Showing 81001 words to 82398 words out of 82398 words
harda hawayen farin cikin ganinsa cikin tsananin farin ciki mara misaltuwa tayi sbd Sam kasa boye farin cikinsa yayi.
Kafin sati biyu dukkanin kuzarinta sun dawo lafiya kalau saidai bata iya komai da sauri ko qarfi Wanda hakan shima ahankali zai dawo.
Washe garin ranarda umma yakurah da ammy suka fada masa samun lafiyarta yatafi wannan karon suhailat qin biyosa tayi sbd ganinta kusa zai hanasu nuna kewar junansu.
Sai dare sosai ya isa Wanda tareda khaleefa dazaije gurin nuratu sukayo tafiyar dole suka sauka masaukinsu kai tsaye sai washe gari suka nufi gidan guraren qarfe goma shima sbd khaleefa daya hanasu tafiya tunda safe.
A babban palo suka tararda su umma da ammy harmada Jakadiya da sabuwar mai rainon abeel suna ganinsa umma tayi murmushi sbd tanajin dadi da farin cikin yanda yake tsananin qaunar rumanah dinsu.
Ammy ma dariyar tayi masa inda aka gabatar musu da abincin breakfast saidai sunyi breakfast already.
Duk yanda yaso ganinta qin barin su kebe umma tayi qarshema anan palo tasa Nana aishat 'yar autarta taje kairawo rumanah din tajima kafin yafito sanyeda dogon hijabi har qasa daya matuqar yimata kyau sbd wannan ne karo na farko daya ganta sanye dashi itama anan din takoya sakashi sai tanajin dadinsa.
Kasa 'dauke mayun idanuwansa akanta yayi musamman yanda ta canza sosai takoma kamar ba rumanarsaba datasha wahalar rayuwa dan lokacin.
Wani irin murmushi yasaki Wanda shikadai yasan yayi abinsa sai ita data gani ta dauke kai tana gaidasu cikin yarensu sbd har gwara khaleefa yafara son koyar yaran Hausa sbd nuratu dayake yawan ziyarta shikuwa haryanxu yakasa koyan komai.
Koyaushe da turanci yake magana dasu umma da alhaji babaye hakama ammy.
Kwanakinsa uku amma Sam umma taqi barinsu kebewa hakan ya matuqar dama lissafinsa shiyasashi tattarawa yakoma gashi ko waya basayi bare yarage zafi.
Koda yadawo suhailat ta lurada bai cikin dadin rai da walwala saidai batai shishigin tambayaba tunda bai shiga haqqintaba.
Bayan sati biyu kai tsaye yakira alhaji babaye yasanardashi yanason rumanah tadawo tunda taji sauqi koda alhaji babayen yayiwa umma magana kai tsaye tace sai wani wata sbd zasuyi walima dakuma 'yan shirye shirye.
Baisoba amma sbd ammy data basa hakuri saiya bari din badan yasoba.
Hidima sosai da gyara irin nasu na asalin 'yan Maiduguri.
Taron biki sosai akayi tamkar yanxune zaa daura mata aure akai walima da yinin biki na alfarma inda ko nanma 'yan jarida basuyi qasa da gwiwaba sunxo ganawa da tsohuwar sarauniyar qasar Ethiopia saidai maheer daya bada gargadi mai qarfi akan karta kuskura barin kowa yadauki hotonta ko fira da ita.
Lokacinda nuratu ta iso gurin bikin sosai sukayi farin cikin ganin juna dakuma auren nuratun da khaleefa keson yi.
Irin gyaran da akai mata da shirin da akai mata ita kanta burge kanta takeyi ga wani irin qamshi daya kama jikinta.
Dukiyarta kai tsaye tace suci gaba da kulawa da ita tabar musu halak malak bata buqatar komai.
Ranarda zasu tafi ammy ce da jakadiya sai umman da matar alhaji babaye da yaransu 'yan mata da nuratu suka rakasu har Libya tareda dukiyar aure mai tarin yawa inda sukai kwana biyu suka juyo suka barota.
Sabuwar rayuwa ta bude a Libya inda nanma ammy wani gyaran ta dora ranarda tacika kwana shida cif aranar aka sai mata ticket ta wuce batareda abeel ba.
Qarfe uku na yamma jirginta ya sauka suhailat ce tazo daukarta sbd ogan na hospital gurin aiki baimasan aranar zata dawoba ammy suhailat kawai tafadawa shiyasa tazo daukarta.
Cikeda farin cikin ganin juna suka rungume juna suhailat na mata sannu da zuwa da cewa,
Where is my abeel?
cikin farin ciki ta amsa tana cewa,
Ammy ce ba ruwana.
Wani gida na daban taga sun nufa Wanda yafi nada girma sosai tun a harabar gidan ta fahimci kowaccensu nada wadataccen gurinta yanxu.
Da gudu su amah suka fito suna mata oyoyo ta riqe hannun fammah data fara mantata tayi kissing goshinta tana cewa,
Famman mum 'dinta.
Babban lafiyayyan qaton palonsu suka shiga nan suhailat ta rakata da luggage dinta har cikin dakinta dake daukeda parlour da two bedrooms aciki ga komai nata is white.
Bayan fitarsu wanka tashiga tana fitowa tayi sallolin dake kanta dasu magrib da akayi tana gamawa ta shirya cikin pencil skinny jean blue daya kama cinyoyinta da White shapeless top sai White club scarf data rufe kanta dashi ta fito fiddo wayarta daga handbag dinta taga misscalls dinsu umma da ammy harma dana nuratu tafara kiransu daya bayan daya tana cikin wayane da ammy suhailat tashigo tana murmushi itama cikin adonta na wani black straight skirt daya fiddota da red chiffon top gashinta daure saidai bata saka hula ba tace,
kiyi sallar ishai kifito muyi dinner already your ango is home.
Murmushi tayi tana cewa,
Ok ganinan zuwa.
Sallar ishai tayi tana gamawa ta gyara scarf dinta tareda fesa turare da humra mai sanyin qamshi ta fesa mouth freshner abakinta ta dauki wayarta ta fito.
Zaune yake kan dining din shidasu amah sai suhailat dake qoqarin zama ta gama zuba nata abincin
Ta bayansa yajiyo wani irin qamshi ya lumshe ido ya bude dan tabbas kodata canza turare kusancinta sanannene a zuciyarsa tana qarasowa gabansa abincin daya saka bakinsa ya sarqesa ya rufe baki yana tari da sauri suhailat tabashi ruwa tana dariya tace,
Easy karka illatamin kanka she's really here ba gixo bane.
Karba yayi yasha yana watsa mata wani kallo yace,
Dake aka hada baki right...
Murmushi tayi tace,
Ba ruwana ammy ce.
Juyowa yayi ya kalli inda take cikin wani irin shauqi da tsananin soyayyarta dake fizgar zuciyarsa duk yunwar dayakeji ta bace.
Ita kuwa abincinta takeci hankali kwance duk da zuciyarta rawa takeyi sbd irin kallonsa datakeji yana yawo ajikinta.
Barin dining din yayi sbd zai iya bada kansa yakoma kan kujerun palon ya zauna yana canxa channel zuwa news duk da dai Sam baimasan meyakeyiba sbd halinda zuciyarsa take ciki.
Bayan sungama Carolina ta tattara gurin suhailat takaisu amah daki sukai duk abinda zasuyi suka kwanta saidata tabbatarda sunyi bacci tafito lokacin ba kowa palon kowa na dakinsa.
Dakin rumanah ta nufa kai tsaye tayi mata saida safe tareda sanarda ita kwana biyu biyu zasu riqa yi tace mata tou.
Tana sane ta sharesa taqi zuwa gurinsa ta tube ta dauko rigar baccinta zata saka saidata daga hannuwanta zata saka taji an zare towel 'dinta da sauri ta juyo Ashe amatse yake da ita tana juyowa sai a jikinsa atare suka sauke ajiyar zuciya yana zare rigar hannunta yayi jifa yana kallon cikin idanuwanta dashi itama take kallo.
Jikin wardrobe ya matseta yana cigaba da kallonta zuciyarsa cikeda wani irin farin ciki ahankali yace,
Wani irin sone zuciyata ke miki ummu-rumanah bulama.
Kunnensa takai bakinta cikin wani irin salo tace,
Irin sonda ummu-rumanah kewa maheer abdulshams..
Wani irin murmushi yasaki tareda hade fuskarsu sbd tsikar jikinsa data tayar masa ya dora bakinsa kan nata yace,
I love you ummu-rumanah bulama.
I love you more maheer abdulshams.
Hade bakinsu yayi suka saki numfashi atare cikin tsananin kewar junansu ya cirata suka isa gadonta ya zura hannu ya kashe wuta.
Washe gari da wuri ya tashi yayi shirin office bayan sun gama lalacewarsu har gurin wanka.
Atare dukkaninsu sukayi breakfast kafin shiya fara fita tukuna yaran sai suhailat data futa qarshe.
Yaso dawowa gida da wuri amma sbd dorarta zaman lafiya da qauna tsakanin iyalinsa yafasa harsaida lokaci yayi yadawo.
A ranarma a dakinta suka bajewarsu saidai duk yanda yaso qin latti saidayayi sosai.
Watanta shida da dawowa tafara laulayin ciki Wanda take samun kulawa sosai daga garesu har Allah yasauketa lafiya tasamu 'yan biyu mace da namiji.
Zaman lafiya kwanciyar hankali tareda aminci da qaunar juna mai cikeda fahimta suke gudanarwa tareda girmama juna.
*_ALHMDLLH nan nakawo qarshen tarayya da yardar Allah masoya ina miqa godia sosai sbd wlh yawanku bazai bari na iya batokuba._*
*_Kusani dai mamuh takuce kuma natane._*
_*idan nayi kuskure kokuma mantuwa ta Kumin uzuri yanayi rubutune Allah yabamu ikon daukar darasin ciki.*_
*_FAHIMTARWA..._*
*_Idan marubuci yayi rubutu za'ace bai San abu ba baiyi bincike akan abu ba amma yaje yarubuta sbd shirme da rashin sanin meye rubutu.._*
*_Tou kuma idan mutum yayi binciken yarubuta yanda abin yazo ace baida ilimi.._*
*_Labarin tarayya yaxone akan tun asalinsu ba musulmai bane akwai kafurci jahilci ataredasu Wanda hakan duk shine silar komai dan haka dole sai an bayyanarda jahilcinsu da kafircinsu ta hanyar sunayensu da ayyukansu yanda labari zai tafi daidai.....ga masu cewa sunayen ciki basu halastaba kenan..._*
*_Masu cewa babu addini,babu riqo da addua da basu komawa Allah ba kuma ta yaya zasuyi hakan bayan anbayyanar dasu marasa sani acikin labarin idan lokacin yi da amfani da hakan yakai ai za'a sakane..._* *_dan Allah muriqa duba asalin tsarinda aka 'doro labari mu riqa binsa daki daki dan sanin abinda zamu riqa cewa._*
*_Nagode Allah yaqara sadamu gaba._*