Showing 42001 words to 45000 words out of 82398 words
tasamu tayi bacci sbd ciwon kai koda gari ya waye bata fitoba saida dukkaninsu suka fice aiki tafito daqyar tasha tea takoma daki tayi zamanta ko kallonma a dakinta tayisa duk da rabin hankalinta baya ga kallon.
Daga office ma yau tare suka dawo da wuri sbd driver yaje yadauko suhailat suka biyo suka daukesa suka dawo gida tana kicin ta hango shigowarsu palo ta lafe taqi fitowa
Suhailat na maqale da hannunsa suka wuce sama tana fada masa wani zance sai murmushi yakeyi harda shafo fuskarta.
Harsuka shige bata daina kallonsu ba ta aje freshmilk dinda tazo sha takoma daki a sanyaye.
Qarfe takwas da minti ashirin suke dinner Carolina tazo kiranta inji suhailat tazo suci abinci.
Batai musuba ta miqe ta nufi qofa tafito.
Tundaga nesa take hango wani irin kallo dayakewa suhailat dataci wani irin ado cikin wata doguwar riga mara hannu black sai qyalli takeyi tana masa magana tana dariya shikuma saidai ido.
Riqo hannun suhailat yayi cikin miskilanci yace,
Hmm my wife is this Talkactive and I don't know wow..
Murmushi tayi tareda yiwa hannunsa dake riqe da nata kiss tace,
I love you maheer.
Shafa fuskarta yayi yace,
Ok time to eat.
Juyawa rumanah tayi jiki sanyaye sbd zuwanta gurin zai rage musu jin dadine kawai musamman suhailat dataga tana cikin farin ciki sosai.
Bayanta yabi da kallo a sace harta shige dakinta sbd tun fitowarta yaganta sbd dama hankalinsa na nutsuwarsa nakan qofar.
Abinci Carolina tazo ta dibarwa rumanah babu Wanda yace tasake kiranta sukaci abincinsu suka yakoma sama suhailat taje ta taya Carolina shirin baccinsu amah.
Yana kwance idanuwansa a rufe suhailat tashigo ganin kamar yayi bacci yasata komawa dakinta tayi kwanciyarta.
Tundaga ranar rumanah taqara nesanta kanta dasu sbd ganin sunfara mantawa da wanzuwarta a gidan
Dama aikinta yaqare tunda tasamu cikin da akeso.
Sati 'daya kenan basu saka juna a ido ba sbd qauracewa musu datayi har gwara suhailat tana zuwa dubata duk tadawo aiki sbd sanin lafiyarta musamman yanxu da Cikin yaqara fitowa.
Yau da wani irin ciwon kai da zazzabi ta wuni ko ruwa daqyar take iya sha sbd komai taci sai amai.
Qarfe tara suhailat tashigo dakinta dubata taganta kwance lamo tayi shiru jikinta yayi matuqar zafi.
Cikin kulawa da tausayawa tace,
Subhanallah bakida lafiya haka shine baki fadaba.
Cikin dasashiyar murya tace,
Kaina ne yake ciwo sosai.
Fita dakin suhailat tayi da sauri ta nufi dakinsa
Koda tashiga yafito wanka yana zaune sanyeda wandon bacci mai tsantsi black bai sanya rigarba yacika dakin da qamshinsa da sanyin AC yaqarawa da'di yana zaune kan kujera ya dora qafafunsa kan table yana waya da ammy.
Cikin 'yar damuwa tace,
Baby rumanah batajin dadi sosaifa tace kantane yake ciwo sosai and the condition she's in kasan ba'ason tana fama da damuwar ciwo ko yayane.
Aje wayar yayi batareda yakalletaba a miskilance yace,
Mezan mata?
Zaunawa tayi kusa dashi tareda dafasa tace,
Baby pls kadubata kasan maganin dazaka bata baza'a barta cikin halinda take cikiba wlh daga gani kuka ta yini tanayi....
Wani kallo yayi mata jin abinda tace kafin ya dauke kai yace,
Idan tabaki tausayi har haka ki kawota naga abinda zan iya yi.
Miqewa tayi tafice cikin jin dadi.
Daqyar rumanah ta tashi tabiyota tana tafiya ahankali sbd Sam har cikinta jitake yayi mata kamar ya kumbura ya danne saman cikinta.
Koda suka isa dakin rumanah sauke kanta tayi har kusa dashi suhailat takaita ta zauna
Shi ko kallon inda suke baiyiba yana duba Abu cikin laptop din dake gabansa.
Cikin kulawa suhailat tace,
Bari naje nasa carolina ta hado miki abinda zakici kafin kisha magani,ta fice.
Shiru tayi numfashinta na fita da sauri jinta kusadashi sosai
Shikuwa aikin gabansa yakeyi sai dai ganin yana neman fara shirme yasashi rufe laptop din yajuyo ya qura mata idanuwansa.
Jin kallonsa na yawo ajikinta yasata 'dagowa ahankali takallesa nan take idanuwanta suka ciko da hawayen masifaffiyar kewarsa dake cinta.
Yana kallo hawaye suka gangaro daga Cikin idanuwanta ya lumshe ido yasake budesu akanta
Hannu ya miqa mata babu musu takama tareda fadawa jikinsa tana sakin kukan datake riqewa duk kwanakin.
Rungumeta yayi tareda rufe ido yana jin nutsuwarda yarasa duk kwanakin tana dawo masa.
Qanqamesa tayi tana sake shigewa jikinsa sbd sabuwar kewarsa dake shigarta dukda tana jikinsa din.
Sun jima ahaka kafin ta dago fuska ta kallesa shima ita yake kallo tasaki murmushin cikar buri
Ya shafo fuskarta zuwa lips dinta yace,
Kukan da aka yini tanayi na ciwon gske ne kona kewar ammy ne?
Soke kanta tayi sbd sarai tagano 'dan ammy yake nufi ba ammy ba.
Murmushi yasaki sbd qin dago kanta datayi sbd kunyar zancen sbd ta tabbarda yariga yagane shine kukanta shine murmushinta.
Dago fuskarta yayi tayi saurin rufe idonta ya zura hannu cikin rigarta ahankali yashafo cikinta
Ta bude ido tana kallon fuskarsa.
Da ido yanuna mata cikin yayi kicking tanajin motsin itama musamman yanzu da hannunsa ke kan cikin saitaji qaunar cikin da maishi sun sake shigarta ta dora hannunta kan nasa dake kan cikin suka kalli juna sbd sake motsi da Cikin yayi.
Suhailat data shigo basusan tashigonba ta tsaya cak tareda kallonsu jikinta na 'dan rawa tayi saurin aje tray din tsakiyar dakin ta fice ko dakinta bata komaba dakinsu amah taje takwanta kusada fammah tareda Rungumeta ajikinta tana kiran sunayen Allah.
Basuyi tunanin suhailat zata dawoba hakama basu lurada abincinda takawoba yabata fruits din dake gabansa wainada suhailat takawo masa tuni tasha kadan yabata magani tasha tana kwance jikinsa daganan ko mintuna nawa batayiba bacci ya dauketa dama akwai na bacci sosai aciki sbd yanayinta daya nuna bata samun isashen bacci.
A jikinsa tayi bacci yazare mata doguwar rigar jikinta yazare mata bra yabarta da pant yasaka mata rigarsa ta bacci duk da ta mata mugun yawa ya kwantarda ita kan gado tareda rufeta bayan yayi kissing idanuwanta dake rufe.
Kan kujera yakoma yabude laptop dinsa yanason cigaba da aiki amma yakasa yayi crossing legs yadauki fruits 'din data rage yana sha idanuwansa nakanta ya zuba mata yana kallonta nutsuwa nasake shigarsa.
Washe gari kusan tare suka tashi hannunsa cikin nata suka shiga toilet sukayo alwala sukazo sukai sallah daganan bacci suka koma Wanda ita rabon datai irinsa ta manta shikuwa banda kallon fuskarta da cikinta babu abinda yakeyi daga baya yasake shigar da ita jikinsa ya lumshe ido bacci yadaukesa.
Qarfe bakwai suhailat tayi shirin zuwa aikinta ta fice ko breakfst bata tsayaba apple kawai taci bayansu amah sun wuce school.
Sai qarfe goma suka sauko tana gefensa sanyeda jallabiyarsa datai mata mugun yawa ta nufi dakinta da sauri sbd batason haduwa da suhailat da rigarsa ajikinta.
Shikuwa black Gucci trouser ne ajikinsa da black shirt fuskarsa sosai take bayyanarda annashuwar da zuciyarsa ya nufi dining yana waya da sultan dake sanardashi abinda ya 'daga hankalinsa na cewar sufara shiri kowane lokaci zasu iya dawowa gida sbd rumanah a mineelik zata haihu.
To kawai yace sbd kai karshen zancen dan zai iya samun matsala da sultan din idan yace aa.
Wata doguwar Turkish gown tasaka Maroon wadda tayi mata kyau matuqa musamman da cikinta yafito tayi rolling kanta ta sanyo loafers black tafito tana fidda siririn qamshin daya zama tamkar na jikinta.
Kai tsaye dining ta nufa itama tunkan taqaraso ya zuba mata ido yana kallonta musamman murmushin dake fita fuskarta dayafi 'daga masa zuciya.
Tana zuwa kusada shi ta zauna tareda duba abincin ta zuba masa Wanda tasan yanaci ta dibi chips kadan taci da mango mango juice mara sanyi ko kadan sbd tuni yasawa Carolina dokar karta kuskura kaiwa rumanah Abu mai sanyi.
Suna gamawa ta sanarda Carolina zata fita ta fice Kodataje yana cikin Mercedes-maybach exelero 'dinsa da alama shine zaiyi driving din
Taqaraso tashiga sukabar gidan.
Asibiti suka nufa,suna isa kai tsaye office dinsa suka nufa
Suna shiga ya nuna mata quryar resting room din dake cikin office din yace tashiga yana zuwa.
Shiga tayi taga harda 'dan madaidaicin gadon hutawa mai kyau a dakin sai couches da table harda TV da fridge ga split ac dake aiki
Ta zauna kan couch tareda lumshe ido tana kallon hotonsa dake cikin qaramin frame kan table.
Murmushi tasaki tareda 'daukar frame din qasan maqoshinta ta furta,
Iwe dihalhu.
Cikin kunnenta taji ance,
I heard that.
Saurin juyowa tayi tana ganinsa ta rufe idanuwanta cikeda jin kunyar kanta.
Ya riqo hannunta yana murmushi ya nufi gadon dakin da ita yana cewa,
Karki damu suhailat is kind hearted bazata hanaki mijintaba.
Murmushi tayi tana zaunawa bakin gadon sbd har lokacin bata daina jin kunyar zancentaba.
Janye rigarta yayi yafara scanning din cikinta cikin qwarewa harya gama yayi rubutun dazaiyi fuskarsa batadaina bayyanarda annurin da zuciyarsa take cikiba.
Tayarda ita zaune yayi suna fuskantar juna ahankali yace,
Babynki saura wata hudu yazo duniya yaga stubborn mom 'dinsa mai kishi da antyntah dabatasan tafita son mijintaba ba.
Kallonsa tayi da sauri jin abinda yace bayan baisan meye sirrin tata zuciyarba saidai baisan tayi masa kyakkyawan saniba dahar tagano maganarsa is like yana challenging dinta akan sonda take masa.
Murmushi tasakar masa tareda kai bakinta daidai kunnensa cikin wani irin salo ahankali ta furta,
Kanason tabbatarwane?
Wani irin murmushin jin dadin daya ratsa zuciyarsa yace,
Tabbatarwar nake buqata.
Murmushi tasaki mai qaramin sauti tareda qara 'dora bakinda kunnensa saidataja wani irin numfashin datasan zai 'daga masa hankali kafin cikin ra'da tace,
Umarni ne ko buqata?
Kasa haquri yayi saidaya ha'data da jikinsa ya shafi wuyanta yana sake sakin wani sabon qayataccen murmushin Shima qasa qasa yace,
Duka.
Tashi tayi tana 'yar qaramar dariyar data sake burgesa yariqota tadawo jikinsa cikin wani irin salo tana fadowa ta dora bakinta anasa bayan tayi qoqarin yakice kunyarta da qarfi.
Cikeda mamaki da farin ciki mai tsanani yake kallon idonta tayi saurin rufe masa ido da hannunta 'daya
Nan suka samu damar kissing juna cikeda kewar juna.
Sai rana tsaka suka koma gida har lokacin suhailat bata dawoba babu kowa sai Carolina shiyasake basu damar sakewa a dakinsa sukayi abinda sukaga dama sukayo sabon wanka suka sauko cin abinci
Ko a dining sosai yau Carolina take satar kallonsu tana mamakin irin abinda taga yana faruwa atsakaninsu.
Koda suhailat tadawo suna sama batai shishigin zuwaba tayi wanka dakinta tashiryo cikin qananan kaya marasa nauyi bata fitoba sai lokacin dinner kuma suma lokacin suka sauko
Rumanah na ganinta taji nauyinta sosai
Shiyasa ko kallon inda yakeyi bata sakeyiba ta maida hankali gurin cin abincin ta hankali kwance.
Suhailat ma bata nuna damuwar komaiba saima qoqarin ganin tasake data ringa mata.
Suna gamawa suhailat ta matso kusa dashi ta ranqwafo tai kissing hannunsa tace,
Gud night baby.
Ta juya gurin rumanah dake qoqarin barin gurin tace,
Gud night rumanah.
Cikeda kunya tace,
Allah yatashemu lafiya.
Dakinta ta nufa tabarsu suna binta da kallon girmamawa.
Da kansa yadauketa har zuwa dakinsa ya kwantar da ita ahankali kan gado batareda yace komaiba ya juya yashige toilet.
Kwananta biyu agurinsa ranar na ukun tana sane da abinda suhailat ke nufi shiyasa tun wuri tayi kwanciyarta dan ko agurin dinner tariga kowa tashi tayi musu saida safe
Shima yagane mai suke nufi shiyasa bai damuba ahaka suhailat tagama kwananta biyu saidai kuma kwanan biyu bata yisu cikin lafiya ba sbd wani irin zazzabi da ciwon kai datake fama dashi.
Tashin farko dayayi mata test cikin wata uku ya bayyana ajikinta Wanda ya basa mamaki ta yanda bai taba luraba ita kuma dama tasan da abinta kawai taga tunda bana farko bane kuma akwai wadda tafita buqatar kulawa tunda ita natane na farko shiyasa kawai tabarwa kanta.
Rungumeta yayi cikin nutsuwa yace,
Thank you suhailat.
Shafo fuskarsa tayi cikin qaunarsa tace,
Why are you thanking me?
Sbd you're always given me happiness.
Murmushi tayi tareda taba hancinsa tace,
Ka godewa Allah not me.
Ina godewa Allah koyaushe daya bani best wife datake qaunata,
Ina fatan komai na zama anan gaba zaki cigaba da sona bazaki barniba.
Hakanan taji faduwar gaba tareda tausayin kansu tace,
I promise to be with you and support you komai rintsi komai wuya koda akan abinda kakesone.
Rungumeta yayi jikinsa da zuciyarsa na shiga wasi wasin komai zaizo gaban.
Ranarda cikin rumanah yacika wata bakwai na suhailat yacika wata biyar mumman saqo ya iso daga mineelik na 'daukar rumanah da suhailat dan zuwa haihuwa.
Lokacinda yakira ammy yasanarda ita atake tafara shirin komawa mineelik 'din tsoro da fargabar data danne na dawo mata sabo.
#mamuhgee
*_TARAYYA_*
_wattpad@mamuhgee_
_Haske writers association_💡
*30*
*_ita soyayya da fahimtar juna Allah ne yake sakata acikin zukatan wainda yaso kuma babu wani shedani daya isa ya raba abinda Allah ya hada sbd shi daya hada yasan abinda yasa yahada dan haka soyayya da qaunar dake tsakanina da daughter na BILLYN ABDUL babu wani shedani ko munafukin daya isa yashiga tsakani bare yaraba_*
*_Wasu sunso hada fitinar cewa labarinmu yazo 'daya to ai dama dole labarinmu zaiyi kamanceceniya sbd ra'ayinmu 'daya shawararmu 'daya abinda yake gudana aranmu 'daya to mezai hana labaranmu kamanceceniya?_*
_*Naso dakatawa sbd wasu dalilai saidai hakan na nufin mundakata gaba 'daya daga TARAYYA har RAINA KAMA sai munafukan dake cewa 'dayane su qarasa labarin tunda dayane ai bazai musu wuyaba saidai kuma masoyi duk inda yake yafi maqiyi shiyasa muka bar komai ya wuce kuma kuji da babbar murya duk munsanku masu halayen kafiran farko*_
_*MAMUH DA BILLYN ABDUL BAZAKU TA6A GANINSU YANDA KUKESOBA*_
_*Tarayya daga yanzu har gamawarsa sadaukarwane ga daughter na BILLYN ABDUL*_💋
_*Z B I i love you guys as much*_💋
_sorry wainda ban daga wayarsuba da kuma basu reply na massage dinsu_
_naga masoya nakuma gode_🤝
Not edited.
Ammy na gama waya da maheer din jikinta yayi sanyi matuqa sbd Dama tasan hakan na zuwa sbd tun barowarsu mineelik tasan sultan yazuba tsaro sosai akansu ta yanda duk wani motsinsu arayuwarsu yana sane dashi saidai batai tunanin zai nemesu da wuri hakaba.
Shikuwa lokacinda saqon ya Isar masa yana hospital kallo 'daya yayiwa abaas dameer aqeel da sultan ya Aiko takanas daga mineelik din ya dauke kai tareda 'daga masa kai alamar yaji yabasa guri,
Rufe ido yayi tareda jan 6oyayyan numfashi.
Da wuri yadawo gidan koda yashigo rumanah ce kawai a gidan tana dakinta kwance tana bacci sbd kwanakin Sam bata cika lafiya ba sbd girma da nauyin cikinta.
harya taka steps biyu na zuwa dakinsa ya tsaya cak tareda juyowa yakalli qofar bedroom dinta,
Yau gaba 'daya baiganta ba sbd suhailat ce keda kwanan kuma tunda safe yafito shiyasa gabaki daya yau ya rasa gane kansa ga qarin saqon sultan daya riskesa.
Juyowa yayi yadawo ya nufi dakinta batareda yayi knocking ba yashiga tareda turo qofar.
Kallonta yayi yanda ta tayi kwanciyar tana dafe da cikinta da alama hannunta nakan cikin tayi baccin.
Sanyin ac dayayiwa dakin yawa yakalla tareda qarasawa yadauki remote yarage ac din.
Bakin gadon yazauna tareda zuba mata ido tsawon lokaci ya lumshe ido yabude ahankali yanajin wani irin yanayi mai zafi game da ita.
Riqo hannunta yayi ya matse cikin nasa ya rufe ido yana qoqarin yakice fargabar datake shigarsa akanta,.
Ahankali ta bude idanuwanta ta zuba a fuskarsa tana masa kallon mamaki sbd baitaba shigowa dakinba a iya sanintama baya shiga dakunansu.
Qoqarin tashi tafarayi ya mayar da ita tareda girgiza mata kai ahankali still yana kallonta.
Mamakine yasake kamata ganin yanda yake kallonta cikin wani yanayi.,
Ahankali ta furta,
Dehina neh?(are you ok?)
Lumshe ido yayi tareda 'daga mata kai.
Cikeda wani sabon mamakin takallesa sbd ganin ya amsa mata ba kamar yanda yasaba zuba maka ido ko shareka idan ka tambayesaba.
Kasa 6oye mamakinta tayi hakan yasashi sakin Murmushi yana sake damqe hannunta dake cikin nasa murya a shaqe yace,
Kinshirya ganin ammynki?
Saidata kalli cikin idonsa tasaki murmushin kwanciyar hankali ta daga kai.
kinason komawa mineelik?
Ba zato taji tambayar takallesa gabanta na faduwa takasa cewa komai.
Kwantawa yayi jikinta zuciyarsa na qara shiga wasi wasin kaita haihuwa mineelik.
Kallon fuskarsa tayi taga idanuwansa a rufe tasan baya buqatar hayaniya alokacin
Sai kawai tayi shiru tareda lumshe nata idanunwan tareda sake riqe hannunsa dake cikin nata itama.
Sun jima ahaka har bacci yadaukesa itadai kasa baccin tayi ta zuba masa ido hankalinta yaqi kwanciya Sam da yanayin data lura yanaciki.
Maida tunaninta ga maganarsa ta zuwa mineelik dayace tayi taji gabanta yayi mugun faduwa,
Tabbas tasan zata koma mineelik haihuwa saidai duk lokacinda ta tuno hakan hankalinta na matuqar tashi sbd jikinta na bata idan takoma shikenan ta rasa maheer,
Maheer yazamo wani babban 6angare na rayuwarta,
Yazamo zuciyarta datakejin bazata iya rayuwa babusaba,
Shine uban abinda zata Haifa saidai tanajin kamar tafison kasancewa da maheer din akan abinda zata Haifa dan idan ta tuno abinda ke cikinta mineelik da zagayenta suke jira ta haifo aga ko menene ke qara bata tsoro da daga mata hankali.
Baccin baiwani dadeba ya farka kansa na 'dan ciwo ya kalleta da sauran bacci a idanuwansa yace,
Ki daukomin kaya zanyi wanka anan.
Saukowa gadon tayi ta nufi qofa yabita da kallon tausayinta da qaunarta mai qarfi sbd ganin girman cikinta cikin laushin murya qasa qasa yace,
Hey.
Tsayawa tayi tareda juyowa ya tashi zaune tareda lumshe ido ya miqa mata hannu ahankali.
Jitayi zuciyrta tasake sanyi ta dawo ahankali ta kama hannunsa ta zauna gefensa sukayi shiru dukkansu sai can yasaki ajiyar zuciya ahankali yana dago da fuskarta suka kalli juna ya shago cikinta cikin wani irin yanayi yace,
Allah ya albarkaci zuriata.
Dora hannunta tayi kan nasa cikin sanyin murya ta furta amin.
Tashi yayi yakama hannunta cikin kulawa suka nufi toilet yayi wanka yayo mata,
Sosai yake cikin wani irin tunanin yanda zaiyi nisa da ita idan suka koma mineelik sbd har cikin zuciyarsa yakejin duk wani laulayin cikin datake ciki.
Suna fitowa da kansa ya bude wardrobe ya dauko mata doguwar rigar chiffon mara nauyi yasaka mata,tasaki murmushi tana kallonsa ta madubi yanda yake gyara kansa.
Tsayawa yayi yana kallon Murmushinta qasa qasa yace,
I'm all yours zaki iyayin abinda yafi kallonma.
Zaro ido tayi cikin wata muguwar kunya ta miqe da sauri zata bar gurin yadawo da ita tareda Rungumeta ta baya jikinsa da babu kaya ya hadu da bayanta da kusan rabi yake abude sbd yanayin rigar.
Shinshina gashinta yayi tareda lumshe ido yana sake matseta jikinsa sbd tuni tasakar masa da sabuwar kasala bakinsa yakai kunnenta cikin kasala yace,
Meyasa zakiji kunya bayan kinsan yes you have all the rights kiyi abinda yafi kallon.
Qanqamesa tayi cikin wata sabuwar kunyar tace,
Please kabari.
Ba musu yayi shiru yana murmushi tareda mayarda hannunsa kan cikinta ya lumshe ido ya bude,
Allah ne kawai yasan irin son dayakewa cikin jikinta sbd ganinta daukeda cikinsa ke sakar masa nutsuwa da wani irin farin ciki sbd ganin ita 'din dai tasace mallakarsa,gonarsa,hurumsa da babu Wanda ya isa tunkarowa duk fadin duniya,
Gonarsa da babu Wanda ya isa yayiwa kallo biyu batareda yasa anraba kansa da gangar jikinsaba,
Allah ya 'dora masa son amah fiyeda dukkanin sauran 'yayansa da abinda ya mallaka kuma bayajin zai samu wani 'da ko 'yar dazaiso kamar amah 'dinsa sbd tsananin soyayyar yarinyar ajinansa take tun ranarda aka haifi har zuwa yanzu,
Abinda ke cikin