suka shige nasu d'akin, hakama hanifa dasu mami.

***** *****

Washe gari tin 6:30am suka farka daga bacci, bayan sunkammala aikace aikacensu dasuka zamemasu jiki sai hamida taje gun HUDAYYA tace,

"HUDAYYA kinga banida wata aminiya wacca tawuce ki, daga ke saisu munawara, sbdhaka kune zaku taimaka man wajen tarbansa".

Murmushi HUDAYYA tai sannan tace "karki damu y'ar uwata insha Allah zamuyi iya kokarinmu, ki kwontarda hankalinki kinji" itama murmushin tai sannan suka fita atare.

Sashensu Amira suka nufa, koda sukaje tana a kwonce tana amsa kiran waya, da'alamu dai da sweetheart dinta take magana.

Zama sukai kusa da'ita hamida takaimata dukan wasa tareda fad'in "oh su o,o ba kunya anzake saishan love ake agaban mama bako d'an sakayawa ashiga uwar daki".

Hararan wasa tajefo mata tana murmushi, itadai HUDAYYA dariyansu kawai take.

Bayan tagama ne tadago daga kwoncenda take tace "kekuma y'ar rainin sense mekike cewa" hararanta hamida tai tace "dama inafa zakiji abunda nace tinda kinyi zurfi acikin shaukin soyayya".

Dariya takwashe da'ita tareda kaimata dukan wasa tace "bakida dama hamida wlh",

HUDAYYA ce tacemata itama tana murmushin rigimarsu "sis...dama yaune hamida zatai babban bak'o shine mukeso adanmasa kayan tarba" zaro idanuwanta tai tana dry tace,

"hegiya kema kice kinfaso zakishiga online, wanene shi kuma daga ina zaizo" HUDAYYA na dry tace "yaya HINASH ne" murmushi Amira tai sannan tace,

"Kai amma wlh naji dadi ssi da wannan abun, Allah i tabbatar mana da alkhairi" HUDAYYA tace ameen.

Daganan suka tashi suka koma sashensu HUDAYYA bayan sunfad'awa mama da ummi abunda ke faruwa.

Su kansu su mama sunyi matukar mamakin wonnan abun sbd daidai da rana d'aya basu tab'ajin lbrn HINASH yanason hamida ba, hakan ya tabbatar masu da wonnan plan ne na momy saudat,


Suna zuwa sukafara tsara kalolin girkinda zasuyi sannan suka shiga kitchen suka fara aikin,.

HUDAYYA tariga data saba da girki sbd haka sam baya bata wohala sab'anin su hamida daba kowanne lkc sukeyiba sai jefi jefi,

Cikin k'ankanen lkc sukai soyayyar shinkafa fried rice da soyayyen naman kaji, sai shinkafa da miya da nama da co-snow, sai kayan snacks da had'in juice na kwakwa da madara da yoghurt da ayba,

Bayan sungama sannan sukai wonka sukaci gayu momy tasaka driver yakaisu shagon make-up na MEENA BEAUTY dake kusa da gidan radio na vision FM.

Kusan 1hr aka dauka ana tsarawa hamida make-up na naira dubu talatin,

Wow masha Allah tai kyau ssi kuwa gwanin ban sha'awa, bayan ankare matane tace ayiwa su HUDAYYA, anan take HUDAYYA tace itadai bataso nanfa sukai tsaye sukace dole sai anmata tinda suma anmasu.

Badan tasoba dole tahak'ura itama akamata, hmm reader's naso kuga HUDAYYA, anan take tayiwa hamida zarra a kyau dikda kuwa tata make-up d'in only casual akeyiwa batada wani cike ciken kayan cosmetic ssi,.

Har ita meena beauty d'in saida tayaba da kyan HUDAYYA bcoz nata kyan is natural koda ba make-up zaka gansa.

3:30pm dot driver yazo yadaukesu yamaidasu gida, koda suka isa har mami dasu hanifa sunzo aikwa nan suka hade da hanifa akaita shan firar yaushe rabo,

4pm suka woce babban parlon bak'i inda suka hadesa suka gyaresa da kamshin tiraruka dana girke girke,.

Sunjima anan zaune suna fira hadda hanifa, ganin har kusan 4:30pm tayi yasa HUDAYYA ta tashi tanufi sashen hajiya kaka domin tayi sallah batareda tafadawa su hamida ba sbd tasan bazasu barta tawonke make-up dintaba matuk'ar bakon nasu bai tafiba,.

Koda taisa bedroom d'in hajiya saita tadda hajiya tashiga toilet donhaka tafito parlor domin tajirata harta fito gashima taji kanta namata ciwo.

Kwonciya tai akan kujera 2seater tadora hanunta d'aya kan fuskarta d'aya kuma akasa.

Tana nan a kwonce batareda tasaniba iskar fankar dake parlon tad'aga rigarta ta bayyanarda cikinta da cibiyarta a fili,

Ahankali yashigo cikin parlon batareda yace komaiba, tozalinda idanuwansa suka masane yasakashi yin tsaye cak yakasa koda motsin kirki,

Ahankali tafara jiyo bak'on daddad'an k'amshi mai sanyaya zuciya yana bak'untar hancinta.

Kasancewar bata tab'ajin irin wannan k'amshinba sai a yanzu yasa tad'ago ahankali domin ganin mamallakin k'amshin.

Ganinsa tsaye cak yakafeta da fararen idanuwansa yana kallonta yasa itama d'in tazuba masa dara daran idanuwanta tana kare masa kallo kamar yanda shima d'in yake kallonta.


Kyakkyawa ne ssi, fari mai ne mai kyan gaske, sanye yake da shaddah galila mai tsadar gaske d'inkin tazarce riga har kusa da k'asa mai dogon hanu anmasa mai gidan clip's, kansa sanye da hula k'ube brown color, hanunsa sanye da watch na Company rano,

Atak'aice dai yahad'u matuka, daka gansa kamasa kallo d'aya bakason ka dauke idanuwanka daga kansa, sassanyar k'amshin tirare mai dadin gaske ke tashi ajikinsa.

Ganin yanda rigarta tayine yasa dasauri tadawo hayyacinta tamik'e tsaye tareda b'ata fuska cikin yanayin alamar b'acin rai tafara gyara rigar tata tana y'an kame kame sannan tace "malam lfy? Me kakeso ne?".

Murmushi yai sannan yace "ina hajiya take ne?" harta bude baki zatai magana saiga hajiya tafito tana tafi tana magana cikin yanayin murna da farinciki tana fad'in,

"Kai marhaban lale lale da mutan Abuja, marhaban da y'an biyun hajiya kaka" shima cikin dariya yaje kusa da'ita yace "hajjaju na barka da maraice, yh kike yh tsufa yakuma bayan rabuwa" cikin fara'a tace,

"Alhmdllh y'an biyu ina d'an uwanka da yayanku da iyalinsa" yace "suna lfy wlh sunce agaidaki".

HUDAYYA kam tinda taji hajiya tashigo tashige ciki abunta domin gabatarda salla,

Bayan sungama gaisawa sannan suka zauna anan parlor, HUDAYYA nafitowa daga toilet hajiya tace,

"Ke HUDAYYA zo ga bak'on naku yazo kimasa iso gun y'ar uwar taki" mamaki ne yakama HUDAYYA a zuciyarta tace.

"Wai dama wannan shine yaya HINASH d'in, to ikon Allah rashin sani yafi dare duhu, amma gsky yanada kyau yahad'u ssi kuma daga ganinsa d'an gaye ne, um mami taiya haihuwa gsky" sai tayi y'ar dariya,

Hijab d'in hajiya tasaka sannan tafito tana murmushi tace "au dama wannan shine yaya HINASH?" hajiya tace "Eh shine koda suka tafi karatu lkcn dik kuna k'anana shsy bazaki sanshi ba".

D'an murmushi tai tace "kai hajjaju kin iya tina bara da bad'i bakya mantawa, bak'onmu bismillah muje ko" harara hajiya ta watsa mata tana fad'in,

"Yo to angaya maki ni kamar iyayenki ce marasa kwari masu mantsuwar tsiya kamar masu kanun kifi" dariya HINASH ya kyalkyale da'ita sbd jin abunda hajiya ke fad'a.

HUDAYYA kuwa murgud'a mata baki tai tace "oho dai iyayena saisunfiki k'arko insha Allah" tai maganar tana barin parlon,

Shima tashi yai yabi bayanta, bayan yasaka takalmansa tana tsaye tana jiransa yasaka sannan suka kama hanya,

Acikin nustuwa take tafiyarta shikuwa sai kallonta yake yakasa d'auke idanuwansa daga kanta wanda kuma yakasa gano dalilin hakan.

A dik tarin shekarunda sukai a k'asar woje baitab'a ganin macenda idanuwansa suka kasa k'osawa da kallonta ba sai wonnan, bakuma wai don tafisu kyauba sbd idan kyaune akwoima waenda suka fita acan k'asar Italy,

Cikin tattausar murya yace "HUDAYYA aji nawa kike a school kuma shekaranki nawa ne" murmushi tai batareda tajuyo ta kallesaba tace,

"Ina ss2 ne yanzu, on this month kuma idan yakai 15 zancika 18yrs insha Allah"

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login