Showing 6001 words to 9000 words out of 23100 words

Chapter 3 - HABIBI DAIMAN Compelet Hausa Novels BY AUFANA.doc

sauti sbd zafinda taji,

Aunty sofiyya ce tafito dasauri jin k'ararda HUDAYYA tai saita gansu a tsugune suna kuka da magiya,

Ba tsoron Allah ba tausayi haka momy tafara gutsurewa HUDAYYA suma, kuka suke sosai suna mata magiya "dan Allah momy kiyi hak'uri wallahi bazamu sakeba mun tuba dan Allah",.

Aunty sofiyya ce tazo da sauri tafara bata hak'uri cikin magiya amma ko kallonta batayiba bare ta saurara masu, haka tabisu da d'addaya dikdata gutsure masu suma,.

Saida tamaidasu tamkar maza sannan ta barsu haka tana masifa "gobe ma idan nace karkuyi abu kuje kuyi, nikuma bazan tab'a gajiyawa ba wajen hukunta ku" tana masifa tafice izuwa bedroom dinta tabarsu anan suna gunzar kuka mai tsuma zuciyar mai karatu,

Kuka sukeyi sosai suka rungume juna gwanin ban tausayi humaida na fad'in "Wlh Allah saiya sakamana bazamu tab'a yafewa dik wanda yazalincemu ba, momy ke azzalima ce ba momyn mu bace",.

Sofiyya ce tazo tadinga rarrashinsu, dakyar suka iya tashi suka fice izuwa bedroom d'insu..




#/Vote
#/Share
#/Comment
#/AUFANA for life
_*HABIBI DA'IMAN*_
_*BY~AUFANA*_
_wattpad@Aufana8183_

_*Intelligent writer's association*_

_*Page 9~10*_

_*Bismillahir rahmanir rahim*_

****A can ma kan bed d'insu suka zauna sunata kuka gwanin ban tausayi, sumarsu dasuke kuri daita irin ta fulani ga tsayi ga sentsi gata kuma bak'a wulik yau anarabasu daita sbd tsabar zalinci,.

HUDAYYA ce ta taso tai tsaye agaban mirror tana kallon kanta, idanuwanta sunyi zajir d'an karamin bakinta yak'arayin ja ssi, doogon hancinta shima yai zajir kamar in Aufana tayi kuka =?? hhh Lol,

Kallon kanta take yanda momy tamayarda ita tamkar namiji, badan y'an kunnayenda take sanye dasuba dakuma kayan mata dake jikinta da za'a iya kiranta da namiji sbd dama su ba ma'abota son yin kwalliya bane,

D'an kwalli ma sai Ammin su tamatsa masu suke sanyawa, yanzu kwa tinda ta kwanta ciwo rabonsu dasu shafa kwalli bare kuma jan baki da powder,.

Suma sauran tasowa sukai sukazo sukai tsaye a bayanta suna kallon kansu a mirror, wasu zafafan kwallah ne suka zubowa HUDAYYA sbd b'acin rai da k'unar zuciya tace,

"Ya Allah narok'eka ka sakamana akan dik wonda ya zalincemu, bazamu tab'a yafewa ba wolla....h...I" tak'arisa tareda fashewa da sabon kuka,

Rungumeta sukai sannan suka koma suka zauna kan bed,.


Washe gari takasance Saturday weekend ranar hutu, saidai agunsu sukam bazasu kirata da ranar hutu ba sbd batada woni bambamci da sauran ranaku a gunsu,.

Humaida ce ke mopping d'in babban parlor hunayya kuma tana gyara parlon momy, HUDAYYA kuma tsaye take tanayiwa momyn tsefa,

Cikin rashin sani tsinke yakub'ce mata a hanu yadogari kan momy,

Wata iriyar kuwa tai bako a'uzubillah sannan tarike hanun HUDAYYA tajuya tawatsa mata muguwar harara tareda watsa mata kyakkyawan mari,.

Dasauri tarufe fuskarta tareda fashewa da kuka tace "wayyo Allah na, dan Allah momy kiyi hak'uri",

Cikin masifa tazago daita tazaunar a gabanta tasake kaimata duka a baya tana fad'in "so kike ki hallakani ko uwarki taita zama itakad'ai da ubanki ko, to wallahi k'aryarki shegiya mai kama da y'ar tsana" saida tagama dukanta sannan tace kuma ta tashi tacigaba da mata tsefar,.

Dolenta ko tasha na jaki tana kuka tana zubda kwallah tacigaba da tsefar

Bayan tagama sannan tace ta wonke mata k'afafuwanta da man wonke k'afafuwa,

Cikin d'ar d'ar tawonke mata tagama sannan tace ta gyaramata dakin ta wonke toilet, dik saida tayi tagama sannan tace kuma taje tabata woje kamin tai ball daita,.

Jiki na b'ari tai saurin tafice daga d'akin,

Koda taje gunsu humaida saita yaddasu sunacin uban aiki, girki suke har kala uku a kitchen dan tace wai bak'i zatai yau,.

Wani littafen girke girke humaida tadakko tabude, aciki suka sami girki masu sauki suka farayi kasancewar komai akwoi a store d'insu,


Dikda tagaji sosai amma hakan baihana tasaka hanunta sukacigaba dayi atare ba, idan wonnan na tuk'a tuwon semovita sai wannan tadinga tadinga zuba mata garin,.

Hunayya kuma itake hada miyar kubewa danya,.

Bayan sungama sane sannan suka sake d'ora shinkafa friad rice, suna duba littafen yanda akace ai saisuyi, dahaka har suka kammalata,.

D'ayan kuma saida humaida taje gun mama maryam ta tambayota tafada mats dik yanda zasuyi sannan tazo suka hadasa,.

Sai kusan 3:30pm sannan suka kammala komai suka kai kan dinning,

Bayan sungama ne suka zuba sukaci sannan sukaje suka fad'amata sun kammala komai, saida tazo taduba tagani sannan tamasu izini suka tafi,


Zaune suka acikin bedroom d'insu around 8pm HUDAYYA na bacci humaida nakaratun woni littafen novel na turanci hunayya kuma na zaune kan mirror tana shafa mai kasamcewar fitowarta kenan daga wonka,.

Amira da munawara ne suka shigo cikin sallama, dagowa sukai suka amsa masu sallamar tareda sakin murmushi,

Amira ce tace "Subhanallah, aunty humaida mezan gani haka, meyasa kuka gutsure sumarku kuka dawo tamkar maza".

Murmushi sukai humaida tace "ai bamune muka gutsure dakanmu ba momy ce tagutsure mana kawai danmun dade bamu dawo gida dawuriba jiya bayan antadamu daga islamiyya",

Mamaki ne tsintsa ya bayyana a fuskokin yaran sukaita kallonsu HUDAYYA suna mamakin wannan al'ajabin, acikin zuciyoyinsu kuwa tsinuwa ce fall izuwa ga momy saudat,.

Basu wani jimaba sukaje dagudu suka fadawa su Ummi da mama,

Ran mama maryam yamatukar baci da abunda saudat tayiwa su HUDAYYA nantake taje gun Abbu Ahmah tazayyane masa dik irin cin amanarda saudat keyiwa yaran,

Cikin tsintsar b'acin rai take magana "haba Abbun yara wannan wone irin cin zaline, tamaida yara tamkar bayinta, yarannan dik sun lallace sunyi bak'ar rama sunyi bak'i sbd wohala, gsky Abbu yakamata kud'auki mataki tin kan takaiga hallakasu dan wollahi komai zata iya aikatamasu abd batada imani kokad'an".

Shuru Abbu yai nawani d'an lokaci yana tinani kamin yad'ago yace "hajiya maryam kekanki kinsan da inada yanda zanyi tabbas da tintini nadade dayi, yaran nan yayanane jininane wollahi da inada yanda zanyi namagance wannan matsalar da tini nayi" saikuma yai shuru,.

Can yacigaba "inda matsalar take shine, da ace shi yaya mahaifinsu zai tab'uka woni abu to kinga dazanji k'arfin yin magana amma kinga dik tsawon wannan lokacin yayi shuru baice komaiba".

Haka dai sukaita jajanta matsalar dake cimasu tuwo a kwarya,.

Washe gari Sunday bayan suntashi sunyi break Sannan suka wonke uniforms d'insu da kayansu nasakawa,

Bayan sungama sannan suka fara aikace aikacenda suka zame masu jiki,.

Humaida na mopping d'in babban parlor hunayya na gyaran d'akin momy HUDAYYA kuma na gyaran kitchen,

Sallama taji da muryarda ko a mafarki tasan kota waye, aikuwa cikin tsintsar murna da farinciki ta yada moper taje dagudu tarungumeta tana fad'in,

"Oyoyo momy fati" suma dake wajen nasu aikin jin abunda humaida tace yasa suka fito dagudu, suna ganinta suka washe da dariya sukaje suka rungumeta,.

Itama cikin k'aunar y'ayan nata ta k'amkamesu ajikinta tana dariya, humaida ce tad'auki Ikram yarta datake goyo kenan cikin farinciki daganan tajasu suka woce izuwa gun Ammin su,.

Koda suka shiga Ammi na bacci amma sbd hayaniyarsu tasa tafarka, tana ganin y'ar uwarta sai fara'a tafara bayyana a fuskarta tateda d'ago hanunta,.

Cikin fara'a da zubda kwallah fatima taje tasakad'a hanunta acikin na Ammi d'ayan hanun kuma tana shafa sumarta,

Suma matsowa sukai suna dariya HUDAYYA tace "Ammi kidaina kuka yau ranar farinciki ce" tai maganar tana dariya,
Murmushi sukaga ya bayyana a fuskarta hakan yasa suma suka tsinci kansu acikin yin murmushin,.

Suna cikin nishad'i kwatsam saiga momy tabanko k'ofa tashigo cikin masifa bako sallama tana fad'in "Wlh zanci ubanku idan baku tashi kunje kucigaba da aikinnan ba".

Dasauri suka mike tsaye jikinsu har b'ari yafara sbd tsoro da sanin halinta, momy fati ce tamike tsaye cikin b'acin rai tace,


"Ba inda zasuje kuma bazasuyi aikinba, wato abunda nakeji ana fad'a acikin gari ashe gsky ne, to daga yau bazasu sake maki koda shara bane sbd suba bayi bane kuma ba bauta aka kawosu sumaki ba".

Wata iriyar dariya momy ta kyalkyale daita hadda tafawa sannan tace "ke fatima kishiga hankalinki sbd ke ba saar yina bace, wannan matacciyar gawar yayar taki itace sa'ana, aiki kuma kaf gidannan ba ubanda ya'isa yahanasu yinsa",.

Mamakine tsintsa yakama fatima tace "rashin mutuncinki wato ba a iya yara yatsayaba harda manyan gida, to wollahi kishiga hankalinki idan bahaka ba kuma yanzunnan nagyara maki zamanki, aiki ne kuma bazasuyiba matuk'ar ina acikin gidannan".

Wata muguwar harara tawatsawa fati sannan taje da nufin ta damko hunayya bata ankaraba taji fati takaimata naushi a baki, dasauri tadawo tareda dafe bakin da hanu tace,

"Kan uban can ni zaki daka fat..." batako Karisa ba tasake damkota tamaka da k'asa, hanunta takai danufin ta damko wuyan rigar fati sai tai saurin rike hanun tajuyasa izuwa baya kamar zata karyasa ne tana fad'in,

"Yau zan koyamaki hankali a gidannan" aikuwa kara tasaki mai sauti taneman ceto sbd zafi da wohalanda taji,.

Dagudu HUDAYYA taje tafadawa su mama abunda ke faruwa tana kuka cikin yanayin fargaba, koda sukaje dagudu saudat tasha wohala dan sai kakarin wohala take,.

Dama fatima tafisu farida rashin hak'uri sam bata daukan raini kamarsu farida sarakunan hakuri, sannan tafisu girman jiki sbd ita sak mahaifinsu take, itace ke bin farida,

Dakyar da wolahaula aka b'anbare fati akan saudat, saida suka zubamata ruwa sannan ta tashi wai ashe suma ne tai,

Tana tashi dagudu tafice izuwa dakinta fati tace "ashe ke karamar mara kunya ce wollahi matuk'ar ina a gidannan saina koya maki hankali".

Nandai su mama sukaita bata hak'uri sannan kowa ya watse,

Tin daga wannan lkc saudat bata sake shigowa side d'in Ammi ba.

A y'an kwanakinda fati tai a gidan kuwa su HUDAYYA sunsami y'anci sunji kansu tabbas su yayane ba bayi ba,

Tinda tazo itace kemasu girki hadda wonda suke tafiya school dashi sannan bacci kullum cikin nishad'i sukeyinsa, kayansu dasukai datti da bedsheets d'insu dika ta tattara tawonke tareda taimakawar y'an aikinsu mama,.

Washe gari kuma ta daukesu taje dasu Super market sukayo siyayya hadda kayan sakawa dasu sweet da chocolate dan rabonsu dasuci chocolate tin kan Ammin su takwonta ciwo,.

Takuma siyomasu tirarika masu dadin gaske da tsada dakuma mayuka kala kala, a ranar ne tafad'a masu tazone ta dauki Ammin su za'a kaita babbar hospital dake k'asar Egypt,.

Nanfa suka fara mata kuka akan ta tafi dasu suma idan tabarsu momy zatacigaba da wohalardasu ne, hak'uri tadinga basu sbd sai kuka suke wiwiwi akan saita tafi dasu,

Saida tamasu alk'awarin zata dawo ta daukesu tamaidasu gidanta sannanfa suka kwontarda hankalinsu, nan taje tayiwa su baba Alhj. Magana akan zata dauki y'ar uwarta sukaita babban asibiti,.

Basumata musu ba kuwa sukai mata fatan alkhairi sannan baba Alhj. yabata kudi naira dubu dari uku da hamsin yace susiyi magani,

Gdy tamasa sosai sannan takoma.

Washe gari kuwa tin 6am dot babie da Abbu dasu mama dasu munawara dasu HUDAYYA sukamasu rakiya izuwa airport, lkcn da jirginsu zai daga kuwa su HUDAYYA kuka suka dingayi ssi kamar ransu zai fita sunajin kewar mahaifiyarsu naratsasu,.

Bayan jirginsu yadaga sannan sukuma suka juyo suka dawo gida,

_____________________
Tafiyar farida tazamewa saudat tamkar bushara aka mata da aljannah, yanzu sai damawa take yanda takeso,

Su HUDAYYA kuwa tini suka koma y'ar gidan jiya yanzuma saiyafi na da d'in,.


**** ****

Haka sukaci gaba da rayuwa acikin matsi da takura dakuma k'uncin rayuwa, rayuwa wacca take a cike da k'unci ita sukeyi acikin gidan,

Rashin kulawar mahaifiyarsu agaresu tasa sundawo marayu waenda suka rasa uwa dakuma uba,.

Mahaifinsu kuma kasancewarsa ba mazauni gida ba yasa bakoda yaushe suke ganinsa ba, koma yana gidan baruwanshi dasu danko gaidashi sukai baya amsawa,

Idan sukamata lefi kuwa haka zata kwashe k'arya da gsky ta fad'a masa yasaka belt yabulalesu tass,.

Izuwa yanzu sunfara sabawa da wohalar momy da aikin gida dakuma cutardasu da take, abun yanzu yafara bin jikinsu sundaina damuwa da tarin aikace aikacenda sukeyi a gidan...

#/Vote
#/Share
#/Comment
#/AUFANA for life
_*HABIBI DA'IMAN*_
_*BY~AUFANA*_
_wattpad@Aufana8183_

_*Intelligent writer's association*_

_*Page 11~12*_

_*Bismillahir rahmanir rahim*_

Momy saudat cin karenta take ba babbaka acikin gidan, sai yanda takeso takeyi da dukiyar Abban su HUDAYYA,.

Kwanan nan ta tura aka siyomata motar 6 millions Naira, shi kansa ma mallakin dukiyar baya hawan motan million shida,.

Dik motocinsa bawacca takai million shida amma ita gashi tasiya kuma bazai tab'a iya mata fad'a ko musu ba,

Dik abunda tace angama nantake yake biya mata buk'atarta,.

Su HUDAYYA kuwa sunzama y'an kallo yanzu hatta school piece d'insu babie ne ke biya komai shike masu,

Hajiya maryam mama kuwa tazamemasu tamkar uwa, dik wani abu da uwa keyi itace take masu shi.

***** *****

*BAYAN WASU SHEKARU MASU TSAYI......*

Lokaci yatafi shekaru masu yawa sun shud'e yayinda abubuwa da dama suka faru kuma suka shud'e,.

Sakkowar jirginsu kenan mai suna mangal airline daga k'asar Italy izuwa garin Abuja gari mai tarin albarka da ni'imomi.

Kyawawan zaratan samari ne naga suna fitowa daga cikin jirgin bayan da mutane suka gama fitowa,

Kyawawa ne nagaske ajin farko nasahum kyawawa.

Cikakkun jinin fulani y'an asalin k'asar kebbi, kamarsu iri d'aya komai nasu iri d'aya ne zamaka dauka dik mutum d'aya ne idan kana kallonsu sbd tsananin kamanninsu kasancewar su tagwayen maza,

Farare ne tass masu matsakaicin tsayi, su ba masu tsayi bane kuma ba gajejjeru bane,.

Ma'abota tarin suma wacca take a cike bak'a wulik dakuma saje wanda yayiwa fuskokinsu kyau, fuskarsu mai d'an tsayice ba faffad'a bace wacca take dauke da doogon hanci da fararan idanuwa.

Komai nasu is accurate, from skin color to foot nasu, eye balls nasu is like paper's, farare ne tass.

Lips nasu is pink color and sunada thick eye lashes and black eye's da beautiful set of teeths nasu, comai nasu dai is so acurrent kyawawane nagaske,.

Ahankali suke sakkowa daga kan step d'in jirgin suna murmushi, sanye suke da galleliyar shadda fara tass gizna,

K'afafuwansu kuma sanye suke da takalma Brian kirar k'asar Italy black color, kawunansu kuma sanye suke da hula k'ube black color,

Tsintsiyar hannayensu kuma sanye take da watch kirar Company Rano, sai yatsunsu nakusa da karshe dake dauke da ring silver color na azirfa.

Atakaice dai sun had'u matuka daka gansu kasan suna hutawa sunajin dadinsu.

Bayan sun sakko daga jirgin suka fito daga harabar filin jirgin izuwa gunda mutane ke zuwa tarban y'an uwansu,

Waige waige suka farayi domin hango waenda sukazo tarbansu,

Can sainaga d'ayan yayi murmushi yace "HANASH ga bro....can tareda matar yaya" yafada tareda nunamasa su da yatsa.

Shima wanda aka kira da HANASH murmushi yai sannan suka woce izuwa gunsu,.

Cikin farincikin ganin juna sukaje suka rungume wanda suka kira da bro... yana fad'in "welcome back, welcome back y'an uwana ina maku barka da dawowa gida lfy".

Cikin farinciki suna dariya d'ayan yace "muna matuk'ar gdy big bro..." sannan yakalli wacca ke gefensu yace "matar yaya ina matuk'ar kewar girkinki ina fatar yau zaki cikaman cikina".

Murmushi matar tai sannan tace "karka damu HINASH yau namaka abincinda kafiso" yai dariya yace "to ngd sosai matar yaya",

Daganan suka shiga wata galleliyar mota bak'a wulik sai shining take bayan ansaka kayansu sannan suka fice,

Almost 30mnts suka dauka suna tafiya kafin su isa ga wani tamfatsetsen gida mai kama dana k'asar turai, tindaga wojen gidan kasan naira tana aiki,

Bayan gate ya wangare ne suka shiga sannan sukai parking a gunda aka tanadar domin ajiye motoci, anan ma wasu galla gallan motoci ne a ajiye different color's.

Suna fitowa kai tsaye suka woce izuwa cikin gidan,

Cikin sallama suka shiga saiga wata kyakkyawar mace dawoni namiji waenda suka tabbatarmin da iyayensu ne, saikuma wata kyakkyawar yarinya wacca bataza woce 16yrs ba a duniya daga gefenta kuma kyawawan yarane guda biyu mace da namiji,

Cikin fara'a suka kariso acikin katafaren parlon wanda yake cike da kayan alfarma, kyakkyawar matarce tafara magana,

"lale marhaban da yarana abun alfaharina, lale lale sannunku da dawowa kasarku ta haihuwa" cikin farinciki sukaje suka rungumeta HINASH nafadin.

"My mami i miss u so so much Wlh, munyi missing dinki mamin mu" d'an bubbuga bayansu tai alamar tausayi sannan suka d'ago.

Namijin dake gefene yace "Uhm yauko ina ganin bambamci a fili bako a boye ba" yai maganar yana kallon woni wojen,

Dariya sukai sannan sukaje suka rungumesa suna fad'in "dadyn mu munyi missing naka sosai" shima dariyar yai yana shafa bayansu.

Yaran dake daga gefe suma sukazo suka rungumesu wacca take babbar tace "my brother's nayi missing naku ssi, sannu ku da dawowa gida lfy".

HINASH ne yace "me too Lil sis, yh karatu inafatar kina mayarda hankali ssi" cikin murmushi tace eh sannan yaduka yad'auki d'aya daga cikin yaran wacca take mace kasancewar HANASH yad'auki d'ayan wanda yake namiji yace,

"Umm my aami yh cice yh school" yai maganar kamar yanda babyn keyi, dariya tai tana tsotsan alawarta tace "fine baby" dan ita yanda ake kiranta baby itama haka take kiran kowa,.

Daganan sukaje suka zauna aka sake gaisawa tareda kara masu barka da dawowa.

Basu wani dade dazamaba mamin su tace suje suyi wonka sufito ayi launch nan suka tashi suka shiga ciki bayan ankai masu kayansu,.

Wonka sukai suka sauya kaya sannan suka fito, daganan suka woce dining area domin gabatar launch d'in,

Cin abincin suke kuma suna fira, bayan sungama sannan suka dawo parlor akacigaba dashan firar.

_____________________


HINASH da HANASH da HISHAM da HANIFA yayan mami Aysha ne hussainar barkindo mahaifinsu HUDAYYA,

Aikine yakawo mijin mami Abuja har yai gidan kansa kasancewar shi likita ne, bayan sun kammala secondary school ne yakaisu k'asar Italy karatu lokacin HISHAM har yai aure da yaro d'aya Abdul'jalal dakuma matarsa Bilkisu,.

Hisham barrister ne wato lauya mai zaman kansa, bayan billy ta yaye Abdul tasake haifar Ameesha inda suke kiranta da aami.

To yanzu kuma su HINASH sun kammala karatunsu na matakin degree sundawo gida,

_____________________

Tubarakallah masha Allah nafurta lokacinda nai tozali da triple d'in Ammin su, sun girma ssi girma yazomasu yanzu,

Dik wonda yasan su HUDAYYA a shekara biyar zuwa shida dasuka shud'e yagansu a yanzu to sam bazai tab'a ganesuba sbd girmanda sukai.

Izuwa yanzu humaida takammala secondary school hunayya na ss3 sai HUDAYYA da hamida suna ss2,

Tsintsar kyansu da wohala ta b'oye yanzu yabayyana sbd lokacin bayyanarsa yayi, dika kamanninsu d'aya amma HUDAYYA

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login