Showing 3001 words to 6000 words out of 23100 words

Chapter 2 - HABIBI DAIMAN Compelet Hausa Novels BY AUFANA.doc

tsafensa da tsibbace tsibbacensa har saida barkind'o yakawo kansa izuwa ga saudat yace yana sonta...

#/Vote
#/Share
#/Comment
#/AUFANA for life
[8/16, 9:49 AM] AUFANA4REAL

_*BY~AUFANA*_
_wattpad@Aufana8183_

_*Intelligent writer's association*_

_*Page 5~6*_

_*Bismillahir rahmanir rahim*_

Murna da farinciki ne suka mamaye zuciyar saudat nantake tai na'am ta karbi soyayyarsa,.

Acikin kwanakinda basufi biyar ba akai baiko tareda sadaki dakuma saka ranar biki,

Kwatsam barkind'o yajewa iyayensa da maganar zai sake aure na biyu, mahaifiyarsa hawansa tai da masifa akan bata aminceba,.

Mahaifinsa kam sam barka yamasa tareda masa kyakkyawar addu'ar Allah yabashi ikon yin adalci atsakanin matansa,.

Hakama matarsa farida kwatsam taji zancen aurensa agunsu maryam da Rukayya daga baya shi yafad'amata dakansa,

Dikda taji ciwo takuma ji zafi da kishi amma haka tajure a fili tanuna kamar abun baidameta ba nan tamasa kyakkyawar addu'ar Allah yatayashi riko yakuma bashi ikon yin adalci a tsakaninsu,

Abun yabashi mamaki sbd baiyi tsammanin hakan daga gareta ba, dikda koda ta tada hankalinta hakan bazai hanasa yin auren ba amma dai a zuciyarsa yanajin ba dad'i kuma yanajin kamar baimata adalci ba,.

Acikin k'ank'anen lokaci akai bikin Barkind'o da saudat aka d'akko amarya daga garin legos aka kawota kebbi state,.

Iya kokari farida tayi kokari sosai ta danne kishinta ta karb'i saudat hanu bibbiyu takuma d'auketa tamkar kanwarta,
Hakama su maryam sai tsokanarta suke suna mata wasan kannen miji,.

Saidai ita saudat d'in da shirinta tazo dan batafi sati d'aya ba kacal tafara nuna halinta, tin bayan wannan sati d'ayan komai yafara sauyawa,.

Watan saudat goma cif a gidan barkind'o tahaihu inda tahaifi twin's maza zallah, hmm wannan haihuwar tazama tamkar itace haihuwa ta farko agun barkind'o,.

Hakama mahaifinta malam haliru yai murna sosai da wannan haihuwar, hakama su abba moallayid'i da hajiyarsu sunyi farinciki sosai,.

Agun farida kuwa hmm ba'acewa komai dan tinda aka haihu saudat da y'an uwanta dasuka tare a gidan kullum cikin yimata arashi da gori suke bama a b'oye ba a fili,

Itakuwa ko kallonsu batayi bare ma tadamu da abunda suke mata,.

Ranar suna akasha shagali da bidiri, farida ma y'an uwanta sunzo gakuma kyawawan yaranta fulani sak masu kama da mahaifiyarsu,.

Bayan biki kowa ya watse akabarta da wata tsohuwa dakuma nanny's masu tayata raino wai ita bazata iya kula dasu ita kadaiba,.

Itadai farida dik abunda ake kallo kawai take binsu dashi.

Twin's nada shekara d'aya da wata biyar farida tasake haihuwa inda tahaifi y'a mace ranar suna aka sakamata *HUDAYYA*, bayan haihuwar hudayya da wata hud'u kacal saudat tasake haifar y'a mace mai suna HAMIDA,.

Bayan sun yayesu kuma suka sake haihuwa inda farida tahaifi HUMAIRA saudat kuma tahaifi Humaid,

Daga nan kuma bawacca tasake haihuwa har izuwa yanzu,.

Izuwa yanzu maryam matar Ahmad ta haifi y'aya shida, hassan da hussain sai Amira, Amrah, Ammar sai autansu Aryan,.

Rukayya kuma tana y'aya bakwai, Muhammad Affan kenan sai mas'uda, mubashir, munawara, muzammil, mudasir, sai maryam wacca taci sunan Momy maryam matar Ahmad kamar yanda yaran ke kiranta.

Rukayya suna kiranta da Ummi, maryam kuma mama, farida Ammi, saudat kuma momy, sai Ahmad Abbu Abubakar kuma babie sai barkind'o Abba, moallayid'i kakansu kuma baba Alhj. sai khadija kakarsu hajiya,.


Dik tsawon waennan shekarun da aka kwashe farida tayisu ne atakure dikda barkind'o yana matuk'ar k'aunar yayansa kuma yana kokarin kula da yayansa dikansu, sam baya nuna bambanci a tsakaninsu amma agun farida yana nuna bambanci sosai akan mu'amalarsu ta aure dan gsky yafi nuna kulawarsa gun saudat.

Dikda haka ita saudat d'in batajin dad'i sbd tafison barkind'o yazama nata mallakinta ita kad'ai, hakan yasa take shigewa farida hanci domin tabiyemata itakuma saitai amfani da damar ta tinzira barkind'o yasaki farida,.

Saidai farida mutum ce mai hak'uri da juriya, dik abunda saudat kemata sam bata kulata, hakan kuwa bak'aramin b'atawa saudat rai yakeba sbd batada wani buri bayan taga bayan farida da y'ayanta,.


Ganin dai abun yak'i ci yakuma ki cinyewa hakan yasa tasami mahaifinta tafad'a masa damuwarta, murmushi yai sannan yace ta kwantarda hankalinta shi da yayiwa wasu magani suka mallake mijinsu suka rabasa da iyalinsa da iyayensa da danginsa bare kuma y'ar sa,.

Aikuwa cikin k'ank'anen lokaci ya aiwatar da mummunan aiki akan farida da barkind'o,

Wasa wasa farida tafara rashin lfy tafara ciwo kullum abu sai cigaba yake amma barkind'o ko kallonta bayayi bare har yai batun kaita asibiti,

Yayansa kuma dayake matuk'ar so yanzu ji yake yatsanesu bama yason ganinsu.

Burin saudat yakusa cika dan yanzu barin farida gidan kad'ai yarage burinta yacika,


Wasa wasa ciwon farida har yakaita kwonce, koda y'an uwanta suka sami labari sukazo tini komai ya lallace don hartakaiga ko magana bata iyayi saidai ta rubuta,.

Cikin tsintsar b'acin rai suka sami mahaifin barkind'o Alhj. Moallayid'i suka masa maganar rashin lafiyar farida,

Abba yai matuk'ar mamaki dan sam baisan farida batada lfy ba, nantake kuwa yakira barkind'o yadinga masa fad'a,

Cikin sauri yasaka aka d'auketa aka kaita asibiti, iya kokari likitoci sunyi kokari amma har suka gama bincikensu basu gano ainahin abunda ke damunta ba, haka aka kashe kud'i aka kwashe watanni ana kula daita daga k'arshe dai aka d'akko ta aka dawo daita gida tareda nurse's har uku waenda zasu dinga kula daita,.


A yanzu komai yak'ara tab'arb'arewa dan yanzu farida sai ankwantar sai an tayar, idan aka mata magana da ido take bada amsa,

Maryam da rukayya harma dasu abba moallayid'i sunji bak'in cikin da wannan ciwon na farida sbd farida mutum ce mai hankali tanada dad'in zama sosai,

Maryam tace dama saudat ce Allah yadorawa wannan ciwon sbd yanzu tasami yanda takeso, dik abunda tace shi akeyi acikin gidan harma a b'angarensu maryam dan datacewa barkind'o abu kaza takeso shikuwa zai kira su Ahmad yasanar masu, dole sumasa biyayya suyi wannan abun,.


A yanzu tamamaye gidan gaba d'aya sai abunda tace akeyi dan yanzu harsu Ahmad mulkinsu take, tamayarda yayan farida tamkar bayi dikta kori y'an aikinsu gaba d'aya waisu HUDAYYA ne zasu cigaba da aikin,

Dikda kuwa tasan k'arfinsu bai kawoba sbd dika dika humaida dake babba shekaranta 13 ne hunayya kuma 11 sai HUDAYYA 9 sai autarsu kuma 4,.

Barkind'o kuma tsakaninsa da farida da yayansa saidai kallo basa ga maciji, tin lokacinda tafara ciwon yadaina shiga d'akinta su HUDAYYA kuma tsakaninsa dasu sai dai kallo,.

Saidai wani ikon ubangiji dik halayyar saudat acikin y'ayanta bawanda yadakko, suna matuk'ar k'aunar y'an uwansu waenda suke uba d'aya dakuma sauran y'an uwansu nacikin gidan,

Allah yahada kawunan yaran sosai suna matuk'ar k'aunar junansu, sam basa k'aunar abunda zai cutarda d'aya daga cikinsu, shys dik abunda momy saudat keyiwa su HUDAYYA hamida sam batajin dad'i kawai dai dan ba yanda zatayi ne, hamida itace sa'an HUDAYYA 9yrs,.

To reader's wannan kenan

**** ****

*CIGABAN LABARI*

6am dot alarm d'inda humaida tasaka yatadasu, cikin yanayin rashin isasshen bacci suka tashi,

Kitchen suka woce kai tsaye domin fara had'a breakfast, saida suka kammala had'a break sukai abincinda zasu tafi dashi school da kannensu sannan suka koma d'aki,

Suna shiga kai tsaye sukai wonka tareda d'auro alwala, bayan sunsaka uniforms sannan sukai sallar asuba,

Bayan sungama sannan suka kammala shirin tafiya School, atare suka fito sukaje sukayiwa momy barka da kwana sannan suka woce gun mahaifiyarsu.

Cikin sallama da fara'a suka shiga koda suka shiga sai suka tadda nurse's masu kula da ita sungama tsabtaceta sun sauya mata kaya,

Amsa sallamarsu nurse sofiyya tai cikin fara'a da murmushi tace "a,a triples har kun fito" humaida tace "Eh aunty sofiyya, ya Ammin mu?".

Cikin sakin fuska tace "Ammin ku Alhmdllh gatanan yauma taci break sosai ba kamar kwanan baya ba",

K'arisawa sukai suka zauna kusa daita HUDAYYA takamo hanunta tasakada da nata tana murmushi tace,

"Ammin mu nobald'e, no b'andu, Allah hwainonmo Ammi amin" ji tai tamatsa hanunta kan nata tareda lumshe idanuwanta sannan tabud'e su fuskarta nad'an bayyanarda murmushi, hakan ya tabbatar mata da ta amsa kenan,.

Humaida itama sakad'a hanunta tai acikin nata cikin murmushi tace "Ammin mu onyallijam mo, no b'andu, Allah hwainonmo anani" itama saitaji tamatsa hanunta alamar ta amsa,

Hunayya kuwa kwantarda kanta tai akan shoulder d'inta tana murmushi tace "Allah hwainonmo ammi amin" su HUDAYYA suka amsa da ameen,.

Humaira autarsu ce tashigo itama cikin uniform tana magana acikin tsamin bakinta "Anci umaida Mama tace kuzo muwuce school bose tazo" kasancewar ita humaira tinda ciwon yakama farida maryam ta d'auketa tamayar daita gunta shys ita ba'anan part d'insu take ba,.

Kallonta Ammi tadingayi hakan yasa humaida tamatso humairan kusa daita, kallonta tadingayi fara'a na bayyana a fuskarta.

Ganin zasuyi letti yasa suka masu sallama suka fice,

Koda sukaje tini sauran kowa ya shirya school bose d'insu kuma tini tazo tana jiransu danhaka sukai sallama suka fice..




#/Vote
#/Share
#/Comment
#/AUFANA for life
[8/16, 9:49 AM] AUFANA4REAL
_*BY~AUFANA*_
_wattpad@Aufana8183_
_*Intelligent writer's association*_
_*Page 7~8*_

_*Bismillahir rahmanir rahim*_
BASAURA INSTITUTE OF COMPREHENSIVE EDUCATION--- B.I.C.E, sunanda naga anrubuta kenan akan tamfatsetsen ginin gate d'in school d'in lokacinda school bose d'insu tak'ariso,.

Tana isowa ta tsaya suka bud'e murfin motar suka fara fitowa da d'addaya,

Dik tarin student's da teacher's d'inda ke harabar school d'in matukar ahalin gidan moallayid'i suka iso to tabbas sai hankalin kowa yadawo kansu sbd yawansu da had'uwarsu da tsarinsu.

Dikda yawansu amma hakan baihana komai nasu yazama iri d'aya ba, tindaga kan uniforms, takalma, school bag's, food flask kai harma da sock's d'insu dik iri d'aya ne,.

Hakan yasa suke matuk'ar burge mutane dikda ita kanta school d'in ta yayan manya ce kuma dik yaronda kagani a school d'in to mahaifinshi wani shege ne a gomnati kokuma hanshak'in d'an kasuwa,

Bayan sungama fitowa sai driver d'in yaja motar yawuce abunsa har anjima kuma yasake dawowa yad'aukesu domin maidasu gida,


Manya daga cikinsu ne suka rik'a hanun k'ananan cikinsu sannan suka shiga ciki,.

Humaida da Affan, hassan hussaina dik class d'insu d'aya primary 5 wanda kuma shine ajin karshe a section d'in primary,

Sai Hunayya, hassan da hussain, mas'uda, Amira, mubashir kuma class d'insu d'aya primary 4, HUDAYYA da hamida, Amrah, munawara, muzammil class d'insu d'aya primary 4,.

Sai Ammar da mudasir primary 2, Humaira da humaid da Ummi wato maryam mai sunan mama maryam kenan sai Aryan sukuma suna Nursery 3.

Saida su humaida suka damk'a su humaira a hanun teacher's d'inda ke kula dasu sannan suka woce nasu class d'insu,

Su HUDAYYA kuwa tini suka shige nasu class.

Basu wani jima da shiga class ba teacher d'insu na maths yashigo, ahankali yafara masu lesson, HUDAYYA bata ankaraba kawai taga tafara gyangyad'i,.

Tanaso tacigaba da sauraron teacher d'in amma bacci yahanata aikuwa kankace me sai kawai ta konta kan tables d'insu,.

Koda hamida ta ankara sai kawai taganta kwonce tana bacci, tsoro da tausayin y'ar uwar tata ne suka mamayeta sbd tasan jiya basuyi bacci kirki ba,

Gakuma wannan malamin nasu sam bashida tausayi dokarsa ce ba'a bacci idan yana koyarwa, dik wanda yakama kuwa yana bacci to saiyamasa hukunci mai tsauri,

Hamida tanaso ta tada HUDAYYA amma tana tsoro kar malamin yaganta itama yahukuntata.

Aikuwa wa bakin boka koda ta ankara har yahango HUDAYYA a kwonce,

Cikin tsintsar b'acin rai da murtuk'ewar fuska yaje gunta yai tsaye, nantake kallo yakoma gunta,

Saida yai y'an sakonni sannan yatadata, cikin yanayin bacci ta tashi tana mitsirtsike idanuwana,.

Koda ta bude idanuwanta saitagansa tsaye a gefenta aikuwa dasauri tadawo hayyacinta tareda mikewa tsaye dasauri cikin tsintsar razana,


Fuskarsa sam babu annuri yajuya izuwa gaban allo ya??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????na fad'in "HUDAYYA come out and kneel down" jiki na b'ari sbd sanin halinsa ta tashi tafita woje,.

Saida yagama koyarwarsa sannan yakoma kanta, wata k'atuwar bulala ce yasaka yafara dukanta daita,

Kuka tafara tana bashi hakuri "am sorry Sir please, I swear i will never do it again, am sorry please" baiko saurareta ba saida yamata iya adadinda yaga dama sannan yakyaleta,.

Kuka take sosai kamar ranta zai fita sbd zafin dukan.

Yana fita hamida dasu Amra sukazo suna kuka sbd tausayin y'ar uwar tasu suka kamata suka koma cikin class.

Rarrashinta suka shiga yi amma takasa daina kukan hakan yasa suma suka kasa dainawa,

Har aka tashi daga school HUDAYYA bata wayeba bata saki jikinta ba kwallah kuwa har yanzu zuba suke daga idanuwanta, idanuwanta dik sun kukkumbura sunyi zajir doogon hancinnan nata irin na fulani dik yai zajir sbd kuka.

Hamida ce tarik'a hanunta munawara tadakko mata jakarta Amra kuma tariko food flask d'inda suka fito,

Gunda suka saba zamane domin jiran zowan driver d'insu can sukeje suka zauna, saida su humaida sukaje suka dakko su humaira sannan sukazo suka taddasu anan,.

Koda sukagansu dikansu ba wanda yake acikin walwala danhaka suka shiga tambayarsu abunda ke garuwa,

Amira ce tafadamasu dik abunda yafaru, hunayya ce tazo tarungume HUDAYYA tana rarrashinta,

Humaida ma rarrashin nata take tana bata hkri, dakyar suka samu tadaina kukan amma sai sauke ajiyan zuciya take time by time sbd HUDAYYA akwoi zuciya kunsan fulani pa hhhh Lol,.


Basu jimaba anan driver d'insu yazo ya daukesu suka woce izuwa gida.


Koda suka isa gida saisuka tadda baba Alhj. yai bak'i abokan kasuwancinsa ne sukazo daga kasar DUBAI,.

Gate man ya wangare masu kofa driver yashiga dasu ciki, bayan yai parking sannan suka fito shikuma yaje ya ajiye motar gunda aka tanadar domin ajiye motoci,

Kowa part d'insu yanufa su HUDAYYA ma part d'insu suka wuce,.

Cikin sallama suka shigo babban parlon gidan anan suka tadda momy dawasu k'awayenta, ko kallonsu basuyiba bare su amsa masu sallamar,

Cikin ladabi suka d'an risina suka gaidasu kamar yanda tace dik suka sake gaidata batareda sun risina ba saitaci kanen ubansu, cikin yatsinar fuska kamar bazasu amsa ba suka amsa masu, itakuwa gogar ko kallonsu bataiba,

Batareda sunjira komaiba dasauri sbd gudun kuma ace sunyi wani lefin sukai saurin shigewa ciki.

Bedroom d'insu suka woce kai tsaye, uniforms d'insu suka cire sannan sukai wonka suka sauya kaya sannan sukai sallar azahar,
Bayan sungama sannan suka woce gun mahaifiyarsu,.

Koda suka shiga sai suka tadda tai bacci aunty sofiyya ce kawai suka tadda tana share dakin, ganin mahaifiyarsu na bacci yasa suka fito,

Kai tsaye kitchen suka nufa suka fara aikinda yazamemasu jiki, HUDAYYA da hunayya ne sukace sufa yunwa sukeji wlh bazasu iyayin woni aikiba har saisunci abinci gashi itakuwa momy ko indomie bata dafaba sbd tsabar mugunta,.

Indomie suka dakko kwaya biyu suka fara dafawa sannan suka fara d'ora girkin dare.

Bayan indomie d'insu ta nuna sukaci sannan suka cigaba da aikace aikacensu cikin nutsuwa,

Koda su munawara sukazo domin suwuce islamiyya saisuka tadda basu kammala aikiba donhaka suka fice kada suyi letti adakesu,

Sai kusan 5pm sannan suka kammala shima dansuyita yin sauri ne sharp sharp suka gama sannan sukaje sukayi shirin islamiyya,.

Bayan sungama sannan suka fito domin ficewa cikin sauri sbd sunyi letti sosai, suna fitowa saiga momy, wani mugun kallo tabisu dashi kafin tace,

"Wato yanzu har kunada ikonda zaku fita batareda kun sanardani ba ko, eh lallai kun girma wuyanku ya'isa yanka" dasauri hunayya tace "baaa...bahaka bane momy islamiyya zamu gashi munyi letti sosai",

Tsawa tadaka mata tareda fad'in "rufeman yagaggen bakinnan naki ko yanzu nabigeshi wlh, wazaku nunawa islamiyya angaya maku ni banje islamiyyar bane dahar zaku wani ce wai islamiyya zaku, sannu malamai hafizai",.

Shuru sukai suka zubamata ido suna kallonta, saida tagama masifarta sannan tace "Wlh kuka kuskura kuka Kara 15mnts bayan antadaku saina gutsure maku suma namaidaku maza" arazane kuma a tsorace suka amsa da,

"tott...to momy" sannan sukai saurin ficewa,

Suna fitowa harabar gidan saiga babie ( abubakar kenan) yadawo daga office, cikin ladabi sukamasa sannu da zuwa ya amsa, mamaki ne yakamasa ganin har 5:15pm amma sai yanzu ne zasu tafi islamiyya bayan yasan tin 3pm suke tafiya,

Cikin mamaki yace "sai yanzu zaku tafi islamiyya? Meya tsaidaku har kukakai wannan lkc" humaida ce tai saurin bashi amsa,

"Wlh babie aikine yamana yawa shys mukai letti" shuruu yai baisake cewa komaiba yafice ganin haka yasa suma sukai saurin ficewa,

Kasancewar islamiyyar a bakin layinsu take shys basuwani dadeba suka isa,

Dasuka shiga class ma kowaccensu saida malamin su yatambayeta akan abunda yahanata zowa dawuri, sam basu saba da k'arya ba kuma basuma iyata ba shys komai aka tambayesu gsky suke fad'a,.


Cikin sa'a kuwa bawanda aka doka daga cikinsu saidai basu sami sun biya karatunsu ba kuma sauran maddodinda akeyi dik ba'ayisu dasuba madda d'aya kacal akai dasu,.


Around 6pm dot aka tadasu daga islamiyya suka fito, abunka da yara koda suka fito sai suka tadda munawara na tikan dambe dawasu yara maza biyu y'an class d'insu hunayya,.

Hakan yasa sukaje sbd ganin y'ar uwarsu ce ake fad'an daita, sunjima sosai kamin malamansu sukashe fad'an sannan suka kama hanyar zuwa gida,.


6:50 suka isa gida, a part d'in hajiya kaka suka woce suna bada ba'asin fad'a, nan dai iyayensu suka kashe fad'an tareda masu kashedin karsu sake yin fad'a a school,
Bayan angama komai sannan kowa yawoce sashensu,.

Suna isa bedroom d'insu suka shige sukai sallah sannan suka shiga bedroom d'in Ammin su domin dubata, sunjima sosai anan daga bisani suka fito sukaje domin su wonke uniforms d'insu,.

Suna cikin yin wonkin saiga momy tazo, dasauri suka mike a tsaye suduka sbd sunsan ba alkhairi ne ke kawota gunsu ba,

Huci take tamkar kumurcin maciji fuskarta ba annuri tamkar bata taba sanin miye dry ba a duniya, cikin tsintsar masifa tace,

"Menace maku dazakuje islamiyya?" sai sukai shuru suna kallon juna, cikin dagawar murya da tsintsar masifa tasake cewa "banace karku kuskura kuk'ara koda minti d'aya ba idan antadaku ku dawo gida ba, ko kun dauka bansan lokacinda ake tadaku bane, to kusani wollahi tinda kuka sab'a umarnina nima saina sab'a maku, maza ku ajiye wonkin nan kuwuce muje",.

Jiki na b'ari sukai saurin ajiye wonkin suka woce,

A parlor tasakasu kneel down itakuma tashige ciki, kamar 5mnts tadawo d'auke da almakashi a hanunta tana fad'in "badai kun rainani ba ko zanyi maganinku ne wlh sannu ahankali",.

Ja da baya suka farayi cikin tsoro da fargaban rashin sanin mezata aikata masu, tana zowa tafige hularda ke kan HUDAYYA tai facali daita sannan tadamko sumarta da karfi har saida tai k'ara mai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login