Showing 33001 words to 36000 words out of 82398 words
tana dan canxa fuska sbd qafafunta dasukai wani iri Sam yanxu bata iya dadewa zaune sai qafafunta su 'dan kumbura.
'Daga qafafunta tayi taji jiri ya 'debeta
Jikinsa tajita ya riqo kafadarta yayi mata wani kallon ciki ciki.
Sunkuyar dakai tayi cikin laushin murya tace,
Yi hkr.
Riqo hannunta yayi cikin nasa dayan hannun kuwa cikin aljihun wandonsa fuskarsa sanyeda shades suka fito jirgin sbd ganin alamar kamar har lokacin jirin bai gama sakintaba.
Daga gidansu suhailat mota tazo daukarsu suna isa gidan nan aka fara hidima da farin cikin ganinsu.
Sosai iyayen suhailat suka tarbi rumanah babu wani damuwar komai.
Daqyar tasake sukaci abinci gaba daya a dining nan takejin su suhailat exam dinsu amah suke jira agama suzo dubiya suma.
Dakin mum din suhailat tayita janta ajiki danta sake jikinta saidai takasa sakewa sosai gashi yafita shida dadyn suhailat har magrib shiru baidawoba.
Ganin har anyi sallar ishai bai dawoba yasa tacire ran komawarsu ranar.
Qarfe tara da rabi yadawo ko shigowa baiyiba dad yabugowa mum din waya yace rumanah tafito sutafi.
Da mamaki tace,
Badai komawaba a Daren nan?
Aa masaukinsa zasu tafi dan gobe flight din qarfe takwas zasubi zuwa labanon akan wani program damukai magana dashi yanxu.
OK tace ahankali jikinta na sanyi sbd hakanan tausayin 'yarta ya shigeta saidai tunda bai wulaqanta musu 'yaba bazasuji zafi akan aurensa da matarsaba.
Cikin murmushi ta tashi ahankali ta nufi wardrobe ta dauko wasu dogayen rigunan Mali masu tsananin kyau guda biyu ta miqa mata daqyar ta karba tana godia suka fito.
#mamuhgee.
[14/07, 00:49] 80k: *_TARAYYA_*
_wattpad@mamuhgee_
_Haske writers associationš”_
*24*
Not edited
Sheraton bamako hotel forth floor room 302 shine dakinsa da ako yaushe yake sauka idan yana qasar.
Babban suite ne dayaji tsari irin na rayuwar dayakeso akoda yaushe.
Zama tayi a darare kan sofa tareda aje handbag dinta tana kallon tsarin dakin.
Tun kafin ya isa yayi musu shopping kayan buqatarsu shiyasa yakalli agogon hannunsa yana 6ata fuska .
Knocking akayi ahankali sbd gudun kar ayi disturbing dinsu
Ga mamakinta ganin tayi ya miqe ya nufi qofar bayan tasan abaya budewa kowa qofa idan kagaji da knocking ne kashigo koka jira amma saigashi yatashi yaje yabude kuma hannu kawai yasa yakarba ya rufe qofar ya aje kan gado yafara 6alle ma6allan rigarsa.
Sauke kai tayi ganin murdadden jikinsa yafara bayyana
Yana gama tubewa ya nufi toilet.
Ya jima yana wanka kafin yafito yabude kayan ya dauki brush da toothpaste yakoma yayo brush yana dawowa ya fitarda turarrukansa da yayi shopping yayi shirin bacci bayan ya fitarda fararen kayan baccin daya siya yasaka ya fidda wayarsa yakira suhailat datun dazu take kiransa.
Miqewa tayi itama tashiga toilet tayo wanka ta fito daureda towel gashinta daure tsakiyar kai sbd karya jiqe gurin wanka.
Duk wani nauyi da kunyar duniya jitake kamar suna kanta sbd mayen kallon daya tsareta dashi tun fitowarta kuma lokacin waya yakeyi da suhailat.
Rigar bacci tagani kan kujerar gaban mirror tadan juyo takallesa ya dauke gira 'daya yana cigaba da wayarsa.
Da mamaki take kallon turaren Prada royal pink for women da shine turarenta,
Ya akayi yasan sunan turaren datake shafawa gashi tamazo da nata suna cikin handbag.
Wanda ya siyo din ta shafa ta dauki rigar tadaga batai mamakin ganin yanayin rigarba datafi kama da babu sbd tun a mineelik da ake sakata sakasu tasaba dasu.
Daga zaunen ya miqa mata hannu na musu tazo ya jawota ya ajeta kan cinyarsa ya zare ribbon 'dinda ke 'daureda gashinta gashin ya zuba yacigaba da wayarsa da suhailat yana cusa hannunsa cikin gashinta zuwa wuyan rigarta.
Cikin nutsuwa suhailat tace,
Zan kiraka gobe insha Allah gud night.
Aje wayar tayi tareda rintse ido da qarfi hawayen dasuka ciko mata suka gangaro kan fuskarta sbd yanayin yanda maganarsa ke fita qasa sosai ta tabbarda akwai abinda yakeyi da matarsa dan mum ta sanarda ita da rumanah yaje.
Share hawayenta tayi tareda miqewa ta nufi 'dakin yaranta takwanta kusada fammah tareda jawota jikinta a hankali tace,
Ya Allah kabani ikon juriya da adauke kai kan abinda bazai shiga haqqinaba nima kodan karna barwa 'yayana abin takaici da kunya.
Rumanah dake lafe jikinsa ta 'dago takalli fuskarta dake kallonta qasa qasa da murya yace,
Kinsa matata ta ajemin waya for the first time banine na aje mata ba.
Wani irin lumshe idanu tayi Wanda yasashi kafeta da ido kafin yakai bakinsa kunnenta qasa qasa yace,
Are you trying to seduce me da wannan idon?
Qanqamesa tayi qarfi ba shiri sbd tsananin kunyar da maganar ta bata ya lumshe ido yana sake shigar da ita jikinsa yace,
Karki damu suhailat is kind hearted ba duka zata hanaki mijintaba.
Miqewa tayi da sauri zata bar jikinsa yasake dawo da ita ta fado masa ya matseta suna kallon juna fuskarsu daf da juna har dogayen hancinsu na gogar juna.
Wani irin murmushi tasakar masa akaro na farko
Bakin dayayi smiling din yakalla kafin yakalli cikin idanuwanta da itama nasa take kallo ya daga mata gira 'daya sai abin yasake sata murmushi
Daqyar ya furta nifa mijin aurene.
Rufe bakinta tayi da sauri sbd wannan karon murmushinta dariya yaso zama takalli cikin idanuwansa dasuka riga suka bayyanarda kasalar dayake ciki murya qasa qasa tace,
Sorry.
Murmushin gefen baki yasaki ahankali tareda 'dan juyar dakai
Cikin shagala da murmushinsa da bata taba ganiba takai hannunta kan kumatunsa ta shafo Tana murmushin dake fitowa tun daga cikin zuciyarta.
Dafe hannunta yayi tareda dora hancinsa kan nata yana kallon cikin idonta ya dora bakinsa kan nata suka lumshe idanuwa atare tareda qara matse junansu musamman ita dataji hannunsa cikin rigarta
Sun jima a sofa suna abubuwansu kafin suka nufi gado dama tun a sofa akayi wurgi da rigar baccin dake jikinta.
Qarfe shida na safe ta fito wanka daureda towel gashinta ya mammanne mata a gefen fuska yana tsiyayar ruwa ko gaban mirror taba isaba ya fito daga toilet din shima yana tsane kansa dake jiqe ya suka tsaya gaban mirror yakalleta ta cikin mirron ta 'dauke kai tana maqala maqala hand dryer datun a jiyan da ita yayo shopping.
Ita tayi drying masa kansa sbd yanda ya zauna ya baice komaiba yasata tasan itace zatayi masa.
Saidaya shirya tsaf kafin tasamu damar shiryawa cikin wani royal blue skinny armani jeans daya matuqar kama hips dinta harzuwa qasanta ya lafe ya matuqar fidda shape dinta sai wata farar Louis Vuitton shapeless chiffon top sai gashinta data saki sbd bayan ta daure ya zare mata band alamar bayason hakan tayi mamakin yanda yasiyo kayan bayan itadai bata taba saka irinsuba saidai batada wani zabi arayuwa sai abinda yace ko ya nuna buqata.
Shima blue armani jean da farar Louis Vuitton wideneck ce ajikinsa sai gashinsa daya saki bai daureba sai qamshin turarukansu dake tashi cikin sanyin AC na dakin.
Breakfast aka kawo shidai black tea da toasted bread kawai yaci itakuma taci fried egg da vegetables sai fresh milk da ammy tasabar mata dasha kullum.
Qarfe bakwai suka fito bayan ta 'daura kimono black akan kayanta wadda ta qarawa shigarta da jikinta kyau suka fito hannunta na cikin nasa.
Babu Wanda yadamu dasu baresu da ko fuska babu daga gurinsa ita kuwa Sam batada damuwa akan duk abinda yanuna.
Mota suka shiga babu 6ata lokaci suka bar bamako sai airport sbd tun jiya sunyi bankwana dasu mum.
A jirgi wannan karon tsuru tayi sbd tsananin ciwo da nauyin da qafafunta suka fara yimata.
Kallo 'daya yayi mata yakalli qafafunta dayaga tana kallo kamar zatayi kuka.
Kallon qafafun yayi dan ta cire qafarta daga loafers din dake qafarta yaga sun 'dan kumbura yadawo da kallonsa kan fuskarta yayi mata kallon mintuna uku kafin ya riqo hannunta batareda yace komaiba.
'Dan sanyi taji sbd kobaiyi mgn ba yanxu tana gane abinda yake nufi wannan sigace ta lallashi yake mata.
Daurewa tayi tasaki jiki duk da vatajin dadin qafafun.
Sai yamma suka sauka direct masaukinsu motar da tazo daukarsu tayi dasu amatuqar gajiye tayi wanka daqyar tayi sallah ko abinci bataciba sai bacci.
Wanka yayi shima yashirya yafice bayan yasa ankawo mata abinci batareda yatasheta daga baccinba.
Sai magrib ta tashi tana ganin abincin tasan bayanan ya fice ta tashi tayo brush tazo tafaracin abincin tana lumshe ido sbd yunwar datake damunta dama.
Saidata qoshi takuna ta tashi tayo alwala tayi sallah tana gamawa tadan zauna tana kallon TV ta nutsu tana sake daukar kalaman turancinda Mr aarib ke koya mata.
Lokaci ta duba ta tashi tayi sallar ishai tana gamawa tayi wanka tayi shirin bacci ta kwanta nan take bacci mai dadi yadauketa.
Koda yadawo tayi nisa a bacci yayi wanka kawai shima ya kwanta tareda kashe wutar dakin ya dora kansa a pillonda kanta yake ya rufe ido shima bacci yayi gaba dashi.
Washe gari bayan yashirya zai fita ya jawota jikinsa yana kallon idonta ya saka mata wayarsa daya a hannu murya qasa yace,
Ammy na nemanki idan takira saiki sanarda ita abinda takeson ji.
Baki tasaki tana kallonsa harya fice yaqi juyowa kar bashi yayi maganarba to ita mezata cewa Ammy? Ko wayarta ma bazata iya dagawaba sbd kunyar rashin komawarsu bare harta iya mata bayani.
Aje wayar tayi tana kallon wayar akai akai hardai takoma tayi baccinta.
Kwanansu biyu kullum yana fita aikin dayazo yi shiyasa ta samu Hutu.
Yauma sai dare yadawo saidai koda yadawo idonta biyu cikin laushin murya tace masa,
Sannu da dawowa.
Aje wayarsa da shopping bags din hannunsa yana kallonta kafin yadawo gabanta yana kallon shigarta ta wata red mini dress dake jikinta ya 'dauke gira daya yace,
Kinason ki lalatawa Ammy yarone shiyasa kikaqi bari akoma.
Zaro ido tayi tareda saurin juya masa baya tana dafe qirjinta da kusan rabinsa yake a bayyane ya zuro fuskarsa ta wuyanta bakinsa a kunnenta yace,
Naga bayan tunshigowata ai.
Da gudu ta bar gurin ya riqo hannunta tareda dawo da ita ya dauketa cak ya nufi toilet.
Ajeta yayi tsakiyar toilet din ya tsareta da ido tasaki boyayyan murmushi sbd tasan manufarsa
Hannu tasa tafara cire ma6allan rigarsa har ta kai qarshe ta zame masa rigar ya shiga cikin bathtub yakwanta cikin ruwan sumi tareda lumshe ido yabude ya miqa mata hannu ahankali tazame rigarta ta kama hannunsa tashiga ruwan ta kwanta saman jikinsa.
Qarfe uku na dare ta farka da ciwon qafa tun tana daurewa harta zame daga jikinsa ta tashi zaune tareda kunna lamp din gefenta ta kalli qafafunta.
Tabasu tayi ta juyo takalli gefensa suka hada ido sbd tun tashinta ya farka.
Hawayen datake riqewane suka gangaro mata ya tashi zaune yana kallon qafafun da kai yayi mata alamar tahowa garesa ta fada jikinsa tareda sakin siririn kuka sbd ciwo suke mata sosai jitake kamar zata gurgunce.
Jin kukanta yakasa tsayawane yasan ciwonne yayi mata yawa yakai hannunsa ahankali yana matsa matasu ahankali
Ta sake shigewa jikinsa tana sauke ajiyar zuciya.
Koda gari ya waye kasa tafiya tayi shine ya dauketa yakaita toilet yakuma dawo da ita wunin ranar kusan shine yakeyi mata komai duk da ya duba qafafun yakira Dr vin yayi magana dashi akan maganinda zai mata sbd ba 6angarensa bane.
Haryasa ankawo masa maganin saiga kiran Dr vin lokacin tana zaune ajikinsa tana bacci shikuma yana duba wasu takardu.
Hello Dr M.A shams I think you should confirm if she's not pregnant first before given her the drugs....
Akaro na farko dayaji zuciyarsa ta girgiza ya qurawa fuskarta ido yaga yanda fatarta take glowing ya daga hannunta yaqurawa tafin hannunta ido take ya rufe ido tareda dafe goshi cikin wani irin yanayi.
Ya jima yana kallonta cikin wani irin yanayi da shikadai yabarwa kansa sani kafin ya dauki na shafawa kawai ta shafa mata kadan ahankali kafin ya tashi da ita rungume ajikinsa ya nufi gadonsu ya kwantar da ita kafin ya zauna bakin gadon tareda rufe ido yana shiga tunani.
Washe gari koda ta tashi taji sauqi sosai saidai kuma yini tayi duk motsinda tayi idonsa nakanta tayi mamaki dukda tasan kallo a gurinsa ba baqon Abu bane agurinta amma na yanxu ya banbanta.
Abinda yafi qara bata mamaki shine yanda yakasa rabuwa da jikinta dole kawai ke tadashi sosai ta lura akwai abinda yake ransa.
Bayan kwana biyu ta warke sosai harya fita da ita sukaje wani babban eatery dakuma shopping sbd ganin zama guri dayane yafi saka qafafun ciwo shiyasa akwanakin kullum da inda suke zuwa musamman beach sbd ta lurada yanason ruwa.
Satinsu biyu cif suka koma Libya.
Da yamma sosai suka iso
Motar dataje daukarsu bata dawo gida direct ba saida suka biya wani babban pharmacy aka siya mata magungunan dabatasan na meyeba kafin suka nufi gida.
Suna isa taji sabon nauyin ammy yarufeta batasan ta yaya zata hada ido dasuba har gwara s salma suna 'dan wasa wani lokacin.
Lura yayi da yanayinta yasaki Murmushin gefen baki kafin yadan ranqwafo yace,
Ina gaida ammynah kafin nashigo anjima.
Yana fadar haka aka bude masa motar yafita batareda yasake waiwayowaba ya nufi sashen sultan jalaluddeen.
Bayansa tabi da kallo tana jinjina alamarinsa kafin aka bude mata ta fito ta nufi hanyar sashen s salma.
Sa'ar dataci ammy bata gurinta nan ta zauna tana gaidata tareda kasa cewa komai duk tsokanarda s salma din ke mata saidai kawai tayi murmushi qarshe dai miqewa tayi ta nufi palonsu.
Da sallama tashiga ammy dake zaune tasaki murmushin murnar ganinta tana cewa,
Munsamu dai yau kundawo.
Sauke kai tayi tana Murmushin dole sbd kunya tace,
Ammy ina wuni?
Murmushi ammyn tayi tace,
Lfy kalau rumanah jeki ki huta nasan agajiye kike idan kinhuta saimu gaisa.
Babu musu ta nufi hanyar dakinta masu aiki biyu suka bita da luggage dinta ammy tabisu da kallo wainda sukaje bada kayaba saigasu da akwati.
Ajiyar zuciya tasauke lokacinda tashiga daki ta zauna sbd Allah yagani taji kunyar ammy tun kafin su dawo.
Wanka tayi tai salloli kafin ta fito ta nufi dakin ammy nan dai suka sake gaisawa ammyn nasake tambayarta jikin mumyn suhailat.
Suna cikin fira sama sama saigashi yashigo babu kunya ya nufi ammyn kai tsaye ya 'dan rankwafa yayi kissing forehead dinta yana cewa,
Ammy barka da hutawa.
Ya zauna kusada ita tareda yiwa rumanah wani irin kallo tayi saurin Sauke kai sbd ganin ammy.
Kasa 6oye mamakinta ammy tayi tace,
Maheer baka taba zuwa dubiya irin wannan ba kokuwa dan kaje da 'yata ne?
Murmushi yayi batareda ya'dago daga duba wayarsaba yace,
Tambayi 'yartaki.
Da sauri rumanah ta miqe ta nufi qofa ta fice tana mamakin iya cabo maganarsa.
Kallon ammy yayi yace,
Gobe insha Allah zan koma.
Kallonsa tayi tace,
Allah yakaimu.
Fira suka dingayi sama sama duk da itace mai maganar iyakacinsa kallo sai daga kai sai sa'a yake bude baki yayi wata maganar.
Da daddare harta kwanta ta tafito taje kicin ta dauko ruwa sbd wani lokacin tana tashi shan ruwan dare.
Kodata dauko ruwan takoma daki kasa bacci tayi ta tashi zaune tareda rufe ido tana kamar daga sama taji qamshinsa acikin dakin ta bude ido da sauri amma babusa ta dafe goshi tareda sake kwantawa ta rufe ido tana fatar bacci ya dauketa.
Daqyar ta samu bacci yadauketa kodata farka da asuba da ciwon kai ta tashi ta lallaba tayo alwala tayi sallah.
Tana gamawa zazzabi ya kwantarda ita agurin ta kwanta ga sanyin AC amma ta kasa tashi.
Jirgin qarfe goma sha biyu zaibi amma tun asuba idonsa biyu yakasa bacci.
Ammy data kwana tunanin basa rumanah yaje da ita kokuwa aa tana gama sallar asuba ta fito ta nufi dakin rumanah dan cewa ta shirya sutafi tare
Tana shiga taganta kwance a inda tayi sallah yanayin yanda ta dunqule gu 'daya ya tabbar matada batajin dadine.
Cikin kulawa ta isa tana kiran sunanta
Ta tashi zaune daqyar tace,
Ammy ina kwana.
Lfy meke damunki?
Babu komai ciwon Kaine kawai.
Fita ammy tayi taje dakinta tadauki wayarta ta danna masa kira kamar bazai daukaba saikuma ya dauka kai tsaye tace,
Kazo yanxu kadubamin ita batada lafiya.
Aje wayar yayi tareda lumshe ido ya bude dan yasan za'a Rina.
Wanka zai shiga amma ya fasa ya mayarda jallabiyarsa ya fita ya nufi palonsu dan har lokacin gari bai gama haskeba.
Koda ya isa palon ammy na tsaye tana jiran shigowarsa palon.
Da qaramar murya yace,
Sabhaul khair ya ammy.
Kai kawai ta daga masa sbd masiffen tashin hankalinda tasamu kanta aciki na fargabar kar ace tunaninta na cikine da rumanah ya tabbata.
Dakinta takoma ta zauna jira ganin yashiga dakin tareda turo qofa.
Zaune take bakin gado tana ganinsa taji idanuwanta sun ciko da hawayen muguwar kewarsa datayi batasan lokacinda ta miqe ta fada jikinsaba ya lumshe ido tareda qara shigarda ita jikinsa.
Jin zafin jikinta yasashi dagota yakalleta cikin wata irin murya yace,
Qafan ne?
Girgiza kai tayi tana kallonsa.
Da gira ya yayi mata tambayar then wat is it.
Zamewa tayi taje bakin gado ta zauna cikin sanyin murya tace,
Ciwon kai.
Zama yayi bakin gadon tareda dago fuskarta yayi kissing bakinta yasake taba jikinta yaji zafin
Baice mata qalaba ya zare rigarsa tareda ajewa ya kwanta kan gadon tareda lumshe fararen idanuwansa
Saidata aje numfashi ahankali kafin ta nufi gadon ta hau tashige jikinsa tareda qanqamesa sukai shiru kowanne najin bugun zuciyar dan uwansa yanaji zafin jikinta na shiga jikinsa ahankali ya saki wata irin boyayyar ajiyar zuciya.
Daga haka baccin dabasuyiba adaren ya daukesu ammy dake zaman jira tashigo dakin tayi saurin juyawa ganin yanda sukai bacci hankali kwance.
Kasa zama tayi ta kasa tsayuwa sbd idan har cikineda rumanah to yazama dole aciresa sbd tsoronta na bata rumanah zata iya haihuwar namiji Wanda hakan shine babbar masifar dazata tono abubuwa ciki harda yanda iyayen rumanah din suka rasu.
#mamuhgee.
[15/07, 02:16] 80k: *_TARAYYA_*
_wattpad@mamuhgee_
_Haske writers associationš”_
*25*
Not edited
Zama tayi tareda rafka tagumi cikin zullumi da rashin sanin madafar tunaninta
Abu 'daya tasani shine tana tsananin qaunar rumanah kamar itace ta haife musamman a yanxu datake hango soyayyarta mai tsanani a idanuwan Maheer 'dinta saidai duk wannan qaunar da yardar zata rushe tazama qiyayya da tsana mai tsanani idan sirrin rasuwarsu asma'u da bulama ya bayyana ga rumanah abinda bazatasoba kenan.
Qarfe goma da mintuna goma sha biyu suka farka yatashi zaune tareda tayarda ita zaune yana gyara mata gashinta daya barbaje.
Kallonsa tayi tareda sakin kasalallen murmushi
Ya shafi gefen fuskarta tareda bude baki yace,
Yaya?
Lumshe ido tayi cikin laushin murya tace,
Yayi sauki yanxu banajin ciwon kan.
Lumshe ido yayi tareda jinjina kai kafin yakalli agogo yace,
Ya salam" yana sauka daga kan gadon.
Tare suka shiga toilet din dakinta sukayi wanka Wanda yadaukesu dogon lokaci sbd tsayawa shiririta.
Koda suka fito kan cinyarsa ya zaunar da ita tana goge masa ruwan jikinsa yana kallon gashinta dake 'digo masa ruwa sbd wasan dasukai acikin bathtub yasa dole suyi wankan tsarki.
Riqo hannunta dake goge gashinsa yayi tareda Shafo gashinta har zuwa fuskarta ya zarce cikin towel dinta ya shafo cikinta dake lafe yana kallonta cikin wani irin yanayi da galabaita da zuciyarsa ke ciki.
Daqyar ya bude baki cikin wani irin taushin murya yace,
I have something precious inside